ZAYN MALIK

Chapter -16

by @maidambu41

Chapter-16


Tun yamma da suka kawo shi, ya kasa tafiya haka ya zauna a jikin shi, karshe abin sallah ma Abul ta kawo mishi, suna zaune a wurin har na wani lokaci, shigowa Uncle Bashir yayi da katon warme na abinci ya ajiye mishi.

"Ya jikin shi?"

"Toh da sauki kenan zan ce dan tun da aka kawo shi dakin yake cikin unconscientious babu wani al'amarin cigaba ba a tare da shi."

Dafa kafadar shi Uncle Bashir yayi sannan ya ce mishi.

"Toh ko zaka zo mu tafi gida ne?"

"A'a zan zauna da shi, karka manta Mr Abdul Malik AY ya bani abubuwa dayawa a military office,. Saboda shi nake tsaye a haka tun ina training yake tsaye a kaina har yau da nake bana aiki, aka biyana albashi. Gaskiya ba zan iya barci a gida ba yana kwance a gadon asibiti ba, kasan zuwan da yayi ba zuwan kowa bane? Zuwa na yayi taya zan koma gida na kwanta. Bayan shi yana nan a kwance"


Ya fada yana kara gyara mishi zaman bargon shi yayi yana kallon shi, tare da jin matsananciyar Tausayin shi. Sai yau.

Yana zaune har Uncle bashir ya koma gida, sai wajen karfe biyu na dare ya farka, amma bai bude ido ba. Idanun shi a rufe suke amma yana zubda kwalla gwanin ban tausayi, bude ido yayi yana kallon dakin da yake, nazarin abinda ya faru yayi a hankali ya mike zaune. Ya zubawa Zayn idanu wanda kan shi yake jingine da gadon, a hankali ya shafa kan shi cikin kulawa ya ce mishi.

"Son"

Bude idanun shi yayi yana kallon yadda Mr AY. Kafin ya mike zaune.

"Ya jikin naka bari na kira Dr"

"Dawo da sauki. Ina son taking shower ne"

Dawowa yayi yana kallon yadda yake cire cannulardin hannun shi, sannan ya wuce ban daki ya haɗa mishi ruwan wanka. Sannan ya dawo ya ce mishi.

"Na gama sir"

"Nagode"

Ya sauka a kan gado, giftawar abu yayi a idanun shi, ya dafe kan shi. Tare da komawa bakin gadon ya zauna, hawaye ne yake sauka mishi me mugun zafi.

"Yallabai me yasame ka?"

Kama gefen kirjin shi yayi, a hankali yana sauke wani irin silent tears. A rude Zayn ya ce mishi.

"What's wrong Sir?"

"I lost wani abu me daraja, ina jin zafin haka a nan dina. Ina jin ciwon haka ina jin kewar abun na rasa abinda yake da daraja a wurina, i'm feeling like na rasa rabin rayuwata" a hankali ya ɗan ciji pink lips din shi, kasancewar shi fari kal kamar bature. Asalin kanuri ne me hade da sirkin shuwa-arab.

"Ayya Ubangiji ya mai da maka me alkhairi"

"I wish haka ya faru amma ban san meye na rasa ba" ya fada cikin shashekar kuka. Kamar yaro karami, kamar ya taya shi kuka shi kan bai san me yasa ba wallahi baya son ganin Babba na kuka, zama yayi har kusan asuba, kafin ya taimaka mishi ya shiga wanka sannan ya fito, da alola. Kayan marasa lafiya ya saka ,sannan suka jera da Zayn suka yi sallah.

Har zuwa sallah asuba a tare suka yi, sannan ya koma gado ya kwanta. Karfe bakwai Abba da Hajiya suka kawo musu abin karyawa.

Lokacin Zayn din yana ta faman aiki da Tap din Mr AY.

Kashe tap din yayi sannan ya ce musu.

"Barkan ku da zuwa"

"Barka dai Zayn ya me jikin dai?"

"Da sauki Abba bai jima da farkawa ba, ruwa suka saka mishi ina ga da alluran barci ne shi yasa "

"Amma sun fada maka Meke damun shi?"

"Sunce yawan aiki da rashin hutu yake damun shi."

"Kai kuma AbdulMalik ya zaka jefa rayuwar ka a cikin hatsari haka? Ai rai dangin goro, idan ta farka kace mishi nace yana hutawa shima "

"Zai ji" ya fada yana zuba kugun tsamiya a

kofi sai soyayyen dankalin turawa da sauce na kwai wanda yaji tafarnuwa da kayan kamshi, daya flask din kuma farfesun kayan ciki ne zalla, sai kamshin attarugu yake, murmushi Zayn yayi sannan ya cewq Hajiya.

"Kicewa Mamana ina son ta,"

"Ba zan fada ba, dan ni ba yar aikanka bace."

"Kefa Hajiya kina da damuwa, amma waye ya gaya miki bana son ki ai kaf matan duniyar nan bani da kamar ki!"

"Dan nima da kai kamar tukunyar girka, karka manta yau ne tafiyar ku"

"Ina sane Hajiya , shima sun ce idan ya farka an jima zasu sallame shi"

"Toh Allah ya bashi lafiya"

Cikin kulawa Abban shi yake ce mishi.

"An sama muku gida unguwar da babu yawan mutane, please ka nutsu"

"Insha Allah!"

"Hmm ba gara shi ba, idan ana niman yara marasa mutunci ai sai Yaran Umaima"

Ajiye abincin yayi ya fito tare da riko kafadar ta, suka fito waje suna hira har wurin motar su, bayan sun shiga ya zuba mata Idanu.

"Hajiya ayi ta hakuri ana kai zuciya nesa."

"Zainu ko zaka dauki bulala ne, tunda bana kai zuciya nesa"

"Allah ya baki hakuri Abba sai na dawo " ya sallame su, sannan ya dawo cikin asibitin ya wanke hannun shi. sannan ya koma gefe yana aiki da tap din Mr AY. Yana cikin aikin Babban Yaron Mr AY ya shigo mika mishi hannu yayi sannan ya ce mishi.

"Ya kwana biyu? Zayn Malik"

"Alhamdulillahi, Haris ya gida yasu Madam?"

"Suna lafiya, jiya da ka kirani bana gari ne, ina hanya shi yasa nace maka zan zo insha Allah. Ya jikin shi?'"

"Da sauki an jima zai farka zan tafi."

Musabaha suka kuma yi sannan suka rabu Zayn ya bar kome, domin Abul ya ishe shi da turo mishi da sakon yayi ya zo ta lagos zasu wuce, dan haka yana isa gida, wanka yayi ya saka jeans da singlet nayv colour, ya fara hada kayan shi, yana me dauko wani hoton shi da Hajiya lokacin da ya gama secondary school, murmushi yayi yana faɗin.

"Zan yi kewar ki sosai"

"Na sani ai" d'ago yayi tare da zuba mishi idanu.

"Dan ubanka, ba a koya maka sallama bane a gidan ku?"

"A'a Malam Zainu sai na shiga makarantar islamiyyar da ka bude zan iya" jefa hoton yayi ya gama hada kayan yana kallon kofar shigowa da yaji gyaran muryan Uncle Bashir.

"Wai na tambaye ku, wai don Allah ba zaku iya rayuwa bane sai dani?"

Cike da mamaki Uncle Bashir ya kalle shi.

"Idan ka gama haukar ka, sai ka fito" dauka wata jakar shi ta sojojin ya rataya, sannan ya ɗauki akwatin shi, Abul yana bin shi kamar Jela.

"Wai kai dole sai ka bi Ni ne?" Ya tambayi Abul da take bin shi kamar Jela. Kuma bai ji haushin Zayn ba,

Haka suka fito daga sama, ya nufi babban falon Hajiya.


A zaune ya same su, Ya gaida Mama da take mikawa Hajiya ruwan zafin tea. Ita kuma ta mikawa Zayn, ba musu ya amsa ya fara sha yana kallon yadda gidan ya cika da mutane.

A ran shi kuwa cewa yake.

*Dole kuyi murna fitanannen cikin ku zai tafi ina ga nan gaba ko mutuwa nayi sai kun yi kwarya kwarya walima*

Kallon shi Uncle Bashir yayi yana nazarin yadda yake kallon kowa shima a ran shi cewa yaƙe.

*Dole kaga kowa na murna ko ba kome Hajiya yanzu zata bawa kowa lokacin ta dan nima ya kwace mana Uwa*


Kallon juna suka yi da Uncle Bashir ya dauke kai.

"Hajiya Idan nace na fasa tafiya zaki min dole?" Da mugun sauri suka zuba mishi ido. Kowa yana addu'ar Allah yasa kar Hajiya ta ba shi goyon baya.

"Zainu karka mai damu mutanen banza, kai kace zaka tafi yanzu kuma kace ka fasa kayi hakuri ka tafi kaji "

A lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya,kowa yana girmama abinda yasa Hajiya kin amincewa ya zauna. Ai kuwa cikin tab'ara ya fara kokarin mikewa.

"Hajiya na fasa tafiya!"

"Innalillahi wa'inna illahi rajauin, akwai abinda aka maka don Allah tashi maza ka tafi ni da kaina zan raka ka" ita Hajiya gani take kamar da gaske asiri aka mishi, shi yasa ta mike tare da saka hijab dinta, ta riko hannun shi, zungure goshin sa Mama tayi yana faɗin.

"Bana son rashin hankali tashi ka tafi"

Kamar karamin yaro haka ya tura mata baki yana faɗin.

"Naga kowa sai murna yake fitanannen zai bar musu gida"

"Inji wa? Waye ya gaya maka haka? Lallai ana cin amanata a gidan nan kasan yadda nake ji kuwa zaka tafi ka bar ni"

Dakyar da lallashin sa Hajiya ta samu ya mike, Uncle Bashir ya cika yayi tam, har cikin mota kin zama yayi sai kwanciyar da yayi a jikin Hajiya.

Haka suka tafi ya sha zagi a zuciyar Abul da Uncle Bashir, kamar yana sane da suna zagin shi, sai kara narkewa yake shi ba zai tafi ba.

"Wayyo Allah na."

"Ayya Zainu meke damun ka ne? Tafiyar nan tana da muhimmanci, ka je idan garin bai maka ba, ka kira ni ka gaya min "

"Hajiya ba Uncle Bashir da Abul bane suke harara na"

"Kunci kaniyar ku Auta zaka fara baza halin ka ko? Kai kuma Abul kake? Kaniyar ka" ta musu dakuwa, kasancewar motar sienna ce, Uncle Bashir yana gaba Abul da Amal suna zaune a gefen Aunty Rukayyah da Annur, shima Zayn din ne. Ita kan Aunty Rukayyah dariya take tana kallon su, domin draman Hajiya da Zayn ba sabon abu bane, haka suka isa airport ana lallaba Zayn, dakatar dan banza aka ja shi zuwa cikin jirgin.

Ita kuma Hajiya Drive da Alhaji Uwaisu suka mai da ita gida Daurewa take amma ji take kamar ta fasa ihu.


 Lokacin da ya zauna murmushi yayi sannan ya gyara zaman shi yana me kallon Abul.

"Banza kawai, kai duk lokacin da muka zauna sai ka haɗa mu da Hajiya"

"Ya da son ranka? Idan da na matse na tawo wallahi sai Hajiya ta sani na fasa tafiya, amma yanzu zata ji a ranta dole aka min na tawo, ka gane idan kana da kaka irin.hajiya dole ka koyi kin abu dan ita sai a zauna lafiya, amma kace zaka nuna kana son abu ita sai tayi tunanin cewa dama baka damu da ita bane"

Shiru suka yi tare da gamsuwa da abinda ya fada.

--

Baya bata kadan.


Suna barin gidan dama kamar jira ake Zayn ya bar gidan Jami'an tsaron, part din Samir suka tambaya, aka nuna musu.

"Lafiya?" Hajiya Umaima ta tambaye su a rikice.

"Babu bincike muke akan shi dama an hana mu ne Sabida Oga Zayn Malik toh sabida baya nan yasa muka tawo"

Shiru tayi tana kallon ikon Allah, tana ji tana gani aka shiga cikin gidan shi aka fara bincike,

Suna gamawa suka fito lokacin su Hajiya sun dawo gidan.

"Toh ya auna arziki babu kome a cikin gidan shi, ya godewa Allah da ya bashi dan uwa irin Oga Zayn Malik idan ba haka ba da mun samu wani abu a cikin gidan da ta kare shi "

Daga haka suka fita abin su.

Cikin borin kunya ta fara kokarin safe zage.

"Idan dan Zayn ne ku tafi da Samir ku rufe ku wurga key din a kogi inda ba za a gani a ciro shi ba, har watsattse irin shi zamu ci albarkacin shi? Toh tir ba zan tab'a cin albarkacin shi ba sai dai ya ci albarkacin Y'ayana."


"Aikin banza zani ya mutu ya bar duwawu, shi danki bai gaya miki abinda suka yi aka Kore shi bane? Toh bari ki ji kafin Zainu ya ci arzikin ki, toh ke da Yaran ki kun ci na shi mahaukaciyar, ba dan Zainu ba da tuni an Kore shi a aikin shi, sannan me kika haifa? Yara masu son kan su sa son zuciyar su? Waye idan ya samu dama ba zai cuci AbdulMalik ba? Zayn ko kudin makaranta Yaron nan bai taba cutar da Uban shi ba, amma Yaran ki babu wanda bai cuci uban su ba, wallahi Umaima kina cutar da kan ki, kina ganin kamar wani abin arziki ne ko? Zaki gani a ƙwaryan cin tuwon ki ba....

*Saura kiris.... Na gama free pages ya kare🤌🏽*