Unexpectedly
by @realsmasher
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*Wattpad link:* ***
🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»🔟:
#Uɴᴇxᴘᴇᴄᴛᴇᴅʟʏ
Har ta fito daga wanka tayi shirin kwanciya bacci daurewa kad'ai take,because zuwa lokacin wani irin ciwon kan da bata tab'a jin kamarsa ba tunda take a duniya ne ya kamata,tana fitowa ta yi k'ok'ari tayi taking pain relievers saboda jin duka jikinta yana mata kamar ana sassara k'ashin jikinta,tana kuma sauraren yadda nerves d'in kanta suke harbawa da sauri²,a daddafe ta k'arasa gaban closet d'inta ta cire wasu floral lightweight pyjama set,wandon short iyakar tsayinsa cinya da kad'an ya wuce pant,sai rigarsa da take sleeveless farare masu adon bak'i a jiki,tana gama shiryawa ta fesa night perfumes masu sanyin dad'i ta bi lafiyar gado had'e da shigewa cikin spreadsheet ta kwanta kusa da Badriyah da tak'i yarda ta san idanunta biyu,since ta kwanta ta lumshe idanunta,bata sake iya d'aga even single finger nata ba,because motsi kad'an idan tayi ji take kamar kanta zai cire,a haka ta daure ta karanto bed time prayers suma d'in a zuciya,bata wani jima sosai da kwantawa ba kuwa wani irin wahalallen bacci ya d'auke ta,da asubah Mom ta zo tashinsu ta tarar da Ismat a saman pray mat already ta tashi da kanta,da yake zuwa time d'in kantan da yake ciwo ma yayi sauk'i sosai tunda ta samu tayi bacci,Mom cike da jin dad'in ganin idanunta biyu ta wuce ta tashi Badriyah dake kwance tana bacci cikin nutsuwa,bayan ta tabbatar ta tashi ta wuce bathroom ta fita,Badriyah tana d'aura alwala ta fito a hankali tana tafiya tana had'a hanya tsabar baccin bai gama sakinta ba ta d'auko wani pray mat d'in ta shimfid'a kusa da wanda Ismat take kai,k'aton hijab har k'asa ta d'auko tasa akan night wears d'in dake jikinta,a haka tayi sallah raka'a biyun farillah da ya hau kanta,tana idarwa babu wani addu'ah ko y'ar nafila ma na raka'atayyil fajr duk bata yi ba bare azkar,ta mik'e ta wuce bed ta sake kwantawa,Ismat da ta idar da sallah ta yi addu'o'inta ta bi Badriyah da kallo,kamar baza ta yi mata magana ba a hankali cikin cool voice d'inta da har lokacin bai koma back to normal ba ta furta "Habibtiiy! Wai me yasa idan kin yi sallah ba kya son yin addu'ah ne? Ba ki da wani buk'ata da kike nema a rayuwarki? Kou kuma dai ba ki da ko wane irin matsala ne da za ki rok'i mahaliccin ki?" Tab'e baki Badriyah dake kwance tayi,idanunta a kulle har lokacin tace "Ni ki rabu da ni bacci nake ji" Ismat ta kad'a kai a hankali tace "Allah kyauta tou,amma dai ko babu yawa idan kina yin raka'atayyil fajr d'in ya fi ba ki yi ba duka,ko dan falalar da yake da shi" a d'an fusace Badriyah dake son komawa bacci Ismat tana yi mata surutu ta d'ago lumsassun idanunta tace "Dan Allah sweetheart kiyi shiru,sallar farillah ma da nake iya yin duka biyar a yini ban tauye ko d'aya ba ai abun farin ciki ne,a hankali shima nawafil d'in zan dunga yi ko nan gaba" takaicin maganar ne ya kama Ismat ta bita da wani kallo,tsabar sanin da ta yiwa Badriyah kawai sai ta ja bakinta tayi shiru,daga hakan sai bata sake magana ba,ta san ko me za ta fad'a ba jinta za ta yi ba bare ta fahimta,alqur'an dake gabanta ta bud'e a nutse,da wannan cool voice d'in nata mai tattare da nutsuwa ta bud'e suratul yusuf ta fara karantawa cike da shauk'i har wani lumshe idanu take saboda akwaita da masifar son tarikh and ita kuma surar dukanta yana bayyana k'issar annabi yusuf (A.S) ne da yadda ya rayu. Lokacin da ta kammala karatunta already 7am har da wasu minutes,ta ci gaba da addu'ah bata tashi a gurin ba,sai da ta tabbatar rana ya d'ago then ta tashi tayi sallah raka'a biyu wanda Annabi (S.W.A) yace (Wanda duk yayi sallah raka'a biyu bayan sallar asubah,bi ma'ana tunda yayi sallaci sallar asubah yake zaune yana addu'ah a gurin,bai tashi ba har lokacin da rana ta hudo,then yayi sallah a wannan lokacin,ladarsa kamar ya yi hajj da umrah ne tare da shi) after ta idar ta sake yin addu'o'i but ba masu nisa ba then ta cire hijab da pray mat ta mayar ma'adanin su,tana gamawa ta fara shirin fita workout,as she finished ta fito sanye da 3quarter na wani pink d'in robber skinny trouser da ya bi shafe d'in jikinta ya kwanta kamar a jikinta aka d'inka,sai y'ar rigarsa itama pink masu duhu,tasa d'an k'aramin band bak'i ta d'aure gashinta,a nutse ta zura k'afafunta cikin wani new versatile shoes bak'ak'e,though babu kwaliyya a fuskarta,hasalima sai wani irin damuwar dake kwance kan fuskarta but sosai tayi wani irin sanyayyan kyau,k'unshinta ya dad'a haska farar fatarta,tana gamawa za ta fita ta fara tashin Badriyah,after she made sure ta tashi tayi mata murmushi tace "Good morning habibtiiy" Badriyah dake jin haushin tashin da tayi mata tana had'e rai tace "morning how are u?" A sanyaye Ismat tace "alhamdulillah" then ta juya ta d'auki phone d'inta da earpiece ta fara tafiya,har ta kai bakin k'ofa ta waiwayo a hankali fuskarta d'auke da damuwa tace "Please habibtiiy hope baki manta da alk'awarin mu ba?" kallonta Badriyah tayi kamar ba za ta ce komai ba ta daure dai tace "Ban manta ba" da wani muryar jin haushi,a hankali Ismat ta kad'a kai then ta k'arasa fita daga d'akin tana sauke ajiyar zuciya,lokacin da ta haura next floor tana shiga fitness room,kasa yin komai tayi haka ta samu guri ta zauna jiran zuwan Badriyah,sai a nan ta fara tunanin shirun da ta ji daga gareshi,a hankali cikin wani irin damuwar abunda ya faru jiya ta bud'e wayarta ta fara dubawa,duk inda ta san suna da wani alak'a da shi duk ta bi ta duba sai dai ko gudan sak'o d'aya bata gani ba,komai zero babu alamun abunda ya faru ya dame shi,tayi shiru tana zaune sai kallon phone d'in take idanunta sun ciko da hawaye,almost one hour da wasu mintuna aka bud'e door d'in aka shigo,har lokacin tana zaune ta rasa me yake mata dad'i,Badriyah dake shigowa cikin shigar train suit irin na Ismat but na ta red colour ta sauke idanunta kan Ismat d'in dake zaune ta zuba tagumi da hannu biyu,kallo d'aya tayi mata ta d'auke kai,ta k'araso wajen a nutse ta wuce za ta hau machine da sauri Ismat ta d'ago tana goge idanunta tace "Habibtiiy please" sai kuma ta yi shiru ta kasa magana,fasa abunda tayi niyya Badriyah tayi ta dawo gefenta a hankali tana kallonta ta zauna tace "Uhn! Ina jinki" Ismat da fuskarta yayi turning zuwa na damuwa tace "Ki fad'a min me zanyi yanzun,kinga bai kira ni ba,and he didn't texted me,me zanyi na san yana fushi ne?" Kallonta Badriyah ta dunga yi kamar ba za tace komai ba,then a nutse tana kallonta tace "Ki rabu da shi kawai,i think shi bai wani damu da ke ba" Ismat da take jin gabanta yana fad'uwa saboda abunda Badriyah ta fad'a tace "But habibtiiy ba kya ganin ni ya dace na kira shi naji eh?" Kai Badriyah ta kad'a tace "me yasa za ki kira? Thought ko hak'uri ne ma ke ya kamata ya fara kira ya bawa,ya san abunda yayi laifi ne,but kinga ai bai damu ba,tunda ga shi bai yi ko d'aya daga ciki ba,babu text babu kira,to ke me yasa za ki damu?" Tace "but habibtiiy i feel negatively on him,ba zan iya jurewa sai shi ya fara kira ba" wani kallo Badriyah ta watsa mata tace "dan kina jin haka a kansa sai aka ce duk abunda ya faru ke za ki bada hak'uri? Tou dama bari kiji wannan maganar ba wai akan so bane akan mutuncin ki ne,but let me tell u one thing,dama daga lokacin da kika fara nuna masa duk abunda ya faru za ki ba da hakuri ko ba laifin ki bane,ki shirya ganin wulak'anci,su ba'a nuna musu so haka k'arara,ki kama mutuncinki and then ki tattara komai ki watsar,ki nuna masa abun bai wani dame ki ba ko da kuwa kina jin zuciyarki bazai d'auka ba,idan kika yi haka for sure zai san kina da mutunci,da kansa zai ji dole ma sai ya nemo ki,but dama kina nuna kin damu ki tabbatar kin gama kashe kanki!" Shiru Ismat tayi tana juya maganganun Badriyah a ranta,bayan wasu y'an mintuna kuma a hankali tana sauke ajiyar zuciya cike da gamsuwa tace "thank u habibtiiy! Na fahimta yanzun,in Allah ya so zanyi kamar yadda kika ce" Badriyah dake tashi daga kusa da ita ta wuce tana cewa "better." Duk yadda Ismat ta so kada ta sawa ranta damuwar al'amarin kasawa tayi,motsi kad'an ta waiwaya ta saci kallon Badriyah,har suka gama abunda ya kawosu suka fita bata wani yi da kyau ba ranar saboda damuwa. Da yake kuma event d'in ranar gidan angwaye ne suka shirya na su dinner d'in and suma dai sai dare ne,shi yasa wunin ranar babu inda Ismat suka je,can gidan su Badriyah ma sunk'i zuwa duk uban kiran da Jawahir take musu,ranar haka Ismat ta wuni sukuku a d'aki a kwance,Badriyah duk tana kula da ita sai dai bata ce mata komai ba because ta san kan wancan maganar ne take ta damuwa,har lokacin da za su fita wajen make-up yayi Ismat tana kwance ba ta da alamun tashi,Badriyah da ta gama shiryawa lokacin tana kallonta tace "Kin san dai mu suke jira kou? Ya kamata ki tashi mu wuce yanzun,tun safe suke nemanmu muka k'i zuwa,though kin san bamu kyauta ba abunda muka yi" lumshe idanu Ismat tayi a hankali fuskarta da yanayin damuwa ta furta "Ni bazan je ba,kiyi tafiyarki kawai" wani irin kallo Badriyah ta watsa mata da sauri tace "Ban gane baza ki je ba? Kina nufin dinner d'in ma baza ki ba?" Kai ta kad'a mata tace "Ehh! That's what i meant" Badriyah dake kallonta a hankali tana dawowa kusa da bed ta zauna kad'an tana kallon Ismat da idanunta suke rufe tace "Saboda me baza ki je ba? Saboda shi ne kou?" Runtse idanu Ismat tayi tana kad'a mata kai,a hankali Badriyah ta rik'o hannunta tace "me yasa ba za ki manta da abunda ya faru ba sweetheart? Tunda haka ya faru dama fa ba na tunanin da gaske yana sonki shi,kiyi hak'uri ki manta da shi kawai,surely Allah zai canja miki da wanda ya fisa" saurin bud'e idanunta da hawaye suka k'awata tayi tana kallon Badriyah fuskarta d'auke da wani irin murmushi mai d'auke da ma'anoni ta kad'a mata kai tace "sure Allah zai canja min dear,thanks a lot da kika tuna min da hakan" murmushi itama tayi mata,a sanyaye tana kallonta ta langab'ar da kai tace "tou tafiyar na mu fa?" D'an tab'e baki Ismat tayi a hankali tana langab'ar da kai gefe ta kumbura baki cike da shagwab'a,Badriyah ta zaro ido tana kallonta a tsorace tace "What?" Ismat ta fashe da dariya cikin ihu tace "Yanzun sai mu tafi" Badriyah tayi ihu ta rungumeta da sauri,bayan sun gama ihun nasu a gurguje Ismat ta fara shiryawa Badriyah tana taya ta,suna yi suna hira kamar babu abunda ya faru,after sun kammala already Mom dama ba ta nan ita,suka wuce wajen da za'a musu make-up. 9:00pm motar da suke ciki ya parker bakin PAP's,da yake yau babu da wanda suka taho su kad'ai ne cikin motar,Badriyah ta fara fitowa daga side na mai zaman banza then Ismat ta fito daga side d'in driver,yau ma dai kamar jiyan sanye suke da kayansu iri d'aya wani irin d'an ubansun material ne,asalin yadin ba silk bane and not a cotton,haka nan dai jikinsa yake rawa,an musu d'inkin riga da sket da yayi asalin karb'ar su ya zauna dai²,kalar yadin yellow ne da ya d'an ciza yayi kamar egg yolk,da bak'in flowers manya da wasu irin crystal fari da aka bishi da su,sosai suka yi wani irin kyau kamar ka sace su ka gudu,takalmansu da vail duk bak'ak'e sai wayoyinsu da suka rik'o,suna tafiya suna hira cikin nishad'i,da yake yau Ismat ta rantse baza ta je gurin a haka ba sai ta sa vail dole itama Badriyah ta hak'ura ta d'auka because dinner ba na su bane,but duk da haka sunyi wani irin sanyayyan kyaun da duk wanda ya kallesu zai so ya sake,tunda suka shigo gurin idanun Fawad suka sauka kan Ismat,lokaci d'aya yaji gabansa yana fad'uwa,musamman ganin irin masifaffen kyaun da tayi,a hankali ya lumshe idanunsa ya bud'e ya ci gaba da kallonta,har sanda suka zauna a wani table suna dariya ita da Badriyah,ajiyar zuciya yayi ya sake lumshe idanu yana jin yadda zuciyarsa take harbawa da sauri²,slowly ya fara k'ok'arin saita nutsuwarsa ya fara kiran wayar Naina,su kam su Ismat da yake sun zo a late,since suka zauna sai basu tashi ba,duk k'aunarsu da rawa kuma ranar kasawa suka yi ko lik'i ma sun k'i zuwa suyi,sai dai hirar da suka dunga yi,suna ta zaune a wajen Naina ta k'araso fuskarta a sake ta ci uban gayu kamar wata amarya,tayi musu sallama da siririyar muryarta,Ismat tana kallonta ta saki fuska haka Badriyah ma suka gaisa,daga nan suka fara hira,Badriyah tana kallonta tace "Ina sis d'inki?" Naina tayi dariya tace "Sis Madeeha?" Badriyah tace "Ehh ita" a hankali Naina ta waiwaya tana kallo saman deck tace "Tana can tana rawa,ku ai na ga yau baku yi ba ma kou me yasa?" Murmushi suka yi a tare Badriyah tace "No! Muna son hutawa yau,kinga jiya sweetheart ta yi ciwon jiki,so yau ba na so ta samu wani matsalar" Naina tayi dariya tace "Da alamu kina ji da sweetheart d'in nan na ki" Badriyah tayi dariya tace "Not a little,kamar k'wai haka nake ji da ita,saboda itama tana ji da ni" suka sake yin dariya,Naina tace "Allah bar k'auna tou" Badriyah ta d'age eyebrows tace "Ameen" kallon Ismat Naina tayi in a serious tone tace "Please dear za mu iya yin magana dake?" Ismat ta kalleta kamar za ta ce mata a'a da farkon sai dai taga bai dace tayi mata haka ba tunda ta tsaga bille ta tambaya a sanyaye tana sakin murmushi tace "why not?" Murmushi Naina tayi a hankali tace "thank u,but kou za muje waje saboda nan kinga akwai haniya and maganar yana buk'atar sirri ne" kallonta Ismat ta dunga yi da wani irin mamaki a fuskarta tace "sirri kuma?" Naina ta lumshe idanunta tana kad'a kai tace "Yeahh!" Kamar Ismat ba za ta sake magana ba tayi shiru tana juya kalmar sirri da Naina ta fad'a then a hankali ta furta "alright" shima d'in duk saboda Badriyah ta mata alamar suje ne ta amsa,a nutse Naina ta tashi tana yiwa Badriyah murmushi tace "kiyi hak'uri dear na d'auke miki ita,but please ba za mu jima ba,zan dawo miki da ita" murmushi Badriyah tayi mata tace "No! Kada ki damu,nima zan je wajen Mom yanzun" Naina tayi y'ar dariya tace "alright! Thanks" Badriyah ta mik'e tana kallon Naina fuskarta da murmushi tace "u are most welcome" ta juya a hankali ta fara tafiya,Ismat ta bi Badriyah da kallo har ta bar wajen then ta waiwayo tana kallon Naina a hankali tace "let's go",can waje suka fita suna tafiya Ismat tace "wane magana ne dear?" Naina tayi ajiyar zuciya tana tsayawa tace "Akan maganar Aakiiy na ne dear" saurin tsayawa Ismat tayi tana kallon Naina fuskarta da wani irin expression tace "ban gane ba" Naina tace "Please kiyi hak'uri akan abunda ya faru" wani irin kallo Ismat ta fara yi mata tana d'aure fuska tace "ban gane hakur'in da kike ba ni ba,wani abu ya faru ne ban sani ba?" Naina tace "Ni dai kiyi hak'uri nace,i just don't know ko wani abu ya faru kou bai faru ba,ni ba na ma son na sani,but ina baki hak'uri ne dai kad'ai on behalf of my brother,please dear kiyi hak'uri dan Allah!" Murmushin rainin hankali Ismat tayi tana yiwa Naina wani irin kallo tace "tou ke da baki sani ba kuma mene ne abun da za kina bada hak'uri? Ni dai na san baki yi min komai ba,so mene ne amfanin hakur'in da kike ba ni kenan? Ko shi Yayan naki yace ya min wani abu?" Naina tace "ni fa aiko ni kad'ai akayi akace na baki hak'uri" Ismat tayi wani dariya tace "Ni dai na san ban san shi ba sai jiyan da kika sa muka gaisa,tou kuma me zai had'a mu,har wani abu ya faru da za ki zo ba ni hak'uri on behalf of him?" Kad'a mata kai Naina tayi tana rik'o hannunta a hankali tace "Ba ina nufin Akhiiy Aadil ba dear,ni fa maganar da nake yi ina yinsa ne akan Akhiiy Fawad!" Zuba mata ido Ismat tayi kamar ba za tayi magana ta mugun had'e rai ta tab'e baki cike da rainin wayo tace "wane ne shi kuma?" Murmushi Naina tayi tana kallonta tace "please dear ni dai na san kin san shi tunda yayi min maganarki but please give him this chance i know idan yayi miki bayani da kansa za ki ganesa!" tana fad'in haka kafin Ismat ta sake yin magana da sauri ta juya ta bar wajen,Ismat ta bi ta da kallo cike da mamakin k'arfin hali irin na Naina,but before she made any attempt kawai sai ganin mutum tayi tsaye a gabanta...
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:***
City:Kano city.
*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
***
*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*
For any other problem/complain/enquiry chat via ***.
#Share pls.
#Asli Smasher.