25&26
*🍏BASMA🍏*
BOOK 2📃
BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
---------
SIRRINKI👂🏻
ƳAR UWA KI KASANCE MAI RUFE SUTURARKI AKO DA YAUSHE,RUFE JIKINKI YANA TAIMAKA MIKI WAJEN YIN RIGAKAFI GA MUTANE DA KUMA SHAIƊANU.
----------------------------------
*25🟢26*
. . . . .numfashin Basma har ya fara ɗaukewa saboda da ɗewar da ta fara yi acikin ruwa,da sauri ya ruƙota ya rungumeta sosai kamar wani zai ƙwace masa ita,abin gwanin sha'awa kamar a india,mutane aka fara tafi awajen da sauri Hafsat ta taho ta rungume Basma tana kuka bayan ya ajje ta a gefen wajen,da kansa ya saka hannuwansa guda biyu a ƙirjinta,sai da yaji wani shork har cikin ƙwaƙwalwarsa ya daure ya fara danna ƙirjinta ruwan yana fitowa har dai ya gama fitowa,ya tsira mata idanuwa yana kallon fuskarta,ya shagala sosai da kallonta,ita kuma a lokacin ta buɗe idanuwanta da sauri ta tashi tana kallon wajen kamar bata san tazo ba.
Da sauri ya tashi bayan ya dawo daga hayyacinsa ya amshi rigarsa daya cire ya saka yana kallon Basma kamar zai cinyeta,Hafsat ta ruƙo hannuwana muka fara tafiya.
Wani abu yaji mai kamada kishi saboda yadda mutanen wajen suke kalle masa matarsa,don shi har ya yi mata don tunda ya ke zai iya cewa bai taɓa ganin macen da ta ƙwanta masa arai irin Basma ba.
Motar su ta sojoji ya shiga ya kafa glass ɗinsa a fuska wato no respect suma sauran sojojin ganin ogansu ya shiga mota da sauri suka shiga suna sara masa.
Muna fitowa waje Hamza ya taho da sauri yana ce wa"iyayen ɗakina lafiya me ya faru?naga Basma duk jikinta ya jiƙe tana rawar sanyi haka?.shiru hafsat ta yi masa ganin ya dage da tambayar sai ta ce"Hamza don Allah kaja mu mu tafi Basma ce ta faɗa ruwa yanzu".
da sauri ya juyo yana ce wa"subhanalillahi sannu Basma,amman babu abinda ya sameta ko?shiyasa banji daɗi ba da muka baro wancen wajen tunda na ga cen ɗin babu irin abubuwa nasu hatsari".
har ya gama maganarsa babu wanda ya ce masa ƙala har ya gaji ya yi shiru,muna zuwa gida Anty shamsiyya ta dinga yi mana faɗa akan mudinga kula da kanmu,daga cewa zamu super market shine muka tafi wani waje harda swiming pool,ganin ranta ya ɓaci ne muka bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin ba zamu ƙara fita ba har mu koma kano.
Sosai suke gudu a motar don su gano inda motarsu Basma take,amman sun duba ko'ina babu su babu labarinsu,dukan sitiyarin motar ya yi ya kifa kansa yana addu'ar da ma yana ɗago idanuwansa ya ganta,tabbas babu abinda zaisa yabar Abuja idan har bai ga Basma ba.
****
Yau ake ɗaura auren Ahmad da amaryarsa,amman fa kana ganin fuskarsa kasan ƙwata ƙwata baya cikin hayyacinsa don tunda ya rasa Basma gani ya ke tamkar ya rasa komai na rayuwarsa,tunda aka dawo daga ɗaura auran na sa yaji baki ɗaya kansa yana wani irin sara masa ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito yasha magani ya ƙwanta.
Yana ƙwanciya babu da ɗewa Hajiyarsa ta shigo ɗakin nasa,ganinsa ya rufu da blanket sai taji gabanta ya yi mugun faɗuwa sosai,a hankali ta isa inda ya ke ta zauna a bakin gadon a hankali ta yaye blanket ɗin ta shafa fuskarsa,wani zazzafan zazzaɓi taji a jikinsa yana tashi harda huci.
Cikin tashin hankali ta kira sunansa tana haɗa baki wajen ce wa"Ah.Ah..Ahmad tashi mu tafi asibiti ba kada lafiya jikinka ya yi zafi sosai.
"Mama ki barshi na fara jin sauƙi yanzu".ya faɗi hakan yana dafe kansa"gaskiya Ahmad bakaji sauƙi ba,ga kanka nan har yanzu zafi zau kamar wuta."
babu yadda ta iya dolenta ta haƙura ganin ɗan na ta ya dage,tana addu'ar Allah ya bawa ɗanta abin sonta lafiya,tunda ta takura masa akan wannan auren shikkenan ya shiga ciwo yau lafiya gobe babu lafiya,ita kanta amaryar ta kasa gane kansa sam,don irin wannan zancen da ake zuwa shi ko sau ɗaya bai je ba,sai dai ita idan har ta matsu tazo da kanta.
***
"Wallahi mama tunda Basma ta yi tafiya na kasa gane kai na baki ɗaya,hankalina duk yana kanta Mama na rasa wani irin so na kewa Basma a tarihin rayuwata babu yarinyar da ta taɓa shiga zuciyata irinta".
"Aliyu kenan ni dai duk wannan tatsuniyar na gaji da jinta idan har kana son yarinya to kaje gidansu kawai ayi komai a gama,don daman a addinance ma idan kaga yarinya kana so to babu abinda yafi sai kaje gidansu ayi maganar aure a wuce wajen,ba azauna kullum ana soyayya ba,iyayen yarinya su gaji har su ba ta wani".
da sauri Aliyu ya ƙwalalo manyan ƙyawawan idanuwansa ya ce"caɓɓi jan ai wallahi mama idan har aka aurawa Basma wani to fa ki siyo likafa ni ji ajje don tabbas margayawa zanyi".
dafe ƙirji mama ta yi ta ce"to Allah ma ya kiyaye Aliyu kai kaɗai fa na ke dashi a duniyar nan?idan har ka mutu ni yaya zanyi da rayuwata,ni dai ina maka fatan akhairi akan Basma don insha Allah ina ji ajikina matarka ce insha Allah."
Ɗan murmushi yayi sannan ya sumbaci goshin mahaifiyar ta sa ya fita,yana mata bye bye,Ɗan murmushi ta yi tana kallon Ɗan nata sannan ta tashi ta saka myafinta,don taga idan har ta biyewa Ɗan nata to fa zaiyiwa kansa biyu babu ne gwara taje gidansu yarinyar da kanta ayi komai a wuce wajen.
Tana fitowa direbanta yaja ta sai gidansu Basma,da sallamarta ta shiga har cikin gidan,hjy saratu tana daga cikin Ɗaki ta ce"Kai wannan wani irin sallama ce tun daga ƙofar gida kamar masu neman gafara".tana faɗar hakan ta fito waje ta saman bene tana hango wata hamshaƙiyar mata tun daga kan suturarta har kan kayan jikinta babu na banza.
Da sauri hajiya saratu ta sakko tana ce wa"lale marhabun hajiya".tana washe baki kamar wacce aka yi wa albishir da shiga aljanna.
Kai tsaye ɗakinta ta kai ta nan da nan ta saka maryam ta kawo mata lemo da ruwa a fridge sannan ta zauna suka ƙara gaisawa,jikin hajiyar Aliyu dai har yanzu ba a sake ya ke ba ta ce"don Allah hajiya ke ce mahaifiyar Basma"?.
Wani irin mummunar faɗuwar gaba Hajiya saratu taji ta ce"eh.eh.amman ba ni ba ce".
ta faɗi hakan duk hankalinta ya tashi don arayuwarta ta tsani taga arziƙi yana ƙetaro Basma ba tare da ya ƙetaro ƴaƴanta na cikinta ba.
Hajiya ta gane wani abu a dangane da matar sai ta ce"oky to don Allah a haɗani da maman na ta".?
babu wanda ya yi magana acikinsu don faɗuwar gaba sai maryam ce ta yi ta maza ta ce"am Hajiya gaskiya ba nan gidan bane ki dai nemi gidansu".
mamaki sosai ne akan fuskar Hajiyar Aliyu ta kalli Hajiyar Aliyu duk taga yadda idanuwanta ya yi zuru zuru saboda tashin hankali bata ƙara ce wa komai ba ta tashi ta buɗe labulen ɗakin a hankali ta fita,tana mamakin waɗannsn mutanen.
Hango gilmawar mama ta yi ta shiga kitchen kuma sai taga kamarsu ɗaya da Basmar Aliyu don yasha nuna mata hotunan Basma awaya don bashi da aiki idan ba kallon hotunan Basma ba.
da ɗan sauri ta bi bayan mama kitchen ɗin,mama taji tsoro don jin mutum a bayanta,da sauri Hajiyar Aliyu ta ce"sannu baiwar Allah nasan baki sanni bako"?.
ɗaga kai mama ta yi sannan ta ce"eh amman lafiya kuwa baiwar Allah"?.ɗan murmushi Hajiyar Aliyu ta yi sannan ta ce"yauwa don Allah ke ce maman Basma"?.ta faɗi hakan tana kallon fuskar mama duk da ko da bata faɗa ba kammanin da sukayi zai tabbatar maka da ita ce mamanta.
*Miss green ce*