Book 3 (End)
by @takori
A cikin gidan-gonar Zaynab da ke garin Gwarzo, walima ce ta musamman Zaynab ta hada musu su takwas kacal. Tana sanye da fararen ‘wedding gown’ dogaye har suna jan kasa, tayi lullubi da farin ‘net’ amarya dai sosai sai walkiya take ta inda duk ta juya, ta matsa jikin bishiyar ‘guava’ ta aje ‘yar karamar (automatic video camera). Bata kai ga dagowa ba Faruq ya karaso ya kwantar da kanshi a bayanta, yace I luv u Zaynab".
Qassim ya sakar masu flash din Camera a hakan. Imran dake zaune can gefe kan wani dutse, Haiti na zaune daga gefen kafafunshi, tana yi mishi jan yatsu a hankali, suka juya suna hango abinda ake yi, wato irin soyayyar da ake zubawa tsakanin Zaynab da Faruq dinta, ya lumshe ido yana murmushi yace "kin ga inda ake soyayya can, ba irin tamu ba" ta harareshi, cikin wata siga mai jan hankali tace “au daga gareni ne ma?”
Ya dirgo daga kan dutsen ya kwantar da kai a kafafunta, ya rintse ido yace “na yarda daga gareni ne, amman nima daga yau na daina HaitiI luv u, I luv umore than I can say. Don Allah mu rike amanar juna.
Ba soyayyah ce ta hadamu ba, iyaye ne, daga baya kauna ta hadamu, in sha Allah bazamu taba ganin ba dai-dai ba a rayuwar auren mu".
“Ya Im! Ya Im!!”
Zaynab ce ke kira daga nesa, cikin siririyar muryarta "ka taho gashi na yi ‘serving’ dinka” ya ce “to Zaynab dina”. Ya kama hannun Haiti suka nufi inda suke.
Makekiyar ledar cin abinci ce aka shinfida, aka shaketa da ‘warmers’, sunkin ‘foil-papers’ da tangarayen abinci. Manyan ‘picinic-coolers’ suma shake suke da nau'i-nau’in kayan abin sha masu dan karen sanyi. A gefe tirkeken rago ne guda aka gashe. Yana tsaye jikin karfe cikin ramin da ake gasa shi sai naso yake ya gasu yayi lugub, mai so sai ya je ya yanko iya yadda yake so ya ci.
Suka soma cin abincin suna nishadI, aka ci aka sha akayi hani'an. Ko kafin su gama duhun dare ya fara shigowa, wato an kirayi sallar maghriba. Suka matsa ga (pipe) din da ake ban ruwan shukoki suka dauro alawala. Faruq ya ja su jam'in sallar magriba, sukayi addu'a ta musamman akansu, domin neman zaman lafiya a tsakaninsu da zuri'ar da zasu haifa a gaba. Ko kafin su shafa Inna dubu ta aiko Halima ta kwaso mata amaren za’a kaisu gidajen mazajensu.
Faruq da Zaynab suka ce da Halima, ta gayawa Inna Dubu su a cikin gidan gonar-nan zasu kwana cikin (Hut), wato irin bukkar nan ta zamani, da ake yi cikin gidan-gona, tuni sun sa an sanya masu dindimemiyar katifa, gobe zasu tafi nasu gidan da kansu.
Halima ta kama baki, cikin dimuwa. Ya daga mata gira yana murmushi yace "Yes, muna son kafa tarihi ne!”.
Ta ce “to Allah ya tashe mu lafiya". Ta juya tabi bayan su Imran.
Har ta kusan tadda su sai ta dawo, ta kamo hannun Zaynab ta jata gefe tace “sai kin yi hakuri da Faruq, don na sha gaya miki yana matukar son ki. Wannan rubabben son na shekaru goma sha takwas, duk a yau zai nuna miki shi. Kiyi dauriya ki kiyi juriya ki zama mace tagari Zaynab, kuma in gaya miki Imran ya cika alkawarin da ya daukar min. Bamba goma sha biyu, suna nan ya bani na kai miki dakinki”.
Dariya tayi cikin annashuwa, hasken farin wata na kara haskaka kwalliyar amarcinta. Tace “Yaya Halima bani da kalmar da zan gode miki".
Ya karaso cikin kaguwa ya kasa kunne yace “wai gulmar me ake yi ne? in ji dai ba gulmata bace. Ke Yaya Halima dadi na dake in baki ki kulla nunkufurci ba bakya jin dadi ('yar mace, da dan namji suke)”. Ta harareshi, ta juya tana cewa
"kai nan har ka isa in nunkufurceka? Sai dai in maka kan mai uwa da wabi" (ta zuge Zaynab taki yarda da shi). Yana dariya ya sakalo Zaynab suka shige bukkarsu.
*** *** ***
Duk wata rawar jiki da karkarwarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wata zakuwa da nuna zalamarshi, ZAYNAB ta fishi. Duk wani kokarinsa da jarumtakarsa da kyar ya iya ya gamsheta. Halittarta na daga cikin halittar matan da turance ake kira ‘nymphomaniac’. To amma shima ai namijin gaske ne. Yayi mamaki amma yai shukurah ga Allah abisa halin da ya risketa. Ya rungumeta sosai tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, hasken farin wata da alfijir daya soma kokarin ketowa, ya haskaka mishi kayatacciyar fuskarta, yace cikin shauki “Zaynab are you O.K?”
Gyada mishi kai kawai tayi, kamin wasu irin hawaye su mirgino su jika kundukukinta. Tana fatan Allah ya dorar da soyayyarsu da rayuwar su da Faruq cikin GIRMA da daukaka kamar yadda ta faro. Shi kuwa addu'a yake Allah ya bashi tsawon rai, karfi da lafiyar da zai cigaba da iyawa bukatar gangar jikin ZAYNAB, har zuwa ranar da suka daina numfashi.
***
GIRMA YA TASHI!
SHEKARU ASHIRIN A GABA.
Z
aynab Mainasara, na daya daga cikn jami'an majalisar dinkin duniya (United Nations) dake wakiltar Nijeriya, sannan (member) ce a kungiyar Tattalin Arzikin Kasa ta Africa ta yamma da aka fi sani da (ECOWAS). Gabadayan karatun ta har zuwa digiri na kololuwa, ta yi shi ne akan tattalin arziki (Economics) daga Jami'ar Porstsmouth, U.K.
Danta na farko data haifa tun a shekarunsu na biyu da aure (Aliyu) ta bada shi ga Mamie Nuratu tun daga shekarun yaye. Ta yi masa aure da Sa'adatu diyar Haiti da Imran, yana da shekaru goma sha takwas. Ta aurar da Rabi'a tun tana da shekaru goma sha hudu, ta aurar da Nuratu (Mamie) tana da shekaru sha biyar. A nan gaba kadan tana shirin aurar da Halima (Dubu), da kanwarta Hibbani, wadanda ke aji uku na sakandire. Sai dan autanta Sa’id, mai kimanin shekaru goma a duniya.
Na daga jaridar (New-Nigeria), mai dauke da kanun labaran bikin cikar su shekaru ishirin da aure. Ban taBa ganin fuskokin mata da miji da suka dace da juna irin ZAYNAB da FARUQ ba. A kasan hoton an rubuta “an extraordinary lady, ZAYNAB MAINASARA, in celebrating her 20th weddinganniversary” da aka yi a Niamey, cikin wannan shekarar. Duk da irin runguma mai cike da kauna da maigidanta yayi mata, cikin hoton, tana kuma murmushi, akwai wasu dunkulallun hawaye cikin fararen idanunta.
Na samu kaina da maimaita lakabin da akayi mata watau ‘extraordinary’, kwarai sunan ya dace da ita. Ban taBa ganin mace mai ban mamaki irin Zaynab Mainasara ba; mijin da Allah ya nufe ta da samu, dukiyar da Allah ya hore mata, ilimin da Allah ya bata, da daukakar da yayi mata cikin kasar mu mai dinbin albarka, bai goge Bacin ran dake cikin zuciyarta ba, bai shafe Boyayyen bakin cikin dake boye cikin kwayar idanunta ba.
Masha Allahu lakuwwata Illa Billah!
Masoyana a duk inda kuke cikin duniya, wadanda na sani, da wadanda ban sani ba, na gode da yabo da fatan alkairin da kuke yi min. Kamar Zaynab, nima nake cewa ;
"Da fatan watarana Allah ya hadamu cikin alherinsa!"
Sai mun hadu a littafina ‘ALHERI’
Taku:
Sumayyah AbdulQadir Takori