Chapter-15
by @maidambu41
CHAPTER-15
Tausayi da soyayyar ta gaskiya ne a gare shi, baya jin bayan mahaifiyar shi zai kuma samun Macen da taso shi bil hakki, kuma take ririta al'amarin shi sama da hajiya, iya soyayyar ta a gare shi gaskiya ne babu algus. Shi yasa yake tsaye a gefen ta ko a bayan ta domin hanata kuka.
Suna zaune Uncle bashir ya shigo da sallama.
"Assalamu alaikum Jama'a ya kuka shi shiru kamar an muku wani abu?" Ya tambaye su, yana gyara zaman shi a kujeran.
"Shima shirun ba za'a bar mutum yayi cikin kwanciyar hankali ba, Auta yaushe ka koyi tsegumi?" Ta tambaye shi tana watsa mishi harara.
"Allah ya huci zuciyar ki, kai kuma ga passport din ku kai da Abul tafiya ranar Laraba ne zuwa, hajiya sai da safe"
Tunda ya mika mishi passport din shi, ya lura da yadda Hajiya tayi shiru, kafin ta ce musu.
"Me kuke bukata ayi muku kafin ranar tunda yau dai Juma'a ce"
Murmushi Uncle Bashir yayi sannan ya ce mata.
"Hajiya duk abinda kika mana, muna so "
"Toh Allah ya nuna mana ranar " gyara zama Zayn yayi yana me kara narke mata kamar yaro dan yaye, a shagwab'e ya ce mata.
"Hajiya na, yana ga baki farin ciki da tafyya ta?"
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
"Kaci gidan ku, waye ya gaya maka bana murna? Babu wanda ya kai ni murnar tafiyar ka, Allah ya maka albarka , kai dai ka zama me yawan taimakon bayin Allah, Zayn nasan zaka iya karka zama me tsannantawa, domin Allah yana tare da masu sassautawa, kayi amfani da halin ka karfin ka domin taimakawa wanda yake niman taimako, Allah yana sane da al'amarin ka, shi kuma zai baka taimako ta fuskar da baka zata ba."
"Insha Allah Hajiya, amma ni dai ba zan zamewa Jama'ar gari kyandir ba, haka kawai na kare rayuwata domin yiwa wasu."
"Allah ya shirya ka" ta fada mishi, tana dariya. Sam yaki tafiya har baban shi ya shigo ya same su,aka shiga hira da shi, kallon Zayn yayi da ya mike yana faɗin.
"Hajiya sai da safe, Abba sai da safe"
"Allah ya kai mu, amma ai ba wurin ka zaka kwana ba a nan ne ko"
"Eh Hajiya a nan zan kwana" ya hura sama abin shi.
"Hajiya ban san me yasa nake da wasi-wasi akan Zayn ba? Hajiya Samir da abokan shi sun yi Safaran miyagun kwayoyi zuwa kasar nan, domin kar sunan su ya fito a Kore su a aiki sai suka saka shi cikin maganar su, wallahi yanzu haka saboda shi an fasa koran su a aiki"
Murmusa mishi tayi sannan ta ce mishi.
"Allah ya mishi albarka, tunda ya fitar da dan uwan shi a cikin damuwa" sam taki yarda yayi magana akan abinda Zayn yayi, sai da zai tashi ta ce mishi.
"Ina fatan haka ya sa ka gane shi din Alkhairi ne ba sharri ba"
Gyada mata yayi yana mata sai da safe.
Hannu Hajiya ta d'aga sama tana addu'oi kuma dukkan akan Allah ya kare mata Zainun ta,
Washi gari da su Uncle bashir suka zo karyawa bangaren ta, yanko musu kudi tayi tace zata yi abu da shi. Ba musu suka mike bayan sun karya , kowa ya koma bangaren shi ya kawo mata dubu ashirin ashirin, anan ta fara lissafin kayan tsarabar da zata yiwa Zainu.
"Hajiya Zaunu yaro ne da duk inda zai tafi sai anyi mishi tsaraba?"
Dama tana lissafin kudin ne, jin haka yasa ta d'ago kanta.
"Kawai kace min na dawo maka da kudin ka mana, ba ka saka ni a gaba kana titsiye ni kamar an kama ni da laifin kisan kai ba"
"Allah ya baki hakuri, zan fita "
"Amin idan kaya ne nad'e gammo ka dauka, mutanen duniya sun b'aci da mugun saka ido, Allah ya tsare ya dawo da ku lafiya, sam ban san lokacin da Auta ka lalace da saka idanu wa mutane ba. Sabo da sakawa masu laifi ido, shine bari a saka mutanen kirki idanu."
"Allah ya huci zuciyar ki Hajiya," ya fita , Baba Uwaisu da Alhaji AbdulMalik kowa fita tayi cikin sauri domin sun san hajiya bata bar autar ta ba, ɓalle su dan haka tayi musu sallama.
Nan haka hautsina gidan da lissafin abinda za ayi na tafiyar Zainu, domin ta fahimci gidan babu me shirin yi mishi, abin magana take nima kuma suma surukan babu wanda ya kulata asalima sai kokarin kauce mata suke.
Kwana biyu daga Zayn har Abul basu zaman gida, sabida akwai wani aikin da Chief of army staff zai yi kaduna, dan haka kusan a tare suke shiga barrack su fito, ranar talata da yammacin ya iso gidan su Zayn inda Abban Zayn da Alhaji Yusuf me goro,Wato Baban Abul suka karɓe shi. A hankali ya fito daga motar shi kiran Mercedes AMG, wanda aka saka tutar Nigeria a gaban shi, tare da tutar Army, daga can sama Zayn ya hango tutar Army din kamar zai karye, sake link din da yake kokarin sakawa a hannun rigar shi yayi, da gudu ya fito dake ya bar Abul a falo. Ganin yadda ya yanko a guje, shima ya bishi da gudu, har yana hada step bibiyu, su kuma suna tsaye ana gaisawa, kafin su shiga cikin gidan, yadda Zayn din ya fito da gudu saura kadan suma su kara a guje, yana isa wurin motar. Ya durkusa a gaban tutar, sannan ya saka hannun shi ya d'agowa yayi yana murmushin jin dadi da tutar bata karye ba, ya gyara ta sannan ya mike ya tsaya kafin ya sara mata, yana jin wani irin karsashi a ran shi, idan ya ga tutar soja, jikin shi yake rayuwar shi da kome he belong to soja, shi yasa yake kara jin wani irin kaunar kakin soja.
Murmushi Chief of army staff, AbdulMalik AY yayi yana cewa.
"Wato ban san dalilin Zayn Malik kin soja ba, amma har yau hidimar shi ga hukumar soja ba sabo ba ne. " Juyawa yayi cikin tsanannin kunyar Chief of army staff ya ce mishi.
"Abba ya hanya?"
"Alhamdulillahi zuwan ka nayi ba zuwan SG ba" kallon shi yayi kafin ya ce mishi.
"Ok Abba muje can part din" ba musu suka wuce Abban AY yana gaba shi yana baya har part din Zayn din suka shiga, sannan suka wuce wani daki can a cikin gidan, ya bude kofar suka shiga.
"Bravo Son amma ka bani mamaki" ya fada yana kallon yadda dakin yake saklae da kome, na computer.
Zama yayi, bayan ya bashi wani kujera.
A hankali ya mika mishi ruwa.
"Am sorry Abba kasan gwauro ne Danka bai ajiye kome daga ruwa sai Juice."
"Ba bukatar Juice ina kiyayye zak'i sabida lafiyata, kuma ina da mata uku cif, dan haka bana shan zak'i ."
Gyada kai yayi sannan ya ce mishi.
"Akan maganar da muka yi last two weeks ago, na kuma dawowa ne, lokacin muna tare da wasu mutane ne, yasa ba gaya maka haka sannan ga wannan ka duba. da nayi tunanin Sweden ne, sai kuma aka samu ba a nan bane, amma dole zaka fimu fahimtar haka "
Shiru yayi kafin ya samu zarafin magana Abba AY ya cire mishi wani driven. Ya ajiye mishi a ranar da na samu wannan sakon a ranar aka kashe mana mutane goma sha daya. Dashi nan ka duba bayanai ne na mutane daban-daban, Zayn i trust you, shi yasa na kawo wannan sakon wurin ka, please"
Zama yayi a gaban Abba AY wato Chief of army staff, sannan ya ce mishi.
"Ba sai ka roke ni ba, aiki ne akan kasata ba akan kome ba, nima na samu labarin haka tun wata shida baya sai dai kasancewar bana hukumar yasa na bar abin."
Mikewa Abba AY, shima ya mike suka sarawa juna.
"Allah ya maka jagora"
"Amin" sannan suka nufi hanyar waje, kallon kakin sojar Zayn yayi an sakata a cikin show glass, murmushi yayi.
"Uniform din ne a show glass?" Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Eh sabida kura ne"
Tsayawa yayi kadan sannan ya ce mishi.
"Ya batun Iyali?" Sosa kai yayi sannan ya ce mishi.
"Hmm! Aikina ba zai bar ni na ajiye iyali ba, idan na ajiye ta ma ba zan iya sauke hakkin auren mu ba, karshe soyayyar da aka gina ta rushe shi yasa na zabi zaman haka yafi min kwanciyar hankali"
Juyawa yayi yana kallon shi, kafin ya ce mishi.
"AZ Malami bai gaya maka bamu cika shekaru ashirin ba aka aura mana mata bane? Dan haka ka tabbatar ja dawo min da matar da zaka aura idan ba haka ba, wallahi zan nima maka duk wacce ta dace da kai"
"Ba dai auren dole zaku min ba?" Ya fada yana yar dariya,
"Tuzuru irin ka ai ya dace da auren dole, domin kafi karfin yarinya yar sha takwas sai dai yar ashirin da dauriya "
"Abba ba dai guzuma zaku aura min ba?"
"Sai dai uwar mata bazawara " dif ya dauke wuta kamar baya dakin shi kan shi Abba AY sai da yayi dariyar Zayn yadda yayi shiru kamar ba shi ba.
"Baka son bazawara ne?"
"Hmm" kawai ya ce suka fito har waje sannan ya raka shi dakin Abban shi, suka baje aka shiga hira shi kan wucewa wurin Hajiya yayi suka shiga hiran su, wanda rabin shi faɗa take da Abul.
"Hajiya ba dai halin yan Nigeria zaki min ba? Ni da nake baki labarin arziki zuwan wannan basamuden zaki juya min baya"
"An juya maka baya ina ce yana shigowa ka hau zagina da Yaren nasara, kai ba dai ina kai zuciya nesa ba ai ba zan tab'a barin Zayn yayi abota da kai ba, ban da Gulma me ka iya?"
"Hajiya yau ni ne magulmaci? Lallai kuwa zan dauki mataki akan Zainu ba zamu tafi wata ƙasa ba, sai na saka yan matan kasar sun mishi rashin mutunci "
"Ikon Allah! Toh kai baka son wasa bane? Zainu ina ce da wasa nake mishi? Kaga yaro da ɗaukar zafi toh la'ilafi"
"Hajiya ni Yaro ne da Abul zai min abu na kyale shi? Ba sai inda karfina ya kare ba" Murmushin jin dadi tayi sannan tace mishi.
"Atoh dai gaya mishi naga sai wani zakewa kake nan kuwa ba wani abin da zaka iya da rantalelen kan shi a wurin "
"Assalamu alaikum!" Suka yi sallama baki dayan .
Mikewa Zayn da Abul suka yi suna amsa sallamar.
"Waalaikumun Salam, Barka ku da zuwa "
"Wa nake gani haka kamar AbdulMaliku"
Cire hular shi yayi na soja, ya isa gaban ta, yana murmushi.
"Hajiya ni ne?"
"Ikon Allah, rabon ka da Kaduna na manta sai shekarun baya kafin haihuwar gudumurki AbdulMalik ya gaya min kun hadu a can wata ƙasa har yake ce min ka kara aure" shiru yayi kafin ya dafe goshin sa, yana jin kan shi na sarawa.
"Lafiya Abba?" Zayn ya tambaye shi. Giftawar abu ya gani a idanun shi, cikin dauriya ya ce musu.
"Lafiya lau, Eh haka ne wani zuwa na Semina da yarinyar da aka aura min, muka hadu a south African."
"Ayya da fatan tana lafiya" kamar wanda aka tsikara mishi allura ya mike, zai fita .
"Ba dai zaka tafi ba"
Jiri ne ya kwashe shi a wurin, kafin ya fadi kasa, Zayn ya tare shi, a rude aka fitar da shi zuwa asibitin sojojin da yake barrack me suna 44, nan aka shiga duba shi.. baki daya sun shiga damuwa sosai