4
*DUBU JIKAR MAI CARBI*
©AMEERA ADAM
FIRST CLASS WRITER'S ASSO...
*Littafin kuɗi ne 200 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin Mtn, ki turo da shedar biya ta wannan lambar ***.*
FREE PAGE 4
Wannan karon gabaɗaya turus suka yi da jin abin da aka faɗa, kallon-kallo aka fara yi a tsakanin juna kowa da abin da yake nazari a zuciyarsa. Suna cikin haka suka sake jin an ce, "Bismillahir rahmanirrahim bari mu fara ɗauka daga kan ta bakin ƙofa." Ai Dubu bata rufe baki ba sai ji ta yi alamar guje-guje, Yahanasun Auwalu tun bayan sallar asuba da ta shiga ɗakin Inna Furai ba ta sake fitowa ba kuma ta ci alwashin ko da fitsari za ta ji sai dai ta matse abin ta, idan ta kama ma sai ta saki abin ta a wurin. To ashe tsugunne bata ƙare mata ba tun da har fatalwar za ta iya kawo musu farmakin dare har cikin ɗakuna, tun da ta ji an ce za a fara ɗauka daga na bakin ƙofa.
Nabila ƴar wurin Hajiya Nafisa, budurwa ce don ta yi sha tara a shekaru. Turo baki ta yi tana cewa, "Maganar gaskiya Mommy ni fa na gaji da wannan abubuwan kullin abu ɗaya wacce irin fatalwa ana zaune ƙalau bayan kowa ya san babu wata fatalwa a musulunci." Cike da ƙosawa Hajiya Nafisa ta ce, "Nabila ya za mu yi kin san dai ba mu da ta cewa tun da zuwan nan na dole ne ya kama mu haka Allah ya ƙaddara mana." Yaya Babba da ke gefe fuskarta ban da gumi da maiƙo babu abin da take yi, ta dubi Hajiya Nafisa da kallon sheƙeƙe ta ce, "Ke Nafi! Zuman ku a gidan na shi ne ƙaddara? Wallahi za ki ga ƙaddara kuwa ganin idonki. Wannan gidan da kike gani kin zo kenan zuwa sojan badaskare." Tana gama faɗa ta yi ƙwafa a zafafe. Dubu daga wurin da take ta jiyo hayaniya na tashi kaɗan-kaɗan ta sake shaƙe murya ta ce, "Ƴan sama jannati basa lamintar kuskure don haka za mu fara bi ta kan dabbobin gidan kafin mu fara taɓa mutanen ciki, ina tawagar Fatale ku fara dirowaaaa." A hankali ta lallaɓa da sauri ta buɗe ɗakin zabbin Baba Munkaila. Hannunta riƙe da muciya ta fara buga ƙyauren langa-langar da ke jikin ƙofar. Nan da nan zabi suka fitowa a tsorace suka fara tsalle da kuka "Ƙurƙet! Ƙurƙet!" Da yake da hasken wutar lantarki tuni zabbi suka fara bazama suna kuka, Dubu ta sa muciya ta riƙa make kawunansu ɗaya bayan ɗaya. Da ta bugawa zabo ɗaya sai ka ji ya yi ƙara ya faɗi ƙasa. Wannan kukan Zabbin ba ƙaramin ɗaga hankulan mutanen da ke cikin ɗakunan ya yi ba. Shiru suka yi suka zurawa sarautar Allah ido. Kowa da abin da yake ayyanawa zuciyarsa. Sai dai a wannan ƙadamin Lantan ta ci alwashin matuƙar tana da rabon ganin wayewar gari, babu wanda zai hanata tafiya don tun da ta zo duniya bata taɓa ganin masifa da tashin hankali irin wannan ba.
Zabbin nan gabaɗaya haka suka warwatsu suka shiga sauran sashen da ke cikin gidan. Muhsana ita ce ƴar autar Lantan, ta taho daga can sashen Baba Sule ba ta san abin da yake faruwa ba ta hangi Zabbin Baba Munkaila suna guje-guje wanda ya tabbatar mata da alama akwai abin da yake faruwa. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin gawarwakin Zabbi kusan bakwai a ƙasa jini duk ya ɓata wurin. Sai dai har lokacin bata ga wanda yake aikata wannan abin ba, ɗaya zuciyarta ce take raya mata ko dai da gaske Fatalwar da ake faɗa ce ta fara aikinta, yayin da ta ƙara riƙe hannu Ɗanta Salihu don dama yaron ne ya fito da ita zai yi kashi. Ta bayan ɗakin Marigayi mai carbi ta je wucewa ba ta yi aune ba sai ji ta yi an fisgi hannun Salihu, aikuwa kusan tare suka ƙwalla ƙara daga ita har Salihun da ake ja, jan Salihu ta riƙa yi tana yi tana ihun neman agaji amma ba a daina jansa ba. Dubu na ganin Muhsana ta kusa fin ƙarfinta ta raɗa mata muciyar a baya tana cewa, "Ki taho mu yi rayuwar barzahu da ke. Ko ki bani Ɗanki Salihu na tafi da shi, ko kuma na ɗauke ku gabaɗaga." Muhsana bata gama jin ƙarashen maganar ba ta saki hannun Salihu ta yi cikin gida da gudu tana tafe tana sosa wurin da Dubu ta maka mata muciya. Shi kansa Salihu da ba a yi masa komai ba ya gama tsorata, dama jikinsa babu riga babu wando haka ya zuba a guje da tiƙeƙen cikinsa a daidai lokacin aka ɗauke wuta Salihu ya rasa wurin da zai bi haka ya riƙa gware da bango yana make sauran zabbin da suma ta kansu suke yi.
Ihun da Salihu yake yi ne ya tabbatar musu da lallai Fatalwa ta fara zuwa kan bil'adam, tun da; da farko sun ji kukan zabbi. A wannan lokacin Yaya Babba da ƙaramin tsorata ta yi ba don ko kaɗan Dubu bata faɗo mata a rai ba bare ta ambace ta. Lantan da ke ɗakin Inna Furai ta fara hawaye bibbiyu don saboda firgici ta tuɓe kayan jikinta ta sake saka su ya fi sau bakwai. Lokacin da ta riski muryar Muhsana na ihu, kuka ta riƙa yi wiwi don Mushana ita ce autarta. Da ta daina jin kukan Muhsana sai na Salihu wannan ne ya bata tabbacin tuni Tawagar Fatalen sun gama da Muhsana sun koma kan Salihu. Da ƙyar Salihu ya samu ya isa wurin ɗakuna ya fara lalubawa yana kuka, hannunsa ya ɗora akan ƙofar su Inna Furai yana bugawa yana faɗin, "Innaaaaa! Iyaaaa" Lantan na jin haka ta ɗare saman gadon Inna Furai hannunta riƙe da ɗan kanfen Badariyya tana ta tura kai duk a tunaninta rigarta ce za ta saka. Inna Furai wani farfari ta riƙa yi kamar wacce take kan hanyar suma, sai motsa baki take tana addu'a.
Zabbin da suka tarwatse wasu daga cikin su hanyar waje suka yi, suna kuka a firgice. Dubu tun da ta ga an ɗauke wuta ta haye katanga ta dira ta bayan gidan. Sai ga ta kamar mumina ta wuce shagon Lamarana ta siyo maganin sauro, da sauran wata hamsin ɗinta. Zuwanta ƙofar gidansu ya yi daidai tashin Baba Munkail kenan yana kaɗa Zabbin da ya ga suna tsalle suna fitowa ɗaya bayan ɗaya. Mutanen wurin ne suka fara taya shi, Dubu na zuwa ta zabga uwar sallama, ta yi haka ne saboda Baba Munkaila ya ganta don ta sake cire zarginta da yake daga kanta.
Cikin masifa ya fara yi mata magana, "Dallah sakarai matsa kina gani zabbina na fitowa sai wani ya ɓace a cikin duhu." Da sauri ta matsa gefe ta ce, "Baba Munkaila don Allah ara min fitila na kaiwa Inna Maganin sauronta tsoron soro nake." Ci kanki bai ce mata ba har suka samu suka kame zabbin, ban da masifa babu abin da Baba Munkaila yake yi, don a duniya idan kana son ganin ɓacin ransa cikin gaggauwa ka taɓa masa zabbinsa ko kuma wani laulawar keken hawansa. Yana gaba Dubu na biye da shi sai mutum uku da suke riƙe da zabbin nasa. Faɗa yake ta saki yana cin alwashi ga duk wanda ya buɗe masa Zabbi sai ya yi masa rashin mutumci. Suna shiga tsakar gida Baba Munkaila ya hasko gawar wasu zabbi biyu daga bakin ƙofa. Nan take cikinsa ya bada sautin ƙululululu! Jikinsa ne ya ɗau tsuma wani gumi na keto masa ta ko'ina, watsar da na hannunsa ya yi; ya kwasa a guje.
Yadda jaruman Indiya suke kwasar gudu idan sun yi tozali da masoyansu haka Baba Munkaila ya watsar da zabbin hannunsa ya kwasa da gudu har da wata uwar ƙara yana zuwa ya zube a wurin ya suri Gawarwakin zabbin ya rungume yana sauke ajiyar zuciya mai zafi, haɗe da haɗiyar wani irin yawu mai ɗacin gaske.
Kamar mai shirin yin kuka haka Baba Munkaila ya rinƙa shafa matattun zabbin yana cewa, "Don Allah wanene ya yi mini wannan ɗanyen aikin. Wallahi duk wanda na kama yana da hannu a ciki sai na ci ubansa." A daidai lokacin Dubu da sauran mutum ukun da ke riƙe da zabbinsa suka ƙaraso. Dubu ta yi tsaye tana kallon yanda gumi ke ɗiga daga jikin Baba Munkaila. Yana ɗagowa ya maka mata duka yana cewa, "Don Ubanki za ki kamo mini sauran ko su ma sai an kashe mini su." Kamar mai jira haka Dubu ta sheƙa da gudu kamar gaske tana dariya ƙasa-ƙasa. Daga can ɗan nesa Baba Munkaila ya fara hango ƙaramin yaro yana tafe yana jan ƙafar wata ƙatuwar zabuwa, wacce da alama ita ce uwar garken ciki. Salihu yana tafe yana murmushi yana zuwa ganin Baba Munkaila na riƙe da sauran zabbin ya sa ya miƙa masa yana sake yaƙe baki yana cewa, "Baba an ci kaza." Kusan suman zaune Baba Munkaila ya yi, ya ƙurawa Salihu ido ya ganshi tik ko wando babu. Cikinsa ya yi kurcici sai sheƙi yake da maiƙon abinci. Baƙin cikin ne ya kama Baba Munkaila ya dubi Salihu murya a daƙile ya ce, "Kai a ina ka gano wannan?" Salihu ya juya bayansa ya nuna ya sake cewa, "Baba an ci kaza"
A fusace Baba Munkaila ya buga masa tsawa ya ce, "A gidan uwarka za a ci kaza?" Salihu ba ƙaramin tsorata ya yi ba don haka ya saki zabon hannunsa jikinsa na rawa. Baba Munkaila ya sake ɓata fuska ya ce, "Waye ya kashe mini zabbi ko kaine?" Tsoro da ganin yanda Baba Munkaila ya ɓata fuska ya sa Salihu bai yi wata-wata ba, ya ce, "Ni ne a cen"
Baba Munkaila zuru ya yi yana kallon Salihu kamar wanda ya yi tozali da sabuwar halitta, ya sake haɗiyar yawu mai ɗaci murya a daƙile ya ce, "Wato kai ka buɗe daga keji suka fito ko?" Salihu ya gyaɗa kai wannan karon har da murmushinsa na ƙarfin hali ya ce, "Ni a Umma ne..." Haushi ya sake kama Baba Munkaila ya ji kamar ya shaƙe wuyan Salihu. Kawai sai ya miƙe ya damƙi hannun Salihu ya juya ba walawa ya cewa mutanen da suka rako shi ciki, "Malam Hamza ga kejinsu ku zuba su a ciki." Mugun kallo ya watsawa Dubu don Allah ne ya taimake ta ba ta yi wani laifin ba da ragowar fushinsa a kanta zai sauke.
Yadda Baba Munkaila yake fusgar hannun Salihu ba ƙaramin tausayi da dariya zai baka ba, yana zuwa wurin ɗakunan ya fara kwaɗawa Muhsana kina. Sai dai babu motsin wanda ya ji hasalima ƙofar ɗakunan gabaɓaya a rufe suke. Haushi da ya kama shi ya hau buga ƙofofin ɗakuna yana faɗin,
"Wai lafiya kuwa mutanen gidan nan wannan wanne irin abu kuke yi ne." Wannan bugun ƙofar ba ƙaramin razana Salihu ya yi ba, don haka ya fara tsanyara kuka yana murza idanu tare da wurga tsilla-tsillan ƙafafuwansa. Cike da takaici Baba Munkaila ya tallaƙe ƙeyarsa yana cewa, "Rufe mini baki don ubanka. Shegen yaro mai siffar ƴan ruwa."
Dukan da Baba Munkaila ya yi wa Salihu ba ƙaramin ratsa kansa ya yi ba don haka ya kuma fashewa da kuka. Lantan da ke cikin ɗaki ta kuma zabura tana cewa, "Innamal A'amalubinniyati..." Sai kuma ta hau gado ta sauko, sannan ta sake cewa, "Sadaƙallahul azeem. Kuna ji fatalwar nan har rikiɗa take yi za ta yaudare mu, mu buɗe mata ƙofa." Inna Furai da ta yi ɗai-ɗai a ƙasa ta ɗauko wani rawanin Marigayi Mai carbi, ta ƙadandane shi tana numfarfashi ta ce, "Ni dai na san idan da zazzagar amana to babu makawa fatalwar nan koda ta shigo ba za ta illatani ba. Wannan rawanin tun na ranar aurenmu ne wannan kaɗai ya isa shaidata..." Bata ƙarasa sambatun ba suka ji bam Baba Munkaila ya ɓallo ƙofar, ya koma ta ɗakin Yaya Babba ita ma ya ɓalle ta. Nan fa suka yo carko-carko masu ihu na yi masu gudu suma suna yi. Tsawar da Baba Munkaila ya buga ce ta saita nutsuwarsu, yana huci ya nuna Salihu da ke rarraba idanuwa ya ce, "Ina uwar yaron nan?" Tsit suka yi aka rasa mai magana sai Lantan da ke zare idanu ta ce, "Ai Muhsana kam tuni Fatalwa ta daɗe da gamawa da ita..." Da sauri ya katse ta da cewar, "Don Allah Inna Lantana ki rabani da zancen fatalwar nan. Ku duba irin ɓarnar da aka yi mini." Ya ƙarasa maganar yana haska musu gawarwakin zabbinsa.
Yaya Babba da fitowarta kenan ta zuba kabbara tana cewa, "Kazalika mun ga tabbaci wallahi ya tabbata fatalwa na bibbiyarmu a gidan nan. Dama fa kafin su aiwatar sai da suka faɗi cewar za su fara ta kan dabbo. Don Allah ku kira mini Garba don idan na ƙara kwana a gidan nan ba Mai Jama'a ne ya haife ni ba."
Ana cikin haka sauran Mazajen gidan da ke zaune a ƙofar gida suka shigo sakamakon Malam Hamza ya sanar da su abin da suka gani. Ganin su Yaya Babba carko-carko a tsaye ya sa su tambayar ba'asi, nan take aka sanar musu Baba Munkaila ya kora musu jawabin zabbinsa. Cikin Baba Auwalu da na Baba Sule kusan lokaci ɗaya ya kaɗa, tuni gumi ya wanke musu fuskoki. Nan fa aka shiga tausar Baba Munkaila akan ɓarnar da aka yi masa sannan magidantan mazan suka ci alwashin ɗaukan mataki a cikin gidan. Baba Abubakar da kansa ya fita ya sanarwa ƴan bijilanti abin da yake faruwa ya basu umarnin kula da gidan tun daga bayan gidan har zuwa cikinsa.
Lantan duk wannan matakin da aka ce za a ɗauka bai yi mata ba, don ta kasa ta tsare akan dole sai ta tafi a daren sai da Baba Abubakar ya lallaɓata sannan ta amince da sharaɗin gari na waye za ta kama gabanta. Hajiya Nafisa na jin haka ita ma ta yi tsalle ta ce washegarin ranar za ta tafi don ba za ta ƙara kwana ba. Gabaɗaya suka ɗunguma zuwa sashen Auwalu da ƙyar can ma aka samu suka buɗe ƙofofi don Muhsana sai da ta suma ya kai sau Uku, da ta farfaɗo idan ta ce ina Salihu? Suna ce mata baya nan take sake zubewa.
Duk plan ɗin da ake shiryawa Dubu ta yi fakare tana sauraronsu, kuma zuciyarta ƙal da ta ji kowa ya ce zai koma inda ya fito.
Sai dai suna haɗa ido da Nabila sai ta bushe da dariyar mugunta tun Nabila bata lura ba har ta fara fahimta. Faɗa suka yi kace-kace har Nabila ta cewa Dubu, "Ballagaza ƴar ƙauye." Buɗar bakin Dubu kuwa ta ce mata, "Ubanki ma ɗan ƙauyen ne kuma kema kin dawo nan har abada." Tsautsayi ya ja Nabila ta kifawa Dubu mari nan take kuwa Yaya babba ta yi tsalle ta dire ta fara faɗa daga ƙarshe har ta ce a kira mata Baba Abubakar.
Ran Mommy ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, don a ganinta hukuncin da Nabila ta ɗauka shi me daidai.
Baba Abubakar cikin ladabi ya je gaban Yaya Babba ya ce, "Inno an aiko kina kirana."
Nuna masa Nabila ta yi tana ɓata fuska ta ce, "Garba don Allah ka gaya mini kana da wani ƙauyen da ya wuce wannan?" Baba Abubakar ya girgiza kai ya ce, "Babu Inno."
"Ka gaya mini ni da Marigayi mahaifinka muna da garin da ya wuce nan?" Yaya babba ta faɗa fuska a gaɗe.
"Babu Inno mai yake faruwa ne?"
"Ƴarka za ta makanta Dubu akan ta ce mata Ubanta ma ɗan ƙauye ne, don Allah meye aibu a nan? To tun wuri ka yi musu tsakani don ba za ta nakasa mini jika ba. Tun zama bai kankama ba har anfara kai ga haka, ina ga in sun kwaso kayansu sun dawo nan gabaɗaya." Nabila ta kalli Yaya Babba a fusace ta ce, "Allah ya sawaƙe wa zai dawo nan da zama..." Tun bata rufe baki ba Mahaifinta ya ɗauke ta da mari don tun kafin su zo yake gargaɗinsu akan taɓa Dubu don ba abu ne mai wuya da zai ɓata ran mahaifiyarsu ba. Marin ba ƙaramin shigar Nabila ya yi ba don haka ta fashe da matsanancin kuka, ita kanta Mommy sai da marin ya taɓa ta dukda ba ita aka yi wa ba.
Yaya Babba ta ɗebi sallati tana tafa hannuwa rai a matuƙar ɓace, ta nuna Baba Abubakar ta ce, "Garba a gabana za ka illata mini jika ina ji ina gani. An ya kana ƙaunar Nabila kuwa? Daga na ce ka yi wa yarinya faɗa shi kenan sai ka kashe ta da mari. Don Allah meye mari ana zaune ƙalau? Wallahi idan ka sake shigowa ɗakin nan Garba sai na watsa maka falsafar rashin mutumci. Don Allah Dije ki fice mini da Garba daga ɗaki tun ban fice na bar masa ba." Yaya Babba ta share ƙwallar idonta ta dubi Baba Abubakar da ke niyyar miƙewa ta ce, "Garba ka fita daga sabgar jikata Nabila wallahi idan ba haka ba sai na saɓa maka." Ya russuna cikin girmamawa ya ce, "A yi haƙuri dai Inno." Biris ta yi ta rabu da shi, ita kuwa Mommy ta cika fam kamar za ta fashe sai harare-harare take, don ma Yaya babba bata lura da ita. Dubu ta raɓe ta gefe tana yi wa Nabila gwalo, ai kuwa karaf akan idanun Yaya Babba.
Da sauri ta riƙe haɓa da hannu bibbiyu cikin mamaki ta ce, "Ke dai an yi makirar yarinya. An ya Dubu halin Ahmad kika yi kuwa wallahi wannan baƙin halin sai dai idan na Kulu ne..." Tun bata rufe baki ba Dubu ta ce, "Ni dai ki daina zagar mini iyaye tun da ba su yi miki komai eheee." Yaya Babba na jin haka ta rushe da kuka tana ƙwalawa Baba Munkaila kira.
Ummou Aslam Bint Adam🌚