ZAFIN KISHI

Page 13-14

by @autararewa101

ZAFIN KISHI







BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM



*DA* *SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI* *JIN* *KAI .




PAGE1️⃣3️⃣➡️1️⃣4️⃣




📝A ranar juma'a da safe kasancewar yara ba islamiyya,Kuma suna cikin hutun makarantar boko,hakan yasaka karfe shabiyu ya dawo daga office.lokacin da yayi Shirin zuwa masallaci suma Yaran an gama shirya su.har jikin motar zulaihat ta rakosu kafin ta koma cikin gidan dan cigaba da ayyuka ita da nafisa mai aikinta.

Cikin Nishadi Suka dauki hanyar masallaci.shadda ce maroum color a jikin shi dinkin manyan Kaya ne,babbar rigar ta sha aikin surfani mai color din zaren milk da ratsin baki a jiki.sai bakar hula da bakin cover shues daya dora.Ahmed da Arfat Suma kayan su iri daya da babbar riga irin ta yara da hulinan su.itako Khadija Abaya aka saka Mata pink color mai dan banzan kyau da tsada.sunyi Shar abinsu sai tashin kanshi suke yi.


Bayan idar da sallar juma'a derect gidan Mama ya nufa.tun kafin ya karasa parking a kofar gidan Suka fita cikin happy suka nufi cikin gidan suna kwana Kiran kaka!kaka! Gamu munzo barka da sallah.

Tana kuryar dakinta bisa abin sallah casbaha ce a hannunta tana lazimi ta jiyo muryar Yan jikokin nata.jitayi wani farinciki ya lullubeta .falo ta nufo Suma daidai sun karaso cikin falon.jikinta suka dane suna faman ture juna kowa Yana so ya jingina da jikinta.

Zama tayi tana cewa "Bari na zauna kada ku kayar da ni,bakwa jin magana idan baku zo ba bana jin dadi,Amma da zaran kunzo to bakina bazaiyi shiruba"tana rungume Khadija.

"A wallahi ku dagamin Mamata kada ku jimata ciwo"cewar Habib da yake bakin kofa yana kallonsu da murmushi dauke akan fuskar sa.

"A a Habibu tare kuke tafe kenan?,nayi tunanin direver ya kawo su"cewar Inna tana murmushi.

"Tare muka taho yau yini zasuyi maki,zakisha fama da rashin jinsu".

"To yazanyi idan basu zo ba bana jin dadi".

Asabe ta shigo tana kawo masu abinci.kasan kafet Suka sauko dukan su suka ci abincin, kasancewar daman haka sukeyi duk randa ya kawo yaran.


Habib shi ne bai bar gidan ba sai lokacin sallar la'asar,kafin yayi ma Mama sallama akan cewar da dare zai zo ya dauke su.yana fitowa wayar shi ta fara ringing.dubawa yayi Dan ganin Wanda yake Kiran shi.sosai yaji kirjin shi ya bada Dammmmmmm da karfi har saida jijiyoyin shi sukayi sanyi.sosai ya Kara ware eyes din shi akan fuskar wayar,A fili ya furta Ihisan ce yau take kirana,to meya faru ne?yake tambayar kanshi.harta katse bai daga ba saida wani Kiran ya Kara shigowa kafin yayi saurin yin picking.cikin sanyi ya ce "Hello Ihsan ya gida"Yana jingina da jikin motar.

Saida tayi shiru na wasu dakika kafin cikin gogaggiyar muryarta ta ce "wato da gaske bazaka neme ni ba ko?kaci moriyar ganga ka yada kauronta ko?to bari kaji ASP wallahi kodai ka aure ni ko Kuma duk matakin dana dauka akanka kaika jawo,gaskiyar maganar mutane da ake cewa kana tsoran matarka,na gano cewar tana aikata sihiri Dan kar ka karamata kishiya ko?to Bari kaji wallahi idan baka aure ni ba zanyi maganinku daga Kai har ita"mtssssssss taja wani dogon tsaki tana katse kiran.

Da karfi ya sauke ajiyar zuciya Yana Kara lumshe eyes din shi.shi wallahi harya manta da ita duk a tunanin shi bata cikin garin kaduna,Dan tun haduwar su ta karshe da sukayi fada akan maganar dole saiya aureta shi Kuma yace a a bazai iya aurenta ba,to shi ne sanadin rabuwar su saifa yau da take neman tayar mai da hankali.

Cikin azama ya shiga Motar ya bata wuta Yana mai barin cikin layin.


A kofar gidan su Habiba yayi parking,wani karamin masallaci ya gani kusa da gidan anan ya samu yayi alwala ya gabatar da sallar la'asar.kafin ya karasa kofar gidan.Wani yaro ya aika a kirata.yaran dawowa yayi yace Wai innajo tace inji waye ne?

"Kace inji ASP Habib ne"cewar Habib Yana Kara tsayawa jikin wata bishiya.


Ba bata lokaci Habiba suka fito tare da yaron daya aika.naira Hamsin ya ba yaron kafin ya dubi inda Habiba tayi tsaye.

"Baki iya sallama ne ba"da sauri ta ce "Assalamu Alaikum,Ina yini"tana Jan gefen hijaf dinta"

A gajarce ya amsa Yana cewa "Malam bayanan ne "

Cikin yin kasa da Kai ta ce "ya fita tun dazu,Amma nasan yanzu zai dawo dan zai fita da kayan Miya"cewar Habiba.

"Ok"kawai ya ce yana faman latsa wayar shi,wani sako ne yaga Ihsan ta Kara turo mai bai duba ba kawai ya kyaleta.

Dukan su shiru suka yi na wasu Yan dakiku kafin a hankali ta ce "zan shiga gida aiki nake yiwa Innajo"Dan ji tayi kafafunta sun fara yin sanyi saboda tsayuwar data Sha.

Bai tankata ba saima Kiran waya daya shiga faman yi.

Daga bayan su Malam yayi sallama.dukan su suka amsa sun juyawa bayan su.Habib kashe wayar yayi Yana amsar ledar da take a hannun malam.har zata shige cikin gidan malam ya ce "Anshi Habiba Kai ciki kafin na shigo"cikin ladabi ta duka ta amsa kafin ta wuce cikin gidan.

Mayar da hankalin shi yayi ga Habib bayan sun karasa gaisawa ya ce "Habibu Daman Ina son ganinka akan wani taimako da zaka yiman"cewar malam Yana yin kasa da kanshi.


Cikin jimami Habib ya ce "to malam Ina jinka,insha Allah zan taimaka maka da iya abinda Allah ya horeman"Dan shi harga Allah Yana da tausayi.


"Akan maganar Habiba ne,Dan Allah nace ko zaka taimaka na baka auren ta danta huta da wannan ukubar ta mai dakina?"Yana zubar da kollah.

Da sauri Habibu ya dago da kanshi Yana kallan tsohon,Amma ganin yadda babba da shi Amma hawaye ke zuba ta idon shi,sai yaji jikin shi duk yayi sanyi.a hankali ya motsa labban shi ya fara cewa.. .................



By


AUTAR AREWA.




✍️✍️✍️✍️✍️✍️.