FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
I proudly a writer,i lov hausa novels
Sample · 1
_*🔖BASMA*🔖_ 📄Littafi na 1*Ummu maher(miss green🍀)*_Noticed🛐:wannan littafin labarine akan wata yarinya wacce ta kasance kurma ce._----------------------*matso kuji👂🏻*Babu abin ƙyama a halittar Allah matuƙar shi ya yi halittarsa don haka mu kiyaye don muma bamu fi ƙarfin ikonsa ba.---------------Bismillahir Rahmanir Rahim 1🟠. . . .A hankali na ke share Ƙaton gidan a zuciyata ina ta istigfari don ban taƁa yin shiru da bakina akan ambaton Allah,shiyasa ko da yaushe zaka ganni cikin nutsuwa da kamala,wata sharar naji an watso min na ɗago kaina Maryam na gani a kaina tana ce wa"to uwar shara ga wata ƙarin sharar nan".bance mata ƙala ba na koma gefe na zauna don nasan tunda Maryam ta fara haka to tabbas tana son ɗebo rigima ne. Cikin fushi ta ce"ikon Allah yanzu don na kawo wata sharar ki haɗa shine zaki koma gefe ki zauna ke ga ki uwar fushi ko?".sunkuyar da kaina na yi hawaye na bin kuncina Allah sarki baki yana da daɗi wani lokacin,yanzu da ina da baki da tuni ko da wataran banyi magana ba to tabbas wataran zanyi don sha'anin mutanen gidan sai a hankali. Ana cikin hakan Hafsat tazo ta sameni ina kuka ta ce"Basma me ya faru ki ke kuka kuma?".tasan halina ba lallai in gaya mata ba don aƙwaini da haƙuri kamar dutse don haka ta juya kan Maryam don taga alamar ni da Maryam ne don ta juya ƙeyarta ta yi irin ɗaurin nan na ture kaga tsiya,don ƙarin neman rigima sai ce wa ta yi"to tsigarallahu to da kika zo rama mata zakiyi ko kuwa inji labari?".ran Hafsat ne ya ɓaci sosai ta ce"kin san ai zan iya rama mata ɗin saboda kin san Basma kurma ce shine ki ke mata duk abinda ki ke so don ki zalunce ta,to wallahi ba zaiyuwuba sai na tsaya tsayin daka na rama mata duk wani cin kashi banza kawai babbar kwabo". Shaƙo Hafsat Maryam ta yi ta ce"ikon Allah yanzu Hafsa ni ki ke zagi saboda wannan kurmar banzar ko?ko da ya ke ƴan ubanci za ki nuna min saboda ita ƴar ƙanwar Mamanki ce dole ki nuna min haka?to wallahi ki maida hankalinki ko kuma inci ubanki hankali ƙwance". hayaniya sosai su Hafsat suka fara ita da yayarta Maryam ni kuka babu abinda na ke sai kuka ina rabasu,muna cikin hakan Hajiya Saratu ta fito tana ce wa"ikon Allah ke Hafsat tsabar tsaurin ido ki rasa da wacce za kiyi faɗa sai sa'ar yayarki?amman ke dai baki da kunya wallahi,ko da ya ke aikin munafukar uwarki ne mai zugaku a kan yi wa mutum rashin mutunci".babu abinda Maryam ta ɓoyewa mahaifiyarta harda ƙarya da sharri duk ta haɗa ta faɗa. Tafi Hajiya Sara ta farayi tana ce wa"ai ni daman nasan babu munafukar da ta haɗo wannan faɗan sai wannan munafukar kurmar.sai ana magana ta yi maka wuƙi wuƙi da idanu tana kallon ka kallon rainin hankali. Ta yo kaina tana ce wa dukan da Hafsat ta yiwa ƴa ta yasin akanki zan rama,da gudu Hafsat ta y...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.