ZAFIN KISHI

Page 37-38

by @autararewa101

ZAFIN KISHI






BISMILLAHIR RAHAMANIR * *RAHIM*





*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .





PAGE 3️⃣7️⃣➡️3️⃣8️⃣






📝Haka rayuwar Habib da Zulaihat take tafiya a cikin wannan satin,ga kwanakin bikin shi suna ta Kara kusantowa.tun randa taje gida Abban ya korota bata Kara komawa ba saboda tana tsoran shi.kuma tunda ta dawo ta dora daga inda ta tsaya ana sauran kwana biyu daurin aure da dare misalin karfe daya na dare Habib ya nufi dakinta.



Ya Jima tsaye jikin kofar dakin Yana so ya shiga,Amma Yana jin shakkun kada ta tara mai mutane da wannan tsohon Daren.Dole ya aro juriya a matsayin shi na namiji ya yafa a zuciyar shi kafin ya tura kofar dakin,cikin sa'a kuwa ya jita a bude.ganin duhun dakin yasaka yayi saurin kunna light din wayar shi.


Lokacin daya kunna hasken yayi daidai da tashin zulaihat tsaye.sosai suke kallon juna dan koba komai akwai kauna da soyayyar juna a zukatan tsaffin masoyan.


A hankali yake takowa zuwa gabanta,har saida ya kure mata.kasa tayi da kanta ganin yadda ya kureta da idanun shi.hakan da tayi ya gano cewa ya kashe Mata jiki dan haka yanzu zai yi Mata wayo.


Hannuwan ta ya kamo cikin yin kasa da voice kaman mai yin rada ya fara yimata magana"Haba Uwar gida sarautar mata,ki gafarce ni Mana,kada ki dauka wannan auren da zan Kara zai rage wata darajar da kike da ita a wurina Koda da kwayar zarrra ne,har karshen rayuwata soyayyar ki tana nan dakau a cikin zuciyata"Kara jan numfashi yayi jin tayi shiru bata tanka ba.

"Ki sani shi Karin aure Allah ne ya kaddara Mana,ba yin kanmu bane,Kuma umarni ne na Allah (S W A ), kada ki bari shedan yayi galaba a kanmu,kada kiyi sake da hanyar da zaki samu aljanna,insha Allah nayi maki alkawarin zaki sameni mai shimfida adalci a tsakanin ku,Amma ki kasance mai yiman biyayya tare da Addu'ar ku.to ni Kuma insha Allah duk abinda kuke da bukata daidai arzikin da Allah ya horeman zanyi maku".

tsura Mata ido ya Kara yi Yana kallon yadda take zubar da kollah.



Cikin fargaba Zulaihat ta rungumeshi tana Kara saurtin kukan ta.ba tare data furta komai ba.


Haka Habib yayi ta rarrashin ta Yana nusar da ita illar abinda take son aikatawa na kauracemai.A karshe dai dakyar ya samo kanta ta bashi hadin Kai.




Washe gari ta kama ranar juma'a,ya gobe daurin aure kenan.tunda ya fita bai dawo ba Yana ta faman hada-hadar biki.

Zulaihat bata gayyaci kowa ba sai kawarta Ikilima,kanwarta ma Jamila da aka turo korata tayi a cewar ta abin kunya ne tayi wata hidima dan za'a yimata kishiya.



Haka Habib yayi ta fama da abokanshi har zuwa dare kafin ya dawo.dan ko gidan su Habiba sai abokanna shi ya tura Suka bata sauran kayan bukata na biki.ya saka an jera komai a gidan da za'a Kai Habiba.



"Ke Ihsan ba inda Zaki je a gobe,dole ne ki zauna muga karshen game din nan"cewar Hannatu da take daura dankwali a gaban mirror.



I hanakli Ihsan ta sauke ajiyar zuciya tana kontawa bisa katifa.

"To kawata na hakura da tafiyar nan,Amma dole nexst week nabar garin nan gaskiya".



Juyowa Hannatu tayi tana kallon kawarta ta "Ba matsala zuwa next week din sai ki wuce.




Sai wuraren karfe 10 kafin Ikilma ta wuce gidan ta bayan ta gama kullawa Zulaihat abubuwan da ya kamata ta rinka yi Dan ganin ya saki amaryar da za'a kawo .



Shi Kuma Habib sai kafshe shadaya da rabi kafin ya samu sukunin shigowa gidan sa.



*RANAR ASABAR*


A ranar Asabar da misalin karfe Sha biyu na rana jama'a da abokan arziki Suka taru masallacin cikin unguwar ,kusa da gidan Malam Hadi mai kayan Miya domin daura auren Habiba da angonta Habib.


Amma Lokacin da aka bukaci a kawo results din su Dan nuna shedar cewa kowannen su Yana cikin koshin lafiya kamar yadda ake yi.Sai dai akasin da aka samu babu wannan results din Sannan babu Doctor Hasan Wanda shi ake faman jira.


Cikin jin Haushi Habib ya fito waje,sai kanin Baban shi kawu Aliyu shima ya biyo bayan shi.wayar Doctor Hasan yake faman kira,Amma matsalar network ta hana Kiran ta shiga.dakyar ya same shi bayan yadan matsa gaba dakan da jikin masallacin.



Cikin daga murya ya fara cewa "Wai Dr Hasan meyasa kake yiman haka ne,bacin Kai da kanka ka dauki alkawarin zaka kawo min"shiru yayi jin irin amsar da abokin nashi yake bayar wa.



Amsawa yayi da "To muna jiranka saika karaso"kafin ya kashe wayar Yana kallon kanin mahaifin nashi.


"Kuyi hakuri Baba ya ce gashi nan zuwa"


A tare suka Juya zuwa cikin masallacin.



Bayan minti goma Dr Hasan ya iso wurin da taimakon address din da Habib ya tura mai.


A bakin motar ya tsaya shi da wani abokin shi mai suna Muktar.


Cikin yin kasa da murya suke tattaunawa,Wanda ni kaina bana jin me suke cewa.



Mukhtar Naga ya shiga masallacin Jim kadan suka fito da limamin masallacin sai malam Baban Habiba da wani babban mutum.


Bayan sun gaisa Suka Mika masu takaddun.liman shiya fara dubawa kafin wannan babban mutumin ya amsa Yana cewa "A gaskiya kun bata Mana lokaci am..........."


Sauran maganar ce ta makale a bakin shi ganin abinda aka rubuta a jikin takardar.sosai fuskar shi ta nuna alamun tashin hankali.


Cikin sanyi yace" ku muje,Kai mukhtar ku biyo ni a baya"yayi gaba Yana gyara babbar riga.

Gaba dayan su suka rufa mai baya kowa Yana al'ajabin wanna rudadden al'amari.


Bayan kowa ya zauna an nutsu za'a fara gabatar da daurin aure.


Wannan babban mutumin naga ya dauko bandir din kudi ya aje a gaban waliyyan Amarya a maimakon su kawu Aliyu da zasu bayar.kowa shiru yayi Yana kallon ikon Allah.dan shi Habib shida zugar abokan shi suna can a bayan mutanen shiyasa basa ganin abinda yake faruwa.



Liman ya fara gabatar da daurin aure,cikin kankanin lokaci aka sheda daurin auren Mukhtar Muhammad da Habiba Hadi akan sadaki naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.




Da sauri kawu Aliyu ya mike tsaye jin wannan lamari,dukda Yana tantamar kunnen shi bai jiyo mai daidai ba.Amma mai maitawar da akayi shiya tabbatar mai da gaske ne.


Daidai nan shima Habib ya mike Yana karkarwa cikin lokaci kalilan mutane suka fara rudewa Dan ganin wannan rudadden lamari da aka samu na lokaci daya.



Habib daidai saitin zuciyar shi ya dafe Yana kokarin yin magana,Amma Ina ya kasa saboda yadda jikinshi ya dauki kakkarwa sai numfashin shi da yake kokarin daukewa.kafin na kusa da shi su ankare Suka ji yimmmmmmmm ya fadi a kasa .gaba daya abokan shi sukayi kanshi suna Kiran sunan shi.Amma Ina Habib ba alamun numfashi a tare da shi..............!












✍️✍️✍️✍️✍️✍️