Chapter 7
Page 7___Sallama TAIMIYYAH tai tayi a falon babu amsa,hakan yasa ta sanya kanta cikin falon sosai tana raba idanu,zuciyanta na tariyo mata baya kaman basuyi dadalmaya a sashin ba,gashi yanzu shigowa ma tayi hira da ƴan uwanta ya gagareta,ba don bata so ba sai don yadda su ɗin suka juye suka maida ta tamkar mujiya a cikinsu,zuciyanta yai nauyi tana jin tasirin damuwan hakan da take dannewa can ƙasan ranta na taso mata,hanyan da zai sada ta da asalin main Kitchen ɗin su Umman ta nufa,don tana hasashen samun ta acan tunda har ta fito bata ji an kaiwa Iya abincin rana ba,watakil yau ɗin sunyi ranan girki ne kaman yadda suka saba duk ranan Friday sukan yi ranan gama abincin rana,sabida yawan aikin da ke ƙaruwa tunda shi ma Baba Sanin sai Weekend yake dawowa daga can Kano inda yake aiki,kaman yadda tai hasashe haka ya kasance,tana sanya kanta cikin Kitchen ɗin bakinta ɗauke da sallama,idanunta akan Umma da ke tsaye jikin Cabinet na Kitchen ɗin ya fara sauka,su Mero me aiki nata faman hidiman kammala abinci ana kwashe su a manyan kulas,TAIMIYYAH ta gaida su Mero tana cigaba da takawa zuwa inda Umma ke tsaye,wacce sarai taji shigowan TAIMIYYAN tana kuma jin gaisuwan da take ma su Mero amma bata juyo ta dube ta ba "Sannu da aiki Umma ina yini."
Cewan TAIMIYYAH lokacin da ta isa daf da Umman,sai lokacin Umma ta juyo ta zuba mata idanu,fuskanta a haɗe tana faman yatsina,ta amsa gaisuwan da faɗin "Lafiya." A taƙaice daga haka ta cigaba da rufe tray ɗin da tai raping Salad,ganin hakan yasa kai tsaye TAIMIYYAH ta aje ledan saƙon a saman Cabinet ɗin tana faɗin "Gashi inji Iya." Daga haka sai ta juyo don baro sashin baki ɗaya,su Mero na ce mata a gaida Iya,Umma ce tayi saurin dakatar da ita tana faɗin "Ke! zo nan ki ɗauki wancan kwandon abincin ki kai min dining ɗin falo ."
TAIMIYYAH ta waiwayo tare da sauke manyan idanunta akan ƙaton Basket ɗin,ta nufesa tana ɗauka ta cigaba da tafiya ahankali dafe da ƙafanta me laluran,ɗaya hannun riƙe da Basket ɗin da aka jere kulolin abinci ta fito zuwa falo,da Zuhura taci karo wacce ta fito daga ɓangaren ɗakunan baccin su,TAIMIYYAH ta ɗauke idanunta daga kanta tana wucewa inda aka aiketa,ta aje kwandon abincin tana shirin juyawa don ficewa daga sashin nasu,sai ga Umma ta baro Kitchen ɗin ta fito falon,idanunta akan TAIMIYYAH tana dubanta daga sama har ƙasa,takaici da tsanan TAIMIYYAN na sake kamata,musamman in ta tuna yadda Sadeeq ya iya duban tsakiyan idanunta ya sanar da ita wai wannan musakan dake gabanta yake so,kuma son ma da aure hakan ba ƙaramin taɓa zuciyanta yake ba, "Koma ki zauna magana zanyi da ke shu'uma kina faman wani ƙus da kai munafuka."
Cewan Umma idanunta fes akan TAIMIYYAH,tuni TAIMIYYAH tayi saurin zama daga ƙasan tiles ɗin wajen,Umma kuma tayi zaune akan Kujeran da ke kusa da ita,yayin da Zuhura ma tayi zaune kusa da Umma domin bazata so tijaran da Umma zataiwa TAIMIYYAH akan Yayansu ya wuce taba,Umma ta soma faɗin "Wato ke dai wannan musakan baki jin magana ko,wai haka gurugu ke da taurin kai ne ni Zuwaira,yo inba taurin kai ba ke da nai miki iyaka da ɗana tun da daɗewa,shine kika cigaba da ribatan zuciyansa,har ya samu ƙwarin guiwan kallon idanuna yana sanar dani wai kece zaɓinsa,to bari kiji in gaya miki ni Zuwaira indai ni na kawo Sadeeq duniya,kuma Nono na ya tsotsa to na haramta soyayya a tsakaninku bare maganan aure ya shigo,in banda ma shi ɗin sakarai ne duk matan duniya ya rasa wacce zuciyansa zai so sai gurguwa musaka,me zaici da ke ya aure ki yace ya auri wa? Salon ya kunya tani ya zubda min aji acikin ƙawaye,to ahir ɗinki ba ki ba shi kije can ki jajibo gurgu irin ki da zaku fi dacewa da juna amma ba jinin shuwa ba,tashi ki bani waje saura kije ki sanar da Iyan ina dai-dai da kowa ne indai akanki ne shashasha kawai,sai shegen kyau da idanu kaman na jinnu."
Umma ta ƙare maganan cikin ɗaga murya,TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta tana zubda hawaye,tayi saurin ɗagowa tai musu kallo ɗaya tana miƙewa,tare da dafa ƙafanta ta fara takawa don fita daga falon,hatta jikinta rawa yake sabida ɓacin rai da wani irin ƙunci dake cin ranta,a haka ta fito daga sashin tana danne kukan da ke taho mata,aiko tana tabbatar da cewa ta fito daga Sashin ta samu bakin inda aka zagaye Flowers tayi zaune tana haɗe kanta da guiwa,ta saki kukan da take dannewa ko zata samu sauƙin ciwan da zuciyanta keyi,kuka take sosai irin wanda ke tasowa tun daga ƙasan zuciyan wanda ya jima yana haɗiyan baƙin cikin wani abu dake cin zuciyansa,sosai zuciyanta ke zafi kalaman Umma na sake ƙona zuciyan tamkar ana zuba tafasasshen ruwan zafi,ta rasa miye aibunta don ta kasance gurguwa,bata san miye laifinta don ta zamo a yadda Ubangiji yaso ta kasance ba,bata san meyasa Umma ta kasa gane cewa Sadeeq baya gabanta ba,ko batai mata gargaɗi akansa ba ita ɗin da kanta bazata taɓa bari zuciyanta tai gangancin faɗawa tarkonsa ba,meyasa Umma tai mata irin wannan tsanan ne? Sabida kawai ta kasance gurguwa me lalura ne ,ko kuwa akwai wani dalilinta ne na ƙinta da take ɓoyewa a ranta? Waɗannan tarin tambayoyin sune suka cigaba da cika kwanyan TAIMIYYAH tana buƙatan amsan su,kuka tayi sosai tana sauke ajiyan zuciya akai-akai,har lokacin kanta na kife cikin guiwoyinta,sam bata ji tahowan mutum inda take ba sai da hancinta ya fara shaqo mata qamshin turaren BENTLEY,sannan tayi saurin ɗago manyan idanunta waɗanda zuwa lokacin suka rine daga farinsu su ka koma jajur sabida kukan da ta sha,bata sauke idanun a ko'ina ba sai akan kyakykyawan fuskansa,hakan yasa tayi saurin sauke kanta ta maida shi inda yake tun farko,wasu hawayen na sake ɓalle mata kaman ana sake ingizo su,qamshin turaren BENTLEY da ya sake ƙarfi a cikin hancinta ya tabbatar mata Yah Sadeeq ya ƙariso daf da ita kenan,kafin tayi wani motsi sai jin saukan hannayen shi tayi a jikinta yana me ɗago fuskanta,cikin wani irin murya yake faɗin "Subhanallah! Kuka Zaynab me akai miki daga ina kike?" Duk ya furta mata tambayoyin har lokacin yana riƙe da fuskanta a tafukan hannayensa,zuwa lokacin tuni dama ya rage tsawonsa yana tsugunne gabanta ne,memakon TAIMIYYAH ta bashi amsa sai kawai takai hannunta tana cire nasa daya riƙe face ɗinta,cikin muryan kuka take faɗin "Babu komi Yah Sadeeq sannu da zuwa."
"Babu komi ne zan sameki anan kina kuka haka Zaynab,common sanar dani me akai miki kuma ke da waye?"
Cewan Sadeeq yana sake sanya idanunsa cikin nata,hakan yasa ta lumshe nata idanun tana jin wani irin ƙunci na sake mamaye zuciyanta,sam ba tayi farin ciki da wannan arangaman da sukai da shi ba,ta sani matuƙar bata ba shi amsan da zai gamsar da shi ba,zasu yi ta zama ne anan har sai wani yazo ya gansu yaje ya faɗiwa Umman,hakan yasa ta furta "Ni babu abinda ya haɗani da kowa na zo fitowa ne kawai daga part ɗinku tsautsayi ya ɗebeni na faɗi,shine naji zafi sosai dama kuma kaina na ciwo,amma yanzu bari in ƙarisa insha magani."
Yadda ta ƙare maganan cikin rauni da sanyin muryan daya motsa zuciyansa,ya bashi tabbacin daga wajen Umman sa matsalan yake,baya shakkan cewa tayi mata halin nata da ta saba,TAIMIYYAH bazata faɗi masa gaskiya bane kawai,hakan yasa shi zuba mata ido kafin ya furta "Kiyi haƙury Zaynab komi me wucewa ne,watarana Umma da kanta zatai nadaman irin halayyan da take nuna miki,bana so ko kaɗan ki dinga sanya damuwa a zuciyanki,yanzu tashi ki koma wajen Iya zan shigo zuwa anjima,ina fata kinyi min girkin da nace?"
Kai kawai TAIMIYYAH ta gyaɗa masa,tana miƙewa tsaye,yayi saurin riƙo hannunta ɗaya har ta tsayu da kyau,kafin ta dafa ƙafanta don fara tafiya ya riƙe mata ɗaya hannun,ta ɗago manyan idanunta ta sauke akansa tana son zame hannunta daga nasa amma kallon da ya jefeta dashi yasa ta barinsa,a haka suke takawa har zuwa ƙofan shiga Sasan Iya,sannan ya sake hannunta ta shige ciki shi kuma ya juya zuwa part ɗinsu,zuciyansa na matuƙar masa ɗaci da irin halayyan mahaifiyansa,yana jiye mata ranan da ubangiji zai nuna mata ikonsa akan nata jinin watakila daga lokacin ne zata gane ubangiji ke yin yadda yaso da bawa,ya kuma halicceshi ta duk irin yadda yaso bawan ya kasance,ko kaɗan bai taɓa ganin aibun nakasan TAIMIYYAH ba,sai ma dai a kullum sake ganin irin baiwan da Allah yai mata yake, wanda ke fitowa a hankali don kaf tsakanin age mate ɗinta su Zuhura tafi so komi,tafi u Brain na karatu boko da islamiya,ta fi su iya kula da kanta da tsaftan jiki da iya girki,akwai ta da nutsuwa da kamun kai da kuma iya riƙe mutuncinta na ƴa mace,wanda duk su ba'a ba su wannan baiwan ba,shiyasa a kullum shi baya hango wata nakasa daga TAIMIYYAH sai tarin abubuwan da ta mallaka wanda ba kowace cikakkiyar me lafiyan ƙafafun aka baiwa wannan baiwan ba,amma ya rasa dalilin da Umma ta ɗauki karan tsana ta ɗaurawa TAIMIYYAH,tare da shan alwashin tsine masa idan har ya dage sai TAIMIYYAH yake so,har ya isa ɓangarensa zuciyansa bata bar masa bitan irin cin mutuncin da Umman tai masa ba alokacin da ya tare ta da maganan TAIMIYYAH sati ɗaya da suka wuce,yasa mukulli yana buɗe ƙofan shigewa ɗakinsa kenan wayansa ya fara ringing,ya dakata daga buɗe ɗakin yana zaro wayan daga aljihun gaban rigansa,ganin sunan My Mum da yayi yasa shi ɗaga kiran kai tsaye,daga ɓangaren Umman bayan ta amsa gaisuwansa tambayansa take ya iso ne? Ya bata tabbacin gashi ma acikin gidan yana ɓangarensa ne zai watsa ruwa ya kintsa ne ya shigo ɓangaren nasu,hakan yasa ta katse kiran shi ma sai ya maida wayan aljihu yana buɗe ɗakin nasa ya shige ciki.
TAIMIYYAH ko tana shiga ciki ta fara addu'an Allah sa Iya bata falo,sai dai addu'an nata bai ci ba don tana sanya kanta cikin falon bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka sauka a fuskan Iya tayi saurin sauke kanta ƙasa tana cangala ƙafan da sauri don shigewa ɗakinta Iya ta kirayi sunanta da cewa "Zainabu zo nan." Cewan Iyan idanunta akan TAIMIYYAH wacce ta juyo ta fara takowa zuwa wajen da Iya ke zaune cikin kujera,ta kai ƙasa tana zama kusa da ƙafafun Iyan take faɗin "Iya gani."
Iya takai hannu ta ɗago fuskan TAIMIYYAH da take faman yin ƙasa da kai don kada Iyan ta gane tayi kuka,cikin wani irin murya a dake Iya ke faɗin "Me ya samu fuskanki,me sukai miki daga shiga kai saƙo maza sanar dani,kuma idan kikai min ƙarya saina saɓa miki don ban miki wannan koyin ba."
Iya ta ƙare maganan tana sake tsare TAIMIYYAH da kaifafan idanunta,hakan yasa TAIMIYYAH sake yin rau-rau da idanu tana me zayyane ma Iya yadda sukai da Umman,ta ƙare maganan da faɗin "Don Allah Iya kar kice zaki tanka mata,indai akan Yah Sadeeq ne ta kwantar da hankalinta ni ban taɓa son sa ba bakuma zan fara ba,amma ni bana so kice zaki je kice mata komi,lokaci yayi da zaki daina tankawa akan komi idan anmin Iya,tunda na kula hakan da kike kaman shi ke sake janyo min tsana a wajensu."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan cike da magiya,abinda ya karya zuciyan Iya kenan,ta dafa kanta tana faɗin "Naji bazan je ince mata komi ba,amma ke kuma ki daina ƙyalesu akan irin cin fuskan da suke miki,bance ki tanka Zuwaira ba amma su Zuhura duk wanda ya sake miki gorin halitta,kice musu idan suke halittan ɗan Adam don Allah su sauyaki daga yadda kike su mayar dake mara naƙasu,sannan ki daina bari suna ganin hawayenki,domin baka bari maƙiyinka ya gane lagon ta inda zai dinga saranka koda da kalamai marasa daɗi ne,ko kaɗan ki tsaida zuciyanki tayi dakewan da ko sauyin fuska zasu daina gani idan sun miki gorin nakasa,hakan zaisa su daina ci miki fuska,sannan ina so ki kwantar da hankalinki indai mijin aure ne wallahi sai sun sha mamakin irin mijin da Allah zai kawo miki,ai ba ita ke bayarwa ba don tace bazaki auri ɗan ta ba sai me? Wallahi ba don bana miki sha'awan rashin kwanciyan hankali ba da saina nunawa Zuwaira cewa daga ita har ɗanta zan iya iko da su,in kuma haɗa auren da take iƙirarin in tana raye bazai yiwu ba,sai dai nafi so Allah yai ikonsa da kansa domin ina da tabbacin zaifi ni iya hukuntata,domin huruminsa take shiga don shi ya halicceki ahakan,shi kuma yasan irin ajiyan da yai don haka ki cire duk wata damuwa a ranki,ko kaɗan kada kiji cewa zaki ji ƙuncin kasancewanki a hakan kinji ko?"
Iya ta ƙare magana tana shafa kan TAIMIYYAH wacce ta kwantar bisa ƙafafun Iyan,kalaman Iyan na shiga kunnuwanta da wani irin tasirin dake ratsa ilahirin zuciya da gangar jikinta,ta gyaɗa kai alamun gamsuwa da tarin kalaman Iyan,wacce itace gatanta da ta maye mata dukkanin guraben da uwa zata cikewa ƴar ta,a hankali ta cusa hannuwanta saman fuskanta tana share hawayen dake gudu,cikin sanyin murya take faɗin "Insha Allah Iya zanyi anfani da dukkanin abinda ki ka ce nagode Allah ya bar min ke Iya har ƙarshen numfashi na."
Iya da tausayin TAIMIYYAH ya gama cika zuciyanta,ta shafa kanta tana faɗin "Ameen Zainab,Allah yai miki albarka yasa ki cigaba da biyo halayyan TAIMIYYAH,ita kuma Allah ya cigaba da kai haske kabarinta,Allah ya nuna min aurenki da zuriyyan da zaki haifa kafin ƙasa ya rufe idanuna."
Ta ƙare maganan muryanta na rawa cike da raunin zuciya,domin a duk lokacin da ta tuna da mahaifiyan TAIMIYYAH me suna Zainab sai zuciyanta ya karye,domin bata taɓa ganin haƙurarriyan mace me tarin nutsuwa da hankali irin ta ba,ga baiwan kyau kaman ita tayi kanta wanda nagartanta da kyawawan ɗabi'unta suka janyo ake kiranta da TAIMIYYAH,kaman yadda labarawa basa sakawa ƴar su ko ɗansu suna TAIMIYYAH sai ya mallaki nagarta irin na Zainab ɗin,shiyasa a lokacin da aka haifi TAIMIYYAH ta sa aka saka mata suna Zainab ɗin kaman tasan uwar mutuwa zatai,bayan rasuwan Zainab ɗin sai Iya ta cigaba da kiran abinda ta bari da irin sunan da ake kiran Zainab ɗin dashi wato TAIMIYYAH,tana me fata Zainab ɗin ta gado halayya da nagartan uwarta,sai gashi ko TAIMIYYAH babu inda ta baro halayyan mahaifiyan nata,Iya ta sauke ajiyan zuciya tare da dawowa hayyacinta daga faɗawa duniyan tuna baya da ta tafi,muryan TAIMIYYAH me sanyi tamkar na uwar ta na ratsa kunnuwanta lokacin da TAIMIYYAN ke amsa addu'an da faɗin "Ameen Iya na,insha Allah bazaki rigani mutuwa bama tare zamu tafi ko zaki mutu."
Iya ta saki murmushin su na manya,tana sake jin ƙaunar TAIMIYYAN me tsanani yana cigaba da ratsa jinin jikinta,sai dai kafin tayi magana sallamansa da shigowan sa cikin falon yasa duk suka bishi da ido,sassanya qamshin nan nasa dai na turaren BENTLEY ya fara kara kaina cikin falon,Iya gaba ɗaya sai ta koma ta tamke fuska,tana amsa sallaman ya ƙariso cikin falon yana zama kujeran dake facing Iya,ya zame ya kwashi gaisuwa idanunsa fes akan qanwar tasa da har lokacin kanta ke saman guiwan Iya,ba yabo ba fallasa Iya ta amsa gaisuwansa sai ya maida dubansa gaba ɗaya akan TAIMIYYAH yana faɗin "Sis tashi ki bani abinci da yunwa na shigo garin nan."
Yadda ya ƙare maganan idanunsa akanta yasa Iya da itama ta tsare shi da ido zabga masa harara,tana riga TAIMIYYAH da faɗin "Kaji min rashin tausayi dai,a memakon ka tashi ka isa wajen cin abincin tana zamanta sai ka tashe ta wani kawo maka abinci kaman mara ƙafafu,to bazata tashi ba in bazaka isa wajen kaci ba ka koma wajen uwar ka marasa kunyan qanninka su zuba maka kaci."
Yadda Iya ta ƙare magana tana faman juya ido ita adole harara take watsawa Yah Sadeeq ɗin,yasa daga TAIMIYYAH har shi uban gayyan sakin dariya,kafin ko wanne ya maze kaman bashi ke dariyan ba,Sadeeq ɗin ya tashi yana nufan wajen cin abincin yana faɗin "Maida wuƙan ƴar tsohuwa amma dai a taimaka ta zo tai sarving ɗina please."
Iya ta ja tsaki tana faɗin "Ka dai ji dashi fitinanne,ke kuma da kike dariya saiki tashi ki zuba masa waya sani ma kina sane nan zaici abincin shiyasa kika dage sai kinyi girkin da kanki mitsuww!"
TAIMIYYAH da dariya ke cinta arai ganin Iya zata ɗago ta yasa ta haɗe fuska,cike da shagwaɓa take faɗin "Kai Iya inda haka ne da baki ga na zuba masa a kula daban ba,ni inama nasan zai wani dawo bare har inyi girki dashi."
"Oho dai ku kuka sani."
Cewan Iya tana taɓe baki ita ko TAIMIYYAH sai ta nufi wajen cin abincin ta fara sarving ɗinsa,har lokacin Hijab ne sanye ajikinta bata cire ba,plate ɗin ta tura gabansa tana dubansa,ganin yadda ya tsareta da mayen kallon da yake addabanta dashi yanzu yasa tayi saurin ɗauke kanta tana faman turo baki,sam ta tsani yawan kallo tun kafin ta girma haka,lemun Fruity Zoɓo da tai ta zuba masa cikin dogon glass cup ta tura gabansa,kafin ta miƙe tana faɗin "Yah Deeku ni zan shiga daga ciki ina da karatun hadda kasan gobe Saturday."
Bata jira cewan sa ba tai gaba abinta yabi bayanta da kallo,yana girgiza kansa kawai tare da jin wani abu na sake fisgansa zuwa gareta,sai dai zuwa yanzu ya fara ji ajikinsa dole ya koyi juriya akan danne duk wani zazzafan son ta dake ɗawainiya dashi,matuƙar yana son ta sami farin ciki,domin shi kansa yasan idan ya dage sai ya aureta alhali Ummansa tai mata irin wannnan tsanan,bazata taɓa samun kwanciyan hankali ba,tabbas kaman yadda TAIMIYYAN ta faɗi ne haƙura da juna shine kawai mafita su cigaba da zumunci tamkar yadda suka faro,a hankali yake cin abincin daɗin girkin na ratsa shi,tare da haifar masa da kasala da mutuwan jiki,domin wani yanayi ke bin jininsa yana yamutsawa,tabbas zaiyi rashi idan ya bar TAIMIYYAH ta suɓuce masa,ya lumshe idanunsa a lokacin da sanyin Zoɓon da ya zuƙa yabi maƙoshinsa,daɗin ya ratsa har tsakiyan kansa,sai ya buɗe idanunsa yana cigaba da cin abincin har ya kammala,ya goge bakinsa tare da tashi a wajen,cikin falon ya dawo har lokacin Iya na zaune ta maida hankalinta ga kallo,sai yai mata sallama ya fice daga Sasan baki ɗaya..........✍🏻
#Ɗansabo ce#