Page47-48
ZAFIN KISHI!!!!!!!!
Written story
By
AUTAR AREWA.
Please kada ku manta da dannamana subscribe a tasharmu ta Autah Novel Tv,A manhajar You Tube channel.
Bismallahi Rahamanir Rahim.
📝.................A ranar aka kammala yima Zulaihat test na jininta da aka ɗauka.Tunda aka kawo result ɗin Zulaihat ta kara suma a karo na biyu saboda tsabar dimaucewa da tayi.Haka dai likitoci suka yi Discharge nasu ganin jinkinsu yayi sauki bayan sun ɗora su akan hanyar magunguna.
Tun daga Asibiti Zulaihat ta saka kuka tana cewa ita wallahi bazata koma gidan Habib ba tunda har ya ci amanarta ya kwaso masu cuta,Ganin da gaske take yi yasaka mamansu tayi dialing Nomber Abban su Zulaihat.Bayan ya ɗaga take sanarmai da abinda ya faru.cewa yayi A bata wayar,Cikin dasashiyar murya irin ta wacce taci kuka ta koshi ta ce "Assalamu Alaikum Abba ina yini?"
Daga ɗayan bangaren Murya cike da ɓacin rai ya amsa da "Ban yini ba, na ce ban yiniba Zulaihat,Wallahi Zulaihat ki fita a idona na rufe,Ai yanzu baki isa ki guji Habubi ba,keda Habubi idan kinga kun rabu to sai dai mutuwa ce zata rabaku,Koma meye kece kika ja tunda kin nunawa duniya bakiso mijinki ya kara aure,Alhalin Allah ya halatta yin haka".
Haka yayi ta faɗa ta inda ya shiga batanan yake fita ba,A karshe yaba Mamansu Umarnin a mayar da ita gidan mijinta,Kada wanda ya kawomai ita cikin gidansa.
Tana ji tana gani haka aka mayar da ita gidan Habib.
Shiko Habib tunda Driver ya ɗauke shi da mama sai kanwar shi Aliya Direct gidan Mama suka sauka,Dan yana bukatar hutu, Har zuwa wannan lokacin yaki yarda ya haɗa ido huɗu da Mama,Saboda wata irin kunyarta da yake ji.Sannan akwai abinda yake ɗauremai kai,game da wannan al'amari,Amma dole ya ɗauki ƙaddarar da Allah yasa suka tsintsi kansu a ciki.
Da dare kuwa tunda Mama ta saka aka kawomai abinci ya ci,Bayan yayi salla tare da shan maganin shi,Haka Mama ta ce Driver ya zo ya mayar da shi gidan shi.
Badan ranshi yaso ba haka ya tafi.
Domin yana zillimin tashin hankalin da zai tadda a gidan.Tun bayan tafiyarshi Mama ta shiga ruɗanin wannan al'amari, Ga sauran yan'uwanta sai faman kiranta suke yi a waya dan su ji Meya faru aka fasa auren, Amma haka taki sanar da kowa bayan kanin Baban su Habubi daya sani.
A hankali motar tayi parking a harabar gidan,Cikin tafiya irin ta marasa lafiya ya fito daga Motar.Jin yadda zuciyar shi ta tsananta bugawa da sauri da sauri,daka Ganshi kasan yana jin jiki,ganin yadda cikin kwana ɗaya ya zabge tamkar wanda yayi shekara a kwance.hakan yasa yayi saurin dafe kahon zuciyar shi ko zai ji sassauci.
Bai tadda kowa a cikin falon ba,Direct ya wuce Bedroom ɗin shi.Jin ko hayaniyar yaran bai ji ba.Cikin sanyin jiki ya tura kofar tare da mayarwa ya rufe.Jakar kayan daya shigo da ita ya aje bisa gado,Bayan ya ciro wayar shi ya tsurama screen ɗin wayar Ido tamkar yana nazarin wani abu aciki.
A bangaren amarya Habiba kuwa sosai take ganin zallar madarar soyayya gurin mai gidan nata muktar,Itama ba laifi tana kokarin bashi kulawa Dukda tana kunyar shi.Tunda aka kaita Inaajo bata je ba,sai kanwar Mamanta data turo ɗiyarta Mai suna Rukayya takaimata magunguna tare da nunamata yadda zata yi amfani da su.Kasancewar Rukayya tafita wayewa anan duk ta kara yimata Lectures akan yadda zata rike mijinta.
Haka suka yini kasancewar Mukhtar ya fita asibiti saboda kiran gaggawa daya samu.
Sai gab da sallar magriba kafin Habiba ta rako Rukayya har bakin gate tare da bata kayan kwalliya da kuɗin mota.
Cike da nishaɗi ta koma cikin gidan.Tare da tunanin Idan Mukhtar ya dawo zata ce ya siyomata karamar waya saboda tana bukatar ta rinka jin Muryar Babanta.
Fuska cike da annashuwa ta fito falon,wasu Mayun riga da wando ne a jikinta masu ɗaukar hankali,wando 3 qeuter ne mai santsi sai yar rigar wacce da kaɗan ta ziro kugunta,Ash color ne masu salki.sai hular wanka data ɗora saman kanta da dukkan alamu daga bacci ta tashi. kusa da Hindatu ta zauna tana cewa
"Wash Allah"
Dubanta ta mayar ga Baby da take faman danna wata ta ce "Pls Baby Kawoman abinci ina jin Yunwa"
Baby da "To" ta amsa kafin ta mike zuwa kitchen.
Fuskantar Hindatu tayi tana cewa "Kinsan haryanzu ban kira mutum ba,Dukda an sanar da ni ɗazu an sallame su daga asibiti".
"Kallanta Hindatu tayi kafin ta numfasa ta ce "Ba shi ya kamata ki kiraba,Ita ya kamata ki fara kira,Domin kara yimata albishir".
Dariya suka saki gaba ɗayansu kafin ta fara kokarin kiran wayar Zulaihat.
Zulaihat da tunda ta shigo ɗakin take aikin kuka,Dukda yadda ta ji kanta yana ciwo amma ta kasa daina kukan.jin ringin ɗin wayarta yasa tayi saurin lalibo wayar tana tsagaita kukan,Ita duk a tunanin ta kawarta ce Ikikima sai taga Nomber IHSAN wacce daman tana da serving ɗinta.
Aje wayar tayi tare da dafe gefen barin kanta wanda take ji tamkar zai bare gida biyu saboda azabar ciwo da yake yimata.
Haka wayar ta katse ba tare da tayi picking ba.
Again wani kiran ya kara shigowa a karo na biyu.
Cike da fusata ta danna receive call ta fara cewa " Dan Allah ki kyale ni,Bayan kin gama da rayuwata kuma me kike nema a cikin rayuwata wanda ya rage mai amfani a gare Ni"?
Dariyar da ta ji sun fashe da ita yasa tayi sororo tana sauraren su.
Saida Suka gaji da dariyar kafin cike da izza Hindatu ta ce "Kaga manyan mata a gidan ASP Habib,Ai bai kamata ace tun yanzu kin karaya ba,Kefa Jaruma ce,Kuma gwarzuwa,wacce take so tayi rayuwa da mijinta ita kaɗai ba tare da wata ba".
Hindatu na direwa IHSAN ta ɗora da faɗin "To yau zanyimaki albishir da cewa na barmaki mijin ki har'abada ki zauna da abinki ke ɗaya,Ko wata yanzu nasan bazata aure shi ko"? Tayi tambayar cikin dariya.
Kuka Hindatu ta saka,cikin kukan take cewa "Tabbas yanzu bana da sauran wani kuzari daya rageman,Domin kuwa sai yanzu na gane kuskuren da nayi tun farko,Amma kinsan ban cancanci irin wannan hukuncin ba,Wallahi da wannan abin da kika yiman to da Habib kika aura muka zauna da yafi sauki a gare ni"ta kare magar tana gurnanin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.
A tare suka amsa mata da "Sai yanzu kika gane haka kenan? To ai kin makara,sai dai ki kiyaye gaba amma wanna ta riga data gama faruwa".
Ta buɗe baki da niyyar ta kara yin magana kit ta ji sun yanke call ɗin .
Haka ta kara saka wani kukan,mai cike da nadama haɗi da dana sani.
Tana haka har aka yi sallar isha'i.Dakyar ta mike ta shiga bathroom.
A bangaren su IHSAN da Hindatu kuwa bayan sun kare kiran dariyar mugunta suka sheke da ita harda rike ciki,kafin bayan sun tsagaita da dariya suka ɗora da labarin yadda plan ɗin ya tafi tare da kokarin shirya next plan.
Dakyar Habib ya Kara gabatar da Wanka tare da ɗauro alwala,A zaune yayi sallar isha'i tare da shafa'i da wuturi, Ya zauna yana tasbihi ga Allah (S W A) Tare Da mika godiyar shi akan jarabawar da yayimasu.
Wayar shi ya ɗauko jin tana ringing alamun ana kiranshi.Sunan Oganshi ya gani saman screen ɗin.
Cikin sanyi jiki yayi picking call ɗin bayan ya kara a kunne yayi sallama cikin natsuwa.
"Assalamu Alaikum"
A can ɗayan bangaren bayan ya amsa cikin harshen turanci yake yimai ya jiki, kasancewar musulmi ne amma yana da yare ,shiyasa Hausar shi bata da daɗi.
Bayan ya katse kiran a hankali ya rarrafa saman gadon, tare da rungume filo ya fara sauke ajiyar zuciya akai akai kamar wanda yayi gudun tsere......!
By
AUTAR AREWA
✍️✍️✍️✍️✍️