MAKTOUB!

Basketballing

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®2020.




          *♡MAKTOUB¸.•💥*

          ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))




*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

*Wattpad link:* ***


🆓 Pᴀɢᴇ..


🅿»7⃣

#Bᴀsᴋᴇᴛʙᴀʟʟɪɴɢ




     Kusan a tare motar Aadil da na Fawad suka shigo compound d'in gidan,but Aadil ne a gaba then Fawad,yana gama gyara parking ya bud'e motar,a nutse ya juya d'aukan jakar laptop d'insa da wayoyinsa dake seat d'in mai zaman banza,Fawad ya k'araso yana yi masa wani irin kallo yace "Ina ka shiga yau baka je office ba?" Sai da ya gama tattara belongings d'insa tsaf ya d'ago,a hankali kamar ba zai yi magana ba da farkon yana rufe motar a tak'aice yace "BUK!" Kallonsa Fawad yayi da mamaki a fuskarsa yace "Me kaje yi can?" Yana gama locking motar ya fara tafiya a nutse ya furta "Daddy ya sani zuwa na karb'i Aakiiy" Fawad ya fara biyo bayansa yace "When akayi hakan?" Bai damu da tsayawa ba yana tafiya zuwa hanyar flat d'insu yace "It was yesterday" Fawad ya gyad'a kai a hankali bai sake cewa komai ba,suna shiga parlor Aadil ya zube all his belongings saman table ya wuce bedroom,zaunawa Fawad yayi saman armchair yana zube wayoyinsa shima da car keys d'insa,a hankali kuma sai yayi relaxing kansa saman armchair yana mik'a because ya yi mugun gajiya,shi kad'ai yaje hospital yau duk wasu ayyuka da meetings kuma da suka taso shi ya jagoranta tunda baiga Aadil d'in bama bare suyi 50². Almost 35 minutes da shigar Aadil bedroom ya fito sanye da bathrobe bak'i wanda yayi masifar k'ara fito da hasken fatarsa ya sake bayyana shi matsayin kyakykyawa ajin farko,cikin takunsa na zaratan maza mai tattare da nutsuwa yana k'arasowa bai kalli inda Fawad yake ba ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa ya fara making call,in less than 3 minutes aka d'auka,idanunsa a lumshe yana matsa forehead d'insa da hannun hagunsa,cikin wani cool voice ya furta "please help and make some coffee,ki kawo yanzun" d'an jim yayi then ya cire wayar daga kunnensa ya ajiye,ya juya ya koma bedroom,lokacin da yake fitowa bayan ya shirya cikin k'ananun kaya,polo t-shirt ne sanye a jikinsa da trouser white sai d'an adon bak'i kad'an a jiki da aka yi rubutu,sumar kansa gwanin sha'awa ya sha gyara kamar ba'a saka masa ruwa,bai gama zaunawa ba aka yi knocking door,a hankali yace "Come in" turo k'ofar akayi a hankali da wani siririn murya aka furta "Assalamu alaikum" ya amsa bai damu ya kalli gurin ba,farar kyakykyawar k'afarta ta fara saukewa cikin parlor'n then a hankali ta shigo tana d'an waigawa ganin bata ga mutum ba,kyakykyawar matashiya ce wacce duka a shekaru da wuya ta k'arasa su Ismat sai wara manyan idanunta take yi,tasowa yayi daga cikin chair da ya nutse ganin bata k'araso ba a hankali yace "Ba ni nan" saurin kallon direction d'insa da taji maganarsa tayi sai kuma tayi murmushi ta fara takowa hannunta rik'e da medium tray na silver,samansa da flask da cups biyu because ta san yana wahala ace shi kad'ai ne,kamar yadda tayi tunani kuwa ta gansu taren dama ta sani yadda suke kamar twins kullum suna manne da juna,tun yarintarsu ma da Mami take bada labari d'aya baya rabuwa da d'aya shi yasa komai nasu tare suke yinsa,yanzun ne da girma ya fara zuwa aka fara samun wasu changes suka fara intervene tsakaninsu,saman table ta ajiye a hankali tace "Masa'al khair Akhiiy" yana lumshe idanunsa ya furta "Kaiifak?" Da yar siriruwar maganarta tace "Alhamdulillah" ya sauke numfashi kad'an yana d'aukan cup,da sauri ta d'auka tace "let me help",ajiyewa yayi ya koma baya,ta matso a hankali ta d'auki cup d'in ta sunkuya tana zubawa,Fawad ya bud'e idanunsa yana tashi zaune,da sauri ta bud'e idanu tace "Akhiiy! Dama ba bacci kake ba?" Yayi mata murmushi a hankali yace "Yeah! Yau nayi stressing kaina da yawa shi yasa" ta yi murmushi kad'an tace "Good evening" yace "Evening,how are u?" Tace "Alhamdulillah! Ya aiki?" Lumshe ido Aadil yayi yana karb'ar cup da take mik'o masa a hankali cikin rashin son magana yace "U can now leave" d'an bud'a ido tayi za tayi magana ya bud'e shanyayyun gray eyes d'insa ya zuba mata su,da sauri ta tashi tana tura baki ta fara tafiya,tana daf za ta fita Fawad ya kalleta yana sakin murmushi yace *"NAINA!"* A hankali ta waiwayo bata amsa ba,yace "Mami ta dawo?" Tace "Ehh! Tana tare da Daddy ma" yace "Alright!" Juyawa tayi ta fara tafiya Aadil ya bita da kallo har ta fita,a hankali ya d'an tab'e baki ya fara shan coffee. Mik'ewa Fawad yayi bayan fitar Naina,yana kallon Aadil da ya had'e rai kamar wanda aka yiwa wani abu yace "Kai dai halinka sai kai" yana fad'a ya wuce hanyar bedroom,Aadil dai bai ko kalli inda ya bi ba ya ci gaba da sipping coffee d'insa har sanda Fawad d'in ya fito cikin k'ananun kaya da suka ainihin amsar jikinsa,yana k'arasowa ya d'auka cup ya tsiyaya coffee ya koma saman rug ya zauna had'e da mik'e k'afafunsa and leaning his back against chair da yake zaune kusa da yayi powering TV,because shi dai bai shirya ma zaman shirun da suke yi ba,even though idan da sabo ya kamata ace ya jima da sabawan,saboda dama haka suke yi idan su biyu ne kamar wasu kurame sai dai kowa yayi abunda yake ga zai fishshesa,kasancewar shi Aadil tun asalinsa dama mutum ne da bai cika son yawan magana ba,idan yana guri ko baya nan ma ba ganewa ake ba saboda masifaffen miskilancinsa,matuk'ar kaga yana magana kuma tabbatar shi da Mami ne,tsayin rayuwarsa da ita kad'ai ne yake iya dogon hira,a bayanta kuwa har yanzun ba'a samu na biyu ba,duk adadin shak'uwarsa da Fawad ba sosai za ka gansa suna magana ba,idan kaga suna dogon magana kuma sai dai abunda ya shafi company,while shi kuma Fawad tun asalinsa ya kasance mutum mai yawan magana,idan har ya zo guri dole sai an sanshi,sannan ba shi da wahalar sabawa da mutane,wannan dalilin yasa lokuta da yawa bai cika son zaman gidan ba tun da suka kammala PhD d'insu suka dawo Nigeria sai lokaci²,saboda shi a d'abi'unsa ba ya son zaman shiru,sab'anin da can baya kafin su tafi karatu da komai nasa yake gidan,since aka yaye su yake hannun Mami,ita ta rainesu tare da Aadil kasancewarsa d'a agurin k'anwar Proff Junayd Mutallab mahaifin Aadil. Waigawa yayi inda ya ajiye wayoyinsa ya d'auka,a hankali ya bud'e net ya shiga dandalin sada zumunta na whatsapp,yana sakin sanyayyan murmushi yaje kan contact d'inta yayi mata sallama because yau tun safen da ya tafi office bai samu lokacin kansa ba,da yaga text d'in yayi delivered sai ya sake yin murmushinsa mai kyau,ya san tana kusa baza'a jima ba zai ga ta yi replying,da aka jima kad'an ya ji ta shiru,here ya fara tunanin kiranta yaji,as soon as kiran wayar ya shiga,a time d'in Ismat ta kammala shirinta kenan ta fito daga bedroom,tana jin ring d'in da wayar yake tayi murmushi because ta san waye zai kirata a irin lokacin,sai da wayar ya d'an jima yana ring har kamar zai yanke then tayi answering call d'in,da yake akwai earpiece a kunnenta tana ci gaba da tafiya tayi masa sallama,Fawad dake zaune ya mayar da kansa ya kwantar saman kujera ya lumshe idanunsa,jin sanyayyar maganarta a kunnensa yasa he didn't know when ya sauke ajiyar zuciya,tayi murmushi kad'an tace "Good evening" a hankali da wani irin kasalar dake cin jikinsa ya furta "Evening dear,how are u?" Tace "Alhamdulillah,ya aiki?" Yace "Aiki Alhamdulillah,ya skul fa?" Tayi ajiyar zuciya kad'an tace "Mun baro shi" amsar ta ne ya bashi dariya yace "Mmm! Sai gobe kenan?" Ta kad'a kai first then tace "Ehh!" Ya kad'a kai a hankali yace "Maa sha Allah,Allah kaimu" tace "Ameen" shiru suka yi dukansu daga haka,lokacin ta gama sakkowa kenan daga stairs ta hango Mom tana shigowa parlor da sauri tace "Mmm! We will talk later please" idanunsa a lumshe har lokacin yace "Kina wani abu ne yanzun?" Da sauri tace "Ehh!" Yace "Alright! Ya za'ayi na sani idan kin gama?" Saurin katsesa tayi tace "I'll call" yayi murmushi yace "Alright! Bye" tayi sauri tace "Bye!" Sai ta fara yanke wayar,da d'an gudunta ta nufi Mom dake shigowa tana fad'in "Oyoyo Mom!" Mom da bata ganta ba sai dai maganarta da taji ta waiwayo a hankali tana sakin murmushi tace "Sweetheart! Kun dawo?" Ta kad'a kai tana sakin murmushi ta rungume Mom tace "Sannu da dawowa Mom,ya aiki?" Mom da ta bud'a idanu tana kallon y'arta kamar yau ta fara ganin ta saka irin kayan tace "Waw! U look breathe taken sweetheart!" Dariya Ismat tayi ta karb'i handbag d'in Mom tace "Thank u Mom" Mom ta rik'e hannun Ismat suka fara tafiya kamar wasu friends tace "Ina habibtiiy'n ki?" Murmushi kwance saman fuskar Ismat tace "Tana bedroom" mom tace "Ba za ta fito ba?" Da sauri tace "Tana shiryawa ne" Mom tace "Alright!" Dai² lokacin suna shiga bedroom d'in Mom,Ismat ta wuce wajen da take ajiye bags ta sak'ale,ta dawo ta wuce bathroom tana b'ata rai take cewa "Mom! Kuma kinga ba mu yi test d'in ba" Mom dake rage kayan jikinta tace "Why?" Ismat ta bud'a hannu tace "Wai Dr ba ya nan,shi ne sai ya turo k'aninsa,but Mom kin san wani abu kuma?" Mom dake jira Ismat ta gama had'a mata ruwan wanka tace "Sai kin fad'a" ta juyo tana kallon door d'in duk da ba ta hango Mom da murmushi a fuskarta tace "Allah duka y'an gidansu sunji dad'i Mom,suna da ilimi sosai both boko da addini,idan kinga k'aninsa kou sai kinyi mamaki,duka ba zai wuce sa'an Bhai ba fa,amma kuma shima Dr ne,sannan ya masifar iya lecture,ni dai Mom kinga ba na son zama da yawa,but yau duk 3 hours da ya share yana lecture gani nayi sun tafi kamar ma fa bai fi 30 minutes da shigowa ba,wai sai cewa yayi lokaci yayi sai wani had'uwar" Mom dake sakin murmushi tana sauraren maganar da Ismat take yi tace "Lallai sweetheart da alama yau kinji dad'in lecture d'in Dr" tayi murmushi tana juyowa za ta fito tace "sure Mom,ko lecture Dr Fadl ban tab'a jin dad'in sa ba kamar na k'aninsa,ko don yana takuramu saboda ya sanmu ne ohoo! Yayi ta tambayar mutane kamar mu kad'ai yake koyarwa,ni dai dama zan fad'i ma Yaa Jawahir tace yayi hak'uri ya daina tambayata,duk ya tambaye ni Allah rikicewa nake na kasa amsashi yadda ya dace" Mom dai dariya tayi tace "Idan da rabon ya saki lecture wata rana kuma maga yadda za'ayi" zaro ido tayi tace "Tabbb' Mom ranar ai nutsewa kad'ai ne bazan yi ba" Murmushi Mom tayi tace "Lallai sweetheart! Bari na fito kou?" Tayi murmushi tace "Ok Mom" ta wuce wajen kayan da Mom ta ajiye saman bed,d'aukansu tayi a hankali tana sakin murmushi ta wuce da su laundry,almost 15 minutes Mom ta fito sanye da bathrobe pink colour gashin kanta nad'e a cikin pink d'in towel,tana kallon Ismat dake kwance saman bed d'inta ta wuce gefen mirror ta zauna saman stool bata yi mata magana ba,a hankali ta d'auki hand dryer ta kunna,Ismat ta bud'e idanunta a hankali ta taso,ta fara tura phone d'inta a cikin pocket ta nufo inda Mom take,Mom tana kallonta tana murmushi tace "je kiyi kwanciyar ki sweetheart na san kin gaji yau" murmushi tayi tace "No! Mom kawo nayi miki" kad'a kai Mom ta sake yi then ta bata dryer d'in,ta san indai Ismat na kusa ba za ta bari tayi da kanta ba,she always use to help her,matuk'ar ba rashin lafiya take yi ko ba ta kusa ba,idan ta fito wanka ita take gyara mata gashinta,even ruwan wanka indai tana nan ba ta bari ta had'a da kanta,sai da ta tabbatar ta gyarawa Mom kyakykywan gashinta then tayi mata kalba da shi guda d'aya daya sauka ta gefen wuyanta,ita dama Mom haka take yi idan ta dawo daga aiki ba ta saka ribbon a jikin gashin,Ismat tana gamawa tayi murmushi tace "Bari na jiraki a parlor Mom" Mom tace "Alright" a hankali Ismat tace "Sai kin fito" Mom ta shafa gefen fuskarta,Ismat tayi murmushi then ta juya ta fara tafiya,har ta kusa door Mom tace "Yayanku fa?" Ismat ta d'an tsaya kad'an tace "Ni dai ban gansa ba" Mom ta kad'a kai tace "Shi kenan" wucewa Ismat tayi ta fita,Mom ma ta mik'e ta wuce arean closet. A parlor Ismat ta tarar da Badriyah kwance saman armchair,ta zauna kad'an kusa da ita Badriyah ta bud'e idanu tana kallonta,a hankali tace "Ina kika je kuma?" Murmushi Ismat tayi tace "Ina tare da Mom" Badriyah ta tashi zaune tace "Ta dawo ne?" Ismat ta kad'a mata kai tace "Yes! But yanzun za ta fito ma" komawa Badriyah tayi ta kwanta had'e da d'ora kanta a thighs d'in Ismat tana lumshe idanu tace "alright!" Ta ci gaba clicking wayarta dake hannunta. While itama Ismat here ta fara making call as she promised him idan ta gama za ta kira,kiran yana tafiya ya katse ya kirata,ta zubawa wayar idanu na wasu seconds tana murmushi then ta d'auka ta kai kunne,hira sosai sukayi but idan ba wanda yake kula da motsawar bakinta ba sam ba zai ce ga abunda take yi ba,hatta Badriyah dake kwance saman k'afafunta da yake hankalinta na kan phone d'inta sam bata ma san me Ismat d'in take yi ba. In just a short period of time,wani irin shak'uwa mai k'arfin gaske ya shigo tsakanin Ismat da Fawad,even though basu tab'a sanin juna ba four about 3 weeks da fara alak'arsu,hasalima basu tab'a ko da ganin pic d'in juna ba,since ya tambaya tace ba ta tura pic bai sake tambayarta ba,but he always use his chance suyi hira ya ga tana farin ciki,ko wane lokaci abunda yake buri shi ne yasa ta cikin nishad'i,yayin da zuwa lokacin ita kanta a nata b'angaren ya kasance idan ma bai kirata ba ita za ta kira shi,sai dai idan ya ga kiran ya katse ya kirata back,Badriyah kam da yake zuwa lokacin Barraq ya koma lagos duk a sake take,sai dai itama yanzun tun daga incident d'in da ya faru ranar ya hanasu fita bata sake sha'awar tace za su fita ba,idan ya zama dole kuma sai dai ta zare jikinta ta tafi ita d'aya,while a gurin Ismat yanzun hakan ba ya wani damunta dan Badriyah ta fita ta barta ita kad'ai wuyar dai ace ta kunna network d'inta ko Fawad ya kira ta,yanzun za ka ganta tana zuba smile,duk da Badriyah a yanzun kusan kamar ta yiwa kanta fad'a ta d'an nutsu,magana ma a gidan ba sosai take saka kanta a ciki ba,ana cikin wannan yanayin ne kuma aka kawo lefen Jawahir,inda aka karb'i kayan a nan gidan uncle d'inta Proff Imraan mahaifin Ismat kasancewar shi ne waliyyin amarya,akwatuna na gani a fad'a guda 12,kowanne cike da kaya maa sha Allah,golds kad'ai da aka lissafa wanda aka zuba cikin lefen sun kai 5 manya,banda bangles da rings da suke daban,aka tsayar da ranar biki next 2 weeks.


*Few days later...*


    Shirye²n biki sun kankama a kowane gefe,yayin da a gefen su Ismat ya kasance kusan kullum basa zama,ba sa nan ba sa can kullum suna hanya,saboda kusan su ne manyan k'awaye da Jawahir d'in take ji da su,sam ta ajiye batun wani shekaru uku da ta basu,da yake kuma dama ba wani girman jiki ne da ita ba idan ba wanda ya sani ba sai yace sa'anni ne su d'in,Barraq kam tuni ya koma lagos,kuma har zuwa lokacin tun da ya tafi sau uku kad'ai suka yi waya da Ismat saboda yanayin aikinsa,lokacin da aka kawo lefe kuma da suka yi waya,suna maganar bikin here yayi musu aiken manyan laces masu tsada ita da Badriyah had'e da shoes and bags duk na fitar biki,ai kam Badriyah tana ganin kayan duk ta rud'e ta ji dad'i sosai,here ta kirasa tayi masa godiya,yanayin da ta nuna masa jin dad'inta yayi ta mamakin canjin da aka samu game da ita,dan ko yanayin maganarta ma ya sauya sosai babu wannan rashin kunyar da tsiwar a ciki,and it was there ya tuna mata batun gift da yace zai bata idan ta bawa Jawahir hak'uri kafin ya tafi sannan ta daina rashin kunya,ita kuma sai bata tuna masa ba,here yace idan ya zo biki za su had'u sai ta fad'i abunda take so,tayi ta murna tana yi masa godiya,while a gefe d'aya duk wannan nisan kwanakin da aka d'auka a gefen Ismat kuwa ko da wasa ta k'i yarda ta sanar da Fawad ainihin abunda yake faruwa,game da batun bikin Jawahir ma ko a hira bata tab'a masa maganar ba,har kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa. Ma su iya magana na cewa "Duk abunda kaga bai zo ba,tabbas sai dai idan ba'a saka masa rana ba",kasancewar yau Wednesday and yau d'in shi ne ranar farko da suka tsara za su fara gudanar da event d'in bikin Jawahir,though ba wani abu ne suka shirya na musamman ba,basketball ne aka shirya yinsa na iya y'an matan da suke b'angaren amarya sai wanda za su wakililci family'n ango suma za su zo nan gidan su Ismat kasancewar a nan y'an matan suke,da yamman kamar yadda suka tsara after asr prayer y'an matan duk da za suyi wasan sun hallara a k'aton compound na gidan su Ismat da yake nan kamar wani gari guda,tun daga get har ciki ko ina an gyarasa anyi decoration mai jan hankali,lokacin da amarya Jawahir da manyan k'awayenta su Ismat suka fito tare da wasu classmates d'inta Aanisah da Farha suma duk da yake y'ay'an manyan Proffs ne,sun san juna sosai tare suka yi karatu har service ma suka fito batch 'B' tare suka zauna da aka kaisu platoon 7 lokacin da suka shiga cam,rayuwarsu da komai tare suka yi har suka yi service suka gama cikin shekarar,sai kuma ga bikin Jawahir d'in ya taso bayan kammalawarsu. Sanye suke da women's basketballs jersey,rigar sleeveless blue da ratsin pink sai wanduna suma kalar rigunansu wanda tsayinsu duka yake iya guiwa,direct basketball court dake cikin gidan suka nufa bayan fitowarsu,suna shiga team suka ware,su Ismat sune kayansu yake blue da ratsin pink,while su kuma family'n Dr FADL na su yake blue da ratsin yellow,bayan anyi gaisuwa tsakanin y'an wasa,su 6 ne duka a team d'in,Ismat ita ce kan gaba because ta fi sauran k'warewa,bayanta Badriyah sai su Aanisah da Farha k'awayen Jawahir sai wata cousin d'in Ismat y'ar k'anwar Mom Hasna da wata cousin d'in su Badriyah,yayin da team d'in gidan ango Naina ta kasance akan gaba sai Madeeha da wasu relatives d'insu da za suyi wasan tare su 4,duk sun had'e cikin sport wear da yayi mugun karb'ar su,murmushi Ismat tayi ta waiga tana kallon wajen court d'in inda mutane suke zaune cikin theatre,fes idanunta suka sauka kan Mom dake kallonta tana sakin murmushi,wani k'arfin guiwar da taji ya shigeta yasa tayi ajiyar zuciya tayi blowing kiss ma Mom tana dariya,here wasan ya fara. In less than 10 minutes da saka wasan,Ismat ta ci first ball inda ta jefa daga nisan 2 metres,nan family'n amarya suka d'auki ihu da tafin murna,aka fara kiran sunan *ISMAT* ana sake zugata,while family'n ango su kuma ganin an ci su,suka sake yunk'urawa a nan wasa ya d'auki zafi,Naina ma da yake ba baya bace wajen basketball since Ismat taci ball d'in farko ta rik'e wuta ta k'i bari a sake cinsu,while itama Ismat ta rik'e wuta tak'i yarda a ci su,haka aka dunga wasan kowa yak'i bari a ci garinsu,ana cikin haka wasan ya kusan k'arshe Ismat ta sake cin wani ball d'in,ihun murna wajen family ba'a cewa komai,bakin kowa sunan Ismat yake kira,tun daga nan kuma sai ba'a sake cin ball ba har aka tashi 2-0,akayi awarding family'n ango saboda amsa gayyata,bayan an k'are wasan duka y'an matan suka yi cikin gida,su Naina k'annen ango suka yi sallama da su Ismat suka wuce gida sai sun had'u gurin dinner...




  #The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,na yi cancelling VIP saboda wasu dalilai.


*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*


1.ACCOUNT DETAILS.* 


Acct name:Hauwa Muhammad Usman

Acct number:0060746882 

Bank name:Access Bank

Phone number:***

City:Kano city.


  *A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*


*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*


***


*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*



  For any other problem/complain/enquiry chat via ***.




   

#Share pls.

#Asli Smasher.