Part 6
by @ummuaffan
*BAƘAR FURA*
© FATIMA SUNUSI RABIU
UMMU AFFAN
PAGE 6
Zaune suke a saman wasu kujeru na ƙarfe bayan an kaɗa break a makaranta (Tara) Humaidah ce ita da ƙawarta Layuza.
Layuza ƙawar Humaidah ce kuma aminiyarta dan tun suna jss1 suke tare, Layuza ita ma iyayenta ba masu hali ba ne amma irin yaran nan ce ƴan ƙarya da burga, da san shisshigewa masu hali, sai dai jininsu yazo ɗaya da Humaidah sannan dukansu suna da ƙoƙari abin da yasa abotarsu ta ƙulle sosai.
Layuza ta ce"Wallahi Humaidah da nice ke ba abin da zai kai ni wani auren gida, ai yarda kike da ƙyawun nan kin wuce ajin wannan Yayan naki Sadeeq, Allah da nice ke idan ba wani gwamna ba to sai babban attajiri, amma Sadeeq ɗin nan me garesa sai dai ya ɓige da ajiyeki gidan gado" Wani kallo Humaidah ta aikawa Layuza kafin ta ce"Sai akace miki sona ya ke? Na rasa me yasa kowa ya ke kallon Yah Sadeeq kamar sona ya ke" Kallon baki da wayau Layuza ta mata kafin ta ce" Ke mahaukaciyar ina ce? Ai ido ba mudu ba yasan kima Humaidah, Wallahi sonki ya ke kuma inda nice ke bazan aure sa ba"
Murmushi Humaidah tayi kana ta ce"Dan Allah Layuza ki kwantar da hankalinki. Yah Sadeeq Yayana ne ba saurayina ba, dan bai taɓa cewa yana sona ba"
"Dan bai faɗa miki ba amma alamu sun nuna" Shuru tayi na wani lokaci, sai kuma ta taɓe baki ta ce"Sai kuma kiyi!" Layuza ta ce''Ai yadda kike da ƙyawun nan ƙyanki ki auri me arziƙi kefa ta gaban mota ce" Humaidah murmushi tayi dan sosai yabon da Layuza ke yawan yi mata ya ke sawa taji kanta ya ƙara girma duk da tana da ilmin addini amma sam bata aiki dashi ita kanta zuwa yanzu da take SS2 tanaji a ranta da zarar ta kammala secondary zata gabatar da wani me kuɗi a gidansu, amma ta yaya? ta tambayi zuciyarta sanin bata da wani saurayi me arziƙi hasalima ba a barinsu fita a gida bazata ce tana da saurayi ba ma balle tayi tunani waye yafi wani kuɗi a cikinsu, ta tsani aiki shiyasa ta ke so ta auri me kuɗi ko dan komi sai anyi mata, ko da shara bata san taga tanayi.
Layuza kuwa sai huɗubar sheɗan take ƙara mata, tabbas ji take a zuciyarta idan ba wani hamshaƙi ba to bazata auri kowa ba.
Ko da aka tashi Ihsan tana ta nemanta su wuce gida bata ganta ba. Ita kuwa suna tare da Layuza da tajata wai ta rakata wani gida.
Kai tsaye unguwar GRA suka nufa gidan Alhaji Ibrahim me neman takarar gwamna, domin Layuza tana taya Hajiya Hindatu matarsa kamfe. Saboda surutunta da yawace-yawacenta yasa tasan mutane sosai hakan yasa ma in dai matar zata fita kamfe tare da Layuza ake zuwa dan tasan kusfa-kusfa na cikin garin Kaduna.
Humaidah sai waige-waige take ganin irin wannan aljannar duniyar, tun da take bata taɓa zuwa GRA ba balle kuma tazo gida irin wannan. Layuza ta ce"Dallah cen ki natsu kar a mayar da ke ƴar ƙauye" Sai lokacin Humaidah ta gyara amma har cikin zuciyarta ji ta ke ina ma ace wannan aljannar duniyar gidanta ne, tabbas ta zarcewa tsara, ganin gidan ya ƙara sa mata tabbas sai ta auri me arziƙi ko dan ta chana ta more rayuwarta.
Ƴan aikin Hajiya Hindatu suka cika musu gabansu da kayan ciye-ciye, domin sun san Layuza sosai tana yawan zuwa gidan. Humaidah ta ce"Irin wannan gara haka? Gaskiya Layuza arziƙi na inda ya ke" Layuza ta kai cinyar kaza bakinta ta ce"Shiyasa nake so kema kiyi aure gidan jin daɗi muzo mu dinga kwasar gara" Murmushi kawai Humaidah tayi tana cin abubuwan a natse.
Suna cikin ci Hajiya Hindatu ta ƙaraso, kallo ɗaya Humaidah ta mata taji gabanta ya faɗi, ƙasa tayi da kanta bayan ta gaisheta. Nan taji suna da magana da Layuza duk akan kamfe ɗinsu ne, da zasu tafi dubu ɗari ta ba wa Layuza akan ta sayi kayayyaki ta ramawa jama'ar unguwarsu kuma kar ta mance ta ce su zaɓi jam'iyyar PRC me alamar fanka, ta ce in sha Allahu sannan suka mata sallama ta cikasu da abin arziƙi suka bar gidan.....
Littafin BAƘAR FURA...Na kuɗi ne yanzu haka zaku iya samun bugagge a kasuwa ko kuma hannuna akan kuɗi nera dubu ɗaya 1000, sannan complete document ɗin sa Nera ɗari biyar 500 idan kuma cikin group mutum ke san shiga domin sakar muku page by page zaka biya ɗari uku kachal 300.
It's via Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 Stanbic bank N300. Evidence of payment *** ko kuma a ɗauki photon katin MTN a turo, Ƴan uwa mutanen Niger zasu turo da 500f ta numberta. ***
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_***_
Ingantacciyar Zuma (GORAN TULA) Da ta sami haɗi na musamman na sahihin magani na gargajiya. Zuma ce mai inganci wacce take ƙarawa mace da namiji inganci. Sannan tana wanke infection, wani abin jin daɗi ga zumar goran tula mace na sha haka ma namiji. Wani bayanin sai an gwada da kanku zaku bada labari amma indai kina san jinki chakwai kamar sweet sai kinyi amfani da zumar nan, bana rantsuwa akan magani na amma idan kin gwada ke da kanki zaki mini bayani.
Tuntuɓeni ta WhatsApp domin ƙarin bayani. *** Ina Kaduna ina aikawa ko wacce jaha dake ƙasar nan.
Idan baki shirya ba dan Allah kar mu ɓatawa juna lokaci dan girman Allah idan ba saya zakiyi ba karki ɓatan lokaci na gode.