MAKTOUB!

Interval

by @realsmasher

💠💠💠💠💠

©®2020.






          *♡MAKTOUB¸.•💥*

          ((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))





*WATTPAD:REAL-SMASHER.**

*AREWABOOKS:REALSMASHER.*

*Wattpad link:* ***


*LAST FREE PAGE.🏃*


🅿»1⃣5⃣

#Iɴᴛᴇʀᴠᴀʟ



   Wani irin shiru parlon ya d'auka na musamman,tsakanin su Daddy an rasa samun mai magana sai kallon-kallo da ake maimaita yi tsakanin su da family'n Fawad da suka zo neman auren,can da aka jima Dr Haroun mahaifin Badriyah yayi k'arfin hali yana sauke wani irin ajiyar zuciya ya furta "Anya kuwa maganar nan haka yake? Mu dai duka nan abunda muka sani da wanda aka sanar damu maganar neman auren *ISMAT* ne ya zaunar da mu,yanzun kuma munji kun zo mana da wani batun daban,me haka yake nufi kenan?" Maganar da Dr Haroun yayi a lokacin yasa mutane sake yin shiru da farko,but daga bayan kuma here musu ya kaure tsakanin families d'in biyu,yayin da family'n Fawad ke ganin ba dai² su Abbah suke fad'a ba,suma suna ganin sune a kan dai²,su dai b'angaren Fawad da suka zo meman aure ne suka yi ba dai² ba,all because su basu san wani batun Badriyah ba na Ismat suka sani,ganin haka yasa Proff Junayd da tun zuwansu bai ce komai ba numfasawa yayi magana "I think ya kamata tunda abun nan yazo da jayayya tsakanin mu,me zai hana baza'a kira yaron aji daga bakinsa ba,gudun kada muyi abu kai tsaye,kou kuwa me kuke gani?!" Yana fad'in haka duka hankalin kowa sai ya karkata kan ayi hakan,here mahaifin Fawad Engineer Dawoud ya d'aga waya kafin ma ace Proff d'in yayi nufin hakan ya kira shi yasa wayar a free yadda kowa zai ji me yake fad'a,Fawad dake zaune cikin parlor ya mik'e k'afafu a saman table hannunsa rik'e da remote yana powering TV kiran mahaifin nasa ya shigo masa,ya d'aga wayar yana kallon sunan da ke yawo kan screen d'in a hankali ya lumshe idanunsa yana sakin murmushi ya kai wayar kunnensa,before yayi magana Eng. Dawoud d'in ya fara magana "Fawad! Kana ji na?" Fawad da ya rufe idanu murmushi kwance saman fuskarsa ya amsa "Ehh! Abbuh" Eng yace "ina so ka fad'a min wace ce ka tura mu neman maka aurenta yanzun?" Shiru ya fara yi na wani d'an lokaci,hak'oransa a waje yana sakin murmushi because he made sure dole za'ayi hakan kafin ya furta "Abbuh! Ni fa *BADRIYAH* nace muku sunanta,wani abu ya faru?" Ya k'are maganar kamar bai san me ya haddasa ba,Eng na jin Fawad yace haka ya furta "Alright!" Kafin Fawad ya sake magana har ya katse kiran,wani irin gumi ne suka fara ketowa jikin Barraq tun da yaji maganar da Fawad yayi a waya,ransa a mugun b'ace muscles d'insa sunyi rad'a² kamar za su tsaga jikinsa,idanun san nan lokaci d'aya suka birkice suka sauya colour,banda tauna tooth d'insa kamar zai ci babu idan ya gani babu a bunda yake,haka su Daddy ma duk sunyi shiru sun kasa cewa komai,tsananin mamaki yasa sai maimaita abunda kunnuwansu suka ji suke but sun kasa zartar da ko wane irin hukunci,Egn da ya gama magana da Fawad a waya ya juyo yana numfasawa ya furta "hope duka kunji abunda ya faru,and kun fahimci inda maganar yake yanzun?" Abbah ne ya d'ago a zafafe zai yi magana da sauri Daddy ya rik'e gefen rigarsa ya hanashi abunda yayi niyya,Daddy dake sakin murmushin k'arfin hali yana girgiza kai yace "Haka ne mun fahimta kam yanzun,think mun samu tangard'a ne wajen fahimta saboda mu da aka bamu maganar ba'a bambance mana ba,but tsakanin Ismat da Badriyah duka d'aya ne,babu matsala in sha Allah" tunda Daddy ya fara maganar Barraq ya kafe shi da kallo with his coloured eyes,tun d'azun da yaji an ambaci Badriyah zuciyarsa ta tunzuro,and duka burinsa shu ne ya gansa a gida sai dai babu halin yin hakan because bai isa barin wajen ba,but jin maganar Daddy na kusan k'arshe yasa shi zabura yayi mik'ewar da bai yi niyya ba,da sauri Daddy ya kai hannu zai rik'osa,kafin ya kai ga yin hakan tuni Barraq ya nufi k'ofa yana tafe yayi taking excuse,within seconds har ya fice,Daddy hankalinsa a mugun tashe ya bishi da kallo,ba ya so yayi magana bak'in su suyi wani zargin shi yasa kawai ya rabu da Barraq d'in,but ya fi kowa sanin halin Barraq a yadda ya fita d'in nan dole ya san za'a samu matsala,addu'ar sa a lokacin bai wuce Allah ya tsare Barraq d'in ya isa gida lafiya ba,shi kansa Abbah bai so aka ce d'an uwansan ya yi saurin zartar da hukunci ba,idan a son ransa ne so yayi su hana neman auren kawai but ba zai iya jayayya da Yayan nasa ba,dole ya hak'ura yayi shiru a gurin but underneath ji yake kamar ana boiling masa zuciyarsa,jira kad'ai yake yayi ido hud'u da Badriyah yaji abunda yake faruwa tsakaninta da yaron because bai yarda da abunda ya faru ba yanzun,dole there's something behind,har aka kammala maganganu Proff ya bada sadaki suka ajiye maganar akan za su fara tuntub'ar Fawad suji lokacin da ya yanke Dr Haroun bai san me suke cewa a kan maganar ba,sai da suka fara sallama da su Proff Junayd za su tafi,su Daddy kad'ai suka yi musu rakiya aka rabu cikin mutunci kamar yadda aka had'u. Since waliyyan Fawad da suka zo nemar masa auren suka tafi,wani friend d'in Daddy Alh Abdussalam suna tafiya a compound d'in gidan za su dawo yana girgiza kai cike da jimami ya furta "I'm sorry to say Proff but maganar nan ina tunanin akwai abunda yake ba dai² ba,sam ban amince da batun da su Proff suka zo da shi ba" murmushi kad'ai Daddy yayi though shi kansa yana wannan tunanin,underneath yana jin lallai ne akwai abunda yake shirin faruwa kou yace ya faru,haka friends d'in nasa duk suka dunga maganar amma shi ya kasa cewa komai sai murmushin k'arfin hali kad'ai yake yi because abun ya tab'a shi sosai jin komai yake amma ba ya fahimtar su duka,suna shigowa cikin parlon Dr Haroun dake tsaye goye da hannuwansa tun fitarsu Daddy raka bak'in nasu yake zarya ya rasa abunda yake ma rayuwarsa dad'i ya juyo idanunsa sunyi wani irin sauyawa saboda b'acin rai,yana kallon only brother d'insa dake shigowa ya girgiza kai cike da takaici ya furta "ban so ace Yaya ka yi saurin yanke wannan hukuncin ba,na so ace tunda suka raba mana hankali haka mu hanasu auren,but me yasa za ka amince ka karb'i batun a haka? Why² za mu basu aure a haka?" Numfashi Proff yaja ya fesar a hankali ya furta "though ban yi haka da wani nufin ba,a gani na da Badriyah da Ismat duka d'aya ne a guri na,idan da farko sunce Ismat yanzun suka ce Badriyah ba komai bane yin hakan,haka Allah ya nufa,so mu bamu isa canja tsarin Allah akanmu ba,ina fatan duk za mu yi hak'uri mu karb'i destiny d'inmu a duk yadda yazo" girgiza kai kad'ai Dr Haroun ya iya yi without ya furta wani abu because ya san kou me zai fad'a ba lallai Proff d'in ya fahimcesa ba ya juya a zafafe ya fice daga parlon kou sallama bai jira suyi da Yayan nasa ba. Barraq kam since ya fito yana shiga motarsa gudu kad'ai yake sharawa,gaba d'aya jin maganar yake ya zo masa a wani irin bazata,ikon Allah kad'ai ya kawosa gida because a wani irin haukace ya dunga tuk'in,tun kafin ya k'arasa shigowa line yake horn,yana zuwa tun get man d'insu bai gama bud'e masa ba ya taka motar a zafafe kad'an ya rage bai bi ta kansa ya wuce ba,direct bai bi ta kan parking lot ba ya wuce arean apartment d'in,kou tsayawa ya dai²ta parking bai ba bare ya kashe motar ya fice ya barta a bud'e,yana wucewa balcony zuciyarsa banda tafarfasa babu abunda yake,da k'afa yana zuwa ya harba door d'in da k'arfi,k'ofar yana gama bud'ewa ya danna kai kou tunanin sallama bai yi ba ya d'aga kai yana kallo sama yana tafiya yake kwala kiran sunan Badriyah da wani irin muryar da ba Ismat ba hatta Mom sai da gabanta yayi mugun fad'uwa suka yo waje daga bedroom da sauri,Barraq dake zarya ya kasa hakur'in jiran ganin ta inda Badriyah za ta b'illo da sassarfa ya fara tsallako stairs,Mom da Ismat dake shirin fara sakkowa all because of yadda suka ji yana kiran Badriyah suka kusa cin karo da shi,Ismat tayi saurin yin gefe saboda tsoron da take ciki har yanzun bai gama sakinta ba sai ma wani multiplying kansa da yake sake mata a duk motsawar second,Mom kam since taji kiran ta san dole an samu matsala da sauri lokacin zai wuce ta rik'o arm d'insa hankalinta a mugun tashe take fad'in "what happened Barraq?" Barraq sai son kwace hannunsa daga rik'on da Mom tayi masa yake bai ma san lokacin da ya furta "rabu da ni Mom dole yau naci uwar yarinyar nan" zaro idanu Mom tayi ta furta "wai me yake faruwa ne?" Kallon Mom yayi with his coloured eyes ya kasa cewa da ita komai sai son wucewa yake,Mom kuma duk ta yi bakaka in front of him ta hanasa wucewa because ta san dole idan ta bari ya wuceta suka had'u da Badriyah a wannan condition d'in da yake ciki za'a samu mugun matsalar da kullum take gudu,Ismat dai na tsaye gefe sai kallonsu take daga nesa² a tsorace but ta kasa magana kou even ma ta k'araso inda suke,a nutse Mom data danne k'irjin Barraq dake wani irin d'agawa tana masa addu'ah ta d'ago kai tana shafa side na fuskarsa ta furta "look into my eyes Barraq! Maza ka sanar da ni abunda yake faruwa,me yasa kake neman Badriyah?" Cikin karajin masifa mai cike da gushewar hankalin da ya mantar da shi wacce ke tsaye gabansa ya furta "i want to see her,ita kad'ai nake muradi,dole yau na shayar da yarinyar nan mamakina,sai na sa ta gane wane ne Barraq" sakin baki Mom tayi tana kallon yadda ya runtse idanu yana zazzaga magana,she know lallai duk abunda ya faru tsakani ba k'arami bane tunda har yasa Barraq yayi loosing control d'insa,bata iya ta ce da shi komai ba sai da ta jira ya dire maganar ta furta "sai ka yi hak'uri har ta dawo,because bata jima da barin gidan nan ba!" Wani irin mahaukacin punch da ya kaiwa wall dake kusa da shi yana furta "damn it!" Yasa Mom zaro idanu tana kallonsa a tsorace,ita kanta yau yadda take kallonsa tsoro yanayinsa yake bata,a fusace ba tare da ya tambayi inda ta tafi ba ya juya zai sauka Mom tayi sauri ta tare shi tana sake tambayarsa abunda ya had'a shi da Badriyah har yake nemanta,girgiza kai kad'ai yayi ya furta "later Mom but ki bari naje naga yarinyar nan,dole ne na karairayata yau" saurin tarar numfashinsa Mom tayi tace "kana da hankali kuwa Barraq kake irin wannan maganar?" Girgiza kai yayi a zafafe ya furta "Mom kou ke dan baki san me yarinyar nan tayi ba da tuni kin tsine mata" Mom data zuba masa idanu tace "me tayi ne? Laifin me ta aikata da kake fad'in haka?" Jijjiga kai kad'ai yake yana tauna lips d'insa but ya kasa sake yi mata magana,Mom tace "da kai nake ka yi min shiru kana jijjiga kai?" Shigowar Daddy a lokacin kou da suka yi ido hud'u da su yasa Barraq kasa cewa komai,shima Daddy dake hauro staircases d'in ganinsu a irin yanayin bai damu da sanin abunda ke faruwa ba kou jin maganar da suke tattaunawa ba though yayi zargin Barraq ya sanar da Mom abunda ya faru,yana zuwa dai² inda suke bai yarda ya kalli d'aya a cikinsu ba ya furta "u two ku same ni a ciki" yana maganar ya wuce parlonsa dake nan saman,kallon-kallo akayi tsakanin Mom da Barraq ganin a yanayin da Daddy yayi maganar bai kou kallesu ba bare ya jira jin uzurinsu ya wuce dole suka bi bayansa,Ismat kam har lokacin da suka wuce tana nan tsaye inda suka barta ta kasa matsawa even nan da can. Duk abunda ake ciki sanda Mom suka shiga sai da Daddy yayi mata bayani,Mom tayi shiru ta kasa cewa komai da farko sai kallonsa da take yi idanunta sun yi jaa sun tara hawaye,ita damuwarta a lokacin duk ba akan komai bane sama da halin da Ismat za ta shiga idan taji labarin,shin wane irin laifi ne ma innocent child d'in nata ta yiwa yaron da zafi da ya zab'i breaking heart d'inta ta this way? Yarinyar da magana yake ma wahala bare har hira mai nisa ya had'ata da mutane,tun tasowar ta ba ta da wata k'awa sama da Badriyah,duk inda suke tare a skul kou a gida always maganarta ba ya wuce na habibtiiy'n ta,bayanta bata san kowa ba,babu da wanda ta aminta,shin me ta aikata musu su duka suka zab'i cutar da rayuwarta haka? Shi kuma Daddy instead of ya hana auren k'ulluwa da dukansu tunda al'amarin ya faro a haka,kawai sai yake ba-ta labarin wai ya bada auren Badriyar ga yaron,me yasa zai aikata hakan,kou kuwa dai bai ji haushin fasa neman auren Ismat d'in da take y'arsa ta cikinsa bane ohoo masa.


*Some hours later...*


       The ring of an incoming call to his phone a time d'in bayan tafiyar Mom da Barraq a gurin quickly yasa Proff. IMRAN ya d'auki kiran da ake masa fuskarsan nan tana bayyanar da tashin hankali mara misali for nothing other than yadda Mom ta zauna ta yarfa masa maganganu cikin gushewar hankalin da ita kanta bata san ta yi masa hakan ba,all because of yadda labarin ya zo mata a wani irin bazata al'amarin ya mugun tab'a mata zuciya ya tada mata hankali over,tsayin shekaru 35 suke tare bai tab'a ganin other half na Mom ba,kullum cikin faranta masa take,bai tab'a ganin b'acin ranta ba,kou da kuwa ya yi mata abunda bata ji dad'i ba,but yau k'arara ta zage akan abunda ya aikata ta yarfa masa maganganu masu kaushi da zafi,kafin Daddy yayi magana daga side da aka kira aka furta "Proff IMRAN ne?" Daddy ya amsa "Ehh! Shi ne" cikin wani sanyin jiki,kafin ya sake yin magana aka ce "Ka godewa Allah da bai nufin y'arka tana da rabon shan wahala ba,sam yaron nan dama ba d'an arziki bane,duk abunda za mu fad'a maka a yanzun mun san ba lallai kai ka fahimcesa ba,but congratulations da y'arka ta tsallake rijiya da baya,ka godewa Allah da ya tsallakar da y'arka daga fad'awa tarkon sa!" Ana fad'in haka ba'a jira ba k'it aka yanke kiran,Daddy da yake jin maganganun suna shigarsa kou da aka yanke kiran,abunda kunnuwansa suka jiyo su suka haddasa masa jin k'afafunsa sun kasa d'aukansa,da gaggawa ya dafe armchair jin yana shirin fad'uwa,but bakinsa bai kasa fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ba,wani irin zafin da ya fara jin yana taso masa yasa shi fara nadamar hukuncin da ya zartar ba da jimawa ba,for nothing other than ya san ba kowa zai fahimcesa shi ba,ba kowa zai masa uzuri akan auren da ya bada na Badriyah ga yaron da aka kira shi aka fara masa highlight wasu abubuwa akansa ba,shin wane irin hali ne da Fawad da Proff Junayd Mutallab kasa saninsa da shi har ya taso ya zo nemar masa aure? Auren ma kuma ya rasa inda zai nema sai wajensa,shin ya san da hakan kou kuwa shi d'in dai suke son binnewa da ransa? Rashin samun wanda zai ba shi gamsashiyar amsa a lokacin yasa shi zaunawa a k'asa kan rug ya kwantar da kansa a jikin chair da yayi leaning bayansa yana maimaita fad'in "Hasbunallaahu wa-ni'imal wakiil... Allahumma ajirniy fiiy musibatin wa'aklufniiy khairan minha.. Laa'ilaha illaa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn.." Shin me haka yake nufi,wannan shi ake kira da an gudu ba'a tsira ba...


  

   

   *#Assalam.. Masoya REAL-SMASHER fatan mun wuni cikin aminci and we all doing well,kamar yadda kuka sani free pages kuke karantawa,so if u are all ready 😀 kuna son jin how this amazing story will turn out,maza garzaya ki/ku/ka biya because daga yau free pages is no more,it's ₦300 transfer/VTU/recharge card duk d'aya ne babu batun VIP,sai na ji-ku masoya,Real Smasher tana maraba da ku a ko wane lokaci. Zan ci gaba da post cikin tak'aiccen lokaci,though yanzun mun d'an samu matsalar NEPA 2 days ago,but da sun kammala gyare² za mu ci gaba in sha Allah. Na bar ku lafiya..😍*

  



  #The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300 via my details.



*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*


*1-ACCOUNT DETAILS.* 


Acct name:Hauwa Muhammad Usman

Acct number:0060746882 

Bank name:Access Bank

Phone number:***

City:Kano city.


  *A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*


*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*


***


  *A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*


  For any other problem/complain/enquiry chat via ***.




   

#Share pls.

#Asli Smasher.