Part 6
by @mrsjmoon
DAMUWATA (Sanin abin adona)
Mrsjmoon
EWF.
*Shafin na my Billy Galadanci ne, Allah ya bar zumunci tare da yalwatuwar nasara agareki mara iyaka, Amin*
Page 06.
"Kayi hak'uri haka Deejah ta ke sam bata da sabo musanman ga Maza."
"Ni ne shaida akan wannan halin na Khadija, tsawon shekaru da muka shafe muna karatu a cikin aji d'aya amma bamu tab'a maganar da ta wuce na mintoci biyu ba sai ko in karatu ne ya had'amu shima sai wurin muraji'a ko amsarwa juna hadda."
"Lallai kai ne ya dace ka sanar da mutane rashin sabonta ba wai asanar da kai ba."
"Uhm k'awar malama Khadija na tsareki da surutu, gashi har ta b'ace miki."
"No bakomi, dama rakiya nayo yanzu dai ka bani wurin zaman da zan dakaci fitowarta."
"Ok muje daga can in ban takuraki ba na tayaki hira kafin lokacin shiga darasina ya yi."
"Aikam ina godiya da karamcin nan, abokin Deejah."
"Aboki kuma?"
"Eh."
"Ina, ai ban isa na zamo abokin Malama Khadija ba saboda ita d'in kayan manya ne irin Sarakuna d'in nan masu fad'a abi dole ko da rai bai so ba."
"Kai Abokin Deejah, duk ita kad'ai."
"Allah kuwa Khadija ta da bance, samun irinta cikin Dubban Mata sai antona domin sauraren kalaman da suke fitowa daga bakinta kawai zai bawa mutum amsar cewa ita d'in ba sa'ar zancen yara irinmu ba ce ko manyanma sai wanda Allah yayiwa gamdakatar."
Dariya sosai Beebah ta sanya wanda hakan ya janyo hankali wasu malamai tare da d'alibai.
"K'awar Malama muk'arasa wurin kada nasamu kira daga hukumar makaranta ace ina zance cikin tsakiyar makaranta."
Motsa kai ta yi tana d'auke dariyar, suka jera cike da wayewa. Aliyu ya dubeta kad'an ya ce "Sunana Aliyu Muktar."
"Masha Allah, ni kuma Habeebah."
"Wow my Aunty, domin sunar babban yayarmu ce wacce muke Baba d'aya.
"A she ina tare da k'anina"
Motsa kai ya yi batare da ya furta kalma
A k'asar bishiyar magoro ya yi musu masauki saman kujerun roba, ganyen bishiyar na kad'awa cikin fitar da iska mai gamsarwa, hira suka cigaba da yi cike da sakewa tamkar sun jima da sanin juna.
***
Misalin k'arfe shabiyu saura mintoci goma na kammala koyar da aju-juwan danake shiga, na fito ina raba ido dan neman inda zan hango Beebah.
"Malama, Malam Auwal yana kiranki."
Idanu na zubawa matashiyar yarinyar tamkar ban gane abinda ta fad'a ba.
"Malam Auwal ne ya ce in kira masa ke, yana office d'insa tare da su Malam Bashir."
Motsa kai na yi, yarinyar ta bar wurin, najima tsaye batare da na motsa ba.
"A'a Malama Khadija kina lafiya kuwa?"
Saida nayi gaba kad'an sannan ta amsa "Ina lafiyalau Malam Hassan, dafatan kaima haka?"
"Alhamdulillah"
Ya amsa cikin nufar office d'in shugaban makarantar tamkar badani yake maganar ba alhalin shi ya soma.kulani, tsaki na ja a cikin raina tare da nufar office d'in nima ina k'issima dalilin kiran da a keyi min.
Office d'in cike da malamai na samu domin malamai shida ke ciki gami da shugaban makarantar bakwai, na zauna tare da gaisar da su a jam'i suka amsa, shiru ya ratso wurin zuwa can na tsinkayi muryan mataimakin shugaba Malam ishaq ya kira sunana, ban amsa ba illa idanu da na d'ago na zuba masa gabana na fad'uwa. Sake kiran sunana ya yi alamun yana buk'atar amsawana, amsawar na yi a hankali, ya yi gyaran murya tare da cewa "Shugaba Malam Auwal ya kiraki ne domin ya nemi alfarman da ki cigaba da koyarwa regular saboda wasu daga cikin malamanmu sun sami takardan cigaba da karatu a k'asar misra, idan sun tafi zamu fusakanci karancin Malamai shi yasa mukaga dacewar ki dawo koyarwa full, dafatan zaki amsa k'ok'on bararmu da hannu biyu?."
Wani dim na ji saboda burina na bar koyarwan baki d'aya sai ga wani batu sabo.
"Dan Allah Malama Khadija ki amince sabidya muna da bukatarki ainun, d'alibanmu na gane koyarwanki haka iyayensu na alfahari da hakan makarantarmu na samun d'auka ta wannan fannin, dan Allah kada ki watsa mana kasaya idanu."
Shiru na yi ina sauraren magan-ganun Malaman wanda duk kaninsu saida suka tofa albarkacin bakinsu ta hanyar rok'on amincewana a k'arshe suka tsuke bakunnansu suna dakacen amsana. Na d'auki mintoci kusan uku kafin na ce "Zanyi shawara da mahaifiyata."
"Allah yasa muji alkhairi."
Shugaba Malam Auwal ya furta cikin saukemin kallon k'urillah wanda na tsana.
"Amin."
Duk suka amsa.
Sallama na yi musu na fito sai dai ban ga Beebah a inda na barta d'azun ba, tsayawa na yi ina nazarin inda ta shiga, maganar Malam Hassan ya sa na juyo ina nemo amsan da zan bashi akan tambayar da ya yi min.
'Me yasa bakya alfahari da abin adonki Malama Khadija?' Tambayar nasa na sake maimaitawa a raina ina son sanin ma'anar kalman ABIN ADO daya ambata. Tamkar kuwa ya shiga raina najiyo yana yimin fashin bak'in manufarsa
"Manufata shi ne me yasa ba kya danganta kanki da Mahaifinki sai dai a koyaushe Mahaifiyarki kike ambata a muhallin Mahaifinki alhalin ita d'in k'asa ta ke da shi ta kowani fuska tun daga halitta har zuwa girman matsayi wanda Allah ya bashi akan sama da nata dan mace bata tab'a jagorancin d'iyoyintaba sai da tsayayyen namiji."
"Malam Hassan kana da k'arancin sani akan muhimmancin Mahaifiya ga d'iyoyinta, tabbas Allah ya S.W.A ya fifita halittar Namiji akan Mace amma a wurin girman matsayi ta fannin biyayya sai ya fifita halittar Mace domin sai da ya ambata da abita sau uku kafin ya ambaci uba kaga kenan ba'aibu ba ne dan na ce zanyi shawara da mahaifiyata, ka san ko masu iya magana sunce ciwon 'ya Mace na 'ya Mace ce."
"Haka ne, kina da hujja mai k'arfi Malama Khadija amma kisani ba kowa ne zaiyi tunanin karatun da kika tunasar dani yanzu ba saboda bayan fitarki k'orafin yarda kike yawan ambaton Mahaifiyarki akan lamuraki sama da Mahaifinki alhali shi d'in jagoran al'umma ne, masanin ilmomin islama abin alfaharin dukkan 'ya'ya a ce shi d'in mahaifinsu ne, wannan dalilin yasa na ce zanyi miki tambaya kuma na gamsu da bayanenki Allah yasa mugama da mahaifanmu lafiya, musanman Uwa."
"Amin."
Na amsa a tak'aice tare da barin wurin cikin jin wani yanayi na rashin jin dad'in cece-kucen da sukayi akaina bayan fitna.
'Dole in bar makarantar nan dan bazan juri gulma ba.'
Cikin zancen zucci na isa bakin gate batare da na nemo inda Beebah ta mak'ale ba.
"Kinganni zaune anan ina dakon fitowarki domin Aliyu ya sanarmin da kin gama darasinki."
Kallon inda ta ke zaune na yi gefen bencin mai saida kayan fruits, da hanzari ta taho ta rik'emin hannu cikin rawar murya ta kuma cewa "Ke da waye Deejah?"
Girgiza mata kai na yi ta motsa hannuna da k'arfi, na kulle ido ina jan hailalah a cikin ruhina.
"Oya tell me! Waya tab'aki? In tafi na ci masa k'aniya."
"Ba kowa Beebah kawai gajiya ne, mutafi gida kada mutane su taru kinsan abin kallo baiyiwa jama'a wahala."
"Ki sanarmin da damuwarki K'awata."
Ta ambata amma cikin rad'a.
Dukan kafad'arta na yi cikin sauke mata murmushin yak'e sabidya yarda ta yi maganar takomamin sak Aminiyata Fanta, mai damuwa da DAMUWATA.
"Jini baya b'uya."
Na furta mata a hankali, ta murta dan ta fahimci inda zancena ya dosa. Hannunta na ja muka isa wurin mai saida fruits, yana ganina yasoma zubawa a leda murmushi ne ya kubcemin ganin abinda keyi wanda faruwan hakan ya tabbatarmin ya gama gane abubuwan da na ke siya duk in na shiga makaranta.
"Gashi Malama."
Amsa nayi tare da bashi kud'insa ya duba ya gyad'a kai, Beebah ta amshi ledar muka nufi bakin titi. Muna cikin Napep Beebah ta cikani da labarin Aliyu Muktar na dubeta kad'an ina k'unshe dariya saboda na san abin da zan fad'a dole yasanya ta barmin kunni ya huta.
"Nafahimci Aliyu ya mallake zuciyar 'yar mutanen Barno."
Aikam d'if ta d'auke zancen na saki siririyar dariya ina kallon idanunta ta had'e rai, sai na juya kaina gefe ina kallon titi domin haka na ke so.
Bayan mun watsa ruwa muka isa farandan Mama ta gabatar mana da abincin, shinkafa mai miya da salad, mukaci sosai tare da korawa da kunun aya mai sanyi. Tashi na yi zuwa d'akina Beebah ta rufamin baya, ina zama gefen katifa ta janyo kujerar kwalliya ta zauna tana wani cin magani dariya na kyalkyale da shi.
"Wato na zame miki mahaukaciyar ko Deejah?"
"No K'awata, kawai nagani ne fushin sam baiyi kyau da kyak-kyawar fuskanki ba."
Murmushi ta saki na jinjina mata hannun ta kama ta rik'e gam tare da cewa "Aliyu Muktar ke yake so ba ni ba."
"So?"
"Eh so tare da k'auna, Aliyu keyi miki kuma na gamsu da halayyansa d'ari bida d'ari dan haka ina baki shawara da ki amshe-shi a matsayin your first love, insha Allah bazakiyi da kin sani ba."
"Yaro ne shi Beebah, bana son b'atawa kaina lokaci."
"Kada ki butulcewa rahman Allah Deejah, domin Allah ne ya amshi rok'onki a yau kika sami wanda ya ambata miki kalman So wanda kike muradin jinsa da jimawa."
"Nagodewa Allah, Allah ya sanya khairan a tarayyanmu."
"Amin ya rabbi, haka ya kamata ki ambata ba wai zancen yarinta ba."
Sosa tsinin gancina na yi tare da gyara zama na ce "Beebah ya akayi Aliyu ya sanar miki da yana So na?"
"Labarin tsarin rayuwarki mukeyi wanda ke burgemu musanman rashin hayaniyarki da gudun abin magana, shi ne ya sanarmin da sirrin ruhinsa akanki wanda ya ce kusan shekara d'aya kenan yake burin ya sanar miki amma kwarjininki na yi masa shamaki sai ya kasa tunk'ararki da zancen, ganina tare da ke ya bashi kwarin guiwar sanarmin."
"Kwarjini kuma?"
"Yes Deejah, kina da kwarjini na ban mamaki wanda shi ne dalilin da ya sanya maza ke shakkar tunk'ararki da kalman So dan ba Aliyu kad'ai ke shakkar furta miki kalman ba hatta da shugaban makarantar tare da mataimakinsa dama wasu malaman duk sun kasa kallon idanunki su ce suna sonki."
"Ikon Allah, to ke wa yasanar miki da wad'annan bayanan?"
"Aliyu, dan ya ce da kunnuwarsa yaji suna tattauna zancen, lamarin da ya sanyashi k'amar jinya amma ganin lokaci ya ja bawanda ya iya tunk'ararki sai ya sami natsuwar ruhi, shi ne yau ya sanarmin domin inyi masa jagora da ki kulashi ko da cikin tsokali ne."
"Uhm to zan kulashi amma dai ina jiyowa ajikina kamar lamarin ba zai d'ore ba."
"Saboda me yasa kike son jifan lamarin da mugun fata?"
"To na yi shiru."
"Hakan ya kamaceki dama."
"Aliyu ya sami 'yar campaign a bulus."
"Eh naji dai kome zaki ce."
Juya kai na yi inajin natsuwar ruhi na ganin a she bana da cutar komi tunda gashi an sami wanda ya furtamin kalman k'auna abin da najima ina tsumayen jinsa a bakin Namiji.
"Aminiyar Fanta ko bakya son Aliyu ne?"
"Ta ya zan iya amsa miki wannan tambayar alhalin ni ban san ya kalman ta ke ba tun tsawon rayuwata."
"Deejah zaki sani da yardan Allah domin na hango tarin k'aunarki mara algus a idanun Aliyu."
"Uhm Allah ya sa hakan ne."
"Amin."
Lumshe ido na yi cikin son yin barci amma sai maganar da mukayi da Malam Hassan ya bijiromin na bud'e ido da sauri Beebah ta sakarmin murmushi cikin cewa "Yanzu bakiji kunya ba da kika ce Aliyu yayi miki yaro?"
Kulle ido na kumayi cikin murmushi batare da nace komi ba.
"Aliyu ba yaro ba ne, ya sanarmin shekarunta talatin da uku, shi ne babba a d'akinsu, yana da k'anni uku mace d'aya maza biyu da kuma wata wacce suke abokan wasa da Hajiyarsu ta rik'e amma ita ta yi aure.
"Tabbas nasan lokacin aurenta, dan naso zuwa Allah bai nufa ba."
"Kinga kenan inda a k'auye ne da yanzu ya kusa ajiye suriki."
Duka na kai mata jin sharrin da ta zabgo. Dariya muka sanya. Zuwa can ta mik'e ta dubeni na d'auke kai.
"Malama ta so muje na gaida Aunty Nafisa kada ta kai k'arata fadar Momy ko Alhaji Babba."
"Sai kindawo amma ni Deejah na gama shiga gidanta insha Allah."
"A she zancen bai wuce ba kenan?"
"Ya wuce amma dai yatsuna har yanzu zugi sukeyimin, kinga ko da ya wuce a raina to a cikin fatana da sauran miki."
"Kina da gaskiya Deejah kuma kin burgene da kika zamo mai fad'ar gaskiyan ruhinki, bari in tafi zuwa dare zan dawo, me kike son in dafo miki?"
"K'awata Fanta da mai da yaji."
Dariya ta kyalkyale da shi ta fice tana dariyar, murmusawa na yi na koma na kwanta na tsirawa ceiling ido, zuwa can na kulle su. Cikin barcin da yasoma d'aukana najiyo sababin Baba na bud'e ido da sauri tare da tashi zaune ina jan hailalah jin muryansa ya nufo k'ofar d'akina. Ina sauke kallona kan bulalan dake hannunsa na daka tsalle sai cikin toilet kafin in kulla ya ritsani ya rizgoni na dawo tsakiyar d'akin, wani tsalla na kuma dakawa na fad'a jikinsa na cukui-kuyeshi.
Gam na ji ya rungumeni har ina jin numfashi nayimin wuyar fita.
"Malam!"
Na tsinkayi muryan Mama cikin tsawa.
Tureni ya yi da sauri tare da daga bulalan zai zubamin Mama ta rik'e cikin wani lakan murya wanda bansanta da shi ba ta ce "Ficemin a gida na barka bari na har abada Malam, sadakinka zan bawa Baba Umaru ya baka kamar yarda ka bashi ya bani. A yau na tsaneka Malam tsana mafi mu...
Kullewa Mama baki na yi jikina na rawa ta ture hannuna abakin nata, kafin ta sake furta kalma na kuma kulle mata baki cikin cewa "Baba shima abin adona ne Mama ki barshi ya hukuntani wata k'ila laifi na yi masa."
"Malam ba abin adon ki ba ne Uwata, Ni ce abin adonki kuna ki barni na kwatar nama 'yancinmu, wallahi na gaji da lamarinsa, daga yau nagama aurensa."
"Mama ki daina fad'ar haka dan girman Allah."
Na ambata cikin matsanancin kuka.
"Na daina, kuma na hak'ura saboda kwanciyar hankalinki Uwata."
Rungume Mama na yi cikin jan hanci ita kuwa ta soma shafan bayana tamkar tana rarrashin yarinya 'yar yaye.
"Nagode Hurera da kalan halaccinki, nagode k'warai."
Muka tsinkayi muryan Baba ya ambata cikin shak'ewar murya. Da kallo muka rakashi har ya fice d'akin.
"Mama me na yi masa ya tsaneni?"
"Zan sanar miki da mafarin komi Uwata, wanda baici ya zama hujja ba ga mutum mai hangen nesa ."
"Ina saurarenki Mamana."
Shafo fuskana ta yi cikin b'oyemin b'acin ranta wanda ni kuma na karantosa amma sai na nuna bangane ba, na sake shigewa jikinta ina sauke numfashi, a haka ina manne a jikinta muka fito daga d'akina zuwa d'akinta.
*TALLA.*
*Ina kuke Mata 'yan kwalisa masu bawa fatarsu 'yancinta musanman babban kadararku wato fuska. To ga dama ta zo muku cikin sauk'i wato samun kayan gyarar fuska da jiki mai inganci na organic wanda aka samar da su da abubuwa masu nagarta. Duk wacce K'uraje, Tabbai, Sunburn, kyafsi suka b'atawa fuska muna da maganin da fuskanta zai dawo fes, sumul, rangad'ad'au. Haka a fannin fatar jiki shima muna da kayan da zaiyi laushi, sulb'i tare da haske mai kyau. Ga kayan kamar haka:*
Sabulu (molato and black soap)
Scrub
Face cream
Oil
Body lotion
Shower gel
Kulachan
Humra (White and black)
Turaren tsugunon
Turaren kaya
Turaren wuta na d'aki
Garin d'a'a (domin k'an-k'aro martaban aure a turaka)
*Duk za'a samesu a farashi mai rahusa, mai buk'atar d'aya ko sari a tun-tub'emu a wad'annan numbers d'in *** ko ***. Sai munjiku.*