Hakuri,tausayi,tsantsar biyayya,makirci
Part 2
A secret writer:๐๐๐๐๐๐
_WAYE_
_MAHAIFINA..?_
โโโโโโ
~Written~
~By~
~A secret writer~
_*A new story by a new writer with a new style.*_
_*This is my first novel happy reading...!!!*_
_*Complain cannot stop what will happen from happening.*_
๐ ฟ 2
Da sallama suka shiga bangaren.
Mama dake Zaune Kan kujera three sitter tana rike da remote a hannunta, ta juyo ta amsa musu sallamarsu sannan ta cigaba da abunda takeyi.
Suka karaso tare da zama a kasan carpet.
"Mama ina wuni.?"
"Lafiya qalau Afifa, yasu mamanki.?"
"Lafiyansu qalau,ya Mimi da Jiki.?"
Alhamdulillahi Mimi jiki Yayi sauki."
"to Allah Kara sauki, Mami tace in gaisheku."
To idan Kin koma kice ina amsawa."
"to insha'allahu zataji..!"
Hayaniyarsu ce ya tada Mimi dake bacci a cinyan Maman.
"Mama ina wuni", Cewar Ismat dake Duke tun dazu Tana Jiran su gama gaisawa da Afifa ta dora Nata gaisuwar.
Ko kallon in da take ba tayi ba bare tasa ran zata amsa mata gaisuwarta.
Mimi ce tace.,
"mama Ana gaisheki."
"Ai Naji tunda ni din ba kurma bace, Amsawan ne bai zama doleba a gurina."
"haba mama abinda kike yi bai dace ba sabida Allah fa, ai ko albarkacin zuwanda tayi taga ji........!"
Cikin fada mama ta katseta..,
"ni kike cewa abunda Bayi bai daceba Saboda na ki amsa gaisuwar wannan yarinyar, kanwar uwarki ce ita..?"
Ta juyo ta Kalli Ismat da ke duke a kasa Tana Mai zubar da hawaye.
Cikin takaici mama tace...,
"ke tashi kibarmin parlour kafin naci ubanki, Ko da yake ba uban nema da keba bare a zageshi, Saboda haka tashi Kiban gurin nan ko na maujeki."
Cikin Sauri Ismat ta Mike ta fita daga parlourn hawaye na tsiyaya daga idanuwanta, tana kuma jiyo irin zaginda mama ke wa mahaifinta.
A wani ษan lungu dake tsakanin ษangaren mama da umminta ta tsugunna tana kuka, har Afifa ta fito ta sameta a gurin.
Cikin sanyin jiki Afifa ta karaso gurin ta tsugunna ta dafata.
Jin an dafata yasa ta ษago.
Hannu Afifa tasa tana mai goge mata hawaye haษe da girgiza mata kai tace..,
"Dan Allah Ismat kiyi hakuri da kukan nan haka kar ki jawa kanki ciwo,Ta kama hannunta suka mike.
Har kofan parlourn su ta rakata.
"Idan kin shiga ki cewa ummi na wuce."
"To ki gaida gida."
Hannu kaษai ta ษaga mata ta fita daga gidan kasancewar an fara kiraye kirayen sallah.
Bata tarar da ummin ta a parlour ba,kawai sai ta wuce bedroom nata.
Tana shiga tafaษa toilet ta ษauro alwala ta fito ta shinfiษa sujud ta tada sallah.
Bata fito ba sai da ta sallaci sallan isha,saboda haka ta tashi taga umminta nayi in tayi mangariba bata tashi akan sujud ษinta zatayi ta tasbihi har sai ankira isha.
Bedroom ษin umminta ta wuce,ta tarar da ita tana ninke sujud ษin da tayi sallah da shi.
"Ismat kin dawo..?"
"Eh ummi."
"To ina kika baro Afifan.?"
"ta wuce gida."
"To Yaya kuka baro jikin Mimin.?"
"Da sauki..!"
"To madallah,sai kije ki ษebi abinci kici ina fitowa yanzu."
"To Ummi ke baza kici bane..?"
"kin manta yau Dadynku yana gari ne..?
Bata kara cewwa komai ba ta mike ta fita,haka kawai taji tana jin haushin abinda Ummi tace.
Wato ita kam ta mijinta ma takeyi ba ruwanta,ta manta da mahaifina kuma ta hanani na mata magana akanshi.
Wannan maganan duk a cikin zuciyarta takeyi.
Haka ta cigaba da tunani da magana a cikin zuciyarta har ta gama cin abinci.
Ta na zaune a parlour tana kallo bayan tagama cin abinci,har ummi ta fito daga ษaki tazo ta sameta suka cigaba a kallon tare suna hira jefi jefi har Dady yadawo.
Ismat ta mike ta musu sai da safe bayan tayiwa Dady sanda dawowa.
Tana shiga bedroom nata ta faษa toilet ta sakarwa kanta ruwa,sannan tayi alwala ta fito.
Tana fitowa ta buษe wardrobe nata ta ษauko sleeping dress nata ta saka sannan tabi lafiyar gado.
_*Daga Alkalamin*_โ๐ปโ๐ปโ๐ป
_*sabuwar marbuciya*_