MADUBIN GOBE

5

by @phartybb

Masu buƙatar complete akwai a Wattpad, ku duba account nawa @phartybb .

 Ko ku yi saving numberna ku min magana don samun complete document ***.


Page 5

"Na amince." Ammah Jidda ta ce da sauri da hakan ya ba wa Alhaji Mamman mamaki.


Murmushi tayi tana kallon shi ta ce. "Ka na mamaki ko? Wallahi ina son sanar da kai amma na rasa hanya, kamar yadda ba zan iya barin ƴaƴana ba haka bana son kowacce mace ta fita ta bar ƴaƴanta. Na sanar da kai gaskiya, na aureka ne don in sasanta tsakaninma da matarka, kuma yanzu allahamdulillahi tun da kai da kanka ka kawo maganar, na amince ka dawo da matarka."


"Allah miki albarka, ya sauƙe ki lafiya." Ya furta cike da farin ciki. Shi kam ya godewa Allah da yake azurta shi da mataye nagari.


"Ameen!" Amma Jidda ta amsa da shi ganin ya gano dai ciki ne da ita na wata ɗaya.


Da safiyar ranar asabar ba aiki, bayan ya gama abin da zai yi a gida ya fita kasuwa, shagon Alhaji Audu ya nufa kai tsaye ya sanar da shi zuwa yamma in anyi sallar la'asar zai kai shi gidan da Sadiya take.


Hakan kuwa a kayi ana gabatar da sallar la'asar suka wuce gidan kai tsaye bayan sun biya gida Zarah sun ɗauki Zarah ta musu rakiya.


Nuratu ta ɗan mata rigimar ciwon ciki da take ji, ta goyeta tana jijjigata ta samu tayi bacci tana ƙoƙarin kwantarta a falon saman katifarta taji sallamar Zarah.


Da murmushi ta amsa ƙasa ƙasa-ƙasa don kar Nuratu ta farka.

"Sannu da zuwa Zarah."


"Sannu Mamin Nuratu, bacci take ne."


"Eh wallahi ciwon ciki ke damunta."

Hajiya Sadiya tace tana dan bubbuga bayan Nuratu.


"Allah kawo sauƙi tare da baƙi muke suna waje."


"Baƙi kuma? Su waye?"

Hajiya Sadiya tace da mamaki.


"Eh ki min izinin shigowa dasu, sai ki gansu."


"To shigo dasu."

Hajiya Sadiya ta ce tana ɗaukar mayafi ta rufe jikinta dashi.


Fita Zarah tayi ta musu iso zuwa cikin falon, tare da sallama suka shiga. Jin sallamar Alhaji Mamman ya saka Hajiya Sadiya duban shi cike da mamaki ta bishi da kallo.


"Kinyi mamakin ganina Sadiya ko?"

Faɗin Alhaji Mamman yana duban Sadiya da ta haɗa rai.


"Sadiya!"

Alhaji Audu ya ƙirata dashi ta kai kallonta gurin shi tana gaishe sa don tana ganin girman shi.


"Sadiya ga Alhaji Mamman ya dawo gareki a karo na biyu yana neman aurenki idan har kin amince, bamu san dalilinsa na ƙin cikinki ba da har ya janyo saki tsakaninku, amma yanzu tunda kin haifa ya dawo zai aureki sai ku koma gidanku, fatan za ki yi haƙuri ki yafe masa ki karbi buƙatar shi."


Kan Hajiya Sadiya ƙasa.

"Ba zan koma gidanshi ba sai ya faɗa mini dalilin da yasa ya ƙi abin cikina lokaci ɗaya, kuma sai ya amince ita ma yana sonta zai bata kulawa kamar sauran yaran."


Sai lokacin Alhaji Mamman yayi magana.

"Sadiya ki fahimce ni, yarinyar nan ba alheri a tattare da ita, in har zan rayu da ita gida ɗaya to arzikina da komai nawa sai na rasa, farar ƙafa ce da ita."


Kallon da Hajiya Sadiya take watsa mishi ya sashi kasa ƙarasa maganar ya dakata.


"Ba zaka rayu da ita gida ɗaya ba. Kuma ka ke son in koma gidan ka? Ta ya kenan hakan zai faru?"

Hajiya Sadiya tace da zuciyarta ya fara tafasa tsabar baƙin ciki jin maganganun shi.


"Dama cewa nayi zan kaita gidan marayu, sai muna zuwa muna dubata, ko in kaita can Nijar gurin yaya Muhammad."


Dariyar baƙin ciki Hajiya Sadiya tayi tana girgiza kanta.

"Ba inda ƴata za taje ina raye, ka je kawai duk ranar da ka shirya karɓar mu ni da ita mu zauna a gidan ka sai ka zo."


"Sadiya ki fahimce ni, duk ..."


"Bana buƙata Alhaji Mamman."

Tace tana ɗaga mishi hannu alamar yayi shuru ta ɗauki Nuratu data farka tana ƙananan kuka ta wuce ciki da ita tana jijjigata.


Zarah da mijinta duk sun kasa cewa komai dan Alhaji Mamman ya basu mamaki jin furucin shi. Uba ya haifi ƴa ya tsana tun kafin tazo duniya. To wanene ya faɗa masa wannan maganar da har ya amince dashi ya yarda ya tsaka tsanar yarshi cikin zuciyarsa. Wannan alamar jahilci ne da yake buƙatar ƙarin haske na ilimi.


Hajiya Sadiya lallashin Nuratu tayi ta koma bacci ta kwantar ta ta fito suka ci gaba daga inda suka tsaya.


Duk yadda Alhaji Audu yayi Alhaji Mamman ya fahimci wannan abun jahilci ne kasawa yayi, sam ya toshe kunnuwanshi ya kasa gane gaskiya.


Abun ya ƙonawa Hajiya Sadiya rai daga ƙarshe tace.

"Alhaji Mamman bana ganin akwai sauran zaman aure a rayuwar mu. Rabon ya'ya ne ya haɗa mu kuma na haifesu, Allah raya su, don haka kawai Allah haɗa kowa da rabonsu."


"Kar kice haka Sadiya."

Zarah tace da sauri ganin ƙawartan zata yanke hukunci bisa dokin zuciya.


Bata kulata ba ta wuce ɗaki ta rabu dasu. Ta tsani Alhaji Mamman da duk abinda ya shafe sa, zata goge babin shi a rayuwarta ta kama mutuncinta kanta ta kula da ƴarta ta bata tarbiyya. Sauran yaran Allah raya mata su, inda rabon tana ganinsu in sun girma su neme ta.


Haka Alhaji Audu da matarshi suka fita cikin juyayin wannan lamarin.

...


Da daren Amma Jidda ta tambayi Alhaji Mamman ya su kayi da Mamin su Rahma dan ko ɗazu Muhsin ya tambaye ta yaushe Mami zata dawo.


"Mun rabu da Sadiya gaba ɗaya, tace ba zata dawo ba."


Da sauri Amma Jidda ta kalle shi.

"Mai yasa? Don Allah fa, ba ta tunanin yaranta."


"Ko ɗaya, ki bar maganar kawai."

Alhaji Mamman yace yana canza hiran dan shima ya tsani hiranta yanzu.


Jikin Amma Jidda sanyi sosai ta shiga damuwa jin abinda mijinta yace. Alƙawari ɗaya ta ɗaukarwa kanta sai ta haɗa uwa da ƴaƴanta.

...


Sati biyu da faruwar haka Aunti Zarah tayi tafiya da ba ta samu damar zuwa duba su Rahma ba. Amma Jidda tayi ta zuba idanu tun lokacin tana jiran zuwan Aunti Zarah shiru, ta damu sosai gashi bata san gidanta ba balle ta je.


Mami Sadiya kuwa hankalinta ta maida kan sana'ar ta na sai da atamfofi da Allah ya albarkacin sana'ar ana saya ba laifi duk da rabi ma bashi ne.


Ana biyan albashi aka tattara mata kuɗinta tayi sari da rabin kuɗin rabi kuma ta fara shirin tafiya Nijar dan sanar dasu halin da ake ciki.

Kwana biyu ta gama shiryawa abinta da ƴarta suka ɗauki hanya.

Yamma lis ta isa kai tsaye gidan Yaya Muhammad ta sauƙa kowa yayi mamakin ganinta da jaririya suna cewa bata sanar dasu ba, sai dai tayi murmushi.


Bata samu sun keɓe da Yayanta ba sai da safe taje gaishe sa ya karɓi Nuratu yana gani ya tambaye ta sauran yaran da mai gidanta.


Kan Mami Sadiya ƙasa tace.

"Mun rabu Yaya, yau wata takwas kenan."


"Rabuwa kuma Halima? Garin yaya? Mai ya faru yayi zafi? Kuma shine bani da labari? A ina kike zaune yanzu?"


A nutse Mami Sadiya ta sanar dashi komai tana yi yana girgiza kansa har ta gama.


"Shikenan Halima Allah yasa haka shi yafi alheri. Ita kuma Allah rayata kici gaba da addu'a Allah zai kawo mafita. Su Rahma kuma Allah rayasu."


Ameen ta amsa dashi yana ta mata nasiha a ƙarshe ta sanar dashi tana son saida kayan gadonta ta ƙara jari dan kula da kanta da ƴarta. Bai hanata ba yace zai saka Shanun a kasuwa zuwa yamma in aka saya zai kawo mata kuɗin. Godiya ta mishi kafin ta mishi sallama.


Kwanan Mami Sadiya biyu ta dawo bayan ta karɓi kuɗin gadonta hannun yayanta da take jin shi tamkar Mahaifinta, sauran biyun kam tama fara mance kamarsu dan tun kafin aurenta suka bar ƙasar.


Dawowarta da sati ɗaya ta saro kaya masu yawa daga atamfofi, kayan yara, da takalma. Yau aka kawo mata kayan cikin falonta ta baza tana kallo tana ware masu tsadar da mai ƙaramin kuɗi.

Gefenta Nuratu tana wasa da kafafunta, yarinyar ƴar wata huɗu tayi wayo abinta, duhu take yi yarinyar irin na mahaifinta dan bata biyo hasken yayunta da suka ɗauka na ta ba, amma kallo ɗaya zaka mata kasan tafi su kyau duk da jaririya ce, irin baƙaƙe masu kyau ne da ake ƙira chocolate beauty.


Sallama taji daga waje cikin baƙuwar murya fita tayi tana leƙawa taga mace da zata haura shekaru talatin gefenta yaranta ne Muhsin da Rahma da Hasiya tana ɗauke da Rukayya data maƙale mata.


Ihu Rahma da Hasiya suka saka ganin Mamin su suna yin kanta da gudu ta rumgumesu cikin farin ciki tana miƙa Muhsin hannu alamar yazo ya tsaya yana son tuna inda ya santa, sai da tace.

"Muhsy na babana."

Kafin yaron ya kwace hannunshi cikin na Amma Jidda ya faɗa kan Mamin shi.


Murmushi kawai Amma Jidda take ganin burinta ya fara cika, ganin uwa da ƴaƴan sun haɗu ta dalilinta.


"Sannu da zuwa."


Mami tace tana miƙewa tsaye ganin ta barta tsaye. Murmushi kawai tayi ta girgiza mata kanta tana miƙa mata Rukayya, yarinyar taƙi zuwa.


"Ki barta kawai ta jima ne, a hankali zata tuna ni. Mu shiga ciki."


Bayan sun zauna yaran suka nufi gurin Nuratu Rahma ta ɗauketa Hasiya na ƙoƙarin karɓar ta.


"Zaku jefar ta ai. Kawo ta nan mu ganta."


Yaran basu so ba suka miƙa Amma Jidda ita ta karɓeta tana gani, Rukayya dake gefenta itama ta zauna alamar a bata yarinyar.


"Mami waye ce?"

Cewar Rahma tana leƙa fuskar Nuratu.


"Ƙanwar ku ce, sunanta Nuratu."


"Allah rayata, bamu samu zuwa ba sai yanzu."

Amma Jidda tace.


"Ameen, sai dai har yanzu ban shaida ki ba."


Shuru Amma Jidda tayi ta rasa ta ina zata sanar da ita hakan ya bawa Mami Sadiya gaskata abinda yazo ranta.


"Auntyn su Rahma."


Kai Amma Jidda ta ɗaga tace.

"Tun da naji labarin rabuwar ku hankalina ya kasa kwanciya, wallahi kinji na rantse ban aure Abban su ba dan ina son shi sai dan in haɗa kan zuri'ar ku. A rayuwata ina tausayin ya'ya da mahaifiya take barinsu ta fita. Tun bayan da ki kayi nesa dasu Rahma, bayan kwana biyu sai Aunti Zarah tazo ganinsu ko kin sani ko a'a, kwana biyu bata zo ba sai jiya, shine na tambayeta gidanki dan ina kawo miki yaran kuna samun lokaci kuna gaisawa da juna, kar gaba sun girma su manta dake musamman yanzu Rukayya da take ƙarama zata iya mantawa da komai daya shafe ki, hakan kuma ba zai min daɗi ba.

Munyi magana da Abban su yace min yazo kunyi magana amma abun bai yi ba, sam banji daɗi ba, dan Allah Mamin Rahma kiyi hakuri ki koma kan ya'yan ki, ki duba yadda su kayi kewan ki, suna buƙatar ki kusa dasu."


Tabbas in har yadda Amma Jidda ta nuna mata tana son ƴaƴanta har cikin ranta ne to ta yarda ko bayan ranta zata kula mata dasu. Gashi nan taga alama yadda suka sake da ita, da bata basu fuska ko kusa ba za su zo inda take ba balle har tayi tunanin kawo mata su.


"Dan Allah Mamin su kiyi tunani akai."


Sai lokaci Mami Sadiya ta buɗe baki.

"Kiyi hakuri amma zama ya ƙare tsakani na da Alhaji Mamman. Ga yarana na baki amana kici gaba da kula dasu, duk lokacin da kike so zaki iya kawo su in gansu bazan takura miki ba."


"Dan Allah kar kice haka ki duba yaranki."

Amma Jidda tace alaman roƙo. Mami Sadiya ta duba yaranta da sun zagaye Nuratu da take cinyar Amma Jidda hatta ɗanta Al-ameen da ido kawai ya zuba mata yana kallonta.


Tana son kasancewa tare dasu har girmansu da aurensu amma abinda mahaifinsu yake so ba za tayi ba. Gwara su su rayu da mahaifinsu da ta kai Nuratu gidan marayu ta girma.


"Ba zai yiwa, kici gaba da kula dasu ɗa na kowa ne."


Shuru Amma Jidda tayi ta rasa mafita, Mami Sadiya ta miƙe ta kawo musu ruwa da abinci data girka dan kanta. Sun ci sosai yaran anan Rukayya ta sake jikinta ta shiga cikin su, tun tana bin Mamin ta da ido har ta ganeta ta fara binta duk inda za taje haka Muhsin ma dama shikam ta saba.


Abin yayiwa Amma Jidda daɗi ganin yaran sun sake da mahaifiyar su shiga su fita tare. Awansu huɗu suka fara shirin tafiya. Anan Mami Sadiya ta ɗauka yarantan takalma iri ɗaya gaba ɗaya da kayan yara kala ɗaɗɗaya.

Rahma, Hasiya, Rukayya nasu iri ɗaya sai na Al-ameen da Muhsin iri daya. Duk yadda Amma Jidda ta hanata ƙi tayi tace su riƙe.

Godiya su kayi tayi yaran suna murna.

Sai da aka zo wajen tafiya suka ce sam sai sun tafi da Nuratu, Rukayya har da kukanta akan a bar ta, dakyar dai aka shawo kansu su ka tafi gida bayan alƙawarin ƙarya da aka musu zasu zo gobe.

Mami taji daɗin ganin yaranta, ta yaba Amma Jidda da ƙoƙarinta ganin tana kula da yaranta, ta san zata basu kulawa har girmansu, sai lokacin taji hankalinta ya kwanta.

...

Gidan Alhaji Mamman Bashir.


Vote.

Comments.

Share.