Chapter 35-36
🪴 *GIDAN BALARABE* 🪴
By
*MAMAN NABEELA*
*MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*
*_ASSALAMU ALAIKUM, MA ABUTA KARATUN LITAFINA NA GIDAN BALARABE, FATAN_* *_ANGAMA IBADAR AZUMIN RAMADANA LPY,KUMA ANYI_* *_SALLAH LPY TOH ALLAH YA MAI MAI TA MANA AMEEN_ _YASA KUMA MUNYI_* *_IBADA_ _KARƁAƁIYA_*
🅿️3️⃣5️⃣↔️3️⃣6️⃣
--------"Hussaina leƙa min ɗakin Laila ki duba naji ta Shiru,har yanzu bata fito ba tun Safe rabona da ganinta" cewar AMMY tana karɓar ƴar Hussaina ta ɗorata kan cinyarta.
"toh'Ammy bana duba Allah yasa dai lafiya,nima tunda nazo banganta ba na ɗauka Ma ko ta kuma gida ne" Hussaina ta faɗa tana Miƙewa.
"A'a tana nan ina ga dai ko Wannan kai Lefen ya hanata fitowa"Ammy ta faɗa.
"Allah Sarki harta bani tausayi,dole taji ba daɗi'bana dubu ta"Hussaina ta faɗa tana nufar Sama.
Ammy ma cikeda tausayinta take Maganar zuci tana faɗin"duk Sakacin ku da rashin tsayawa ko kula da Mijinku ya kaisa ga ƙarin Aure,Allah dai yasa Wannan Aure ya zame Maka Alkairi ya Samar maka da ƙwanciyar hankali da nutsuwa SON"Haka Ammy tayi ta Maganar zuci Har Hussaina ta dawo daga dubo Laila tana cewa "Ammy bafa ta Ɗakin,na duba Har Banɗaki bata ciki kamar ma ta jima bata ɗakin!"
"Kamar ya bata ciki ina kuma ta Shiga?"
"Wallahi dai bata Ɗakin dan ina Shiga da naga bata ciki, na nufi Banɗaki nayi Norking ko tana ciki Sai na tarar ƙofar a buɗe ina turawa naga bata ciki kamar ma ta jima bata ciki dan a bushi yake banɗakin ba alamun anyi amfani dashi"
"Kin ga karɓi yarinyar nan Mu duba ko ina,kiramin Hannatu ta duba min garden ko tana chan!"
"toh Ammy"Hussana ta faɗa tana karbar yarinyarta ta nufi Kicin.
Ammy Ɗakin karatun Su Huda ta fara dubawa bata ciki'duba lungu da Saƙo na cikin gidan ta ringa yi amma babu Laila babu dalilinta.
Hannatu da Hussaina ne Suka Shigo,Hannatu tace
"Hajiya bata garden"
"innalilahi'wa'innailahirraji'un Ammy ta faɗa cike da tashin hankali tana lalubar Wayar ta ta danna kiran Layin Laila Amma a kashi "Hasbunallahu wa ni imal Wakil, ina yarinyar nan ta Shiga?"Ammy ta faɗa cike da tashin hankali tana zama gefen kujera.
Huda ce ta Shigo bakinta ɗauke da Sallama ganinsu kamar cikin tashin hankali yasa tashigo da Sa Sarfa tana tambayar meke faruwa?.
Hussaina ce tayi ƙarfin halin gaya mata abinda ke faruwa,nan itama ta zube kayan dake hannunta tana faɗin "AMMY an duba pat ɗin Yaya?"
"a'a toh me zai kaita nan bayan ba kuwa a ciki"
Hussaina ta faɗa dumin Ammy ta kasa cewa kumai tsabar tashin hankali.
"Amma Anty Hussaina ai hausawa cewa Sukai in raƙumin ka ya ɓata har cikin kura tandu bincikawa kake!"
"Hakane toh'muje mu duba" Hussaina ta faɗa.
tashi Sukayi Suka nufi Sashin tsab yake babu ƙura, dan Ammy kansa a gyarashi,dubawa Suka fara yi lungu da Saƙo amma babu Laila babu me kama da ita fitowa Su kayi Suka dawo gurin Ammy inda Suka Shaida Mata bata chan Ma'Cikin tashin hankali Huda tace "amma Ammy ko a kira Yaya aji ko Suna tare?"
"eh' bari na kirashi da kaina Allah yasa dai Suna taren!"
"Ameen"Suka haɗa baki Suna faɗe,inda kuwanensu ya Zauna Cikin Zullumi,fuska ɗauke da damuwa.
Ammy Wayar Balarabe ta kira bata daɗe tan ringing ba ya ɗaga dan yana kan hanyar zuwa gurin Khadija, daga nan kuma ya tahu gidan nasu.
Bakinsa ɗauke da Sallama ya ɗaga Wayar yana faɗin "Ammy barka da yamma"
Ammy Sallamar kawai ta amsa tana cewa "Son kuna tare da Laila ne?"
"a'a Ammy meke faruwa?"
Nan Ammy ta faɗa Masa abinda yake faruwa'inda Shima cikin tashin hankali yace"Ammy ganinan ƙarasuwa dama ina hanyar zuwa"
ya faɗa yana nufar hanayar gidansu haɗe da kashi Wayar.
Be ɗauki lokaci me tsayi ba ya ƙarasu inda ana buɗe masa gate ko gama dai dai ta perkin beyi ba ya fito ya nufi cikin gidan.
"Hajiya dama inaso na faɗa miki Wani abu....?"
Hannatu ta faɗa dai dai da Shiguwar Balarabe Wanda kuwa ya zuba Mata idano yana Son jin abinda zata faɗa.
"ina jinki Hannatu faɗamin!"
"Dama!dama jiya naji Matar Alhaji ƙarmi tana Waya tana faɗin a Sama mata jirgi,Lokacin da kika ce na kaimata Abinci Ɗakinta,Sai kuma Ɗazu kafin a tafi kai Lefe na ganta da Wani ta ƙofar baya Suna Magana amma bansan Waye ba".
Hannatu ta faɗa tana ƙasa da kanta.
"innalilahi'wainnailaihirrajiuun"Ammy ta faɗa, Wani gummi na keto mata tsabar tashin hankali.
"Amma Hannatu meyasa baki faɗa ba tun Wuri? tunda kinsan ita ɗin ba lafiya ce da ita ba Wata ƙela ma mutanen kanta ne ganin ana neman fin ƙarfinsu Suka Sata ta bar ƙasar".
Dan Allah Hajiya ku gafarceni bansan Sanadin hakan,bansan Sanadin hakan za'a iya Rasa Matar Alhaji ƙarami ba.Hannatu ta faɗa tana goge ƙwalar da ta zubu Mata.
Ɓalarabe neman guri yayi ya zauna,yana nazarin Maganar Me aikin Ammy,inda Gefe guda kuma yake tunanu lokuta da dama da yake wa Laila Maganar dena Waɗɗannan harkukin da irin Amsar da take bashi......Maganar Ammy ta dawo dashi daga tunanin da yake.
"Son baka ce kumai ba,Ni yanzu tashin hankalina Ma Yadda Zan Sanar da Iyayen yarinyar nan"
Ammy ta faɗa cikin Share Zufar da ta jiƙe Mata fuska duk da Sanyin E.c.n dake tashi a Falon......
Ɓangaren Asiya a Ranar da aka kai Lefe itama Balarabe ya danƙa Mata Saitin kayan faɗar Kishiyar da yayi Musu Wanda,yayi musu a ƙwatuna Shidda Masu azabar kyau ita da Laila Wanda na Laila, So Suna gidan Ammy kuwanensu haɗe da Makulin Sabuwar Mota Ƴar yayi, Faɗin irin dukiyar da aka Siyi aƙwatunan,da kayan dake ciki Ma ba'a Magana,
Dan ko Motar ma abar kallo ce.
Asiya Ana gama Shigo da kayan bayan ta gama yaƙe Wanda hausawa ke cewa yafi kuka ciwo ta kira Wayar Aminiyarta' ta Shaida Mata inda tace gata nan tahuwa.
Ko da ta iso nan Suka baje kayan inda Aminiya ta ringa fito da kumai dake a cikin a ƙwatunan,Wani ɓangare na Zuciyarta najin tsananin bakin ciki'amma Sai ta danne tana faɗin "amma ƙawata kaya kawai ya baki be baki kuɗi ba?"
"uhm ƙawata bari Wallahi kin gansu Sai Mota kawai da ya haɗan da ita"
Asiya ta faɗa tana yatsin fuska irin abunnan beyi mata daɗi ba.
"Kai yanzu duk kuɗinsa amma Wallahi na ɗauka yadda yake da kuɗi,kawai kuɗin Zai baki kiyi yadda kike So da Su!"Aminiya ta faɗa tana Maida kayan.
"Ai Wallahi ni kayan ma gaba ɗaya ƙara min ta kaici Suke,amma kinsan me?"
"Sai kin faɗa"Aminiya ta faɗa tana duban Asiya.
"Bazan Sai da kayan ba amma Mota kam Siyar da ƴar banza zanyi dan dulle Muje gurin nan,kuma bawai zan ƙyaleshi bane a'a Sai nasan yadda nayi na tatsi ko dubu ɗari biyar ce,Wannan Auren da yake ta rawar ƙafa akansa ɗaƙƙ" taja ƙwafa tana jin jina kai.
Cikin kecewa da dariya Aminiya tace"Hhhhhhhh'yanzu naji batu ƙawata karda ki Zauna kiyi Sanya Wallahi Wata Shigiya tazu ta ƙwace miki gida".
"Hmm dena faɗar haka kedai kiyi Shirin tafiya"Asiya ta faɗa,inda nan Suka cigaba da kitsa abubuwan da zasu aiwatar da zarar aikin boka ya fara.....
BALARABE
"Ammy ki kwantar da hankalinki ki dena Ɗaga Hankalinki ni zan Sanar da Mahaifin Laila, abinda ke faruwa'Nasan ze fahimceni'Nifa bana tunanin Laila............"
*ALLAH KA GAFARTA MANA* *ZUNUBAN MU AMEEN.*
*MAMAN NABEELA CE...✍️*