4
by @phartybb
Kwana biyu da haka Hajiya Sadiya ta koma sabon gidanta ta fara rayuwarta. Ta sayi kayan abinci da sauran kuɗin hannunta da duk abinda take buƙata. Sai daga baya take jin haushin barin Rukayya da tayi, ji take kamar taje ta ɗaukota amma tana gudun wulaƙanci gurin Alhaji Mamman.
A lokacin ta fara tunanin sana'ar da za tayi don taimaka kanta.
Ƙadarorinta na filiya biyu ta sayar ta fara saro atamfa da taimakon Zarah ta fara tallata maƙota.
...
Bangaren Alhaji Mamman bai sanar da kowa abinda ke faruwa ba sai Alhaji Tukur, har yake ce masa ya nema mishi matar aure da za ta kula masa da ya'ya.
A ranar suna cikin yin maganar budar bakin shi yace.
"Ga ƙanwata Jidda, shekarun mijinta goma da rasuwa ta ƙi aure har yanzu, tana da yaro ɗaya Muhammad Al-ameen."
"Jidda dai ɗaya."
Faɗin Alhaji Mamman sanin ya ganeta.
"Eh ita dai, ka gwada sa'ar ka ko za ka samu shiga. Nima kuma zan mata magana."
"To shikenan Allah yasa ta yarda, ka fara gabatar da kaina a gurinta sai in je mu dai-daita, don bana son a ɗauki lokaci."
A haka suka rabu. Alhaji Tukur yana komawa gida ya sanar da mahaifiyarshi yadda suka yi, ya ɓoye mata cewa ga dalilin da ya rabu da matar shi, ce mata yayi kawai yana neman auren Jidda. Mahaifiyarsa bata kawo komai a ranta ba tace yaje ya samu Jidda ya sanar da ita duk yadda su kayi shine dai-dai.
Bayan fitar shi daga gurin mahaifiyarshi ya sameta har ɗakinta ya sanar da ita yana da magana da ita.
Bata kawo komai a ranta ba ta amince suka fita falon da ba kowa suka zauna.
"Kin san abokina Alhaji Mamman Bashir ɗan Gombe ko?"
Da mamaki Jidda tace.
"Eh na sanshi Yaya, wani abun ya same shi."
"A'a ko ɗaya, aurenki yake nema, babu dole in har ba kya so, amma dai kiyi tunani bisa maganar nan, ɗazu muka yi magana dashi yace shi dagaske yake yi, idan har kin amince baya son a ɗauki lokaci."
"Ni kuma Yaya? Haba dai, don Allah yayi hakuri, ina zan kai shi ga mata ga yara, kamar kwanaki naji kana cewa matar shi ta haihu. Balle ma ni bazan yi aure ba in bar Muhammad Al-ameen."
Jidda tace tana haɗa rai.
"To ai sun rabu da ita Hajiya Sadiyan, kuma kin san dai babban mutum ba zai iya zama ba mace ba, to shine yace in nema mishi mata ni kuma naga ga ki nan me zai sani neman wata."
Jin furucin shi ya bawa Jidda mamaki tace.
"Rabuwa dai? To ina yaransu?"
"Suna gidan, mai aiki ne take kula dasu."
Sam har cikin ranta ba ta ji daɗin abin ba na rabuwar Alhaji Mamman da matar shi Hajiya Sadiya ba, kamar yadda take samun labari suna zaman lafiya ta san da kyar in ba wani abun bane ya faru babba da zai raba su.
Lallai akwai wani abun a ƙasa tsakanin miji da matar da har cikin ranta taji tana son sani da kuma jihadin mayar da ita ɗakinta kan ƴaƴanta.
"Tunanin me ki ke Jidda, ko dai bakya ra'ayi."
"Na amince."
Ta bashi amsa kai tsaye.
"Dagaske? Yazo kenan?"
Kai ta ɗaga mishi, ya yi mamaki yaji farin cikin jin ta amince da wuri.
...
Cikin wata ɗaya daya wuce iyaye suka san maganar auren Jidda da Alhaji Mamman Bashir. Lokacin da yayun Alhaji Mamman suka samu labarin fitar Sadiya sun mishi faɗa sosai duk da ba wanda yasan dalilin rabuwarsu. Anan babban yayansu yace maza ya maida matarshi a fili yace to amma a zuciyar shi bai shirya yanzu sai lokacin daya ɗauka ya cika.
Biki saura sati biyu Alhaji Mamman Bashir ya gyara gidanshi, ya maida shi babba bangaren amarya daban, nashi daban sai na Hajiya Sadiya da shima ya gyara mai aikinsu babbar mace ita take zaune taci gaba da lura da yaran da suke ganinta tamkar kakarsu. Sun shaƙu da ita musamman Rukayya. Ita take shirya su suje makaranta ta musu wanka ta musu girki da komai na buƙata dan ta san suna buƙatar kulawa, kuma ko ba Hajiya Sadiya zata iya riƙe mata yara dan kyautatawa da take mata itama lokacin da take gidan.
Sati biyu wata ranar Jumma'ah aka ɗaura auren Alhaji Mamman Bashir da Amaryar sa Jidda Lawal sati ɗaya da biki ta tare a gidan mijinta. Ƙin ɗauko ɗanta Al-ameen tayi ta barshi a gaban mamarta.
...
Zarah da take zuwa ganin yaran Sadiya a ɓoye ko ita Sadiyar bata sani ba daga ita sai Innana mai kula da yaran Sadiya. Anan ta samu labarin auren data kasa barin abin a ranta ta je gidan Hajiya Sadiya ta sanar da ita.
Har hawaye Hajiya Sadiya tayi tana zaune ga katon ciki haihuwa yau ko gobe.
"Yara na Zarah, kar su haɗu da kishiyar uwa mai mugun hali ta cutar min dasu. Gashi ban san wani hali suke ciki ba musamman Rukayya."
Ita kanta Sadiya taji ba daɗi amma ba yadda za tayi da ta goge wannan shafin Ƙaddarar tsakanin su, bata da wani taimakon da zata basu sai na addu'a. Zuwanta gidan jiya ta haɗu da Jidda a yadda ta ganta ta sake mata fuska suka gaisa fatan ta har cikin zuciyarta haka take.
Dogon numfashi ta sauke
"Addu'a za kiyi ta musu inshaAllah babu abinda zai same su, mahaifinsu kuma shima addu'ar yake buƙata Allah dawo dashi hankalin shi ya dube ki."
Kai kawai Hajiya Sadiya ta girgiza tana share hawayenta. Tunanin halin da yaranta suke take.
"*"
Amarya Jidda da angonta rayuwarsu suka kafa cikin amince dan Jidda akwai nutsuwa da hankali. Binshi take sau da kafa tana son bashi lokaci kafin ta fara abin da ya kawota.
Alhaji Mamman Bashir kuwa da ikon Allah sai ya zama babu abinda ya ƙara faruwa daga ɓangaren aikin shi zuwa kasuwanci. Ƙoƙarin shi yanzu ya samu kuɗaɗen shi ya dawo da yayi asarar su.
...
Tun cikin dare take jin ciwon mara duk tasan alamun naƙuda ne, haka ta daure tayi ayyukan ta da basu da yawa. Wajen karfe goma ta lallaɓa tayi wanka ta zurma dogon riga dakyar dan ciwon yana cinta dauriya kawai take. Tana gamawa kayan haihuwa ta ɗauka ta nufi gidan Zarah ta samu bata nan ta bar sallahu kafin ta wuce asibiti.
Kafin ta isa ciwo sai gaba yake tana isa dakyar ta ƙarasa cikin asibitin kai tsaye labour room ta nufa suna ganinta suka karɓeta suka taimaka mata ta shiga ciki. Sosai ta wahala a nakudar har dare bata haihu ba. Zarah data samu labari ta iso amma an hanata shiga haka ta zauna ta jira a waje.
Sai gabanin asuba naƙuda ya taso mata gadan gadan da taimakon Allah ta samu ta haifi ƴarta mace ƙatuwa. Hamdala tayi ta jerowa da godiya ma Allah kafin a gyarata da yarinya, ganin lafiyarsu dukka ƙalau da safe ƙarfe tara aka basu sallama.
Duk yadda Zarah tayi suje gi
idanta ƙi tayi suka wuce gidanta. Wuta Zarah ta hura ta ɗaura ruwan wanka ya tafasa ta wanke yarinya kafin Hajiya Sadiya tayi, Zarah ta kawo mata abincin da tasa mai aikinta ta dafa ta aiko. Bayan taci ta sha shayi data haɗa mata ta samu shayar da babynta da sam bata da kuka sai bacci take, bayan ta gama ta kwanta gefenta itama bacci ya ɗauketa.
Ganin sunyi bacci Zarah ta koma gida ta samu mijinta ya dawo ta sanar dashi, kuɗi ya bata yace ta musu siyayyar ɗan abun buƙata ta karɓa ta mishi godiya kafin ta shiga kasuwa.
Abubuwan da tasan mai jego take buƙata ta siyo da su kayan baby. Data koma ta nuna Sadiya tayi murna tace ta saka mijinta da ita wahala.
"Ba komai wallahi Sadiya, duk garin nan kin manta ke kika fara zama kawata."
Murmushi kawai tayi tace.
"Hakane, nima akwai wasu kuɗaɗe hannuna sai a saya abin yanka."
"Shikenan zan samu wani ko Audu mai gadi in bashi ya sayo."
Anan suka yanke maganar Hajiya Sadiya ta bata kuɗin ta bashi ya sayo.
Washegarin kuwa ya cika alƙawari ya kawo. Kafin satin makota duk sun leƙo mata barka haka har ranar suna gidan da ɗan mutane.
NURATU shine sunan data sakawa jaririyar ta.
Da Zarah taji haka ta tambayeta.
"Mai yasa kika zaɓi sunan nan Sadiya?"
"Haske ce a gare ni in har mahaifinta ta zame masa duhu."
Hajiya Sadiya ta bawa Zarah amsa tana kallon ƴarta dake bacci abinta.
Jinjina kai Zarah tayi tace.
"Allah raya Nuratu. Amma mahaifinta ya kamata ya san da haihuwarta."
"Ameen, bana buƙata, kamar yadda baya buƙatarta nima bana buƙatar ƴata ta san shi."
Kai kawai Zarah ta girgiza tana mamakin ta ya uba lokaci ɗaya yace baya son cikin jikin matarshi bayan duk son da yake ma matarshi da sauran ya'yan sa. Haka aka watse Hajiya Sadiya taci gaba da kula da yarinyarta
...
"Ya ku kayi da Sadiya ta amince?"
Girgiza kai Zarah tayi tana miƙa ma mijinta ruwa a cup.
"Wallahi taƙi yarda, amma ni kam a nawa ganin ka je ka samu Alhaji Mamman Bashir kuyi magana dashi, mai yiwa mu samu takamanmen amsa ko dalilin da yasa yayi sakin."
"Hakan za'a yi kawai. In ba haka ba bana jin daɗin ganin Sadiya zaune ita ɗaya a gida daban anya ma can gidansu an sani."
"A'a bata sanar dasu ba har yanzu."
"Kinji irinta ko, wata huɗu fa yanzu gashi yanzu har ta haihu ta gama idda, ya kamata ƴan uwanta su sani. Amma bari muji ta bakin Alhaji Mamman ɗin in zai mai da aurensu."
"Shikenan sai yanda ta yiwu."
Cewar Zarah tana ajiye abincin data zuba mishi.
...
Washegarin mijin Zarah yana fita bai shiga shagon shi ba ya biya shagon Alhaji Mamman bai zo ba sai da azahar anan ya bar sako ya tafi. Azahar yanayi ya dawo ya samu yana nan. Bayan sun gaisa ya kawo masa maganar da ya zo da ita.
"Dama jira nake ta haihu mu maida auren mu."
Cewar Alhaji Mamman cike da murna
abin ya bawa Alhaji Audu.
"To Allah yasa hakan shine alheri, sai mun jika."
"InshaAllah za kaji ni cikin satin nan, zan zo har gida na same ka."
Alhaji Audu yayi makin maganganun Alhaji Mamman, da ya koma gida ya sanar da matar shi Zarah ita ma tayi mamaki kuma tayi murna jin yadda Alhaji Mamman ya amince da wuri zai mai da Hajiya Sadiya, fatan ta itama Sadiya ta amince ta koma kan yaranta.
...
Fitina Rukayya ta saka mata sai ta goyeta, haka ta saɓata a baya ta goya tana yawo da ita a falon. Yaran gaba ɗaya sun fi wuni a gurinta dan yadda take zuwa har ɓangaren su ta ƙirasu suzo nata, jansu take a jiki sosai tun basa sakewa har suka saba da ita ya zamana watarana har bacci suke a bangarenta.
Rahma tana koyawa Hasiya rubutu a takardunta na makaranta, gefe kuma ɗanta Al-ameen ne da Muhsin suke kallon American film. Al-ameen kasa zama yayi a gidansu Jidda ya dawo gurin mahaifiyar shi. Alhaji Mamman ya amince zai riƙeshi har ya cigaba da biya mishi kuɗin makaranta da yake aji biyu na sakandare.
Sallamar Alhaji Mamman cikin falon ya sa yaran barin abinda suke yi suka tareshi da gudun su, ya ɗaga wannan ya sauƙe yana tambayar su ina Rukayya suka ce tana kitchen da Amma. Sunan da suka sakawa Jidda kenan kamar yadda su kaji yaronta yana ƙiranta dashi.
Samunta yayi tana aikinta ga Rukayya a bayanta ya tsaya baƙin kofar kitchen din.
"Sannu da aiki."
Yace mata ta juya haka Rukayya ma jin muryar Abbanta ta juya, sai ta fara kukan za taje gurin shi tana haɗa sunanshi da hausar da ta fara yi.
"Bazan sauƙe ki ba, tun ɗazu ki ka kafa min fitanar sai na goye ki, yanzu kuma kina kallon Abba kice in sauƙe ki."
"Ki bari in kin haifi naki mana kiyi ta goyon yadda ki ke so, sauƙe ta dan Allah."
Sarai ta gane nufinshi dan ta lura ya sa mata ido cikin kwanakin nan, basar maganar tayi ta juyar kanta tana sauƙe Rukayya da gudu tayi gurin Abban ta ya ɗauketa suka fita a kitchen ɗin.
Da dare suna shirin kwanciya Alhaji Mamman ya sako zancen da yake son mata amma yana son ta fahimce shi.
"Rukayya ta samu ƙanwa."
Kallonshi Jidda tayi ya ƙara da cewa.
"Kin san dai da ciki na rabu da Mamin su Rahma, to ta sauƙa lafiya, shine nake son maida auren mu, banyi hakan dan ɓata miki rai ba ki fahimci ne Jidda."
#comment
#phartybb