ZAFIN KISHI

Page 7-8

by @autararewa101


ZAFIN KISHI




BISMILLAHIR RAHMANIR* *RAHIM*



*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .




PAGE7️⃣➡️8️⃣



📝Yana fita daga gidan ta jiyo Karan tashin motar shi,da sauri ta fito daga kitchen da ludayi a hannunta Amma Ina sai kurar shi ta gani,anan ta yada ludayin ta juya cikin gidan da gudu.dakin shi ta nufa Amma gani tayi wayam babu shi Babu alamar shi sai wayar shi daya akan gado.dauka tayi tana huci ta saka wancan nomber tashi ta fara Kiran shi tana ta ringing Amma yaki yin picking.a karshema switch off dinta yayi gaba daya ya aje Yana ta faman tsula gudu.tana Kara Kira taji a kashe kawai ta dora hannunta a kanta ta fara rusa kuka.sosai take kuka duk tayi wujiga-wujiga ta fita hayyacinta,ji takeyi Daman tasan inda ya nufa ta bishi da ba abinda zai hana ta kashe ko wace Yar iska ce ya tafi gurinta da yammacin nan.




Shiko tunda yasa kai bai tsaya ko inaba saida yaje unguwar kawo.A wani Dan matsakaicin gida yayi horn wani Dan matsakaicin saurayi ne ya leko ganin mai gidan ne yasa da sauri ya koma ya wangale mai gate din ya kunno hancin motar shi cikin gidan.da sauri ya nufi cikin gidan saboda sauri kamar zai kifa kasa.yana wuce Dan karamin falon da ba komai a cikin shi sai tiels a shimfide sai labulaye masu kyau da wani Dan karamin kafet a tsakiyar falon,wani bed room ya bude a konce ya hangota tana faman danne wayar ta.yana zuwa jikinta ya shige Yana sinsinarta kamar wani Dan akuya.ba laifi itama kyakkyawa ce Amma Bata kai zulaihat hasken fata da diri ba.ba tare da bata lokaci ba suka fara aikata abinda ya kawo su wurin.(Allah kasa mufi karfin zukatan mu).





Ita ko zulaihat tana nan inda take tana faman aikin kuka ko yara Bata san driver ya dauko su daga islamiyya ba,sai yarinyar da take kula da su ta saka sukayi salla ta Basu abinci suka ci ta kunna masu kallo a Falo.





A S P Habib sai karfe takwas ya kyale yarinyar shi,bayan ya kimtsa sallah yayi itako yarinyar Bata da niyyar yi,wayar shi ya dauko a Mota yayi mata alart na 50k kafin ya yimata sallama ya nufi hanyar gidan shi kafin itama ta wuce gidan su.


Tun a hanya yake zilimin yadda zasu Kare da zulaihat Dan yasan yau ba zasu yi bacci ba saboda bala'in ta,gashi ya manta bai koma gidan su yarinyar nan ba Dan kara duba lafiyar ta.da wannan tinanin ya karaso gidan shi dake cikin rigasa Yana horn aka bude mai ya shiga ciki.zulaihat tana jin tsayiwar Motar shi ta tashi tana jiran shigowar shi.yaranshi ya taras a Falo suna kallo anan yadan zauna Yana yimasu wasa yarinyar dake yimata aiki mai suna sakina cikin ladabi ta gaishe da shi,amsawa yayi Yana karemata kallo kafin ya nufi dakin nashi Dan yasan sarkin masifar tana nan tana jiran shi.



A tsaye ya isketa ta kama kugu,Yana shigowa yayi kamar bai ganta ba gaban shi Tasha tana hucin masifa ta ce "Wai Habib Meka dauke ni ne mahaukaciyar ko me?"



Da sauri ya kalleta ganin yadda ta tsareshi kamar wani tsaranta.cikin fushi ya ce "Duk yadda kika dauki kanki,to Nima haka na dauke ki,kina abu kaman wata jahila katsani ki bani wuri Kona Zane ki yanzun nan"Yana kokarin tureta.


Rikeshi tayi tana Kara karfin kukanta ba tare data Kara cewa komai ba kyaleta yayi saida ta gaji dan kanta kafin ta sake shi tana wucewa zuwa tiolet din cin dakin.da kallo ya bita Dan harga Allah Yana bala'in san zulaihat Amma kwata-kwata tana da dabi'u marassa kyau musamman *ZAFIN* *KISHIN* ta yayi yawa saboda duk lokacin da yayi yunkurin Kara aure sauta lalata al'amarin kafin daga baya tazo tana gwarashi,Kuma Bata kulashi yadda ya kamata....Karan wayar shi ne da yaji yasa ya dakata da tinanin da yake yi.yana received call din yaga ta fito daga toilet tana goge fuskarta alamar wanka tayi.


Da mamarshi yake waya cikin ladabi yake gaishe da ita, kafin take tambayar shi ko lafiya yau taga bai zo ganinta ba.hakuri ya bata akan uzuri ne yayi mai yawa,Amma gobe insha Allah zai shigo da safe kafin ya wuce office.da haka sukayi sallama ya aje wayar.



Kallanta yayi ganin tana sallah yasa ya mike, kitchen ya nufa.abinci ya zubo a plate da coc guda daya sai ruwan paro guda daya.a kasan kafet din jikin gadon ya zauna Yana ci harta idar da sallah ,duk Yana kallanta kafin ta fita.yabi bayanta da kallo.



Yaran ta iske a Falo ta tambaya sunci abincin Suka amsa da "eh munci"

"To ku muje ku kwanta da wuri saboda zuwa islamiyya"dakyar muryarta take fita saboda masifar kukan da tasha.sai Ahmed yake cewa "Ummah meya sameki muryarki take haka?"


"Kai ku muje ku kwanta kunji ko,mura ce take damuna shiyasa"tana jansu zuwa dakinsu.yarinyar ta gyara masu gadon kafin ta canza masu Kaya suka konta,dayan gadon Kuma Khadija ce da wannan Yar aikin .




A hankali ta turo kofar tana sadda Kai kamar wata munafika.yana kallanta ta kasan idonshi ya kyaleta Yana ci gaba da duba system din shi.a kusa da shi ta zauna tana kallanshi Dan ta rasa ta Ina zata fara yimai magana.




A fannin gidan su habiba kuwa lokacin da malam ya dawo daga wurin sana'ar kayan miyanshi,ya riski ta dawo yayi farinciki Dan ita kadaice Diyar da Allah ya bashi,Amma Mamanta ta rasu daga baya ya auro innaji wadda yana ji Yana gani take cutar da ita Amma ba yadda zaiyi dan shi kanshi zaman hakuri yake yi da ita.




Zulaihat ganin Ahmed yayi banza da ita yasa ta saka mai kuka.dariya ta kusan bashi ganin tana neman raina mai da hankali,dazu ya nemeta ta mai wulakanci yanzu Kuma tazo tana yimai kuka dan taga ya fita.


Kasan guyoyinta ta durkusa cikin kuka ta ce "Dan Allah kayi hakuri karka yiman kishiya,wallahi na tsaneta,Kuma Dan Allah karka bi matan waje insha Allah zanyi kokarin gyarawa bazan Kara guje maka ba"tana faman goge hawaye fuskar ta.


A hankali yadan dubeta ganin duk yadda ta fice daga hayyacinta,Amma sai yayi fiska Dan shi Yanzu zam yake jinshi taje ta rike kayanta baya so.


Kukan taci gaba da yi duk Yana jinta,domin Daman ta Saba yimai haka sai tayi abu tazo tana damunshi da kuka,daya hakura to Bata dadewa zata Kara maimaita irin laifin Dan haka yake kyaleta,shidai Yana ta addu'ar Allah yasa ya daina wannan mummunar dabi'ar ta bin mata,ita kadai ke daminshi wannan ma duk itace sanadin saka shi a ciki saboda San zuciya irin nata.


Rufe system din yayi ya mayar da ita,kayanshi ya canza zuwa na bacci Dan yaga har karfe goma ta gota.kan gadon ya haye yayi konciyar shi ya barta anan,gajiya tayi da kukan itama ta konta a bayanshi tana sauke ajiyar zuciya,Amma zuciyar ta cike falla da kishin inda yaje.


Bai cemata komai ba da haka har bacci ya dauke shi,ita ko indonta biyu tana ta faman




By



AUTAR AREWA.







✍️✍️✍️✍️✍️✍️.