Rumanah (Zabin Iyaye)

Last page

by @shooly84

...Rumanah🕊️

 (Zabin Iyaye)



©️ Aisha Machika



*last page*


*_Daman short story ne_*🙄



Jin jiri yana niyyar kwasata yasa nayi saurin dafe bango, hakan ya fargar da su ina tsaye a wajen, muna haÉ—a ido da Jamila ta saki murmushi tana faÉ—in amarya Rumanah ashe kin dawo? Maraba lale ya kika baro su Baba da Iyalle, kema ya kika iso da fatan komai lafiya? 


Ban bata amsa ba idona da hankalina gaba ɗaya suna kan fuskar Saraki ina kallonshi, shi kuma kamar baisan da wanzuwata a wajen ba yaƙi yarda ya kalleni sai cewa ya yi Wifey muje mana ki samu ki huta, ina dafe da bango suka wuce ni zuwa ɗakin Jamila.


Da bin bango na shige ɗakina na samu na kai bayana kan katifar gado, zuciyata sai wani irin harbawa take da sauri, mamaki ne danƙare cikin zuciyata, shin me ya dawo da Jamila gidan nan harda tsohon ciki? Ko dama Saraki ba sakinta ya yi ba? Ko kuma zuwa yayi ya dawo da ita,?


Tambayoyin dake ciki zuciyata kenan wanda babu mai bani amsa sai su ɗin, wannan dare dai da ƙyar na runtsa da tunanika kala-kala, sam kuma Saraki bai shigo ba koda zuwa ganin yaran shi ne, sai washe gari wajen ƙarfe goma na safe ya shigo, cikin shirin shi na fita ya shigo.


Bayan sallamar da yayi na amsa ciki-ciki ba wanda ya sake ma wani magana, shi dai su Al'amin na ganin ya shigo suka ruga inda yake ya ɗaukesu gaba ɗaya ya rungume yana sumbata da tambayarsu ya ya suka kwana, suna ta mai surutun yanzu sun dawo nan da zama ne yana basu amsar eh, suna tare da Mummy da Daddy yanzu, ya gama masu wasa yace masu zai je aiki ya dawo anjima, hakan yasa suka ƙyaleshi suna mashi bye-bye.


Da kallon mamaki na bisa harya fice, ban niyyar fita ko ina ba ranar, amma takaicin Saraki yasa na tashi na shirya na fice da yarana, ban ko bi takan ɗakin Jamila ba balle na leƙa, asibiti na wuce harda su Saudat ɗin.


Sai bayan la'asar na dawo gidan dan ko a asibitin kasa duba marasa lafiya nayi sosai, muna shigowa na iske Jamila zaune a falo da ƙatoton cikinta ga filat a gabanta da yankakken apple tana ci tana kallo, muna shigowa naga su Al'amin sun saki hannuna sun ruga inda take suna faɗin Aunty, nayi galala ina kallon ikon Allah.


Gaba ɗaya kan jikinta suka kwanta tana shafar kansu cikin tsananin farin ciki da gani sun shaƙu da ita, nayi tsaye daga bakin ƙofar ina kallonsu ina mamakin yaushe suka yi wannan sabon da ita, ko Saraki inya ɗaukesu nan ya kawo mata su dama?


Kinyi tsaye Rumanah daga ƙofa...ta faɗin idonta a kaina tana murmushi, nima sai na wayance na yi ɗan murmushin yaƙe, ina ida shigowa cikin ɗan basarwa na ce kina hutawa ne haka, wallahi ko zaman ɗakin ya isheni danma ina jin motsin Larai daga kitchen, tunda naji gidan shiru nasan kun fita har yaran.


Wallahi ko na leƙa asibiti ne, nace mata haka ina nufar hanyar ɗakina da cewa bari na watsa ruwa a gajiye nake, ban jira cewarta ba na shige.


Bayan kwana biyu na kasa haƙuri da Saraki ya shigo ganin yaranshi, na daure nai mashi maganar Jamila, da farko ko kallona bai yi kamar ma baiji ba dan harya kama hanyar barin ɗaki sai kuma ya juyo ya ƙura man ido na ɗan lokaci kafin ya juyo ya dawo har inda nake tsaye, cikin wani kallon raini yace, da dai banyi niyyar ce maki komai ba amma tunda kin tambaya bari na baki amsa.


Da farko dai dama can kinsan Jamila matata ce ta fari, uwar gida ko?, toh har gobe haka ne domin igiyar aurenta bata taba girgiɗi ba, taje dai gida kamar yarda kika sani, taje ta huta ta koyo tattali da hakali da kuma iya kula da miji, da lokacin dana ɗibar mata ya yi naje na dawo da matata domin jin labarin cikin jikinta, dan ina son abuna ina sonta kuma, a yanzu ma sai ince maki babu macen da nikejinta a jikina sama da ita, domin tasha wahala kan so da ƙaunata, tunda ta fara sona bata taba hutawa ba da gaya man tana sona.


Dama kuma masu iya magana sunce kaso mai sonka shi ne so, ba son maso wani ba ƙoshin wahala, yana faɗin haka ya juya ya fice ya barni satata ina binshi da kallo, kafin in farga kawai naji hawaye na wanke mun fuska, dan Saraki bai taba kallon tsabar idona ba yaci mun fuska irin na yau ba.




******



Wajen wata ɗaya kenan da dawowata gidan Saraki amma bata canza zani ba, tun ina ɗaure-ɗaure harna yarda makaman yaƙin ganin bana gaban Saraki, bai taba yarda magana ta haɗamu sai dole, gashi tunda na dawo bai taba man magana kwana ba dan ina jin ma bani da girki a gidan, bashi da aiki tunda na dawo sai tattalin Jamila da cikin jikinta, kuma baya shayi ko kunyar idona dan wai ina wajen bai hanashi abinda yayi niyya, a wannan lokaci na raina kaina, a yanzu na tuna lokacin yana yayina ashe ba ƙarafin aiki Jamila tayi ba na dauriya da ɗauke ido akanmu.


Yanzu da reshe ya juye da mujiya na É—anÉ—ani koÉ—ata, dan sai dai na shige É—aki nasha kuka na na wanke fuska na fito, yanzu na riga na haĆ™ura na kuma sadaĆ™ar cewa ina bala'in son Saraki, ina kuma tsananin kishinshi kamar me, nayi dana sani, nayi nadama kamar me, wani lokacin har zama nake ina mamakin anya wannan Sarakin dana sani ne mai so da Ć™aunata da tattalina, shi ne Sarakin dake zama yana man kuka kan soyayyata? 


Lallai rayuwa abun tsoro ce, ka guji shantakewa cikinta, idan tana yayinka ka rinƙa ganin kamar ba zata canza ba, lokaci ɗaya take juyin ɗanwake da mutum, ana irin wannan zaman ne aka wayi gari naƙuda ta kama Jamila, gaba ɗayanmu muka tafi asibiti ni da Sarakin daga baya na dawo saboda yara da muka bar ma Larai, Jamila tasha wahala sai dai kuma duk da haka bata haihu ba dan haka akayi mata aiki aka fiddo mata kyakkyawan yaro mai kama da Saraki sak.


Kadaran kadahan na tsaya tsakani da Allah nayi abubuwan da suka dace amatsayina na abokiyar zamanta, har tayi kwanakin da aka sallomota suka dawo gida da wata Ć´ar dattijowa daga gidansu domin kula da ita, komawa nayi gefe ina kallon bidirin da Saraki yake kan wannan haihuwa kamar ita ce haihuwarshi ta fari, ya kasa zaune ya kasa tsaye sai hidima yake da aljihunshi da kuma lafiyarshi.


Gaggarimin suna aka yi na gani na faÉ—a, dan tun daga dangin Jamila har na Saraki na nesa dana kusa duk an hallara, anci ansha anyi rabon abubuwa masu yawa, ni kaina na kashe kuÉ—ina wajen yin wasu gudunmuwa da siyayyar jariri, akayi komai aka gama cikin son barka bayan sati biyu da haihuwa kenan.


Komai ya natsu ya lafa maijego taci gaba da jinyar jikinta da kuma shayar da Alyas'ah sunan babyn kenan tare da Ć´ar dattijowa mai kulawa da ita.


Gida ya koma yarda yake daga mu sai mu sai ƙarin baby, muka ci gaba da irin rayuwar da mukeyi kafin haihuwar, kowa ya ci gaba dayin harkokin gabanshi kamar koda yaushe.



Tun ina sa ran Saraki zai sauko , zai daina fushi dani ko kuma ya soma kulani harna cire, dan gaba É—aya kamar ya mance zamanshi nake yi, irin dai zaman da sukayi da Jamila farkon aurensu shi yake yi dani nima a yanzu, wata biyu yanzu da dawowa naji ba zan iya ba, haĆ™uri na ya kai Ć™arshe, sam ba zan iya irin zaman da Jamila tayi da shi ba na sanya ma juna idanuwa kowa na harkar gabanshi, inaaaa! 


Da dai ban ɗanɗani kulawa da soyayyarshi ba ce sai in haƙura, yadda yake shagwabani da riritani da nuna man duk wata kalar kulawa a da, yanzu da babu ko ɗaya zuciyata ba zata iya jurewa ba gaskiya.


Dan haka a ayau na yanke shawarar tunkararshi naji makomar zamana gidanshi, ina jin shigowarshi da daddare bayan su Saudat sun jima da yin bacci na tashi na ɗora hijab kan ƴar guntuwar rigar baccita dana sanya da gayya, ga ƙamshi ta ko ina jikina yana yi, na fito falon babu kowa dan haka nayi saurin shigewa ɗakinshi.


Baya ciki dana shigan sai alamar motsi a toilet dan haka na zauna bakin gado, kusan minti goma sai gashi ya fito, muka haɗa ido yayi man kallon mamakin ganina ɗakinshi yau, bai ce man komai ba yaje yana shiryawa, ina zaune ina kallonshi harya gama shafanshi yabi jikinshi da turaruka masu ƙamshi sannan ya nufi inda ma'ajiyar kaya take domin ɗauko kayan bacci.


Na miƙe tsab na cire hijab ɗin na taka a sannu har inda yake, ina zuwa banyi wata-wata ba na rungumeshi ta baya, lokaci ɗaya yayi still inajin sauyawar bugun zuciyarshi a tafin hannuna, jin bai motsa ba nace cikin sanyin murya, kayi haƙuri da komai ma dan Allah, horon ya isa haka na gasu da yawa, na gane kurena ba zan sake ba da yardar Allah, ina matuƙar son mijina a yanzu wanda rayuwa ba zata yi daɗi ba sai tare da shi, kayi haƙuri ka yafe mani duk abubuwan dana jima ina yi maka su.


Jin nayi shiru ina shesshekar kuka yasa ya juyo muna fuskantar juna, kallon sama da Ć™asa ya yi mani, ya turani jikin katakon wadrop sannan ya Ć™ura man ido yana kallon yarda hawaye ke sauka a kumatuna, murya can Ć™asa yace yanzu me kike son nayi maki Rumanah eye? 


Ya miƙo hannu ya ɗago habata muna kallon juna, murmushi yake yana faɗin, yanzu so kike na haƙura mu koma zaman ma'aurata masu son juna da tausayi da mutantawa tare da soyayya mai ƙarfi kome? Na sauke ido ƙasa ina tura mashi baki, yasa yatsa yana zagaye lips ɗina ya gangaro wuyana sannan kan ƙirjina, ina jin saukar hannunshi kan ƙirjina na sauke wata irin ajiyar zuciya ina runtse ido da ƙarfi, ya kama murza boobs ɗin a hankali kafin ya duƙo kan dokin wuyana yana shinshina.


Tuni naji ƙafafuwana sun soma rawa, na dunƙule hannuwa na da ƙarfi, na sadakar na gama miƙa wuya babu abinda nake muraɗi sai kawai inji ya sureni zuwa kan gado dan ya kawar man da abinda ya taso mani da shi, ya kai bakinshi kan kunnena yana magana a hankali, dama nasan abinda ya kawoki kenan, wata da watanni ba'ayi maki service ba haƙurinki ya gaza, yaja baya da sauri ni kuma na buɗe ido a wahalce ina mashi kallon mamaki, murmushi yayi yana ɗaga kafaɗa, koma ɗakinki kawai ki kwanta Rumanah domin bana cikin mood ɗin yin wani abu da ke, yanzu ba abinda ke gabana ba kenan, lokacin da nike so ina marmarni sai kinga dama kike bani, toh nima yau bana ra'ayi.


Hijab ɗina ya ɗauko ya miƙo mani na amsa jikina a sanyaye ga hawaye na zuba, yace just go Rumanah, Allah ya bamu alkhairi.


******

Na girgiza na kuma tsorata da wulaƙancin da Saraki yayi mani lokacin dana kai kaina ɗakin shi, washe gari kuma ya yi mursisi kamar bashi bane yai man haka, yaci gaba da harkokinshi hankali kwance, nima dai tuni naja girmana na koma gefe nasa mashi ido, sai dai salon tsarin zaman namu na canza.


Dan kullum safiya idan mun haɗu zan gaishe shi da ina kwana ko ina wuni, in dawowa yayi daga wani waje zan mashi sannu da zuwa, abinci kuma ba kalar wanda bana yi na aje mashi duk abinda na zan zai faranta ranshi shi nake yi, na canza ƙawarai domin naci ɗamarar zaman aure irin na kowace mace a gidan aurenta.


Nayi shirin dawo da soyayyata da kuma darajata a idon Saraki ta halin ko yaya, tsakani na da Jamila zaman lafiya ake, duk da cewa kowacce cikin ni da ita muna kishin juna amma kowa ya barma zuciyarshi, sai dai kuma kowa na iya ƙoƙarinta dan ganin ta kyautata ma Saraki, dan tafi ɗayar kima da kuma daraja a idanuwanshi.


Yara ma bamu banbantasu kowa É—an kowa ne, tsakani da Allah kowa ke zama da Ć´ar'uwarta ba cuta ba cutarwa.


Ana saura kwana biyar Jamila tayi arba'in, muna zaune a falo mu duka kallo muke da fira tana gaya man inda zata yawon arba'in ina dariya da faÉ—in kina lissafin wata sati biyu kenan fa zakiyi wajen yawon, kina zaton Saraki zai barki ne?


Tana murmushi tace dan Allah kada ki maimaita a kunnenshi yace ya fasa, dan tuni mukayi maganar kuma ya barni, nace toh nayi shiru idan haka ne kam, haka mukaita fira cikin raha gwanin ban sha'awa.


Ana gobe zata yi arba'in ɗin kuwa yace ta shirya ya kaita gida tayi a can cikin ƴan uwa da dangi, dan haka tayi mani sallama suka fice harda yara aka barni ni kaɗai dan Larai ma jiya taje ƙauyensu dubo mahaifiyarta zata yi kwana biyu.


Ganin ba kowa gidan yasa na gama girkina da wuri nai wanka, ina cikin fesa turare naji ana kiran isha'i, na sanya wata riga tashan iska mai ƙaramin hannu a zuciyata ina tunanin ina Saraki ya tsaya haka ne da yara har yanzu basu dawo ba, na kabbara sallah nai raka'a ta farko na tashi na kawo ta biyu naji shigowar motar Saraki.


Har na idar banga su Al'amin sun shigo ba, sannan banji hayaniyarsu ba, na miƙe na fita falon banga kowa ba, har ɗakin Sarakin na buɗe na leƙa daga ƙofa shima ba kowa cikin ɗakin, wata ƙila yana toilet, dan haka na rufo mashi ƙofa na koma ɗaƙi.


Ina shiga naga wayata na haske, na É—auka dau-dai lokacin wani kiran ya sake shigowa, Khalipha ne yake kira, na É—aga tun kafin in magana naji hayaniyar su Al'amin daga can cikin wayar, murmushi nayi nace nan ya kawo maka su ashe?


Ina fa Rumanah, sun de biyo shi ne suka maĆ™ale wai nan zasu kwana, nace lallai kuÉ—an riĆ™esu kwana biyu dan Allah nima na huta, mukasa dariya...jin sallama yasa na juya ina amsawa, ganin Saraki nayi daga Ć™ofa ba yabo ba fallasa yace zoki ban abinci, jin haka yasa Khalipha yace je kiji da mijinki sai da safe.


Nayi shiru bayan yanke wayar da mukayi ina mamaki Saraki, danni nama mance yaushe rabon da yayi mani magana haka, na aje tunanin gefe guda na fita, kan dinning din na iske shi zaune shima yana waya, jin yanayin wayar nasan da Jamila ne dan naji yana tambayar Alyas'ah ya daina kukan.


Na matsa na zuba mashi abincin na aje mai, sannan na matsa na zauna kan kujera cikin falon ina daƙilar wayata, dan bana ra'ayin kallo tv ma a kashe take, a ƙalla na kusan shafe awa zaune ina chatting da sisters ɗina da kuma Bilkisu, duk da cewa ita Bilkisun iskanci take mani dan tambaya take wai har yanzu ban ƙunso wani cikin bane sunji shiru.


Saraki tuni ya gama cin abinci sai dai bansan abinda ya tsayar dashi kan dinning ɗin ba, shima dai daƙilar wayar yake sai lokaci zuwa lokaci kuma yana amsa waya, banga tasowarshi ba sai ji nayi an warce wayar hannuna.


Na bishi da kallo, fita whatsapp ɗin yayi tare da kashe Data, sannan ya miƙo mani wayar, na miƙo hannu in amsa ya haɗa da hannun ya fisgoni na miƙe ba shiri sai gani kan ƙirjinshi, kafin in dai-daita naji ya sureni ya ɗaga sama, hanyar ɗakinshi ya nufa dani.


Tsakiyar gadonshi ya ajeni zaune, nikam tsabar mamaki da kaɗuwa sun hanani cewa komai, ya ɗauki remote ya ɗan ƙara ƙarfin Ac ya kashe wuta mai haske sai dim light, yana dawowa kwantawa yayi ya ɗora kanshi kan cinyata yana faɗin kallon na nawa ne wai ni Rumanah?


Ko baki taba ganin É—an kyakkyawan namiji bane sai yau? Ya É—ago yatsunshi biyu saitin fuskata yana faÉ—in daga yau sati biyu zamuyi cur muna amarci sabo, dan duk wasu watanni da kikai bamu tare sai na fanshe abuna dan bashi ne dama kika ci.


Danna lura ke a ganinki idanuwan dana sanya maki dan na gane tuban gaskiya kika yi ko akwai sauran daru kin zaci kyaleki nayi, No...No... Rumanah, so da ƙaunarki a cikin jinina suke, ba zan iya son ko wace mace ba irin son da nike maki, amma dole na ba zuciyata haƙuri na lallasheta na kuma takura kaina duk da irin azabtuwar da nike ciki na baki fili.


Rumanah dole na ƙaurace maki dan ki fahimci kina matuƙar sona, ki gane muhimmanci na ki kuma shiga taitayinki ki aje duk wasu hayaƙin saman kanki, masha Allah kuma duk nayi nasara hakan, na daɗe da fahimtar halin da kike ciki kawai na ƙyaleki ne kema kiji abinda nake ji.


Ya kamo hannuna É—aya ya É—ora saitin zuciyarshi, nan É—in Rumanah gaba É—aya taki ce sai kuma Ć´a'Ć´a na É—an sauran abinda kuka bari ne na tursasa zuciyata mallaka ma Jamila shi, nayi saurin kallonshi, yace Ć™awarai ko Rumanah Jamila ta cancanci ita ma na sota ko yaya ne na kula da ita, duk da cewa itama ba kanwar lasa bace amma tasha wahalar soyayyata.


Tun ranar dana kusanceta naji zuciyata ta amince da in amsheta a matsayin matata, shiyasa koda Mahaifinta ya zo da Baba Sarki suka buƙaci in saketa naƙi, na rubuta masu ina son matata amma dai bana son ta sani taje gida sai ta gane shayi ruwa ne zan zo na ɗauketa.


Rumanah tafiyarki gida da kuma bullowar ciki Jamila yasa naje muka dai-daita na dawo da ita, na É—an janye hannuna ina tura baki, nace ita kuma wacce kake kai su Saudat wajenta fa wacce zaka aura? 


Ya ƙyalƙyale da dariya yana miƙewa zaune, Rumanah kishi, ba wata wacce zan aura, all dis while dama nan gidan nake kawosu wajen Jamila, ni ku biyu kun isheni ina zan kai mata uku haka kawai ku saka man hawan jini, ya janyoni yana faɗin yanzu dai zo kiji gaya man bashin wata nawa zan soma karba yau, dan so nake nan da wasu watanni kije masu Baba Sarki da ciki tsoho zama da ƙyar tashi da ƙyar dan su yarda lalle da gaske Rumanah tana son Saraki.


Na hau kai mashi duka ina faɗin wallahi ban yarda ba bashin yau kawai zaka yi, haba yarinya ai ƙarya kike yarda na kwana biyun nan banjini tsundum ba kema kinsan kinzo hannu ne kawai, karki damu da kaina zan gashe maki jiki dan wallahi yau sai abinda hali yayi, harfa yara na kai ma Khalipha danma kada su takurani, kafin in sake magana naji lips ɗinshi kan nawa ya cafke yana masu wani irin tsotsa kafin ya fincike ƴar rigar shan iskan jikina.....





*_TAMMATULLAHI!, kura-kuren dake ciki Allah ya yafe mana, abubuwan amfanuwa kuma Allah yasa ayi amfanin dasu, godiya lodi-lodi sai mun sake haɗuwa a sabon littafina mai suna TOH! WAYE? in me kowa da komai ya ara mana rayuwar, taku AYSHA MACHIKA ni ke cewa ku huta lafiya_*🙏🏻🙏🏻🙏🏻