DANGINMU NE SILA

Sauyin rayuwa mai cike da ƙalubake kala²danginmu ne silar faruwar haka 008

by @jameey123

_*DANGINMU NE SILAR KOMAI*_


    Na


YAR MUTAN KANKIA❣️


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC.*


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM.*_

____________________


   _Free Page 8_


 *Wannan Book na kuɗi ne akan farashi mai sauki akan #500(two* 

*post in a day)via acct no 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello show ur evidence via O8160508316.*


_Domin magana da writer kai tsaye danna wannan blue link din_👇🏻***


*Ina jin dadin yanda kuka karbi labarin nan alkhairin Allah yakai gareku a duk inda kuke yar mutan kankia na alfahari da masoya a ko ina💓*


  

        *_COURT_*

          

"Yau 14/7/2022 Kotu zata cigaba da sauraran shari'ar da Nazima Abdulhamid Maikaba takawo karar mijin ta Nizamuddeen Abubakar Maikaba akan tana bukatar mijin ta ya SAKETA.wannan shine case dinmu ranka shidade."izinin zama Alkali yai mashi yakoma ya zaun yana cigaba da yan rubuce rubucen shi. 

Alkali ne yasa kallan Jama'ar Kotun a nutse sannan yace."Ko lauyan mai ƙara yana kusa."mikewa yayi yace."Yes my Lord,i'm Barr Mukhtar Musa Waziri,am here to support my client in person of Hajia Nazima Abdulhamid Maikaba thank you."ya koma ya zauna sannan Alkali ya sake cewa ko lauyan wanda ake kara yana kusa."?shima miƙewa yayi yace."Am here my Lord my name is Barr Nafi'u Hassan Nakowa nike kare wanda ake ƙara Alhaji Nizamuddeen Abubakar Maikaba thank you,my lord." shima ya koma ya zauna. 

  Alkali ne yaci gaba da magana cikin nazari da kwarewa yace."Court na bukatar ganin Barr Mukhtar Musa Waziri dan cigaba da gudanar da shari'a akan tsari."Sake mikewa lauyan Nazima yayi ya fito a gaban Kotu yace."Ya mai girma mai shari'a ina son Kotu tabani dama ingana da mai ƙara wato Hajia Nazima Abdulhamid Maikaba."Alkali yace."Anbaka dama Barr Mukhtar."thank you my Lord,Kotu nason taga Hajia Nazima."baki ɗaya Court din kowa ya koma kallan Nazima jiki mace ta taso harta shiga cikin wajen da ake tambaya ta tsaya."Hajia Nazima ko zaki iya faɗawa Kotu dalilin dayasa kike son mijinki ya sake ki."? "Eh, ina son mijina ya sakeni saboda bani son shi."murmushi Barr yayi yana girgiza kanshi yace."Saboda baki son shi,shiyasa kike bukatar saki."?Sake cewa tayi."Kwarai kuwa Barr banjin kaunar shi araina."jinjina kai yayi yace."Gaskia ne saidai nasan kamar bazaki rasa wani dalili ba ko."?.."Saboda DANGINMU."banbarakwai yaji saukar maganar ta cikin dodon kunnen shi."Dangin ku."?ya sake tambayar ta yana jaddada maganar a saman labban sa."Eh Barrister."Gaskiya ne."a hankali ta juya ya maida kallan sa ga Alqali yace."My Lord,kodaban tsawai ta tambaya ga mai ƙara, zanso wannan kotu mai alfarma tabani dama ingana da wanda ake ƙara." Alkali yasake cewa."Go ahead Barr Waziri."ko Dr Nizam na kusa."? A sanyaye ya mike ya iso bakin Kotu ya tsaya a wajen tambaya yana facing din matar shi banda kallan ta ba abinda yakeyi Barr Mukhtar yace."Doctor Nizam,ina fatan kaji abinda matar ka ke buƙata a wajen ka mi zakace akan hakan."? Wani irin kallan tsana ya watsa mashi yace."Ba abinda bazan ce Barrister,abinda nasani nidai bazan iya sakin matata ba."cikeda mamaki yake kallan Nizam yace."Ko saboda me."?murmushin takaici yayi yana kallan Barrister yace."Saboda ina son ta." gyaɗa kai Barrister yayi ya yasake cewa."Inaga yanzun kaji tace bata son ka mizai hana bazaka sauwake mata ba."? Wani irin kallan tsana ya aikawa Barr Waziri sannan yace."Kamar yanda na faɗa duk ƙiyayyar da Nazima zatai mani ta banza ce saboda nasan taba sona,kuma ko yanzun tana sona dan haka mizaisa in saki matata."Wani irin kallo Barrister ya aikama Nizam yace. "Dr Nizam idan na fahimcika kaƙi sakin Nazima ne kawai saboda kana da wani mugun nufi akanta, shiyasa kaƙi sakin ta."da sauri Barr Nafi'u yace. "Objection my lord,yana da kyau abokin aikina ya daina jingina munanan kalamai akan wanda ake ƙara,sabod baisan abinda ke cikin zuciyar shi ba."ka kiyaye Barr Mukhtar.Thank you my lord."Brr Nafi'u yace ya zauna,sannan Barr Mukhtar yaci gaba da cewa."Dr Nizam ko zaka iya bani ɗan taƙaitaccen bayani akan zaman dakayi da matar ka."? cikeda tausayin kanshi yace."Nayi zama na mutunci da amana da matata,tana sona ina sonta tun lokacin da na auri Nazima har zuwa yanzun ban taɓa ganin wani abun ƙi daga gareta ba asalima kullin ƙoƙari takeyi taga ta bani kulawa,kowane lokaci tana kokarin karemin daraja ta sannan ta rikemin mutuncin ta,kullun kokari take ta girmama iyayena da DANGINA bata sakaki da dukiya ta kowa ne lokaci tana kulaman da komai nawa,a gaskia Nazima ta cika ƴar halak tako ina matata bata rageni da komai ba,bata da wani buri sai taga tafaran tamin sannan tana ƙoƙari wajen bawa ɗana tarbiya, yanzun haka maganar da nikeyi Barrister ba abinda zan iya cewa saidai ince Allah yai mata albarka."da mamaki yake kallan irin karfin hali na Nizam yace."A haka bayan duk wannan alkhairan nata sun tashi a banza miyasa kake yaba mata."?Barrister kenan mai ɗaki shiyasan inda yake masa yoyo nidai abinda nasano Nazima tagama man komai a rayuwa kuma kullin kara son ta nike ina mata so na haƙiƙa Barister wannan kaɗan ne daga cikin zaman da nayi da matata tun auren mu."duk wanda ke cikin Kotun nan tunda ga yan gari har zuwa dangin su saida mamaki ya kama su,kowa da abinda yake sakawa a zuciya,duk irin wannan soyayar dake tsakanin su amman take neman saki a wajen mijin ta anya Nazima bata da taɓin hankali kuwa?idan har lafiyar ta qalau,ta zama cikakkar butulu.cikin kankanin lokaci yan gungunai suka fara tashi a cikin kotun Alkali ya dakatar dasu ta hanyar magana sannan kowa yai shiru Barr Mukhtar yace."Naji abinda kace,amma kasani babu yanda za'ayi ace kana kyautata ma matar ka kamar yanda kake ikirari kuma har zata bukaci takardar saki daga gareka,saidai idan akasin hakan kake mata Dr Nizam,nasan dai ba yanda za'ayi ace miji na kyautatama matar shi hakan tace ya sake ta sam hakan ba mai yuyuwa bane dagani wannan labarin da kabada labarin ƙanzan kuregene saboda kasan bazaka iya gamsar da Kotu ba,akan son da kake iƙirarin kanai ma Nazima ba."Objection my Lord ina son Kotu takara jan hankalin abokin aikina ya daina karyata wanda ake ƙara,dan kawai ya faɗi abuida ya sani wannan kamar karya doka ne sannan yana nuna mashi hanyar da zai ƙirƙiri ƙarya ga barin gaskia nagode ya mai girma mai shari'a."Korafi bai karɓu ba Barr Nafi'u,kabar abokin aikin ka yayi aikin shi."komawa yayi ya zauna.Murmushi Barr Mukhtar yayi yace."thank you my lord,cigaba da cewa yayi."Doctor Nizam kace Dangin ku me kake nufi da haka?Sannan ka tabbatar da, ba abinda akema matar ka da har take neman saki a wajen ka."? 

  Iska mai zafi Nizambya fesar yace."A iya zaman da nayi da matata,bata taɓa zuwa ta kawo karar yan uwana ba har zuwa dangi baki ɗaya,wannan dalilin yasa nace ba abinda naima matata,sannan maganar *DANGINMU* da kaji na faɗa dole ince haka duba da yanda nike nida Nazima asalin mu ɗaya tunda kanwa tace."Murmushi Barrister yayi yace."Nizam kenan, kanwar ka fa kace?taya akai ta zama kanwar ka."?..."mahaifin ta kanin mahaifina ne,uwa ɗaya uba ɗaya suke,sannan mahaifiyar ta kanwar mahaifiya tace uban su ɗaya,wannan shine dangantaka ta da matata."

Kallan kallo akema juna tsakanin ƴan Kotu,mamaki ya cika ransu kowa alama'rin ya daure masu kai musamman yanda ake gudanar da sarƙarƙiyar shari'ar da kowa ya rasa bakin zaren ta.A wajen Barr Mukhtar kuwa tunda Nizam ya gama bashi amsa ya rasa mizaice mashi saidai abinda ya ɗaure mashi kai miyasa Nazima take son saki a wajen shi,da alama sunyi zaman soyayya da mijin ta! kafin hali yayi yace."Zaka iya zama Dr Nizam kafin insake waiwayar ka."jiki a matukar sanyaye ya koma ya zauna yana mamakin yanda Nazima take nuna ƙiyaya akan shi,sai kallan ta yakeyi kamar wat bakuwa kullun sabuwar abu take koma mashi har yanzun gani yake kamar a mafarki,a fakaice take satar kallan shi karaf idon su ya sarke dana juna wani irin bugu kurjin ta yayi batasan sanda ta sauke nata kan kasa ba,shiko girgiza kai yayi duk da haka ji yake kamar ana ƙara rura wutar so da kaunar ta,a cikin zuciyar shi. 

"Hajia Nazima kinji abinda mijin ki ya faɗa tun daga dangantakar ku har zuwa auren ku sannan yace kuna son junan ku,ko abinda ya faɗa haka ne,kina son shi."?a hankali ta soke kanta kasa tanajin tambayar da Barrister yai mata a wani sashen na zuciyar ta tanajin nauyi da kunyar abinda take aikatawa saidai tanaji bata da wani zabi daya wuce hakan a hankali ta dago kanta cikin sanyin jiki ta kalli Barrister,kowa ya gama kasa kunnuwa dan yaji ta bakin Nazima Shiki Nizam ko kauda ido yakasayi kamar yasamu tv haka yake aikin kallan fuskar Nazima,ga faɗuwar gaba data ɗarsu a ranshi ba abinda yakeji idan kana kusa dashi zaka iya jin yanda numfashin shi ya sauya a lokaci."inalillah...."abinda yake maimaitawa kenan

saida Barr Mukhtar ya sake jaddadama Nazima tambayar da yai mata sannan tace."Gaskiya ne Barrister,idan nace ban son mijina nayi ƙarya naso Ya Nizam kuma ya rike nisa amana mutun ne mai karamci,amma daga baya shine mutumin da nafi tsana a duniya kuma mafi munin kalma agareni,banji zan iya furta kalmar so akan sa,na roƙeku ku fahimci yanda na tsani Ya Nizam banji zan kauna ce shi dan girman Allah Ya mai girma mai shari'a,kasa mijina Nizamuddeen Abubakar Maikaba ya SAKE NI,dan bazan iya zaman aure da shi ba."ta karashe maganar tana rushewa da kuka mai tsuma zuciya,shi kanshi Nizam baki ɗaya kanshi ya juye banda juwa ba abinda yakeji na ɗibar shi dan komai bishi bishi yake ganin shi,baki ɗaya kotun juya mashi takeyi,banda kalaman Nazima ba abinda ke mashi yawo a cikin kwakwalwa.Alkali ne ya buga desk yace."Malama Nazima Kotu ba wajen kuka bane,ra'ayin ki kawai muke bukatar ji,fatan zaki kiyaye gaba."Jinjina kanta tayi tana rufe bakin ta har ynzun tears dinta basu daina sauka ba saman fuskar ta."Barr Mukhtar ko akwai wasu tambayoyin da zaka kara yi mata."?Cikeda ƙosawa yace."Aaa my lord saidai ina neman alfarma wajen ka,ka ƙara man lokaci dan neman karin haske akan wannan shari'ar."Jinjina kai Alqali yayi yana ƴan rubuce rubucen shi yace."Anbaka dama Barrister Mukhtar."godiya nike my lord."ya koma ya zauna bayan umurni da kotu taba Nazima dan ta zauna itama.Alkali ne yaci gaba da magana yace."Duba da yanda wannan Kotun mai alfarma taji hujjojin lauyan mai ƙara da yanda ya tattauna da mai ƙara da kuma wanda ake ƙara,wannan kotu ta tafi hutun minti talatin asha ruwa kafin ta dawo taci gaba da zama a karo na ukku."buga guduma Alkali yayi sannan ya mike kowa ya mike ya fita kowa ya kama gaban shi,kowa na faɗin albarka cin bakin shi musamman ma yan Maikaba Family kuma sunje da yawa Kotun wasu daga cikin su na tsinar Nazima da yawa daga cikin su na ganin gazawar Nizam da yaƙi sakin ta,da haka suka fita suma yan gari na tofa nasu albarka cin bakin, cousin din Nizam yazo ya kama shi suka fita yana bashi kwantar mashi da hankali,danko Hajia Zaituna Buhari takaicin ɗanta ya gama kamata shiyasa ma ana tafiya hutu tai tafiyar ta gida rai ɓace itako Nazima ita da kannen ta su suka fito danko kowa jiki mace,tana ganin halin da aka wuce da Ya Nizam saida gaban ta ya fadi duk ta rasa sukuni a cikin zuciyar ta ga wani irin faduwar gaba mai tsanani ya addabe ta Wani bangare na zuciyar tsantsar tausayin sa ya kamata....... 

_(Lallai kam Nazima kefa kikace baki son mijin ki mene naki da zaki damu da halin daya shiga nasa ko mutuwa zaiyi ba zaki damu ba😂koda yake bari nayi shiru,har yanzun bamu san dalilin dayasa kike neman saki a wajen mijin ki,muna gefe nida tawaga ta,mun zuba👀muga yanda zata kaya🤨let's go my fans🏃🏻‍♀)_



*Sdeendtm*

 I'm sell data to all Nigeria network


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I'm

 selling MTN data with this cheap price* 


*MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.

 *Validity 1 month* 


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.* 

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp ***

_____________

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_***_



 _Yar Mutan Kankia ce❣️_ 



Share

Pls