Chapter 8
Page 8_______Suhailah sai yamma sosai ta koma gida daga gidan Hajiya,bayan ta sha faɗa da nasihun Hajiyan haɗi da razanarwa,tuƙi take amma gaba ɗaya tunaninta na ga yadda zasu kwashe da A.Maleek ɗin idan har ta samu matsala,bata ji zuciyanta ko da wasa zata iya ɗaukan ganinsa da wata mace da sunan matarsa,har ta isa gidanta ranta a jagule yake,mayafinta kawai ta cire ta faɗa Kitchen,samun Ameena tayi tana aikin ɗaura abincin Dinner,Suhailah ta dubi Ameenan tana faɗin "Me kike shirin girkawa ne? ina ga yau kiyi abinda zaku ci ke da megadi,ni zan yi girkin da zamuci da Ogan."
Cike da mamakin Suhailan Ameena ta dube ta,tana risinar da kai alamun girmamawa take faɗin "Okey Mah ba damuwa,dama tuwan Semo ne zanyi sai Macaroni Salad sabida Oga."
"Bar shi kawai yanzu ki ciro min kaza kiyi marinating ɗinta ki mayar cikin freezer,sai ki gyara min kayan miya ki fere Dankali kaman guda 6,yanzu zan dawo in ɗaura girkin okey."
Cewan Suhailah tana barin Kitchen ɗin don amsa kiran Raudha da ke shigowa,sun daɗe suna magana kafin ta saka wayan a silent ta dawo Kitchen ɗin,da taimakon Ameena ta shirya lafiyayyan gashin Kazan da aka wadata shi da Irish gashin yai wani irin kyau,akai raping cikin foil paper tare da saka shi a kyakykyawan mazubi,sai haɗin Macaroni Salad da yaji liver da zallan tsokan kaza shima aciki,da kanta ta ɗauki ƙaton Tray ɗin da aka jera komi ta haura zuwa up stairs,bisa dining ɗin da ke falon saman ta aje ta wuce zuwa ɗakinsa,yana nan yadda ta gansa da safe,ta fara da kwashe kayan dake kan bed ta zuba a kwandon adana kayan wanki,sannu a hankali take gyaran ɗakin tana mita,jikinta ko'ina yana ansawa da gajiya hatta toilet ta daure tai masa kyakykyawan wanki,sai da ta ga komi ya yayi fes sannan ta fito ta nufi ɗakinta ta ɗakko abun zuba turaren wuta,ta zuba ta kunna tana kaiwa ɗakin ta turare ko'ina da ina,bisa sofan dake ɗakin ta zube tana maida numfashi a fili take faɗin "Wai Allah! Anya ko zan jure wannan bautan, gaskiya da kamar wuya zan dai ta lallaɓa ka har ka yadda asake samo me aikin da zata dinga gyaran ɗakinka Hubby."
Yadda take maganan can ƙasa cike da mita zaka ɗauka wanda ake yi dominsa yana ɗakin ne,ganin lokaci na sake tafiya yasa ta miƙewa ta fito daga ɗakin,ko da ta shiga nata ɗakin direct Bathroom ta nufa tayo wanka,ta fito ana kiran magriba amma sanin fana off yasa kai tsaye ta nufi wajen mirrow don tsara kwalliya,sosai ko ta fente face ɗinta da light make-up,domin ita ɗin gwanace a iya kwalliya da son ɗaukan hutuna tana posterwa a media kai ba kace matar aure bace,duk waɗannan halayyan ke sake haɗata faɗa da Maleek ɗin domin ya tsani hakan sosai amma ta kasa dainawa,sabida yadda qawaye ke zigata tana kuma samun Followers sosai a shafukan nata musamman a Instagram,Riga da Skat na wani haɗaɗɗan Voile laces ta saka wanda ɗinkin yai asalin zama ajikinta,tare da fidda shape ɗinta sosai,tayi anfani da sirirn sarƙan gwal ɗinta da ɗan kunni wanda suka sake haske kwalliyanta,hannunta warawarai ne guda biyu suma na gwal ne ta saka,nan da nan tai wani irin kyau tamkar wacce zata wani haɗaɗɗen Dinner Party,ita da kanta ta yaba kyawun da ta zuba sai fatan miskilin mijin nata ya yaba kawai take,zama tayi bayan ta gama wadata jikinta da turaren MISS DIOR banda daddaɗan Body Mist da tai anfani dashi,daga ciki sosai haɗaɗɗen humra ne na DOLCE tai using,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me saukar da tarin nutsuwa ga duk wanda ya shaqa,wayanta ta ɗauka ta hau online don rage lokaci,bayan tayi kiran layin Maleek ɗin har su biyu bai ɗaga ba.
A gajiye sosai ya shigo gidan misalin takwas da rabi na dare,lokacin har Suhailah ta gaji da zaman jiransa a sama ta sakko falon ƙasa,tana kallo a mamaken Smart TV dake manne jikin wani irin LUXURY TV Stand da ke falon,tunda hancinta ya shaƙo mata qamshin turaren RALPH LAUREN wanda yakan sirka da ɗayan turaren nasa na AMOUAGE tasan cewa shi ne ya shigo falon,kallo ɗaya yai mata ita da adonta ya ɗauke kai ya fara takawa zuwa hanyan da zai sada shi da Stairs ɗin da zai kaishi sama,ganin hakan da yayi yasa Suhailah tabbatar da akwai sauran ƙura kenan,Hajiya ta gama nata shi kuma yanzu zai hau nasa,cikin baiwa kanta ƙwarin guiwa ta bishi zuwa saman,samun sa tayi yana rage kayan jikinsa don shiga wanka,sai ta riga shi shiga bayin tana tara masa ruwan wankan cikin tube,abinda ta mance yaushe rabon da tayi ,shiyasa ko da ya shigo bai kalleta ba ya fara ƙarisa cire abinda ya rage a jikinsa,ganin hakan yasa ta juyawa ta ba shi waje,ya saki ƙaramin tsaki yana me jin wani haushinta na kamasa,domin shi mutum ne daya tsani ai masa abu bada zuciya ɗaya ba,ya riga ya gama sanin duk wannan tarairayan bame ɗaurewa bane ne,tana yi ne don ta sakko dashi da zaran ya fara sakin jiki zata sake komawa gidan jiya ne,shiyasa shi kuma ya shirya bata mamaki a wannan karon,lokacin da ya fito samunta yayi kwance bisa Sofa,ganin fitowansa yasa ta saurin aje wayan da ke hannunta ta nufesa,tana faɗin "My Hubby bari in taimaka maka da shafan please kar ka gwaleni,don Allah Maleek kayi haƙury wallahi zan canza dukkanin halayyan da baka so."
Har ta dasa aya bai tanka ba illa ma janye jikinsa da yayi daga gareta,ya fara shafa mansa ganin ta iso ta amsa man sai ya rabu da ita ta ƙarisa shafa masa,gaba ɗaya sai wani narke masa take tana komawa kalan tausayi,qamshinta gaba ɗaya ya gama cika hancinsa,yana taso masa da wani irin feelings akanta,yayi kewanta don rabonsa da gari sati biyu kenan sai a daren shekaran jiya ne ya dawo,amma rashin samun tarba me kyau yasa suka samu saɓanin da ko nemanta baiyi ba bare ya sauke nauyin da ya dawo dashi,sai dai ko kaɗan fuskansa ba asake yake ba,sam Suhailah ta kasa samun yadda take so,jallabiya ta ɗakko masa Milk Colour ya amsa ya saka,ta ɗauki turaren da ta fi son yai anfani dashi,wato AMOUAGE ta fesa masa tana me kwantar da kanta bisa jikinsa bayan ta aje kwalban turaren,ahankali ta kai hannunta zuwa bayansa ta rungumeshi sosai tana shaqan daddaɗan qamshin daya karaɗe ɗakin baki ɗaya, "I Luv u My Maleek." Ta furta cikin wani irin salon da ya motsa zuciyansa,hakan yasa ya zare ta daga jikinsa yana binta da wani shu'umin kallo,domin sosai ta taɓo duk wani feeling da ya danne akanta,har lokacin fuskansa a haɗe yake cikin muryansa me cike da ginshira da izza yake faɗin "Mu je ki bani abinci banci komi ba tun safe sai ruwan juice da nake ta sha."
Bai jira cewanta ba ya fara takawa don fita daga ɗakin,Suhailah ta rufa masa baya har suka fito zuwa dining ɗin,da kanta tai Sarving ɗinsu a plate ɗaya don itama bata ci komi ba ta tsaya jiransa,da farko da kansa ya fara cin abincin amma ganin ta shagwaɓe masa lallai sai ta ciyar dashi yasa ya sakar mata spoon ɗin,sai da ya nuna ya ƙoshi sannan ta maida hankali taci nata,shi ya fara barin wajen ya koma ɗaki don akwai abinda yake son aiwatarwa ta Computern sa,hakan yasa itama Suhailah komawa ɗakinta bayan ta kammala cin abincin,bata sake gigin zuwa garesa ba don ta gama ganesa idan yana wannan fisge-fisgen to gara itama ta ɗan dinga jan kanta bawai ta zaƙe ba,sai da agogo ya buga ƙarfe sha ɗaya sannan tayi shiri cikin wasu Nighties masu kyau,Rigan me transparent ce wanda ita da babu duk ɗaya ne,sai wandon wanda duka tsayinsa iya cinyanta ne,gaba ɗaya wani irin qamshi take fitarwa me motsa zuciya,wayanta ta ɗauka ta fito xuwa ɗakin Maleek ɗin,ga tsananin mamakinta har zuwa lokacin yana zaune bisa tsakiyan gadonsa,da Laptop a gabansa yana ta faman aiki,qamshinta da ya jiyo yasa shi ɗaga manyan idanunsa ya sauke akanta,ƙirjinsa yai wani irin motsawa nan take dukkanin sha'awansa ya gama tasowa,ya cigaba da kafe ƙirjinta da ke bayyane cikin Rigan da kallo babu ko ƙiftawa,har ta iso zuwa kan Bed ɗin tare da yin masauki kusa dashi sosai tamkar zata shige jikinsa,hakan yasa shi sauke ajiyan zuciya yana ji gaba ɗaya bazai iya cigaba da abinda yake ba,shiyasa yayi hanzarin kashe Computern yana janyota jikinsa gaba ɗaya ya rungumeta,Suhailah da ta tabbatar ya gama shiga tarkonta sai ta sake lafewa a jikinsa ta saki kukan kissa,cikin kukan take sake bashi haƙury akan ta tuba wallahi zata sauya ta koma yadda yake so,A.Maleek da yai nisa a aika mata da gigitattun Kisses tako'ina ya kai bakinsa ya haɗe da na ta alamun baya son surutu a wannan time ɗin,ai sai Suhailah ta fara maida martani don itama tayi missing ɗinsa sosai,don ma rashin tsarkin da take ciki dole zai takawa zalaman su birki,lokacin da Maleek ya fahimci bazai samu zuwa inda yafi muradi ba yaji babu daɗi amma da taimakonta ya samu gamsuwa,don ita ɗin ba baya bace wajen kula dashi awannan fannin,shiyasa ko yayi fishin indai aka zo nan ɗin baya ma sanin ya sauka sai komi ya lafa sannan zai cigaba da ɗauke kai da basarwa,a yanzu ɗin ma hakan ya kasance lokacin daya tabbatar ya samu gamsuwa,sai ya zareta daga jikinsa da ta kanainayesa ya nufi Bathroom don tsarkake kansa,ko da ya fito kallo ɗaya yaiwa Suhaila da tai ɗai-ɗai bisa Bed ɗin babu kaya a jikinta ya ɗauke kai,ya nufi wajen da Jallabiyansa yake ya zura yana kai manyan idanunsa ya dubi babban agogon bangon da ke ɗakin,lokacin time ke nuna 12:05am na dare,dole sai yasha ruwan zafi kafin ya kwanta hakan yasa ya nufi inda Suhailah take fuskansa a tamke kaman bashi ya gama mata kalamai da sambatu ba a ɗazu,ya tsare ta da manyan idanunsa yana faɗin "Suhailah tashi kije ki wanka ki zo ki haɗo min Shayi okey."
Ya ƙare maganan da janyota ya miƙar har ta sauka daga kan Bed ɗin,bata damu sam data nemi wani abu ba haka ta wucesa tik ɗinta ta nufi Toilet,ya bi bayanta da kallo yana wani lumshe idanunsa sabon feeling na fisgansa,sanin bazai samu abinda yake so ba har sai ta samu tsarki yasa shi danne komi,har ta fito bai sake yadda idanunsa sun sauka akanta ba,har sai da ya tabbar ta maida kaya a jikinta duk da dai babu maraba da babu wannan rigan nata,ficewa tayi tana faman zumɓure baki sam bata son takura,lokacin da ta kawo masa shayin sai ya dube ta yana faɗin "Sorry na manta bance miki i need some lemon aciki ba,jeki ɗakko min in matsa kaɗan."
Yayi maganan ne idanunsa fes akan face ɗinta,don haka akan idanunsa ta saki ƙaramin tsaki tana juyawa tai waje,ya girgiza kai ransa yana sosuwa,shi dama yasan da wuya Suhailah ta koma masa yadda yake so,duk rawan ƙafan da takeyi na yaudara ne da ɓacin ran da ta gani a wajen Hajiya,har ta kawo lemon sai faman cika take yai kaman baisan tana yi ba,yana gama shan shayinsa ya wanko baki yazo yai kwanciyansa ba tare da ya sake bi takan Suhailan ba,har bacci ya fara ɗaukansa ya jita cikin jikinsa,hakan yasa shi gyara kwanciyansa yana shigar da ita jikinsa sosai ya sake jan Duvet ya rufe su.
________
Ƙarfe 9am na safe TAIMIYYAH ta fito cikin shirin zuwa makarantan Hadda,sanye take da dogon Hijab da ya sauka ƙasa sai dai baya sharan ƙasa sabida laluran ƙafanta,sosai kalan Hijab ɗin da yake dark Brown yai mata kyau,hannunta Qur'ani ne Izu Sittin ta aje sa daga saman kujera ta nufi ɗakin Iya,a bakin gado ta samu Iya tana ƙarisa shiryawa alamun wanka ta fito,ta durƙusa ƙasa tana gaida Iyan,Iya ta amsa da fara'a tana faɗin "Har kin kintsa zaki wuce ɗin TAIMIYYAH,to maza dai ki karya kafin ki tafi,ki kuma shiga ki gaida Baban ku Sani tunda jiya ya shigo kinyi bacci,idan su waɗancen sun shirya sai ku wuce tare ma kawai."
Da "Tuh." Kawai TAIMIYYAH ta amsawa Iya,tana juyowa ta fito zuwa falon ta nufi wajen cin abincin su inda Ladi ta gama shirya komi,Kunun tsamiya ta zuba a Cup ta saka Sugar tana juyawa,kafin ta aje ta buɗe kulan da aka zuba soyayyan Doya me egg ajiki,ta ɗibi guda 4 ta zuba a plate ta fara ci ahankali tana shan kunun,lokacin da ta kammala sai ta goge baki bayan ta ɗan sha ruwa,ta ɗauki Qur'aninta ta fito ta nufi Part ɗin Baba Sani,tana shirin shiga shima Yah Sadeeq da ya taho daga ɓangarensa yana isowa don shiga Sashin nasu,tunda TAIMIYYAH ta jiyo qamshinsa ta waiwayo tana sauke manyan idanunta akansa,ta saki murmushi kaɗan lokacin da ya ƙariso inda take,suna jerawa da juna zuwa cikin gidan,bayan ya amsa gaisuwanta ne ya amshi Qur'anin hannunta ya riƙe mata,a haka suka ƙarisa zuwa cikin falon gidan,su Zuhura da Basmah ne da alamun tashin su kenan,ko wanka basuyi ba TAIMIYYAH ta dube su tana faɗin "Sannun ku dafatan mun tashi lafiya,Basmah baku shirya ba ashe da har ina cewa zamu wuce tare."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana ɗauke kai daga dubansu,ganin kallon da Zuhura tai mata wai don ma Yayan su na tsaye a wajen ne,Basmah ta taɓe baki tana faɗin "Ai kinsan mu Malamin mu bai cika zuwa akan time ba zaki iya wucewanki,ma biyo bayanki."
Daga haka suka haɗa baki wajen gaida Yah Sadeeq ɗin,wanda hankalinsa na kan danna waya sai dai yana jin duk abinda suke faɗi,ɗago idanunsa yayi lokacin da yake amsa gaisuwan nasu,ya sauke idanun akan Zuhura yana faɗin "Oya ku tashi kuje ku sanyo Hijab ko bakuyi wanka ba ku tafi haka,tunda ku ƴan banzan yara ne da bakwa son zuwa makaranta,na baku mintuna goma kowacce ta fito cikin shiri shashashai kawai."
Yadda ya ƙare maganan da tsawa yasa su miƙewa,suka wuce fuu zuwa ɗakinsu don cika umurninsa,shi kuma ya maida dubansa kan TAIMIYYAH yana faɗin "Mu je Baby mu gaida Baban kafin su kintsa."
TAIMIYYAH bata ce komi ba ta fara takawa zuwa hanyan da zai sada su da falon Baba Sanin,a tare suka shiga bakinsu ɗauke da sallama,Umma da ke zaune tana facing ƙofar shigowa falon,ta ɗago idanunta ta sauke akan su,xuciyanta na bugawa da wani irin ɓacin rai,amma sai ta danne ta amsa sallaman nasu,TAIMIYYAH ta zube tana gaida Umman,Umma ta jefa mata harara tana amsa gaisuwan a wulaƙance,Sadeeq ma ya gaidata ta amsa tana jifansa da wani kallo da shi kaɗai yasan ma'anansa,Baba Sani ne ya fito daga ɗaki ganin TAIMIYYAH yasa shi sakin murmushi yana faɗin "Zainab idon ki kenan na dawo jiya ke kaɗaice baki min sannu da zuwa ba,lokacin da na shiga wajen Iya kuma kinyi bacci."
Ya ƙare maganan yana zama kusa da Umma,TAIMIYYAH ta saki murmushi tana faɗin "Baba kayi haƙury bacci ne ya ɗauke ni da wuri,ina kwana ka dawo lafiya."
"Lafiya lau Zainab,har anyi shirin Haddan ba sannu da ƙoƙari,ina fata su ƴan uwan naki sun shirya sarakan shiririta."
Cewan Baba Sani yana maida dubansa kan Sadeeq da ke gaida sa,TAIMIYYAH ta furta "Yanzu dai zasu shirya Baba."
"Okey! To Allah yayi albarka ya bada ilimi me anfani,zuwa dare zan tara ku akwai maganan da zanyi da ku don haka kar ki yadda ki bacci da wuri kinji Zainab." Baba Sani ya ƙare maganan da raha,hakan yasa TAIMIYYAH sakin murmushinta me faɗi tana bashi tabbacin zata jira,daga haka ta miƙe ta baro falon nasa ta bar Sadeeq ɗin aciki,saman kujera ta ɗosana mazaunanta tana kallon agogo,ganin lokacin na tafiya yasa ta saki ƙaramin tsaki,Yah Sadeeq da ya fito yana miƙa mata Qur'aninta,ganin har time ɗin su Zuhura basu fito ba yasa shi nufan ɗakinsu,ko mintu biyu baiyi da shiga ba sai gasu sun fito kowacce fuska a haɗe suna jefawa TAIMIYYAH mugun kallo,kaman yasan zasu iya mata wani iskancin a hanya,sai yace su jira shi ya ɗakko mukullin mota zai sauke su daga bakin hanya su ƙarisa cikin makarantan,tunda makarantan babu nisa yana da daga farkon shigowa layin su ne,aiko sam basu ji daɗi ba so sukai ya barsu su taka da ƙafafunsu,don su samu daman cin zarafin TAIMIYYAN akan hanya,amma sai Yah Sadeeq ɗin ya toshe wannan kafan,a bakin gate ɗin shiga ma ya sauke su yai tafiyansa,suka shige ciki kowacce ta nufi ajinsu,don TAIMIYYAH ta riga tai musu nisa sosai duka saura Izu huɗu ya rafe su haɗa a yaye su..........✍🏻
#Ɗansabo ce#