TAIMIYYAH

Chapter 11

by @ayshadansabo


 

     Page 11

____TAIMIYYAH a lokacin da suka girma suka kai matakin gama Secondary School,tun a sannan ta sake gane irin tsanan da Umma tai mata bana wasa bane,da irin huɗuban da takewa Zuhrah da Basma akanta, tana cusa musu tsana da kishin TAIMIYYAN a zuciyansu,ko da yaushe tana nuna ma Zuhrah da take babba cewa,kakarsu Iya tafi son TAIMIYYAH ne kasancewan Abie Baban TAIMIYYAN yafi Baba Sani kuɗi,abinka da huɗuban uwa tun yaran basa maida kai akan zantukan ta a hankali suna girma suna sake wayo,har Zuhurah ta fara gasgata hakan tana jin kishin TAIMIYYAN a zuciyanta da jin haushin yadda TAIMIYYAN ta fita kyawun halitta,a islamiyan da suke kowa TAIMIYYAH yafi so ba ita ba,haka a dangin su Baba Sani duk idan sun je can Rimi Family House ɗinsu kowa TAIMIYYAH yafi ja ajiki da yaba kyawun halittanta,hakan ya sake jefawa Zuhurah ƙin TAIMIYYAH ta ɗauki ɗabi'an ƙuntata zuciyan TAIMIYYAN ta hanyan kyaranta a bainar jama'a,tana sukan nakasanta da kiranta gurguwa musaka,wanda ta gama gane hakan shine weakness ɗin TAIMIYYAN,domin bata iya daurewa a duk lokacin da sukai mata gorin halitta takan ji wani irin ƙunci da ɗaci har ƙasan zuciyanta,wanda take kasa controlling kanta har sai ta zubar da hawaye,tun Iya bata farga da irin rayuwan da ƴan uwan junan suke ba,har ta gama gane yadda su Zuhuran ke cin fuskan TAIMIYYAN ko agaban waye,abinda ya fusata zuciyan Iya har watarana ta haɗa Zuwairan da su Zuhurah tai musu wankin babban bargo,tare da hana su Zuhuran takowa zuwa sashin ta sai da wani dalili me ƙarfi,itama kuma TAIMIYYAN Iya tai mata iyaka da shiga Sashin Baba Sanin,sai idan ya dawo taje gaida shi ko ita Iyan ta aiketa ta fito,amma sam ta hanata zuwa ta zauna bare har su samu daman cigaba da muzantata,wanda hakan ya sake janyowa TAIMIYYAH wani sabon tsanan a zuciyan Umma da Zuhurah,Alhaji Sameer da TAIMIYYAH ke kiransa Abie bai taɓa banbanta TAIMIYYAH da Zuhurah a wajen siya musu tsadaddun Situru na xamani ba,amma sam Umma da Zuhurah basa gani gani suke a komi TAIMIYYAN sai ta zarta Zuhurah tunda Iya tafi son ta ,ko kaya me tsada aka sai ma Iyan sai ta ce TAIMIYYAH ta ɗauka ta ɗinka,da kuɗinta ma take siyawa TAIMIYYAN duk abin da tai sha'awa ta kuma ji tana son TAIMIYYAN da shi,a kwana a tashi su TAIMIYYAH suka kawo lokacin girma suka shiga shekaran gama secondary skull,zuwa lokacin duk wani kyawu da cikar halitta da Allah yai mata baiwansa ya gama fitowa fili,Yah Sadeeq lokacin yana shekaran ƙarshe a jami'an NILE Abuja,wanda Baba Sameer da yai kuɗi sosai zuwa time ɗin shi ya ɗauki nauyin karatunsa zuwa can ɗin,abinda ya faranta ran Baba Sani matuƙa tare da sake jin ƙaunar Yayan nasa,TAIMIYYAH ta fito da result me kyau tare da samun manyan kyautuka a ranan Grad ɗin nasu,sai dai lokacin da suka zo zana Jamb sai akai rashin sa'a bata samu makin da ake nema ba,domin burin ta shine tana son zama Nurse ko cikakkiyar Lawyer,domin tarihin mahaifiyanta da taji wacce tana shekaran kusa da ƙarshe ta kammala nata karatun ta haifeta ta rasu,hakan ya dasa mata son maye gurbin marigayiya TAIMIYYAH,sai dai du ka Allah bai xana hakan a goben TAIMIYYAN ba sai ta bige da shiga Federal Collage of Education da ke Zaria,kwalejin da suke kusa sosai aka bata Course ɗin ENGLISH/ECONOMICS course me wuya amma TAIMIYYAH ta dage akan cewa ya kwanta mata zata yi shi komin wahalansa,don a ganinta idan batai karatun ba bata san me zatayi ba,musamman a lokacin da take jin kanta cikin wani irin kaɗaici na rashin abokanan hira a gida,tunda ƴan uwanta na jini da xata raɓe su taji daɗi sun juya mata baya,tsakaninsu da ita sai kyara da hantara daga su har uwansu,hakan yasa daga kallo sai kallo sai kuma wayan da Abie ya kawo musu kyautan sa a wani tafiya da yayi xuwa UK,ya zo musu dashi ita da Zuhurah iri ɗaya samfurin Iphone 12Pro Max,to tunda ta buɗe shafukan sada zumunta nasu Instagram,Whatsapp,Twitter da sauransu sai suna ɗebe mata kewa sosai,musamman da Maryam Salis tasa akai adding ɗinta a groups na littafai,sosai take jin daɗin karance-katance especially idan ba Skull ranan,suna hiran su da Iya sosai domin komi nata kai tsaye take tinkaran Iya,sabida haka ta hore ta dashi,don riƙon uwa tai mata bana kaka ba,sai dai ita TAIMIYYAH ba hakan tafi so ba,tafi sha'awan ta jita cikin tsararrakinta,a skull ita ba gwanar tara qawaye bace,daga Maryam Salis,Murja Gubuci,sai Fatima Lawal, ko kaɗan TAIMIYYAH bata taɓa fuskantan kyara ko gorin halitta a skull ba,duk da yadda take kame kanta sam bata son shiga cikin mutane sabida gudun gori ko kyara akan kasancewanta me laluran ƙafa,lokacin da suke primary ne ma take samun irin yara masu tsokananta suna kiranta da gurguwa-gurguwa,ko yara suyi ta binta suna kwaikwayon tafiyanta har sai Teachers sun gani sun tsawatar,domin TAIMIYYAH zama take tai ta kuka idan ana tsokananta,ta sha cewa Iya akaita a gyara mata ƙafanta ko za'a daina kiranta da gurguwa,amma tunda ta ƙara wayau ta sanya dangana ko an kwaikwayeta bata kuka,duk qawancen da suke yi da su Maryam ɗin dukkaninsu Iya bata taɓa bari taje gidajensu ba,sai sau ɗaya ne taje gidan su Maryam Salis dake Gaskiya Layout,su dai sun zazzo nan musamman Murja da Maryama suna matuƙar son TAIMIYYAH sosai,sai wata ƴar islaminyansu Bushira wacce suke layi ɗaya,amma itama ɗin Iya bata cika bari taje gidansu ba,a cewanta bata son yawan bin qawaye gara su su biyoka gida,Yah Sadeeq tun da TAIMIYYAH ta girma ta xama budurwa sai ya sake ninka kulawan da yake bata,yana janyota a jikinsa sosai tayi sabo da shi ta yadda har yake iya sanin wasu damuwoyinta,shi kuma duk a lokacin danne Soyayyanta da yake ji yake,har ta kai ta kawo abin ya fara fin ƙarfinsa,tuni Umma ta lura da irin shaƙuwan da ke tsakanin TAIMIYYAN da Sadeeq ɗin,watarana ta sa akai mata kiran TAIMIYYAN tai mata kyakykyawan gargaɗi akan ta fita mata daga harkan ɗa,xagi da cin mutunci ranan TAIMIYYAH ta sha har ta gode Allah,haka ta baro Sashin ta koma wajen Iya tana kuka sosai,Iya batai ƙasa a guiwa ba bayan ta tirke TAIMIYYAH taji yadda sukai da Umma,taje tai mata wankin babban bargo,TAIMIYYAH sam bata damu da zuwa Lagos wajen Abie ba,domin a shekaran da ta shiga FCE a wannan shekaran ne Abie ya samu canjin wajen aiki aka maida shi Lagos,can Port-authority a kuma babban matsayi aka kai shi wajen,sai ya ɗauke Samha daga Kaduna suka koma Lagos ɗin da zama,a lokacin an haifan ma TAIMIYYAH qanni biyu duk mata Raudha da Maryam da ake kira da Nahar,yaran sun shiga ran TAIMIYYAH amma rashin samun fuska a wajen Ummie matar Abie ɗin yasa sam bata jin daɗin zuwa wajensu ko ta samu hutu,ta gwammace tai zamanta da Iya duk sanda su suka zo sai ta ga qanninta wanda suma suke tsananin son ta,sabida yadda take jansu a jiki idan sunzo garin,sau ɗaya ta taɓa zuwa Lagos ta ga inda su Abie ɗin suke,tai Sati biyu Iya ta matsa akan a dawo da ita,dama Abie ɗin tabi a jirgi lokacin da zai koma,da zata dawo ma a jirgin ya haɗo ta da wani abokin aikin sa da zai zo Zaria,tun daga lokacin bata kuma zuwa ba har ta kammala karatun NCE ɗinta baki ɗaya,ita kuma Zuhurah ta kammala Diploma da tayi a ABU Congo inda ta karanci Public Administration.Lokacin da Yah Sadeeq ya ga sun kammala karatun ne,ya fallasawa TAIMIYYAH sirrin zuciyansa akanta,amma sai TAIMIYYAN ta nuna masa rashin yiyuwan abinda yake muradi,ba ƙaramin ƙiyayya Umma take mata ba,TAIMIYYAN 

Duk da kasancewanta nakasashshiya hakan bai hanata cika burinta na samun ingantaccen ilimi ba,matsi da ƙuncin rayuwa tare da gorin halitta da take fuskanta daga ahalinta su Zuhuran,duka bai raunata zuciyan TAIMIYYAN ba bare har taji cewa ita ɗin kasashshiyace har ta kasa maida hankali akan karatun ta.Abu ɗaya ta sawa ranta shine Allah shi ke halittan bawa ta yadda duk yaso ya gansa,ta kuma sawa zuciyanta cewa nakasan halittan bawa baya tashi abanza domin ubangiji yai mata baiwa da tarin ni'imomi cikin rayuwanta.Wanda a yanzu ne take sake ganin cewa lokaci yayi da zata bi shawarwarin Iya wajen dake zuciyanta,ta nuna ma su Zuhuran cewa a yanzu duk wani gori da cin fuskansu ya daina damunta,zata maida hankali wajen inganta rayuwanta da ilimi ta kowani fanni,domin tana sha'awan takai wani matakin da zata dogara da kanta har ta tallafi nakasassu irin ta,waɗanda basu da gata tunda ita Alhamdulillah cikin gata da kyakykyawan rayuwa ta tsinci kanta .


 _To masu karatu mun ji miye asalin TAIMIYYAH da yadda ta taso,yanzu labarin zai fara inda zamu ji cikakken ya rayuwan TAIMIYYAN zai cigaba da kasancewa da ƴan uwan ta su Zuhurah? shin burikan ta zasu cika,wani me rabon ne zai yi nasaran shi ga zuciyan TAIMIYYAN har ya cire mata duk wani tsoro da shakku da take ji akan aure,gurgun ne ɗan uwanta zata samu kaman yadda su Umma ke faɗi,ko kuma wani ne na daban ubangiji zai jefo shi cikin rayuwanta? Duka zaku ji amsoshin idan kun cigaba da bibiyan alqalamin Ɗansabon,_ 



 Assalamu alaikum! My peoples duka anan na kawo ƙarshen free pages da zan iya baku.