IN-LAWS

Enamored

by @realsmasher

đź’ đź’ đź’ đź’ đź’ 

©®2021.





           *♡IN-LAWS¸.•💥*

     



BĘŹ.

  *HAWWA MUH'D USMAN.*

    (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).đź’•

*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

     

*FREE PAGE*


                07-08


#Enamored 


   Murmushi Abba yayi yana gyaÉ—a kai yace "tou Shaheed! Yanzu dai bazan iya cewa komai akan maganarka da *FADWAH* ba,saboda ban taÉ“a kawo zan yi mata aure da wuri ba,na so ace sai da tayi karatu kamar sauran Ć´an uwanta,ta yanda ko ba na raye za ta iya dogara da kanta,ba sai tana nema ayi mata ba.. Sai dai kamar yanda ka mutunta ni,baka fara tararta a hanya ba,kazo neman izini na,wannan dalilin yasa na maka izinin fara zuwa gurinta,kuna gaisawa kafin Allah yasa ta Ć™arasa secondary school É—inta" wani murmushi Shaheed yayi cike da jin daÉ—i yace "in dai wannan ne Abba nima bazan hanata karatu ba ko da tana gidana,tunda na nima Ć´an uwana suna yi" Abba yace "tou! Shi kenan,yanzu kana iya fara zuwa gurinta,even though suna shirin fara SSCE,and za tayi JAMB cikin watan nan" Shaheed yace "na gode sosai Abba,Allah ya saka da alkhairi ya Ć™ara girma.." Abba yayi murmushi yace "ameen²" cike da alkunya duk da zumuÉ—in da Shaheed yake ya ganni kafin ya wuce yace "Abba zan wuce gida.." Abba yace "baza ka jira tazo ku gaisa ba?" Shyly Shaheed yayi Ć™asa da kai bai ce komai ba sai murmushin da yake yi,Abba yayi murmushi ya tashi ya shiga cikin gida bayan sun yi sallama,yana tafiya Shaheed ya É—ago kansa yayi wani murmushi yana lumshe idanuwansa,a hankali yayi baya yayi balance akan armchair da yake,then ya zubawa Ć™ofar shogowa idanuwansa. Sanda Abba ya shiga cikin gidan direct parlon Aunty ya nufo yayi sallama,dukanmu muna zaune su Yaa Umar suna hira,ni kuma gama cin abinci na kenan,sanda muka amsa yana kallona daga tsayen da yake yace "Fadwah tashi kije parlon baĆ™i ku gaisa" sanda na É—ago na kalli Aunty da su Yaa Umar kamar munafuka kafin nace "toh Abba!" Then na tashi na saka hijab É—ina har Ć™asa na nufi Ć™ofa na fita,Aunty ta bini da kallo kafin ta janye idanuwanta akaina tana taÉ“e baki,Abba yayi murmushi ya juya zai fita yace "Asiya zo ina son magana dake" Aunty dai mamaki yasa bata iya magana ba ta tashi tabi Abba suka fita. Ina fita cikin sanyi na wuce parlon baĆ™in Abba,ta Ć™ofar cikin gida na buÉ—e,sanda nayi sallama kafin na shiga,idanuwansa suka sauka kaina kamar yanda ya gama sawa ransa,calmly ya amsa min har na zauna bai daina kallona ba,haka nan duk na ji na takura saboda idanuwansa da nake ji a kaina,ina lumshe lumshe idanuna nace "ina yini?" A hankali ya lumshe idanuwansa ya buÉ—e yana sauke numfashi ya amsa min,yace "how are u,and ur grad?" Ina fidgeting fingers É—ina nace "Alhamdulillah!" Yace "Allah ya sanya alkhairi,yasa na tsoron Allah ne.." Nace "ameen" daga haka dukan mu muka yi shiru,sai can shi yayi breaking silence É—in yace "let me introduce myself to u kou?" Da yaga na yi shiru ban amsa ba,yace "My name is Muhammad Mahmoud,but siblings É—ina and all my family suna kirana da Shaheed.. I'm the first born of my parents,mahaifina shi ne Alh Mahmoud Tafeeda,i've 4 siblings,maza biyu mata biyu.. Na yi karatuna har zuwa masters in law department.. Now i'm working with a chamber.. Briefly wannan shi ne history na,sauran abunda ban sanar miki ba idan an kwana biyu za ki sani." Slowly na gyaÉ—a kaina bance komai ba,yace "and u?" Kaina a Ć™asa saboda yau É—in was the first day of my life da saurayi ya sakani gaba,duk sai nake jina not comfortably,kamar wanda idan nayi magana zai kama nace "sss.. Suna na.. Fadwah" sai nayi shiru na kasa ci gaba,yayi murmunshinsa mai kyau yana kallona yace "yes! Say whatever u want to,ba tafiya zanyi dake ba idan kin sanar min" calmly ina runtse idanuwa nace "I'm the last born of my parents,i've four elder brothers,Yaa Umar was the first born a gurin Aunty'nmu and he's a militant,and then Yaa Mukhtar,then Yaa Waleed da nake bi" murmushi yayi yace "woww! U gotta nice name" a hankali nace "thank u.." Yace "wane school kike zuwa?" Nace "bradford college.." Yana kallona yace "wane guri kenan?" Nace "gandu new layout behind trade fair.." Yace "oohhh! I understand.. When za ku fara exams?" Nace "soon" yace "how many days or weeks ya rage muku?" Nace "just 2 weeks" ya gyaÉ—a kai yace "maa sha Allah,Allah ya bada sa'a.." A hankali na amsa "ameen." Daga nan babu wanda ya sake magana,can da aka jima ya tashi yana kallona yace "i'm going Fadwahhh.. Thanks for ur time,sai na sake dawowa.." Wani irin thunder storm naji har cikin kaina,sanda naji kamar ya fi kowa iya faÉ—ar suna na,na lumshe idanuwana na buÉ—e,calmly nace "nima na gode sosai.. A gaida mutanen gida" cike da zolaya yace "zan faÉ—a musu idan na koma,but wa zance tana gaishesu?" Not minded nace "Fadwah mana" yayi murmushi yace "ai basu san me sunan ba" a hankali na É—ago muka haÉ—a ido,na kautar da kaina ina murmushi na watsa hannuwa nace "tou ai nima ban san wa zance ba" yace "alright! Ni na san me zan ce musu" da sauri na wakgo ina buÉ—a idanuwa nace "me za kace tou?" Yace "ina ruwanki da abunda zan faÉ—a?" ShagwaÉ“e fuska nayi kamar zan yi kuka nace "ayyah mana Yaa Shaheed,ni fa Ć™anwarka ce" sosai yayi murmushi yana buÉ—a idanuwansa akaina yace "woww! I really love it,do it again please" zaro idanuwa nayi nace "what?" Yace "shagwaÉ“ar da kika yi nake son gani" saurin rufe fuskata nayi da palms É—ina shyly,yayi É—an murmushi mai sauti yace "ohh! Har da kunya ma?" Na Ć™yalĆ™ale da dariya,a hankali ya dunga takowa sanda yazo kusa da ni ya durĆ™usa in a way style a gabana,calmly yace "É—an buÉ—e fuskar tou zan tafi" slowly na fara yin Ć™asa da hannuna,sai dai na kasa kallonsa,yayi min murmushi yace "thank u for everything.. I appreciate" murmushi kawai na iya yi masa,ya miĆ™e kaÉ—an hannayensa zube cikin aljihun light green É—in shaddarsa,Ć™amshinsa duk ya cika parlon yace "kiyi haĆ™uri na zo ban kawo miki gift ba.. But next time in sha Allah.." Nayi Ć™asa da kai na Ć™i cewa komai,yace "ko bakya so ne?" Na É—ago kaina kaÉ—an nace "what?" Yace "i said zan kawo maki gift É—inki na ji kin yi shiru" still na sake kautar da kai ban ce komai ba,ya É—aga shoulders yace "any ways.. Till we met" nace "Allah ya kaimu" yace "ameen.." Instead of ya tafi kamar yanda yace,sai naga ya tsaya yana operating tsadadden wayarsa mai idon mujiya (iPhone 12 pro) sanda ya kai wayar kunnensa yace "Hello! Where are u friend?" Yaa Waleed da ya É—auki wayar yace "ina cikin gida" yace "okay! Fito muyi sallama zan wuce.." Daga haka ya sauke wayar ya É—an juyo yana kallona yace "Oops! Ur digit please *My Jewel"* sanda na É—ago ina juya idanuwana nace "ba'a barni na fara riĆ™e waya ba" kallona ya tsayi kamar yana mamaki,sai kuma naji yace "okay! Amma za'a bari na baki?" Na watsa hannuwa nace "don't know" yace "ya kamata ki sani" nace "tou! Zan tambaya" yace "wa za ki tambaya?" Nace "Abban mu ko Aunty" yace "alright! But before na dawo,za muna gaisawa ta wayar Waleed?" Nace "ai basa ba ni wayarsu" yace "uhmn! Zan kirasa nace ya baki" a hankali na gyaÉ—a kai nace "tou!" Yace "bye.." Nayi murmushi kafin nace "bye" wayarsa ya fara ring,sanda ya É—aga min hannu then ya juya ya fita yana ce min "ki gaisar min da Aunty da su Yaa Farouk" nace "za su ji" yana fita nayi baya a hankali na kwantar da kaina jikin wing É—in chair ina sauke numfashi,ina ta mamakin kaina da yanda na sake da shi though ban sanshi ba,sanda na gama calming kaina down then na tashi na É—auke tray na shiga gida ina sakin murmushi,zumuÉ—i duk ya cika ni kamar na janyo gobe nake ji,saboda yanda na matsu na sanarwa Umaimah labarin yau nima Abba ya barni na yi zance,kuma da kansa ma kira ni yace naje. Aunty kuwa lokacin da Abba ya kirata ta bishi,sanda suka shiga parlonsa,ya zauna saman kujera yana kallonta fuskarsa da murmushi ya fara bata labarin abunda ya faru,Aunty dai banda kallon Abbanmu babu abunda take yi,sanda yace "kawai saboda na san mahaifinsa shi yasa na barshi yazo gurinta amma da wani ne gaskiya haĆ™uri zan bashi" Aunty ta sauke numfashi tace "tou! Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Abba ya amsa da "ameen." Ina kwance É—akinmu around 9pm bayan tafiyarsa,Yaa Waleed ya Ć™walo min kira,lokacin har na yi shirin bacci na tashi na saka hijab na leĆ™o,yana kallona ya miĆ™o min wayarsa yace "dillah can karÉ“i ni ban son iyayi kin wani tsaya kallona" ina karÉ“a ya juya yayi shigewarsa É—akinsu,na juya nima a hankali ina turo baki,sanda na shiga É—aki na kwanta kan gado a hankali na kai wayar kunnena nayi sallama,calmly ya amsa min then na gaishesa,a hakankali ya dunga ja na da hira,sanda na saki jiki da shi sosai kafin yayi min sallama yace na kwanta,da Ć™yar bacci É“arawo ya É—auke ni ranar cike da nightmares iri²,washe gari da safe kuwa ina gama abunda nake nace wa Aunty zan shiga gurin Umaimah,tace "a dawo lafiya.." Na fita da sauri na faÉ—a gidansu,a can muka shiririce,ranar banda hiran abunda ya faru babu abunda muke yi. A haka lokaci yaita tafiya,shaĆ™uwa tana sake shiga tsakaninmu,lokacin kuma gaba É—aya kwanaki ne suka mana saura mu kammala neco É—inmu,duk zuwan Yaa Shaheed gurina a lokacin bai wuce a Ć™irga ba,duk da mun kusa 3 moths da haÉ—uwa,sai dai muna yin waya da shi sosai yanzu tun da ya siya min waya mai kyau da tsada,bai ba ni ba sai da ya sanarwa Abba. On the other side kuwa,duk abunda ke faruwa gaba É—aya Hjy Umma bata da labari,kasancewar Abba bai sanar mata ba,ranar da muka yi final exam,bayan na dawo gida muna waya da Yaa Shaheed yace "My Jewel ina son zuwa na ganki" murmushi nayi cike da tsokana nace "when?" Yace "ko yanzu kika ce zan bar office nazo na ganki" zaro idanuwa nayi nace "no! Ba yanzu ba" yace "sai yaushe?" Nace "Mmm!" Nayi kamar ina tunani,ya sassauta muryarsa yace "please Jewel kin san na yi missing É—inki,ki sassauta min ki bari nazo ko baza ki bari na jima ba,na ganki na tafi" dariya nayi nace "uhmn! Za ka zo ne?" Yace "ai baki ce kina son ganina ba" nace "tou kazo anjima" yace "alright! Thank u.. I love u" ina rufe idanuwana na faÉ—a saman kujera nace "nima.." Da sauri yace "kema me?" Da sauri nace "babu komai.. Sai ka zo" yayi murmushi yace "idan na zo za ki faÉ—a min abunda kika ce" muka kashe waya cikin farin ciki,it was there na tashi na cire kayana na wuce bathroom na watso ruwa haÉ—e da É—auro alwala na fito saboda it's almost asr. After isha lokacin ina ina zaune bedroom time-time nake É—aga kaina ina kallon agogo,na matsu banji ya kira ni ya ce min ya zo ba,duk na shiga damuwa ganin lokaci sai tafiya yake,nayi tagumi da hannu bibbiyu na zubawa wayata idanu,ji nake kamar zan fashe kuka,dai² nan kiransa ya shigo,da sauri na É—auka,calmly yace "My Jewel ga ni a Ć™ofar gida" da sauri nace "ga Ni nan fitowa" yayi murmushi yace "a fito lafiya *My princess jewel"* murmushi kawai nayi na ajiye wayar hannuna,sanda na É—auki turare na Ć™ara spraying a jikina na gyara veil É—ina then na fito,har Ć™asa na durĆ™usa gaban Aunty nace "Aunty zan je Yaa Shaheed ya zo yana jirana" tace "a dawo lafiya.. Ki gaishesa." Na amsa na miĆ™e na fita,sanda na fita har Ć™ofar gidanmu,na sameshi a cikin motarsa,na fara tafiya idanuna a Ć™asa,tunda ya hango fitowata ya buÉ—e motar ya sauko da Ć™afarsa É—aya,amma saboda mulki sai da ya jira har na Ć™arasa,sannan ya fito ya rufe motar,yana sanye da wani men's cashmere navy blue,hular kansa ya turata baya can,sosai yayi kyau sai Ć™amshi yake bazawa,sanda ya juyo yana kallona ya langaÉ“ar da kansa yace "My Jewel.." Kunya ce ta kamani nayi Ć™asa da idanuwana nace "sannu da zuwa" ya amsa yana kallona yace "i really missed u" ban kalleshi ba nace "mu Ć™arasa" yayi min wani kallo yace "ina magana kina basar da ni,zan yi maganin ki fa" dariya nayi nace "me nayi kuma?" Yace "ohooo! Kin sani ai" na sake yin murmushi muka jera muna tafiya,na buÉ—e mana parlon Abba'nmu kenan za mu shiga Mardiyya ta leĆ™o ta Ć™ofar cikin gida muka haÉ—a ido,na É—auke kai ban sake kallonta ba na bashi hanya ya shigo ya zauna,a hankali nace "ina zuwa please" yace "okay!" Na buÉ—e Ć™ofar na shiga cikin gida,a Ć™ofar É—akin Hjy Umma naga su Juwairiyya suna leĆ™owa,ban kallesu ba nayi wucewata,sanda na É—auko tray dana É—ora ruwa da lemo,sai snacks É—in da Aunty tayi mana na murnar grad É—inmu ni da Umaimah na fito,ina wucewa ta Ć™ofar É—akin Hjy Umma naji suna magana Mardiyya tana cewa "wallahi Umma da saurayi na ganta,ta buÉ—e musu parlon Abba'nmu" Hjy Umma tace "saurayi? Da ita Fadwan?" Mardiyya tace "wallahi Allah da gaske nake miki,idan baki yarda ba ki leĆ™a da kanki ko kisa a gano maki" mamaki duk ya cika Hjy Umma ta kasa magana,na taÉ“e baki nayi sallama bakin Ć™ofar shiga,operating waya na tarar da shi yana yi,na janyo coach na É—ora tray É—in hannuna,ban koma na zauna ba na buÉ—e lid É—in apple flavor drink É—in,ya É—ago yana kallon abunda nake yi,sanda na gama na É—ago muka haÉ—a ido nayi masa murmushi nace "Bismillah!" Yayi murmushi yace "na gode" then na koma na zauna...



   *This book is not for free,it's #200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit *** to be added in the paid group. Ćłan Niger za ku iya tuntuÉ“ar wannan number +22770766074.*


   



#Follow

#Vote

#Comment

#Share fisabilillah!

#Asli Smasher.