Negative emotional
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*Wattpad link:* ***
🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»9⃣
#Nᴇɢᴀᴛɪᴠᴇ ᴇᴍᴏᴛɪᴏɴᴀʟ
Wani irin lumshe idanu yayi a hankali ya sake bud'e idanunsa ya sauke su akanta,fuskarsa d'auke da kinda beautiful smile,idanunsa sun d'an yi wani irin sauyawa na lokaci d'aya yana kallonta ya sake mata hannu,hawayen bak'in ciki da suka kawo idanunta suka gangaro saman fuskarta a guje,duk kuma ita ba komai ya fi b'ata mata rai ba a lokacin sama da yadda yake jifanta da murmushi,sosai abun ya k'untatawa zuciyarta,tana kallonsa da wani irin b'acin rai a cikin idanunta bata iya cewa komai ba hurriedly ta juya za ta bar wajen hannayenta rik'e da gown d'inta data tattare,ta tsinto asalin muryarsa cikin wannan cool voice d'in san da ta sani yana fad'in "Thanks dear!" Wani irin k'amewa Ismat tayi a gurin kamar wacce aka yi pausing,jin muryar da ko cikin taron arfa ta had'u da mai shi baza ta tab'a iya mantawa da shi ba a cikin kunnuwanta da kwakwalwarta yana mata yawo,a rikice ta waigo tana yi masa wani irin surprised look hawaye suna ci gaba da saukowa saman fuskarta,ya sake yi mata murmushi a karo na babu adadi,a hankali ba tare da ya sake yin magana ba daga haka ya juya ya fara tafiya. Aadil dake zaune cikin mota tun d'azun after ya gama yiwa su Naina lik'i yana jiran Fawad ya fito su wuce gida,kamar ance ya d'ago daga nan inda yake zaune cikin mota,his illuminated eyes suka sauka kan Fawad dake rik'e da hannun yarinyar da Naina tasa suka gaisa not too long,wani irin fad'uwa yaji gabansa yana yi sakamakon abunda ya gani a hankali ya zuba musu idanunsa,babu zato yana kallonsu da wani irin yanayin da ya kasa gane na mene ne kawai yaga yarinyar ta fallawa Fawad mari,abunda ya faru akan idanunsa lokaci d'aya ya matuk'ar girgiza shi,sai dai bai san ma lokacin da wani irin smirk ya kufce masa ba,ya sake lumshe idanunsa ya bud'e ya ci gaba da kallonsu cikin wani irin yanayin da ya kasa rarrabewa farin ciki yake ko damuwa? Gani yayi Fawad ya yi murmushi then a hankali ya sake mata hannu,abun da ya faru ya mugun bawa Aadil mamaki ya d'aure masa kai,but bai gama mamaki ba sai da yaga lokaci d'aya yarinyar da take niyyar fara gudu,saboda a yadda ta tattare riga kana kallo za ka san a shirye take ta k'arawa k'afafunta sauri,kawai sai yaga ta yi wani irin juyawa tana kallon Fawad d'in da fuskar mamaki hawaye suna sauka kan fuskarta,bud'a idanu ya sake yi sosai yana kallonsu gabansa sai fad'uwa yake,still a nutsen yaga Fawad ya sake yi mata murmushi bai yi magana ba ya fara tahowa wajen motar da yake ciki. Aadil couldn't stop looking at them har lokacin da Fawad ya bud'e motar ya shiga side na mai zaman banza,ya waiwaya continue looking at him lokacin yana kwantar da kansa jikin seat had'e da lumshe idanunsa ya kasa magana,almost 5minutes yana kallonsa then ya sake juyawa ya kalli inda take,har lokacin tana nan yadda Fawad ya barta rik'e da gown d'inta ta kasa tafiya,Aadil dai mamaki duk ya hana masa tada motar su tafi,sai da Fawad ya d'ago a hankali yana tura hular kansa baya yace "Muje mana,tsaiwar me muke yi kuma?" Tab'e baki Aadil yayi a nutse ya d'auke kai ya tada motar ya fara riding,sun d'auki hanyar komawa gida motar yayi wani irin shiru,though dama hakan ba sabon abu bane a gurinsu,a nutse Aadil ya katse shirun ta hanyar watsowa Fawad tambayar "Me ya had'a ku?" Lumsassun idanunsa Fawad ya bud'e a hankali,kamar ba zai yi magana ba da farko ya dunga kallon Aadil then a hankali yace "Nothing" Aadil ya waiwayo ya kalleshi kad'an yace "Haka kawai ta mare ka kenan?" Saurin bud'a idanu Fawad yayi yace "Na fad'a maka babu komai" Aadil yayi murmushi yace "Akwai abunda kake b'oyewa my friend" a d'an fusace Fawad dake kallon waje yace "Tunda ka sani mene ne abun tambaya?" D'age eyebrows Aadil yayi a hankali ya tab'e baki yace "Saboda ina son sani" siririn tsaki Fawad ya saki then kamar ba ya son cewa komai ya fara sanar da Aadil d'in alak'arsa da Ismat,Aadil dake driven lokacin suna tsayawa dai² get d'in gidansu ya dunga kallon Fawad da wani irin mamaki,but bai ce komai ba yayi horn malam Jibrilla ya bud'e masa get,yana riding motar zuwa cikin compound d'in gidan,a hankali kamar ba ya son magana yace "U made a mistake!" Saurin kallonsa Fawad yayi yana bud'a idanu yace "Mistake wane iri?" Aadil yana gyara parking a carline yace "Me yasa za ka rik'e mata hannu daga had'uwar ku?" Shiru fawad yayi yana kallosa,Aadil yace "U know! Kai ba muharraminta bane right? Besides baku had'a ko wane irin alak'a na jini ba,hasalima baku tab'a ganin juna ba,on ur own speculation nake so ka fad'a min,me ya kamata kayi a had'uwar ku na farko wanda zai bawa alak'ar ku damar d'orewa? Me kake tunanin ita za ta d'auki abunda ya faru tsakanin ku yanzun? Daga had'uwa ka rike mata hannu,duk wacce ta san mutuncin kanta yaya za ta d'auki al'amarin,and then mene ne ya kamata tayi wanda zai ba ta kariya,mutane ba za suyi zarginta ba a matsayin y'a mace da aka ga namiji ya rik'e?" Wani irin kallo Fawad ya dunga yi masa,sai dai ya kasa magana,a hankali Aadil ya bud'e motar yana fita yace "A nawa ganin bata yi ba dai² ba dan ta yi haka,saboda haka kada ma ka fara ganin laifinta because ta yi abunda ya dace a matsayinta na mace da bata tab'a saninka ba!" Fitowa Fawad yayi ya kasa magana har lokacin sai kalaman Aadil dake masa yawo a cikin kai,daga haka babu wanda ya sake magana suka fara tafiya zuwa flat d'insu. Ismat kam since Fawad ya barta tsaye a gurin,gaba d'aya taji jikinta ya kasa motsawa,duk wasu veins dake taimakawa jikinta lokaci d'aya suka yi wani irin rik'ewar da all joints dake jikinta suma suka yi mata wani irin nauyin da even index finger d'inta ya gagareta d'agawa bare ta iya motsa harshenta,shin idan ma ta bud'e bakintan mene ne take da shi da za ta fad'a masa har ya saurara? Wane magana za ta iya furtawa a yanayin da take ciki? Cewa za tayi yayi hak'uri ko kuma yaya za tayi? Haka ta bishi da wani irin kallon tsoro ba tare da ta iya tsinana komai ba har motar da ya shiga ya bar gurin,while a gefe guda kuma abunda ya faru tsakaninsu tuni y'an gulma sun kai rahoton sa cikin hall d'in,jin kunnen Mom taji wai Ismat ta mari wani a waje yanzun,amma ba'a san me yayi mata ba an dai ganshi ya rik'eta,hankalinta a tashe ta fito wajen tare da su Mama,tana hango Ismat tsaye tun kafin ta k'araso ta fara kiranta "Sweetheart!" In a kinda frightful voice,Ismat dake tsaye tun d'azun kamar wata statue banda hawaye babu abunda yake sauka kan fuskarta,Mom tana zuwa ta rungume ta tana dudduba ta da fad'in "What happened dear? Ya miki wani abu ne?" Fad'awa jikin Mom tayi hurriedly ta fashe da wani irin kukan da kamar ana fizgar mata rai,hankalin Mom da su Mama ya sake tashi ganin irin kukan da take yi,babu shiri Mom ta rik'eta securely a jikinta,Badriyah dake cikin mota tana jiran Ismat taron jama'ar da ta hango yasa ta fito da sauri daga mota tana ratsawa,Mom tana ganinta tayi saurin rik'ota hankalinta a tashe a rud'e tace "Maza habibtiiy wuce muje gida" tana maganar tana had'a hannayensu duka tana rik'ewa,because a lokacin Dr Hinda ta mugun tsorata da yadda taga gudan jininta tana wani irin kuka mai ban tsoro,da kyar Mama suka samar musu hanya suka fita cikin taron mutane,a gaggauce tana saka su a mota ta shige ko sallamar da su Mama suke yi mata bata iya tsayawa ta amsa ba tasa driver yaja motar suka bar wajen da mugun gudu,tunda suka taho tunani iri² suke kawowa ran Mom,zuciyarta ta yi wani irin rauni musamman ganin yadda Ismat take kwance jikinta ta kasa daina kuka,suna k'arasowa gida ko parking bata jira driver ya dai²ta ba ta fito rik'e da hannun Ismat suka wuce cikin gidan,bata saketa ba sai da suka je bedroom d'inta,tana kallon Ismat da har lokacin hawaye sunk'i daina zuba a fuskarta da wani irin fuskar damuwa ta rik'e kafad'unta tana kallonta,cikin sanyayyar magana irin na lallashi mai cike da tsoro ta furta "Sweetheart!" Ismat bata iya amsawa ba,Mom tace "Kalle ni,maza d'ago idanunki ki fad'a min ya miki wani abu ne?" Kasa d'agowa Ismat tayi ta kalli Mom,Mom cikin wani irin tashin hankali ta sake furta "Sweetheart! Maza ki sanar da ni abunda guy d'in yayi miki,me ya miki? Ya rik'e ki ko kuwa? What happened between ke da shi? Ki fad'a min kafin na kira Daddy ko Yayanki!" Wani mugun fad'uwa gaban Ismat yayi jin Mom tana ambaton za ta sanar da Barraq hurriedly ta d'ago idanunta da suka fara kumbura fuskarta kansa yayi wani irin jaa abunku da farin mutum,tana kallon Mom tashin hankali k'arara cikin idanunta ta fara girgiza kai alamun a'a,Mom cikin damuwa tana share mata hawaye ta furta "idan ba kya so Daddy ko Barraq suji maganar nan,maza tou ki sanar da ni abunda yayi miki" da kyar muryarta har ya dashe ta bud'e baki tace "Hannu kad'ai ya rik'e min" tana fad'an haka tayi shiru bata sake cewa wani abu ba,Mom tana jin abunda Ismat ta fad'a bata san lokacin da ta sauke wani mugun ajiyar zuciya ba ta rungume ta tightly,a hankali ta lumshe idanunta tana shafa bayanta ta furta "Alhamdulillah alaa kulli halin" sai kuma ta sake d'agota ta zaunar da ita gefen bed and to sit next to Ismat d'in tana calming nata,a hankali ta kamo Ismat ta kwantar a jikinta tana shafata da wani irin murya tace "Allah ya taimakesa iya nan ya tsaya.." Saurin d'agowa Ismat tayi da kumburarrun idanunta tana kallon Mom tace "Mom!" Sai kuma tayi shiru ta kasa cewa komai,Mom tana kallon wani guri ta furta "Da ace yayi kuskuren tab'a min mutuncinki,surely ba zan tab'a barinsa ya sha ruwa cikin salama ba,dole ne ya biya zunubin da ya aikata.." Wani irin kallon Mom Ismat ta dunga yi a hankali tana zare jikinta daga na Mom tace "Mom please! Ni ki bar cewa komai kan maganar" a hankali Mom tana shafa kanta tana kallonta ta girgiza kai tace "Baza ki fahimci damuwar ba baby,amma tunda Allah ya tsare alhamdulillah,yanzun maza ki tashi kije kiyi wanka,sai ki kwanta kada kanki yayi ciwo" lumshe idanunta tayi a hankali tana turo baki cike da shagwab'a tace "Ni dai a gurinki zan kwanta yau" Mom ta lumshe idanu a hankali tayi tak'aitaccen murmushi tace "Ita kuma habibtiiy'n ki barta ita da waye?" Shagwab'a Ismat ta fara yiwa Mom tana cewa "ni dai gaskiya Mom a nan zanyi bacci na" Mom tace "A'a kije bedroom d'inku" a hankali Ismat tace "shi kenan bari na tafi tunda korata kike yi" murmushi Mom tayi kad'an tana kallon Ismat dake k'ok'arin sauka a jikinta tace "Ni ban kore ki ba,na dai ce kije d'akin ku,za ki bar Badriyah ne ta kwanta ita kad'ai?" Turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Tou Mom mu zo mu kwanta a nan duka?" Mom ta girgiza kai tace "Ni dai kada kuzo ku lalatamin bed,dama kuyi zamanku a can" kamar za tayi kuka ta tashi tsaye tana rik'e gown d'inta,bata sake cewa komai ba ta fara tafiya,Mom ta bita da kallo tana sauke ajiyar zuciya,dai² lokacin kiran Mama yana shigowa sai bata sake cewa Ismat komai ba har ta fita,a hankali ta juya tana kallon wayarta dake ajiye gefe,ta kai hannu ta d'auko tare da answering call d'in ta kai wayar kunne da fad'in "Assalmu alaikum! Hjy Layla kun koma gida ne?" Mama dake cike da damuwar abunda ya faru ta furta "Dr komai lafiya dai kou?" Mom tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Alhamdulillah! Lafiya k'alau Hjy" Mama tayi ajiyar zuciyar samun nutsuwa tace "Maa sha Allah,dama abunda na bugo naji kenan,since kuka tafi hankalina ya kasa kwanciya,ina ta kira ma wayar yak'i tafiya sai yanzun" Mom tace "Allah sarki,network bai da kyau cikin kwanakin nan" Mama tace "Tou tunda komai lafiya Alhamdulillah,but gaskiya ina ga ki abunda yafi ki tambayeta ko ta san yaron" Mom tace "Ba na tunanin haka gaskiya,because duk abunda take ciki ina sani,ba na jin ta san shi at all" Mama tayi shiru a hankali tana tunani sai kuma tace "tou shi kenan dai,amma da kin fara tambayarta ko wani abu ya tab'a had'a su,ni ina jin tsoron irin wad'annan samarin,gara idan da wani problem d'in tun yanzun a yiwa tufkar hanci" Murmushi Mom tayi tace "Babu damuwa Hjy in sha Allah zan tambayeta naji zuwa da safe,yanzun ta gama min rikici ma ta fita" Mama tayi murmushi tace "Auta kenan,tou Allah ba mu alkhairi zan je gurin bak'i,Allah k'ara kiyaye mana su" Mom tayi dariya tace "Ameen,a gaishe da yallab'ai,sai na shigo" suka yi sallama,Mom tana ajiye wayar ta yi shiru ta fara tunanin maganar da suka gama da Mama,bayan wani lokaci ta mik'e a hankali ta fara rage kayan jikinta. Since suka shiga flat d'in babu wanda ya sake magana da d'an uwansa,Aadil kam dama suna shigowa kai tsaye ya wuce hanyar bedroom,while shi kuma Fawad here ya kwanta saman armchair had'e da lumshe idanunsa ya fad'a duniyar tunanin abunda ya faru not too long,yana kwance zuciyarsa sai sak'e² da tunanin abunda zai faru next yake but ya rasa mafita d'aya da zai rik'e,a haka har Aadil yayi wanka ya fito cikin wasu lightweight pyjamas da suka karb'esa,lokacin da yake fitowa daga bedroom ya d'an saci kallon Fawad dake kwance kamar mai bacci a hankali ya tab'e baki ya k'araso cikin parlor'n ya zauna had'e da d'aukan remote yayi powering TV,Fawad da tun shigowarsu ya rasa tunanin da zai yi,ya bud'a lumsassun idanunsa then ya tashi ya fara tafiya slowly kamar yana counting steps,binsa da kallo Aadil yayi har ya shige ciki ya sake tab'e baki ya mayar da hankalinsa kan TV,bayan Fawad ya shiga bedroom ya fara cire kayan jikinsa a nutse ya d'aura towel a waistband d'insa ya wuce bathroom fuskarsa babu wani walwala,jikinsa duk ya yi wani irin mugun sanyi,a haka ya daure ya had'a ma kansa ruwan wanka ya shige,d'umin ruwan dake ratsa shi a hankali ya fara taimaka masa tunaninsa ya fara warwarewa,zuciyarsa da tayi wani irin k'ullewa lokaci d'aya ta fara dawowa dai²,almost 35 minues ya d'auka a cikin ruwan yana ta tunane² kafin yayi wankan ya fito,as he finished ya fito sanye da pyjamas y'an ubansu da suka sake fito da asalin kyaunsa,banda k'amshi babu abunda yake yi mood d'insa kad'ai ne da ya sauya shi ne ya so b'oye kyaunsa,a hankali jin takun tafiyarsa Aadil ya d'aga kai ya kalleshi,bai ce masa komai ba har ya wuce ya zauna had'e da d'aukar wayoyinsa da ya zube saman table,ya zauna saman rug ya mik'e k'afafunsa and leaning his back against chair dake nan kusa da shi,so yake ya kirata sai dai ya rasa ta ina zai fara,zuciyarsa duk a cunkushe yake tunda incidence d'in ya faru,ga wani irin tsoron da ya kama zuciyarsa har zuwa yanzun da yake ganin kamar ya samu mafita,but k'irjinsa bai daina bugawa very fast ba,a hankali bayan wucewar wasu sa'o'i,lokacin ya gama yanke shawaran abunda zai yi ya fara k'ok'arin kiran line ta. A hankali wani zuciyar ya sake kawo masa shawaran ko dai zai gwada yayi amfani da Naina sai ta ba-ta hak'uri,because yana jin wani irin negative feelings a kanta,yana jin ba zai tab'a iya rabuwa da ita ba musamman a irin wannan lokacin,rik'e hannunta kad'ai yayi ya tsinci kansa cikin wani irin yanayin da bai tab'a shiga ba,wanda shi duka a gurinsa yin hakan ma kamar ba wani bak'on abu bane duba da irin society da mutanen da yayi mu'amala da su a rayuwarsa,sai dai a mahanga ta addini da tarbiyyar malam bahaushe shi da kansa ya sani abunda ya aikata bai dace ba,a matsayinta na wacce ba muharramarsa ba,sannan ita kanta ya san ta d'auki abun da zafi,to amma shin ita abunda tayi masa ya yi dai² kenan? Saboda ya rik'e mata hannu sai kawai ta mare shi ba tare da tunanin komai ba? Hakan shi ne abunda ya dace tayi ba tare da tsayawa ta saurare shi ta ji uzurinsa da dalilinsa na yin hakan ba? Lokacin da Ismat ta baro bedroom d'in Mom a wani irin gajiye ta shigo bedroom d'insu tana tafiya tana jan k'afafu saboda masifar ciwon da taji suna yi mata,ta tura door d'in a hankali tayi sallama da dasashshiyar muryarta,Badriyah dake tsaye gaban mirror tana aikin busar da kanta data jik'a da sauri ta ajiye dryer hannunta ta fara tahowa gurin Ismat d'in because lokacin da suka dawo Mom bata jira ba ta wuce da Ismat bedroom d'inta,suna shiga kuma ta kulle k'ofar sai bata samu damar binsu ba,Ismat ta kalleta ganin tana tahowa gurinta da fuskar damuwa a nutse ta d'an saki fuskarta,fuskar Badriyah da damuwa sosai ta rik'o hannunta suka wuce bakin bed suka zauna,tana kallon Ismat da itama take kallonta tace "Sweetheart! Za mu iya yin magana yanzun please?" Shiru Ismat tayi da farko,har Badriyah ta yi tunanin ba za tayi magana ba sai kuma tace "Ehh!" A hankali Badriyah tana sauke ajiyar zuciya tace "Please! Za ki iya sanar min alak'ar ki da wancan guy d'in? Me ya had'a ku? Do u know him anywhere please? Kun tab'a had'uwa kou wani abu ya tab'a faruwa tsakaninki da shi?" Kallonta Ismat tayi bata ce komai ba,sai da ta sake magana then a hankali Ismat ta fara sanar da ita komai game da Fawad,har alak'arsa da Proff Junayd Mutallab duk bata b'oye mata ba wanda ta sani game da shi da ya sanar mata,tunda Ismat ta fara magana Badriyah take binta da kallo har ta k'are,a hankali itama tana kallon Badriyah jikinta yayi wani irin sanyi ta furta "Habibtiiy na yi kuskure da nayi haka kou? But yaya zan yi tou? Ni ban san shi bane ai da ba zan yi masa haka ba,me yasa zai min haka tou shi?" Badriyah dai kallonta kawai take ta kasa magana,Ismat tace "Kawai zan bashi hak'uri yanzun ni dai,even though ban san komai akansa ba after wannan bayanin da nayi miki,muna ta b'oyewa juna wasu abubuwan because no one thought had'uwar mu zai zama haka,me yasa zanyi masa haka tou eh? And u know what? Da jimawa yana fad'a min dama shi yana ji a jikinsa duk ranar da muka fara had'uwa ranar zai kasance kinda special day,ba zai tab'a mantawa da lokacin da zai fara gani na ba,but me yasa ranar zai zo a haka? Why had'uwar mu na farko zai kasance mai muni? Please habibtiiy ki fad'a min yaya zanyi ni,ban san me zance masa ba,me zanyi ya fahimci ba da gangan na mare shi ba eh? Pleasee habibtiiy! Help me out mene ne zanyi ya fahimci dalili na!" Wani irin lumshe idanu Badriyah tayi,kalaman da Ismat take sanar da ita sosai suka yi wani irin b'ata mata rai suka ba ta tsoro,shin dama Ismat tana soyayya ne bata sani ba,yaushe suka fara shiri da guy d'in ma har suka samu damar gina wannan mugun bold relationship d'in a tsakaninsu? Ita kad'ai ta kasa magana sai juya idanu take akan Ismat da fuskarta yake nan kamar za ta fashe da wani sabon kukan saboda damuwar da abunda ya faru tsakaninsu ya haifar mata,a hankali Ismat ta sake rik'o hannun Badriyah tana kallonta ganin bata ce komai ba tace "Please habibtiiy help and find out this solution,ina son sanin abunda zanyi na wanke laifina a gurinsa" wani irin bayannanen ajiyar zuciya Badriyah tayi tana kallon Ismat a hankali ta sake lumshe idanu then ta fara k'ok'arin mik'ewa because she's totally out of speech,maganganun Ismat sun sa ta ji even yawun bakinta ya k'afe,saurin rik'o ta Ismat tayi tana marairaice fuska tace "baki ce komai bafa habibtiiy" da sauri² Badriyah ta fara had'iye yawun da yake k'ok'arin kawowa bakinta a daburce ta furta "Arhhmm! Please let me think dear,u know maganar kin nan yana buk'atar nutsuwa da dogon nazari kou? Please ki bari ko zuwa da safe,ni kaina tunani na ya kulle.." Ajiyar zuciya Ismat ta ci gaba da yi tana kad'a kai a hankali tace "Okay! But please kada ki manta habibtiiy" Badriyah ta k'irk'iri murmushin k'arfin hali tana kallonta tace "Ba zan manta ba dear,but kije kiyi wanka yanzun sai ki kwanta,i know kin mugun gajiya,kinyi kuka d'azun so kada kanki yayi ciwo,je kiyi wanka first kizo ki kwanta" ta kada mata kai a hankali tana yin ajiyar zuciya then ta tashi a sad'ad'e bata ce komai ba ta wuce,Badriyah ta bita da wani irin kallo har ta cire kayanta ta wuce bathroom...
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
1.ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:***
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
***
*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*
For any other problem/complain/enquiry chat via ***.
#Share pls.
#Asli Smasher.