ZAYN MALIK

Chapter -14

by @maidambu41

Chapter -14

Idan zai kwana yana Iskanci da ita abu daya take rokon shi kar ya tab'a mata mutuncin ta, haka ba karamin bashi haushi yake ba, shi yasa idan ya fara kokarin yin haka take hana shi ta hanyar tuna mishi da haka, Imaden ya fito babban gidan sarautar Edo ne, kuma iyayen shi manyan mutane ne,, kuma wani abin da ake yawan fada shi zai zama next king a cikin masarautar Edo shi yasa ya dauki rashin arziki ya sakawa kan shi kakan shi yana masifar kaunar shi, dan da bakin shi yake fada Imaden ne sarki na gaba.


Rashin mutuncin da yakewa Titih ta biyo bayan lokacin da ta bar Nigeria ta dawo Denmark shi kuma yazo ganin ta anan yaga Aina'u dama tun kafin ta zo Kakan ta Ademola Ades ya gaya mata tayi a hankali da mutanen da suke tare dan ba dukkan su, suke kaunar ta ba dan haka ta kiyayye fadar samun ta da faduwar ta, haka yasa bata gayawa Aina'u haduwar su da Imaden ba, sai ranar da ya zo.


  Tunda suka hadu Aina'u take kara fahimtar ai ita baki daya rako mata tayi duniya domin kuwa, duk wani mijin kera sa'a yana wurin Titih duk wani cigaba da samu da zata yi toh kafin tayi tunanin haka Titi ta rigata, dan haka ta shiga rigar mutunci, da kamewa tana nuna mishi, wannan dalilin yasa shi fara tsanar alakar shi da Titih ga duka a ko ina marinta yake, ko haushi ta bashi zai dake ta a ko ina, har a makarantar su bai d'aga mata kafa, ganin haka yasa mata masifar tsoron shi, kuma kamar wanda ya asirce ta duk abinda zai mata bata fushi bata gayawa yan uwanta, hatta mahaifiyar ta bata taɓa yiwa zancen ba, sai Aina'u. Shi kuma baki daya yana mata haka ne sakamakon soyayyar da ya fada na Aina'u, domin yana hango ita ta dace da rayuwar shi. A wani zuwan Titih Nigeria yin wani workshop ya kai ta cikin gidan su, anan aka gaya mata duk lalacewar da zata yi ta tsare mutuncin ta, domin idan ta sake wani abu ya faru da budurcin ta, toh ta kwana da sanin cewa ba zata tab'a samun kima da daraja ba, a cikin gidan baki daya kuma zai tab'a kowa na gidan da yake da alaka da Imaden. Hatta mahaifiyar shi.

Wannan dalilin zai iya janyowa ta daina fita cikin Masarautar da kome na cikin gidan sarautar.

Da wannan kashedin Allahya kuma cusa mata tsoron kare mutuncin ta, tare da tsayawa iya inda taga zata iya rage karfin sha'awar ta.


Sabida tsoro da tashin hankali, ko irin party nan na kawaye bata zuwa, tana rayuwar ta a karamin yanayi da ta zab'awa kanta.

Dake shakara uku ne har da wani project da zata yi yanzu haka ta samu shekara biyu da wata biyar, tana komawa gida sai bikin su. Sannan duk wani motsin ta, akan idanun Imaden yake, domin ya zame mata kamar bakar inuwa, tana wani motsi zai gaya mata abinda take yi, shi yasa kome nata da take yi takatsantsan take sabida mutuncin ta, maganar gaskiya ita kanta bata san wani irin jarabawa take ciki ba, wannan halin yasa matukar ba zama zaka yi da ita ba dogon lokaci ba, ba zaka tab'a sanin halin da take ciki ba, haka kuma ta bangaren Aina'u itama tana iya takunta, har ma tafi Titilopemi wayo akan halin ta, sannan yadda take kokarin lallai kota halin k'ak'a sai ta bayyana mugun halin da Titih, kuma burin ta kenan, shi yasa take makale da ita kuma kar kuyi mamakin haka, domin a duniya bata da abokiyar sirri sama da ita.

Wannan kenan.

**

KADUNA

Yau tun safe take raba idanun tana son ganin ta ina zai bulo amma shiru kake ji, har kusan la'asar bata gan shi ba, dan haka ta yanke shawarar zata fita niman shi, kasancewar wani lokaci idan rana yayi zafi tana saka Medical glass haka ta lalubo abin ta , ta saka sannan ta fito waje.

Kallon harabar gidan tayi bata hango motar shi ba, dan haka ta nufi dakin part din shi ta fara bugawa, babu alamar shi sai Muhideen ne da zai wuce ya tsaya.

"Hajiya Umma ba dai shanshani kike nima ba?" Duk da Zayn din take nima amma bata ji dadin yadda ya kira shi shanshani ba dan haka tayi banza da shi. Amma kiris take jira ta surfa mishi bala'i.

"Zainu kana ina?"

"Hajiya umma baya nan fa?"

"Dan banza munafiki mara mutunci, wato ga sakarai nazo ina magana bari ka min maganar banza, toh kayiwa Uwarka." Daga haka ta wuce cikin tsokala ya ce mata.

"Allah ya baki hakuri Hajjos " tsaki tayi tana me gyara zaman zanin ta, a hanyar komawa part dinta suka hadu da Uncle Bashir.

"Auta ina ka ga Zainu?"

"Hajiya ya tafi Abuja" wani shekeke ta kalli Uncle Bashir. Kafin ta watsa mishi harara.

"Ban da salon munafunci taya za ayi Zainu ya bar garin nan bai gaya min ba, indai ba shiga tsakanin mu kuka yi ba?"

Kamar ya fasa ihu ya kalle ta, sannan ya ce mata.

"Hajiya ke kika ce ya koma aikin shi ko? Toh nan ya koma dan haka babu wanda ya isa shiga tsakanin ku"

Shiru tayi tana kallon shi, kafin ta ce mishi.

"Allah ya dawo da shi lafiya" ta fada tare da wucewa dakin ta.

Shima wurin motar shi ya wuce da sauri dan yasan halin Hajiya yanzu zata kuma kawo wani rigima, ai kuwa tana tadda motar tana lekowa, kafin tayi wani yunkuri yayi hon ta bar gidan, Hajiya zuciya ya sauke lokacin da ya bar gidan kiran Zayn yana shigo mishi.

"Son ya kake?"

"I dey fine ya Granny?" Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce mishi.

"Hmm sai kai zaka iya mata ayi magana ta ce maka ai an shiga tsakanin ku"

"Hm"Zayn ya fada yana sake murmushin gefen baki.

"I love Hajjos"

"Toh Malam kar a manta Uwata ce da ake cewa ana Love dinta"

"Auta yaushe ka koyi mugun hali ko?"

B'ata rai uncle Bashir yayi sannan ya ce mishi.

"Koda wasa bana son rashin kunya, yau babu Uncle bashir sai auta itama Hajiya babu yadda na iya da ita ne, dan haka kar na kuma jin haka"

"Toh masu shiga tsakanin masoya" daga haka suka shiga tattaunawa kafin suka ajiye wayar.

Bayan fitar Uncle bashir ba kuwa cikin gida Hajiya ta nufa tun a bakin kofar take kwalawa Mama kira.

"Talatu!" Fitowa Mama tayi tana amsawa.

"Na'am Hajiya"

"Hmmm maza kira min Zainu naji ko ya ci abinci, dan nasan kaɗan da aikin shi yaki cin abincin."

"Toh Hajiya "

"Tabawa shiga ki miko min wayata " Mama ta fada mata, da sauri ra shiga ta dauko mata.

"Gashi Maman Uban ɗakina"

"Allah yasa ya kai zuci dan nasan halin wasu mutanen al'amarin su bai kai zuci ba"

"Kai Hajiya har zuciyata nake kaunar Zainun ki "

"Ai nasani" ta fada tana kallon Maman Zainu.

Bugu biyu ya shiga, yana dauka ta ce mishi.

"Ga Hajiya nason magana da kai"

"Talatu yana ga kina wani shashake murya kamar kina bakin ciki da wayar da zamu yi da jikana"

Ware idanu tayi akan Hajiya kafin ta ce mata.

"Kiyi hakuri ba haka bane gashi" amsa tayi tare da cewa.

"Zainu Allah ta maka albarka kaf gidan nan bamu da masoya a cikin makiya muke gaba da baya dan haka ka kula da harkokin ka, karka kula kowa ita Uwarka da ta zame maka dole sai ku gaisa, sannan karka kuma tafiya baka gaya min ba, ko ba kome ai zan saka maka albarka karka kuma min haka hankalina ya tashi "

"Toh Hajiya, amma dole wata rana za a dawo miki da gawa na, duk yadda kika so da ganin kin tsare lafiya ta da rayuwata dole wata rana zaki ji labarin bani nan, fatana na idan kika ji bana nan karki shiga damuwa."


"Zainu me yasa kake gaya min haka? Ko dan na damu da kai ne? Ka daina fadar haka insha Allah ba zan tab'a rufe ka ba, sai burina ya cika akan ka, ina ta addu'a Allah ya bani nisan kwana domin nagan ka cikin farin ciki shine kake kira min mutuwa Zainu anya asirin da nake zargin an yi maka bai fara kama ka ba, dan haka kama dawowa dole a sauke maka Alkur'ani domin na fara hango haka kamar shi yake damun ka."

Murmushi yayi mata sannan ya shiga rarrashin ta. Kafin suka gama wayar dakyar.

Bayan sun gama wayar kamar wacce aka mata duka, jikin ta babu kwari ta koma wurin ta, tana shiga falon ta zauna shiru tana kallon gefe guda kafin ta fashe da kuka, sosai kamar ba ita ba, domin kukan ba wai na damuwar Zainun ta bane a'a kukan na daban ne daga kasar zuciyar ta take, sai da tayi me isarta dan sai da kanta ya fara sara mata, sannan ta kwanta.

**

Kwanan shi biyu a garin Abuja, sannan ya dawo a matukar gajiye, tunda ya dawo ta shige dakin shi, ya kwanta bai fito ba sai bayan sallah isha. Wurin Hajiya Umma ya wuce. Tana tsaka da shan kunun gyadan da aka dama mata, domin azumi tayi yau kuma dukkannshi akan Zainu tayi shi.

Sanye yake da jalabiya ash colour me sheki, zama yayi yana murmushi. Tura mishi flask din kunun tayi, tare da wani warme na kosai da aka mata, dauka yayi ya zuba yana faɗin.

"Yau ba Alhamis ba, ba Litinin ba amma kina azumi da fatan ba azumin nisan kwana kike min ba" murmushi tayi tana kara kallon shi cikin wani irin tsaftattacen kauna, wanda take jin sji daga Indallahi ba daga mutum ba, bata jin a ranta dan kasancewar shi jikanta take mishi wannan kaunar , a'a kaunar shi halittace ne daga bottom of heart dinta, duk Yaran gidan bata jin tana wani yaro kaunar da takewa Zayn.

A hankali ya d'ago kai, sakamakon jin idanun ta a kan shi. Kamar yadda yayi tsammanin haka ya samu. Murmushi yayi mata, itama murmushin ta mai da mishi, hawayen da take dannewa ne ya sauko daga idanun ta.

"Hajiya ba gani ba!" Ya fada cikin tsannanin damuwa, tare da ajiye kofin yana kallon yadda take shashekar kuka. Rabon shi da yaga Hajiya a wannan halin tun bayan wani kama shi da yan sanda suka yi, domin a ranar ya fara ganin boyayyen kaunar da take mishi, a ranar ta fitar da kaunar shi da take boyewa, domin bata taɓa zungurin shi ba, sau gashi ita da kan shi ta mare shi, kuma ta ce shine bai da gaskiya, koda aka tafi da shi, ita kuma ta fita ta karbo shi, a ranar ya gane ita Hajiya ba iya so bane al'amarin ta, kauna ce ta jini da jini. Domin kasa shiga mota tayi ta riko hannun shi, suna tafiya tana fada tana gayawa mutane abinda yayi mata, da ta gashi a gaban jama'a ta rufe shi da duka , sannan ta fashe da kuka. Tana kuma rungume shi.

Shi kan shi zai iya cewa a ranar da girman shi yayi kuka,domin yadda Hajiya take kuka sai yake ji kamar mahaifiyar shi ce take kuka a gaban shi. Har suka isa gida da kanta ta haɗa mishi ruwan wanka sannan ta saka shi a gaba ya tafi yayi wanka , yana fitowa ta zauna tana faɗin.

"Zainun kai din wani abu ne da Ubangiji ya boye al'amarin shi, kai kyauta ne daga Rabbil Alamina, karka kuma haka ka ji. Domin zuciyata zata iya bugawa don Allah."

Da wannan maganar yake rike da shi tun kankantar shi har girman shi. Hajiya bata iya rintsawa sai ta ga yayi barci.

Riko hannun ta yayi yana faɗin.

"Hajiya kiyi hakuri ba zan kuma maganar da nayi nan don Allah kiyi hakuri"

"Allah ya maka albarka ya jibanci alamarin ka. Zainu karka kuma fada min haka ni idan na mutu lokacina ne yayi kai kuma fa? Duk da lokacin ka ne amma akwai saka rai dayawa a kan ka don Allah kar ka kuma"

"Insha Allah "

*_ZAYN MALIK NA KUDI NE 300₦_*