ƊAYA MAFARIN IRGA.
ƊAYA MAFARIN IRGA.
MAFARI.
Da gudunta ta fito daga babbar makarantar 'yan mata ta gaba da primary mai suna Fikra Acadamic kamar wata ƙaramar yarinya, bakinta ya ƙi rufuwa dan murna da farinciki. Tare abun hawa ta yi kai tsaye ta bayyana masa wajen da zai kaita suka yi ciniki suka ɗauki hanya sai gida. Burinta ɗaya ne Abbunta ya ga sakammakonta don ya cika mata alƙawarinta na siyan (lap-top) kasancewar ta matsawa Yaya Sulaiman da aro da zarar ya dawo gida to kuwa zata ɗauka ta hau bincike.
Ita ɗin kwai ta da ƙwaƙwar bincike hakan yasa ta san abubuwa da dama game da Jiharta da kuma fanin karatunta dama wasu abubuwan dama da suka fi ƙarfin shekarunta. Cikin zumuɗi ta biya mai abun hawan ta faɗa cikin gidan tana ƙwala kiran,
"Ummuna Abbuna ku zo ku gan!"
Sulaiman dake zaune duk ya gaji da zirga-zirgar makaranta ya dubeta ransa a ɓace cike da ginshirar da ra zamo masa al'ada kamar zai daketa,
"Ke ni ki yi mini shiru ko na doke ki."
A shagwaɓe ta taɓe fuska yanayinta kenan komai zata yi sai ta yi a shagwaɓe da dama ɗauka suke sangarta ce kawai ɗabi'arta ce a hakan ita kanta bata san tana yi ba.
"Kai fa haka ka ke ka cika takura. Baka sani ba wani daddaɗan labari zan baka kawo kunnuwanka faka-faka da su kamar funkasau ɗin Ummu na sallah..."
Duk cikin sigar wasa da barkwanci ta ke maganar, hakan duk yana cikin (nature) ɗabi'arta akwai ta da son barkwanci da wasa amma ga inda tasan ba zata siyawa kanta raini da ƙasƙanci ba.
Miƙewa ya yi ya yi kanta ta kwasa da gudu suka soma zagaye ɗakin tana dariya hakan ya bayyana haƙoranta a waje ajajjere farare tas dasu sunata sheƙi, kasa kamata ya yi inda kasan ɗiyar mutan (China) wajan calikanci haka ta ke dariya ta ke tana ƙarawa ɗan bakinta na furta,
"Sule sulalallan karas, abin kashewar yara"
Tana yi tana gwalo da dariya tare da sake buga Ƙafa irin na tsokana da tura ciwo a zuciya.
"Jamila da Jamilu a ɗaura musu aure da Malam Sule dogo."
Cikin shammata ya cafketa, ta saki ƙara ga tsoron tsiya ga kuma tsokana,
"Wana kama?"
Marairaicewa ta yi tana nuna alamun nadama,
"Haba Yaya ila amu angon Sa..."
Dum! Wani sauti mai firgitarwa ya doki kunnuwansu wanda ya jaza masa sakinta ita kuwa Shukuriya sakin ƙara ta yi ta ƙanƙameshi tana ihu. Sautin ya cigaba da tashi cike da amon firgitarwa ga ma'abota saurara ƙarar ababban fashewa kawai ke ratsa kunnuwansu. Sun shafe minti huɗu a haka wata karar ta sake tashi mai karfin gaske sai ta ƙwace ta faɗa ɗaki da gudu ta shige ƙarƙashin gado tana ƙwala kiran,
"Ummuna! Abbuna!!"
"Gaddafi dake ɗaki ya fito da gudunsa dai-dai lokacin shi ma Sulaiman ya faɗa ɗakin da yake mallakinsa ɓuya ya yi cikin banɗaki can ƙarshan bahon wanka daga ƙasa akwai wani ɗan saƙo ƙarami kamar dai yadda Shukuriyar ta yi. Mutan gidan gaba ɗaya sun rikice a guje mahaifansu suka fito. Kafin su yi wani yunƙuri garada majiya ƙarfi kimanin mutum goma sun shigo tare da yi musu ƙawanya wato zagayesu daga inda suke suna jiyo sautin iface-ifacen jama'ar dake waje gaba ɗaya jikinsu rawa yake yi Gaddafi cikin ci da zuci ya furta,
"Mene ne ya kawo ku? Me ku ke nema?"
Wani kakkaura baƙi cikinsu ya shaƙo, mahaifiyarsu, a sukwane Gaddafi ya yi wata katantawa ya doki ƙirjinsa. Ga mamakinsa ƙyam! Ya tsaya ko gezau sai ma dariyar mugunta da yake yi. Ya zuciya ya sake tahowa tamkar matashin ɓauna ya dumfareshi suka soma dambe sai ga shi ya ɗaga shi ya damfara da ƙasa tare da binsa ya murƙushe tamkar wani zaki a fillin dawa.
Wani ne ya sake yunƙurin tahowa ya ɗaga shi ya maka da ƙasa sai ga shi ya fasa masa baki su Shukuriyya suka leƙo suna dubansu basu yi mamaki ba kasancewar Yayan nasu ƙarfi ne da shi kamar Soja. Amma sun yaba jarumtarsa sai da ya raunata mutum uku kafin daga bisani su sami nasarar damƙeshi suka ɗaɗɗaureshi. Babban cikinsu ya dubi sauran ya furta,
"Wannan gwani ne za mu je da shi ku cika masa aiki."
Take wani ƙarami cikinsu ya watsa masa wani ruwa a fuska sai suka sake shi abin mamaki ko gezau bai yi ba bai kuma yi wani yunƙuri ba bale ya sake nuna jarumtarsa a karo na biyu. Babban ya sake cakumo Yakura mahaifiyarsu ta saki ƙara ya fyaɗata da ƙasa da ido ya yi wa yaran inkiya, suka gane in da ya dosa nan suka hau faɗawa ɗakunan gidan suna binciken gidan gaba ɗayansa.
Da sauri su Shukuriyya suka koma maɓoyarsu suna ƙunshe bakunansu ƙirjinsu banda dukan uku-uku babu abinda ya ke. Sossai suka shiga dudduba gidan amma basu ga koda ƙwaro ba bale su Shukuriyya. Dawowa suka yi tare da sanar masa abinda ya ke faruwa. Cikin tsantsar rashin imani a wajan ya kwance zariyar wandonsa ya nufi Yakura da iya ƙarfinsa, ko ajikin Gaddafi sai ma binsu da idanu ya ke yi.
Cikin tashin hankali Goni ya yi kansa amma kan ya ƙarasa sun caka masa wuƙa a agara, ya yanke jiki ya faɗi ƙasa tim! Suka hau ƙyalƙyala dariya yana ji yana gani aka lallata iyalinsa a kan idonsa daga bisani suka yi masa yankan rago suka fice bayan sun sawa gidan wuta suka tafi da Gaddafi da mahaifiyarsu. Duk abim da ke faruwa akan idanun Shukuriyya sai dai ta kasa ƙwaƙwaran motsi, minti biyar da fitarsu. Shukuriyya da Sulaiman suka fito.
Da gudunsu suka fito amma ganin gawar mahaifinsu a zube yasa Sulaiman sakin wata giggitaciyar ƙara ya finciki hannun Shukuriya data faɗa kan gawar tana tumami. Ƙwace hannunta ta yi ta nufi ma'ajiyar waya da gudu ta ɗauka ta dana kira aka ɗaga daga ɗayan ɓarin,
"Wake magana?"
Cikin kuka da rawar murya ta furta,
"Ofishin taimakon gaggawa kutaima ka mana wasu 'yan ta'ada ne suka shigo sun kashe mana mahaifi sun tafi da yayanmu da mahaifiyarmu...Eh titin Askira layin Bama...Wata wawwar fincika Sulaiman ya yi mata sakammakon wutar data kama ganga-ganga ta saki wayar suka nufi ƙofar fita gadan-gadan. Gaba ɗaya wuta ta mammaye ƙofar fitowar haka suka ratsa ta ƙofar baya wadda ta kasance ƙofar sirri suka fice daga gidan.
***
Garin shiru babu hayaniyya sai ƙauri da balbalin wuta da yake ci ta ko'ina sai kuma kukan yara ƙanana wanda da dama basu wuce goyo ba Sulaiman ya ja hannunta saboda motsin da suka ji kwanciya suka yi cikin gawarwwaki tamkar matattu suka ɗauke numfashi. Suna ji suna wucewa suna takasu da takalma masu katako a ƙasansa amma babu wanda ya yi gigin motsawa cikinsu.
Wucewar rabin sa a suka fice daga unguwar suka rarrafa ƙarƙashin wani kwalbati suka samu suka shige suna hangen yadda ake safa da marwar fita da matasan 'yan mata tsofafi kuma wasu a yanka wasu a wulasu cikin wuta.
A haka har suka fice daga garin tsit babu kowa. Cikin ikon Allah sai ga saukar ruwa kamar da bakin ƙwarya wanda ya haddasa mutuwar wutar da take ci a cikin garin. Sulaiman haka ya rufu kan Shukuriyya saboda kadda ruwa ya daketa, haka suka yini suka kwana cikin wannan hali banda karkarwar rawar ɗari (rawar sanyi) babu abinda suke yi kamar mazari. Baƙincikin Shukuriyya ɗaya ta dinga tambayar kanta,
"Shin ina jami'an tsaro suke?"
Tambayar data gaza samun amsarta kenan. Garin ya yi wani irun tsit kamar babu mai rai cikinsa ta yi jugum tana tunanin rayuwar da zasu fuskanta. Washegari da sassafe motocin jami'an tsaro suka fara shigowa, Shukuriyya ji ta yi kamar ta kashesu don baƙinciki wata irin tsanar jami'an ce ta ɗarsu a ranta, shin me yasa basu kawo musu agaji ba lokacin da suke cikin masifar? Mene ne amfanin kayan jikinsu? Dama ba dan al'ummah suke aikin ba?
Su ne tambayoyin data dinga jerewa kanta. Lokacin da aka soma binciken gawarwakin ne hankalin Shukuriya ya ƙara masifar tashi, kuka take sossai tare da wurgawa jami'an mugun kallo mai cike da tuhuma ana haka aka fito da gawar mahaifinta take Sulaiman ya ƙwala ƙara ya fice a guje yana kururuwa bisa akasi wata mota ta shigo cike da jami'an tsaro ta dake shi ji ka ke fus! Kansa ya fashe take ya baƙuncin lahira. Nan fa ta sake sakin kuka tana faɗin,
"Shikenan ba ni da kowa sai Allah Ummu ta tafi Abbu ya tafi Yaya ma ya tafi wayyo! Rayuwata..."
Wani dattijo cikin ma'aikatan ne ya ƙaraso tare da riƙe hannunta,
"Yi haƙuri baiwar Allah..."
Ta ɗago idonta jajjir ta kali dattijon da ya yi furucin sanye da kakinsu na sojoji.
"Dalla ka ƙyaleni! Ai duk kuka ja, da kunzo kun bamu agaji da ba ayi asarar al'ummah har haka ba. Mene ne amfanin kayan jikinku in ba kare lafiyar al'ummah ba? Kaico kunci amanar ƙasarku..."
Cikin zafin nama wani ɗan tsamurmurin ma'aikaci ya nufota ya kwaɗeta da mari, ai kuwa yana ɗaukewa dattijon ya yi masa mari uku a jere. Ya ɗora da faɗin,
"Baka da hankali ne? Kabarta ta ji da rashin da ta yi mana, ƙarya ta yi? Ko mun zo a daidai lokacin daya da ce ne?"
Gaba ɗaya jikinsu ya yi sanyi suna dubansa, da alama shi ne shugaban tawagar haka aka kwashe matattun da suka mutu, wanda suka jikkata aka wuce dasu cikin jihar Maiduguri zuwa babban asibiti yara kuma aka wuce dasu gidan sansani. Sun sami mutane da yawa kimanin mutum dubu biyar amma yara ƙanana sun fi yawa sai tsofaffi da magidanta yawan 'yan matan azzaluman sun yi awan gaba dasu.