DANGINMU NE SILA

Nidai ina bukatar saki a wajen mijina saboda bakin halin DANGINMU...Page 005

by @jameey123

_*DANGINMU NE SILAR KOMAI*_


    Na


JAMEEY❣️


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC.*


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM.*_

____________________


   _Free Page 5_


_Follow me in my acct AREWABOOK dan samun sabon update cikin lokaci https://arewabooks.com/book?id=62c8312350d01a38ea3bec0f username Jameey123.


Domin magana da writer kai tsaye danna wannan blue link din👇🏻

_***


_Payment is on going hanzarta ki mallaki naki yar uwata kada ayi babu ke it's 500 via 0777512438 Acces Bank Jamila Abubakar Bello and show ur evidence through this number ***._ 

______________

"Ni zaka faɗama haka?dan Momy ta ɗauko ka amatsayin lawyer na sai akace maka ni bansan right dina ba?kaga Barrister ka fita a idona tun muna shaidar juna akan Nazma ba abinda bazan iya ba ka saurareni da kunnen basira inda akana dasu ni bazan taɓa sakin matata ba,undersatand?malam fitar office ina aiki kada karka ɓata man rai a banza a wofi,kuma ina gargaɗarka kayi gaggawar fita harkar DANGINMU! tafi karfin duk tunanin ka,kasa ido kawai ko mu dake da madafan iko munsa ido bare kai ɗan karere,idan kuɗi kake so zan baka ko nawa ina so ka bijerama umurnin Mahaifiyata."Girgiza kai Barrister yayi yana nazarin Nizam dan ko shakka babu Hajia Zaituna zatayi artaba da ɗan nata kafin ya saki matar shi dan ga tsantar son da yake mata atattare dashi."Kai ko wane kalar mutun ne Nizam?mi zai hana bazakayi kishin mahaifiyar kaba?Kasani amatsayina na Lawyern ka nai maka alkawali bazaka rabu da matar kaba haɗin kanka kawai nike bukata kuma ka ɗauke ni a matsayin lawyern ka kamar yanda mahaifiyar ka ta buƙata."Wannan karon wani irin matsiyacin kallo ya watsa mashi gani yake ya bala'in raina mashi wayo da tunani cikin tsanan bacin rai ya nuna mashi kofa."Get out of my office."Haba Doctor Nizam ka jira kaji me zance maka mana."Sake nuna ma Barr Nakowa kofar fita yayi,ba karamin kulewa Nizam yai ba kuma ya fahimci duk abin da kannen shi kema Nazim tabbas Momy ta sani kuma ita ke saso tunda gashi har ta shiga cikin case dinsu saɓanin Ummi dake alkunya bata cewa komai"Doctor Nizam kayi shiru kace wani abu mana pls."kallan shi kawai yayi ya kauda kai."Yanzun mi kake bukata wajena."? kafe shi da ido Barister yayi batareda ya kuma cewa komai ba,wani kululun bakin ciki ne ya tokare Nizam cikeda kosawa yace."Dakai nike magana zaka kafeni da kallo kamar wani mai laifi idan baka buƙatar komai ka fitarmin office inada aiki a gaba na."yanayin inƙina daya zoma Barister cikim kankanin lokaci yace."Aaa doctor ba haka bane inada abin cewa mana ina bukatar kabani taƙaitaccen tarihin ka dana matar ka dan insan ta inda zan kama kafin next week mu koma Kotu."Wani irin takaici ne ya kama Nizam take."Ina kaunar matata kuma ina son ta,kuma inaji a raina da sonta zanyi numfashi na,na karshe wannan shine takai taccen tarihina.Hope hakan ya gamsar dakai ko."?gyaɗa kai Barrister yayi."zaka iya tafiya."

   Tunda Barister Nafi'u ya fahimci Nizam bazai bashi haɗin kai ba jiki sanyaye ya mike yaima Nizam sallama ya tafi cikeda da takaici.Yana fita Nizam ya mike yana kaima bango duka da karfi banda zafi ba abinda zuciyar shi ke mashi a lokacin"Why Momy? mike damunki ne?miyasa dangin mu zasu saka ido akan matata?me suke shirin yi!Da sauri ya dafe kanshi dakeji yai mashi nauyi kamar zai bare gida biyu yace"tabbas idan har Momy zata dinga yiman haka ta ɗauko tubbar lalacewar rayuwar ɗanta da kanta zata kashe ni Momy kada kimin haka."haka yaketa surutai kamar yana gabanta yanda ya koma abin tausayi.Bai aune ba yaji ana rafka uban tafi cikin office din shi."Lallai Ya Nizam nayi mamakin jin waɗannan kalaman a cikin bakinka! saime danka rabu da Nazima mene a ciki?insa wannan wawiyar yarinyar daka nace mawa bata fimu da komai ba,idan ka rabu da ita,saika sake auren wata a cikin mu koya ka gani."cewar Fadila da tayi nisa cikin kogin kaunar Nizam,ɗiyar kanwar momy ce wadda suke ciki ɗaya a hankali takaraso gaban table taja sit ta zauna ta harɗe kafa ɗaya bisa ɗaya tana taunar chewgam ƙas ƙas haka take bata sauti,cikeda karairaya take kallan Nizam tana zame dakeken glashing idonta wanda yakara mata kyau sosai ta sake kallan Nizam,da kanshi ke haɗe da bango office din baice uffan ba."Na fahimci kana mamaki dan nace karabu da waccen aurakar matar......tun kafin takai aya Nizam ya wanke ta da tagwayen maruka a kunci wani irin masifaffan raɗaɗi ya ratsa Fadila.har kwanyar kanta bata san ta fara sakin fitsarin wando ba tsabar kidima."This is last warning da zaki dinga jifan matata da mummunar kalma,uwar ƴaƴana zaki cema aura agaban idona?kaf DANGINMU ban ɗebema kowa hula ba wlh duk wanda ya kira Nazima da haka sai na wulakanta shi bare ke stupid get out!"mikewa tayi a tsorace tana dafe bakin ta dake fidda jini kamar wadda kai.ya fashemawa a ciki ta isa bakin kofa ta juyo ta kalle shi tace."Ya Nizam ni zaka mara akan waccen yarinyar? "Call her Nazima,kada in sakejin wannan kazamin bakin naki yasake gigin kiran ta da yarinya tafi karfin yarinya awajen ki bebcareful."Kuka ta kece dashi wani irin bakin ciki ya takarema Fadila makoshi Ji take kamar ta mutu tsabar takaici tace."Tabbas baka cikin hayyacin ka Ya Nizam i think so take ta kasheka."ta kasheni mana kinada problem da hakan?koda zata kashe ni ba ruwan ku,look Fadila kada kishiga abinda bai shafeki ba zaki iya fita."Ya ida maganar yana nuna mata kofa,itako ta kasa ko murza handle din takaicin Nizam na neman kasheta da ranta."Haba Ya Nizam ka s...."Stop it Fadila idan kika ida maganar nan wlh sai nayi suspension dinki a Company nan take note! I say get out of my office!."Ya ida maganar da mugun bacin rai.A sanyaye Fadila ta fita jiki ba kwari,a ranta kiwa ta dauki aniyar saita raba Nizam da Nazima kota halin ƙaƙane sai ta maye gurbin ta a cikin zuciyar shi,shiga mota tayi ta figeta da matsiyacin gudu tana huci kamar wata damisa tsabar fushi tabar office tana driving tana kuka....


Zaune take a ɗakin ta ita da kanwar Hajia Hassana Buhari,faɗa takeyi mata akan neman sakin da take nema wajen Mijinta."Haba Nazima baki da hankali zaki nemi saki wajen mijinki duk labari ya karade family kinkai Nizam Kotu ke ko kunya bakiji anya kinada hankali kuwa?kaf zuri'ar mu ba wadda takaiki dacen miji mai sonki da kishin ki kamar Nizam amma baki gani,dan haka wlh ki farka daga nauyayyen baccin da kikeyi tunda wuri,matukar kikace zaki biyema cuzgunawar da Hajia Zaituna zata dinga yimaki abbas ba ranar da zaki samu jindadi a gidan mijinki dan baki ga komai ba wlh,haka mahaifiyar mu tasha fama da mahaifiyar su Zaituna ba irin wahalarta da bata shaba haka sukayi artabar da bamu fata a sake maimaita kwatankwancin ta cikin family din nan kwara ki rike mijin ki dakyau so suke ki rabu dashi ga ƴan matan family nan su aure,daman tayaya kika aure shi kowa na san Nizam amman yace ke yake so kwara kisan abinda kikeyi tun wuri.


ita ko a zuciyar tajitake kamar zata fashe."dan yana sona damuwar shice nidai bazan iya zama dashi ba kodan DANGINMU! mutanen da suke suyi ajalina."mikaka ce."ɗan sosa keyar ta tayi alamun jin kunya tace."Anty nifa wlh yan uwansa basa kauna ta kinga fa yanda suke wulakan..."kinga Nazima banzo nan dan bincike ba nidai ina baki shawara a matsayin ki na ƴata kuma shaƙiƙiyar ki,kimaida komai ba komai kinji?kinga bari in tafi kada sirikin nawa ya tadda ni zaune."a sifar zolaya ta ida maganar.Suna mikewa sukaji ance."Ba dole ki gudu ba bayan kin gama kunso a sirrain ki,na gadon gado kin kawo mata dan ta kashe mamu ɗan uwa,to wlh ta Allah bata kuba Hajia Hassana."Cewar Fadila da tazo gidan Nizam dan cima matar shi mutunci. 

 Cikin ɓacin rai Hajia Hassana tace ma Fadila."Ke Fadila ni kike cewa ƴar asiri toh indai ni zakice ma haka ki saka a ranki kin faɗama Na'ima Buhari wannan maganar duk jirgi ɗaya ya dauko mu nida ita."Da sauri Fadila tace "Kinga malama karki kuskura ki taɓo uwata inba haka ba sai nayi maki rashin mutun ci!."Cikin kosawa Nazim tace."Amma hakan baidace ba Fadila baki da kirki kanwar mahaifiyar ki zakima rashin kunya."?..Dakama Nazima."ta daka mata tsawa ta nufota a fusace tace."Wato ke karamar munafuka zaki saka mani baki a cikin magana ta ko? Ke gaki yar iska kanwar uwar kice dai amman ni ba abinda da ya haɗani da wannan koɗaɗiyar sannan kiji abinda zance maki kina gadara akan Ya Nizam wlh blh sai na tarwatsa alaƙar ki da Ya Nizam munafuka jahila daƙiƙiya fasiƙa."tunda Fadila ta fara magana a firgice yasa Salma fitowa da gudu ta fara jan Fadila ta nasan tabar gidan baki ɗaya ita ko Nazima kanta ya kulle wai itace fasiƙa! shanye damuwar ta tayi tafara ba Anty hakuri tuni Hajia Hassana ta ɗauki jikarta zata tafi,itama ta hade fushinta,takara karfafama Yar tata guiwa sannan ta fita ta hau motar ta ta tafi gida duk acikin Estate ne.

 koda Salma tayi nasarar fidda Fadila a cikin gidan Nizam tsayawa tayi gab da motar Fadila tafara cewa."Haba Anty Fadila kinada hankali kike waɗannan maganganun karfa ki manta Anty Hassana kanwar Umma ce,sannan kalaman da kika gayama Anty Nazima gaskia sun taɓa zuciya ta!."Bankaɗe ta Fadila tayi tace."Munafuka ai daman tuni Hajia Aisha ta fidda ki a cikin zuriyar Jikokin ta Nazimar banza da wofi nace mata auraka kuma fasiƙa,kiyi abinda zakiyi sakara dake marar kishin zuci."tasaka kai ta shige cikin motar ta."Haba Anty Fadila idan rai ya ɓaci....tuni ta fizgi mota ta fita a guje kotakan Salma bata biba komawa cikin falo tayi duk ranta ba dadi,abin mamaki iske Nazima tayi tana kallan tasha bollywood kamar ba ita aka cima zarafi, zama Salma tayi kusa da ita ta fara bata hakuri cikeda da jin daɗi tace. "Komai ya wuce ƴar uwa kadaki damu kanki."cigaba da yar hirar su sukayi gwanin dadi saidai duk taraiyar su taɗan ja baya ba kamar da ba,da basu iya boyema junan su sirrikan su aminaine sosai kowa yasan tarayyar su amma tunda Nizam ya auri Nazima saidai Momy ta lalata alqar su.Kiran sallar da akayi ne ya tashe su,suka nufi daki dan gabatar da sallahi.....


 _Payment is on going hanzarta ki mallaki naki yar uwata kada ayi babu ke it's 500 via 0777512438 Acces Bank Jamila Abubakar Bello and show ur evidence through this number ***._ 


Koda Nizam ya yadawo gida da daddare bayan isha'i bedroom Nazima yafara biyawa saidai tasa lock tunda ta tafara neman saki wajen shi bata bari wata tarayyar auratayya ta shiga tsakanin su,duk wani hakkin shi Nazima ta hana shi haka yake hakuri shidai fatan shi, bai wuce ta hakura da maganar sakin da take nema ba tanajin yana knocking amman taki bude wa,saka kanshi yayi jikin kofar kamar mai raɗa yace."Heart beat badai harkinyi bacci ba? kiyi addu'a kinji Ummin Sadiq,I love u so much take care of ur self to me.."tunda yafara magana Nazima ke kukan zuci abubuwa masu yawan gaske ke mata yawo a cikin kwakwalwa musamman soyayyar su da yanda suke matukar kula da junan su shiru kawai tayi kamar mai bacci.A nashi bangaren koda yajita natace komai ba shima tafiya yayi yana karajin kaunar kwance a kasan zuciyar shi,kafin ya shiga ɗaki ya nufo falo ya zare wani karamin abu a jikin bango da alama camera ce,yana zarewa ya shiga ɗaki ya watsa ruwa sannan ya dawo kan bed ya zauna yana kurɓar black tea dama bai rabuwa dashi a flask a hankali ya saka memory a jikin system din shi yana cewa." Yaudai banso inga abinda DANGINMU kema Nazima idan bani nan narasa gane meke faruwa a cikin gida na."ya ida maganar yana fesar da numfashi mai zafi ya aje Aje cup din saman side drower cikeda natsuwa yafara kallo ga mamaki Fadila ya gani tanata wulakanci tunda ga abunda taima Anty Hassana har munanan kalaman da taima Nazima da fadan da Salma tai mata zuciyar shice ta fara duka da ƙarfi da karfi da sauri yasa hannu ya rike wajen dake mashi zafi yana kiran matata zata kira da jahila kuma fasiƙa! lallai yau saina koyama Fadila Nura Maikaba hankali a cikin Estate din nan duba wist clock din hannun shi yayi yaga 8:30 a fusace ya fita ya shiga mota da sauri mai gadi ya bude mashi gate ya fisge mota daga shi sai farar jallabiyar jikin shi harya isa cikin harabar gidan su Fadila ko parking kirki baiba ya kutsa kai cikin falon su,lokacin tana kallo ita da kanwar ta Mami baki dayan su, suka miƙe tsaye ganin Nizam ayam dandai duk tsoro ya kama Fadila duk ta raima gaskiyar ta......

★★★

*Sdeendtm*

 I'm sell data to all Nigeria network


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I'm

 selling MTN data with this cheap price* 


*MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.

 *Validity 1 month* 


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.* 

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp ***

_____________

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_***_


 *Anfara kuma anakan yi kema garzayo kada ayi babu ke Danginmu ne Silar Komai na kuɗine kizo ayi tafiyar taredake domin tafiyarma ta musamman ce* 



 _Yar Mutan Kankia ce❣️_ 



Share

Pls