Rumasa'u

Part 17

by @mrsjmoon

RUMASA'U. (The Innocent girl)


BY SAFIYYA.


WATTPAD @Mrsjmoon.


Page 17.


Jikinta ne yasoma rawa murmushi ya kuma sa ki daf da kunninta ta k'ank'ame jiki k'irjinta na matsanancin bugawa, ja da baya ya yi yana gyara trouser nasa ya ce.


"Labiba wannan sabon dabi'ar tabbas bayin kanki ba ne da alama gurguwar shawara aka baki please tell me, who told you this nonsense advice?"


"Samha ce." Ta ambata cikin rawar murya.


"Ai kam na san sai ita mara kamun kai, dan taga kina da natsuwa shi ne ta ke son ku taru ku lalace, to ta fad'o k'asa warwas burinta bazai tab'a cika ba domin muna tare cikin kariyar addu'ar iyaye wanda ita ta rasa shi."


"Hamid ba ka fahimceta ba, bashi ne manufata ba, wai taga zaka tafi...


"Ai dama ba zan tab'a fahimta ba dan haka ki rufemin baki da zancenta ko in kwad'a miki mari! Mara wayau kawai" Ya katseta cikin hargagi.


Da sauri ta zauna gefen bed ta sunkuyar da kai sai jan hanci ta keyi jikin ta nacigaba da rawa, sai kuma ta bashi tausayi yasan kome ta yi so da k'aunarsa ne sanadi. Kneel nasa ya zube gabanta ya dafa shoulder nata ya kira sunarta a hankali


"My Labiba loot at me." D'agowa ta yi ta kallesa hawaye na bin cheek d'inta, dik ta muzanta wani irin kunyarsa ta ke ji.


Girgiza mata kai ya yi tare da matsa kafad'unta kad'an ya saita murya zuwa sigan lallami ya ce "My Labiba ina son ki sa aranki Hamid ya na sonki ba zai tab'a rabuwa da ke ba, dik rintsi sai kin zama matarsa ta sunnah da yardan Allah, fatana ki tsare martabanki na d'iya mace ka da na tafi wani ya yi nasaran yaudararki da dad'in baki ya amshe abin tink'ahonki kuma cikar martabanki ako ina, domin shi ne ke alamta mace mai aji da ballagaza, kisani ita mace tamkar lemun zak'i ta ke da da zarar aka tso-tse ruwansa angama morarsa sai ajefar da b'awon to haka mazaje ke yiwa mace da sun gama morarta suke soma jifarta da kalaman b'atanci a k'arshe suyi mata korar kare in kuma sunyi alk'awarin aure basa cikawa sabida sun gama da ita ta koma tsohuwa sabuwa dal su ke muradi ya yin da ita kuma ta yi tarasa martabanta na har abada so kada ki bari shed'an da d'anginsa su rud'eki, ki sami raunin imani ki aikata abinda har ki mutu ba zaki daina dana saninsa ba." Ya ja numfashi cikin kallon ta ta yi hanzarin kauda kai gefe tana kuka mara sauti domin kalamansa ya tunatar da ita mugun waftar da taso aikata wa.


"Labiba nasan kina da matsala na sha'awa tun ba yau ba to ina so ki jajirce ki yak'i dikkan dire da zai jagoranci fad'awarki ga halaka ki yawaita azkar d'in Lahau wala kuwwata... Zuwa k'arshenta. Sau 10 safe da marece, Hasbunallahu wal ni'imal wa... Zuwa k'arshenta. Sau 450 shi ko sau d'aya ne arana bayan sallar farillah sannan ki ya waita ambaton sunayen Allah a dik inda kike sannan istiggifari yazamo abinda ya zauna a harshenki afili ko a zucci ya kasance kina yawaita ambatonsa kuma in kikaji sha'awar ta motsa miki sai kik'ara k'aimin wurin neman tuba sannan ki soma azimin nafila dan neman kariya daga sharri zuciya da iblisai. Insha Allah ina dawowa maganar aurenmu zai tabbat in yaso kina kammala laratunki sai ki tare."


"Nagode Hamid da yardan Allah zanyi aiki da shawar-warinka, Allah ya dawo da kai lafiya."


"Amin. Rubutamin address d'in gidan ku a Abuja inason halarta kafin in dawo wata k'ila ma tare da Dady zamuje."


Rubuta masa ta yi a paper ta ba shi ya amsa yana tsokanarta "Kaga Amaryan Hamid d'in ba." Kulle ido ta yi cikin dariya.


"Honey ka bar paper kawai sai na tura maka ta sms."


"Oh kuma fa hakan zaifi amma ki turo ta can d'in ai dik bai b'aci ba Hajiya ta."


"Kaganka ko." Ta furta cikin nunoshi da yatsa.


"Wal-walanki na ke son gani domin ganinsa na sanyani nishad'i.


"Honey kaima wata rana fa baka da dama."


Gyara fuska ya yi ba alamun wasa ta zuba masa ido cike da fargaban.


"Dan Allah Labiba kada na dawo na sami sanji game da turban da muka hau yanzu domin kinsan dalilin had'uwarmu kuma tundaga ranar na aminta da tarbiyyarki, bazan b'oye miki ba wallahi tsoron da na gani a idanunki lokacin da Mr. Khamil ya ritsaki a office d'insa ya taka rawa wurin sanyamin k'aunarki na tsakani da Allah. Please Labiba ba dan ni ba ki yak'i shed'an dan cikawa mahaifanki burinsu da ni kaina."


"Insha Allah nayima alk'awari lafiya zaka dawo ka sameni kuma ina godiya da k'aura mara algus."


Gyad'a kai ya yi cikin murmushi ya kamata ta mik'e tsaye ya kuma zube hannayensa saman kafad'unta a hankali yace "Wai na ce ba dana amince mun aikata abin in kika koma gida me zaki cewa Mam?"


"Wallahi ban sani ba, wayyo Allah dana shiga uku na lalace yau da jarabar Mamy."


"Uhm to in da munyi kuma k'addara ya afka kika samu ciki shi kuma shiga nawa zakiyi?"


Ido ta zare ya doki shoulder nata da k'arfi ta rintse ido. Cikin fitar sautin murmushi ya furta "Yes answer me."


"Wayyo Allah! Please Honey mubar maganar tunda dai Allah ya kiyaye bamuyin ba, ni wallahi dik hankalinsa ya tashi tsoron Allah ya kuma shigata."


"Very good alamun shed'an d'in da ya rab'i zuciyar ki ya gudu dan haka kada ki sa ke ya kuma yin nasara akanki."


"Tam insha Allah"


"Good taho mu tafi lokaci ya kusa cika."


Bayarsa ta biyo jiki a sa ke wani jin kunyarsa ne yake kuma lullub'eta amma ta lura shi ko a jikinsa.


Bayan ya kulle gidan ya mik'o mata key "Ki ajiyemin."


Amsa ta yi batare da ta yi magana ba. Suna isa wurin motar ya bud'e kusa da driver ya zauna ya kalleta "Drive us Madam."


Shiga ta yi tana murmushi tayiwa motar key suka fice. Tafiyar 20 minutes ya kaisu Airport d'in, tana gyara parking ta zame jikin seat ta lumshe ido shafar fatar idonta ya yi ta bud'e su da sauri murmushi ya sakar mata ta maida masa da martani ya gyara mirya cikin kallon idanunta "My Labiba bazan gaji da nusar da ke yarda rayuwa ta ke ba domin ita tana tafiya ce bisa juyi sannan cikin k'udurorin ubangiji."


"Haka ne Mine."


"Yanzu misali Allah ya k'addara bamu auri juna ba sai Allah ya had'aki da wani abin rayuwar to ina kuma rok'onki domin darajar manzon Allah kada ki nuna masa abinda kikayimin sabida ba kowa ne zaiyi miki adalci kamar yarda na yi miki ba. Ba yabon kaina na keyi ba ina dai k'ok'arin sanar da ke halin mazaje ne wanda tunaninki bai kai wurin ba, dan mafi yawancin mazaje yanzu sunfi kwad'aituwa da jikin mace akan rik'on amana dan haka kiyi karatun ta natsu kada ki sa ke soyayya ta rufe miki ido ki fad'a tarkon fargan jaji."


"Dan Allah my Hamid ka cire magar rabuwa, na ce maka natuba abinda na yi d'azun kunyar kaina na keji, wallahi bazan sa ke mai-maitashi ba har abada."


"Masha Allah a she my Labiba ansan shika-shikan tuba." Ya yi maganar cikin zolaya.


Murmushi ta yi tare da cije gefen lip.


"Abu na k'arshe kuma Samha tabi hagu ki bi d'ama domin banga dalilin k'awancen ba tunda ba k'asa d'aya kuka fito ba balle ace zumunta dole ne."


"Angama Yallab'ai abin kace shi za'ayi."


"Godiya na ke dear." Ya ambata tare da jan cheek d'inta, dukan wasa ta kaiwa hannunsa suka kyalkyale da dariya.


Tana tsaye jirginsu ya d'aga sannan ta shiga mota ta kife kai saman steering ta saki kuka ji take tamkar bata da kowa a k'asar UK.


A cikin jirgi shima Hamid kewar rabuwa da Labiba ne cike da ruhinsa. Dafe forehead d'insa ya yi yana hasko cikar surarta. 'Iya mace Labiba kin kai amma k'aunar da ke tsakanin mu na gaskiya ce bazan tab'a iya cutar da ke ba.' Ya ambata cikin ransa, afili kuma ya ce "Allah ka cika mana burinmu mu zamo ma'auta." Sai ya sa ki murmushi ya zame kad'an ya lumshe idanu bakinsa d'auke da addu'ar fatar Allah ya saukesu lafiya.


*

Momy tunda ta tashi ba ta zauna ba d'ora wancan sau ke wan can har saida ta tabbatar komi ya kammala ta jera saman dinning.


"Oh Momyn Hamid yau fa ba zama shalele zai dawo."


Murmushi ta yi kawai tana sa ke gyara dinning.


"Wannan gara ai da baki wahalar da kanki ba Aminatu, ga restaurant masu kyau a gari."


"Hubby kenan Hamid ne zai dawo ba wai bak'i zamuyi ba, ai ya iso ya samu da kaina na shirya masa komi zaifi yin farin ciki."


"Haka ne, to sannu da k'ok'ari Allah ya faranta miki kema."


"Amin."


"Zan fita amma ba zan jima ba."


"Ok kadawo lafiya amma dan Allah ka dawo kafin Hamid ya iso sabida so na ke hatta Umma ya samu a gidan."


"Insha Allah I'll try dan gidan Alhaji Bala kawai zani dubo jikinsa, bazan jima ba." 


"Ayya bai da lafiya ne?"


"Wallahi ifti'i ya sauka masa da kyar aka kwacesa a hannun wani mahaukaci majiyin k'arfi, Alhaji Abubakar ya sanarmin najin jiki dan ya sami karaya a hannun dama."


"Subbahallahi, Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ce."


"Amin ya rabbi."


"Wai Hubby me ye had'in abokinka da mahaukata ne?"


"Kawai haka Allah ya rubuto masa amma banjin yana da wata alak'a da su ba in ma da ita to bai wuce kyarsu da ya keyi ba cikin rashin tausaya musu."


"Hubby tunda naga taku tazo d'aya ka daure ka nuna masa abinda yaci kashi ne wanda ya bada shi ne zai amfanesa tun a duniya har zuwa lahira."


"Inayi masa Aminatu amma yak'i d'auka, kawai na bar abinda akan baida rabon samun lada ne ta hanyar taimako kuma wata k'ila a kwai hanyar da ya ke badawa ban sani ba."


"To Allah ya sa mu dace."


"Amin." Ya amsa tare bin hanyar fita waje ganin ba ta biyosa ba ya juyo.


"Yau ba rakiya Madam?"


"Wai da naga kamar kasoma zama dattijo ne, rakiya sai ka barwa su Mahmud da matarsu " Ta yi maganar cikin tsokana.


Dawo da baya ya yi ta yi hanzarin taransa ta kama hannunsa suka fice harabar gidan cike da nishad'i.


Bayan da dawo raka Alhaji part d'in su Mahmud ta nufa domin duba gyaran da ta sanya ajiwa d'akin Hamid ya yi ko da saura. Tana sanya kai parlourn ta dawo da baya tana jan hailala sai kuma tari ya sark'eta, dik inda ranta ya ke ya b'aci dan haka ta kutsa ciki kai tsaye dik suka mik'e cike da tsoro musanman Mahmud wanda baitab'a zaton ganinta ba.


"Mahmud tantirancin naka yanzu har a cikin gida? Anya kuwa kai cikakken mutun ne?"


Juya kai ya yi gefe yana cije lips danshi ganinsa tana yarfashi gaban abokansa da su ke kiranda da babban yaro. (Babba illar zama da abokan banza kenan sanyawa mutum girman kai)


"Dan Ubanka! maza tattara sokayen abokanan ka ku ficemin a gida, wallahi yau na baka damar tafiya dik inda kaga dama, in kaso ka bar k'asar ba abinda zai dameni, oya wuce ta d'ebo kayanka ka fice na sallamawa duniya kai, Allah ya gani nayi iya yi na duniya ta koyama karatunta tunda hakan ka zab'a."


"Momy kiyi hak'uri ba fa abinda kike zargi mukeyi ba kawai idanunki ne ya has...


"Mahmud shin zakayi abinda na umurceka ko sai na sab'a maka ta hanya mafi muni!." Ta ka tseshi cikin tsawa.


Bedroom nasa ya shige afusa ce ya bugo k'ofa, tsaki ta ja ta sauke dubanta kan abokansa da suka yi cirko-cirko cike da shakkanta domin tana da kwarjini ainun saidai wani lokacin sam baya tasiri a idanun Mahmud.


Wani mugun kallo ta watsa masu suka soma neman hanyar fita.


"Idan na sa ke ganinku a gidan nan wallahi sai nayi shari'a da iyayenku, wawayen banza kawai wanda suka maida sab'on Allah ado." Ba wanda ya tanka mata suka fice jikinsu na rawa.


Zama ta yi tana toshe hanci sabida mugun k'aurin da ya cika parlourn da ta sanya akayi masa gyara na musanman. "Ya Allah ka shirya mana Mahmud, kasa yagane gaskiya ya nesanta kansa wurin sab'on Allah." Ta ambata muryanta na rawa.


Ganin da ta yi Muhmud baida niyyar fitowa sai ta nufi bedroom d'in kai tsaye ta tura k'ofar batare da naiman iso ba, abinda ta gani ne ya sanyata dafa bango sabida jiwa da ya d'ibeta, bata san sadda ta zube saman kneel d'inta ba ta ambaci sunarsa cikin in'ina "Ma..h.mu..d." Hawaye na bin cheeks d'inta.


Shi kansa bayyanarta ya gigita shi dik kuwa da tarin tsaurin idanunsa.


_Alhamdulillah a nan zan dasa aya. Dan Allah kuyimin adalci fans banda kalaman b'atanci dik da nasan banfi kowa ba. Dan Allah ku maramin baya na mori basira ta akan wasu can su moreta a bilis. Nagode da bibiyar labarin batare da gajiyawa ba. Allah yabar k'auna ta hak'ik'a, Amin._


*Me Momy tagani ta firgice haka? Ina asalin Rumasa'u? Me ye labarin mahaukaciyar mahaifiyar ta? Shin Hamid na komawa UK? Ya ya lamuran Rumasa'u zai cigaba da tafiya? Shi zata haifi cikin jikinta kuwa? Wai shin wa ye ya yi mata wannan cin zarafin? Shi wa Rumasa'u zata aura cikin zaratan samarin da ke cikin labarin? Me ye sirrin wannan k'auna da su Alhaji Ahmad da matarsa Hajiya Aminatu ke nunawa RUMASA'U? Shin ya dangartakan baki d'ayan ahalin gidan Alhaji Ahmad su ke da juna? Anya kuwa babu lauje cikin nad'i dan ga ne da lamuran Alhaji Bala? Warwara,tifka gami da tarin amsoshin tare da dama wasu dik zaku samesu a cikin cigaban labarin da yardan Allah. Nagode da k'auna masoyana. Safiyya na yi muku k'auna ta tsakani da Allah sannan a dik inda kuke tana yinku domin da bazarku ta ke rawa, k'unarku shi ne tsanin hangenta.*


_Bazan barku haka sai na sa ke sanar da ku Labarin RUMASA'U labari ne da ya taro gabas da yamma kudu da arewa ya dunk'ule wuri d'aya. Jigon labarin ya rarrabu dan haka ku garzayo dan sanin ta inda zai warware ya had'e kansa tsaf ya fitar da matsaya na ban mamaki._


Zai cigaba da sauka a wannan website din insha Allah.

*Ta ku Mrsjmoon*