KWANTACCIYA (2nd Edition)

Chapter 16

by @phartybb

Zaina buɗe idanuwanta ta yi ta jawo wayar da take ringing ta duba screen ɗin ta ga Musa. Ɗauka ta yi, da dishashshiyar muryarta ta ce. "Boyfriend."

"Girlfriend kina ganin wannan hukuncin shine dai-dai." Ya tambayeta ta ɓangaren shi.

Hawayenta da suka gangaro ta share tace. "Boyfriend ban samu wani mafitar ba sai shi, Boyfriend mu gudu, mu gudu a ɗaura mana aure shi ne kawai mafitar mu."

Shuru Musa ya yi don yadda yake son Zaina komai ake ce ya yi zai iya. A hankali ya ce. "Kina ganin hakan shine mai kyau."

"Shi ne Boyfriend." Ta faɗa cikin muryar kuka.

...

Har yamma Zaina tana ɗakin a kwance tana bacci bayan gama wayar su da Musa, ta samu baccin da yau kwana uku ya kauracewa idanuwanta ya ɗauketa.

Uku da rabi ta ji bugun ƙofa, ta buɗe idanunta da suka mata nauyi ta tashi ta buɗe ƙofar ɗakin taga matar Yaya Ado ne Surayya da wasu ƴan mata da basu kaita ba su biyu ƴan uwansu.

"Lafiya?" Zaina ta tambaye su tana ƙarewa ƴan matan kallo.

"Mun zo miki kitso da lalle ne." Ɗaya ta faɗi haka.

Zaina ta buga tsaki tana komawa ciki ta ce. "Dalla ku matsa ku bani guri ba za ayi ba."

Ciki Surayya ta shigo ƴan matan suka tsaya a waje, ta zauna kusa da Zaina tace. "Haƙuri za ki yi Zaina ki bari a miki ko don maganar mutane."

"Su yi mana, ni fa sun ishe ni komai abun magana, magana baya ƙare musu." Zaina tace tana fitar da hawaye, haushin kowa take ji a dangin su.

Roƙar duniyar nan Surayya ta yima Zaina akan ta tashi ta ƙi, ƙarshe ma da ta ishe ta miƙe a harzuƙe tace. "Wai ke ana dole ne ki rabu da ni mana, ina ganin girman ki kar kisa na faɗa miki magana."

Shuru Surayya ta yi ta miƙe ta ce. "Allah ba ki hakuri."

Daga haka ta fita tare da ƴan matan Zaina ta bisu da tsaki.

Da suka shiga wajen Inna suka sanar da ita, tace su rabu da ita kawai.

Ƙarfe takwas anyi sallar isha'i Zaina ta miƙe ta fita a ɗakin, ta shiga cikin gidan da yake cike da jama'a, hijabinta taja ta rufe rabin fuskarta don kar a ganta ta wuce ɗaki ta ɗauki abubuwan buƙata ta fito ta wuce bangida, jikinta ta kimtsa ta fito kasancewar ba ta sallah.

Ɗakin Tahiru ta shiga ta ɗauki wayarta ta fito, daga nan ba ta koma cikin gidan ba ta leƙa waje ta ga babu mai zuwa ta sa kai ta fita.

Tafiya kawai take kamar zata ari ƙafa, cikin sauri take yi ko duba bayanta ba ta yi don kar a ganeta, har sai da tasha kwanar da zai kaita layin bayan su kafin taji hankalinta ya kwanta taci gaba da tafiyarta a hankali, ta zaro wayarta ta ƙira Musa.

Bayan Musa ya amsa da da ma zaman jiran ƙiran ta yake, Zaina tace. "Boyfriend na kusa gurin ka zo za ka ganni jikin wani transformer, idan ka iso ka ƙirani."

...

Daga ɓangaren shi ya amsa mata ya kashe wayar, ya fita a ɗakinsa zuwan waje ya shiga motarsa ya kunna da sauri yana barin gidan su bai sanar da kowa ba ga inda zai je ya fita.

Cikin mintuna biyar ya iso gurin, ya ƙira wayar Zaina ta amsa tana cewa. "Na ganka ganin nan zuwa." Tana kashe wayar taja kafarta don ƙarasawa wajen shi taga mota yayi parking gabanta. A mugun tsorace taja baya za tabi ɗayan gefen na cikin motar ya yi saurin fitowa ya fizgota, ta ƙwace jikinta ta fasa ihu tana tace. "Ka rabu da ni Ya Hash."

Ƙin sakinta ya yi, ta fara turjewa ya kwasheta da marin da ya sakata dakatawa ta dube shi, ransa a mutuƙar ɓace da ba ta taɓa gani ba ya ce. "Ina kike tunanin za ki je?"

Ba ta ba shi amsa ba ta ci gaba da ƙoƙarin ƙwace jikinta, ganin ya ƙi sakinta da ƙarfi yadda Musa zai ji ta ɗaga murya tace. "Boyfriend zai sace ni ka taimake ni."

Ai ba ta ƙarasa maganar ba Musa da yake shirin fitowa ganin wani ya tareta ya kwasa da gudu yayi gurinta.

Jin abinda ta faɗa ya saka Hashim saka hannuwansa ya ɗauketa gaba ɗaya ya nufi motarsa da ita. Zaina ihu take tana dukan shi ya sauƙeta ya ƙi, har sai da ya isa bakin motar ya ajiyeta ya buɗe motar ya sakata ciki ya rufe, ya juya don ganin Musa ya iso gurin.

"Ka rabu da ita ko in ƙira maka Police." Musa yace yana zaro wayarshi.

"Ka ƙira su zo, amma ka sani kai ya kamata a kama saboda kana kula matar wani." Hashim ya ce cikin dakakkiyar muryarsa. 

Musa duk da abin da ya ji amma ya ce. "Girlfriend ba za ta taɓa zama matarka ba tawa ce ni ɗaya, ka rabu da ita ka buɗe mata ta fita."

"Baka da hankali." Hashim yace ya zagaya ya shiga motarshi ya kunna, zai bar gurin Zaina ta riƙo hannunsa da suke saman sitiyari a fusace ta ce. "Ka buɗe min na fita."

Hannunta ya cire saman sitiyari, ya cire lock din motar ya ce. "Fita to."

Hannu tasa tana ƙoƙarin buɗewa ta fita ya fizgota ya saka lock. "Ashe ba ki da hankali." Ya ce ya ja ya bar gurin da gudun da ya mugun tsorata Zaina, ganin haka shi ma Musa ya koma motarshi da sauri ya bi bayan shi.

Gudu kawai Hashim yake iya ƙarfin shi Zaina duk ta tsorata ta waro idanuwanta jikinta ya hau rawa. Cikin gari yayi ganin motar Musa yana bin shi, ya shiga ya fita har ya ɓacewa ganin shi ya canza hanyar suka kamo hanyar gida.

...

Taƙaici ne ya kama Musa ya faka motarshi a gefe ya buga sitiyarin da ƙarfi, ya jima kafin yaja motar yana yin gida.

...

Tafiya kawai Hashim yake har ya samu masu sayar da kifi, ya tsaya ya fita ya saya mata ya dawo kafin su bar gurin. Cikin unguwa suka shiga ya samu gurin da ba mutane sosai ya faka morarshi, ya ƙi kashewa balle ya cire lock ta saka ran fita.

Hannunshi ya miƙa seat ɗin baya ya ɗauko ledar da kifin yake ciki, ya buɗe ya ajiye mata a gefe, cikin tsarewa ya ce. "Oya ki ci na san ba ki ci komai ba."

"Na ƙoshi." Zaina tace tana juyar da kanta gefe. Hashim yace. "Idan har kina son haɗuwa da shi kici, ni da kai na gobe zan kai ki gurin shi."

Sai lokacin ta juya ta kalle shi, ya ɗaga mata kai, ta saka hannu za ta fara ci ya hanata ya saka nashi hannun ya ɗauki ƙarami ya kai bakinsa ya ce. "Bari inji ya nuna."

Da ido ta bi shi, ya saka a bakinshi ya tauna kafin ya ciro ya nufi bakinta da shi, ta kawar kanta gefe da sauri, ya saka ɗayan hannunshi ya juyo da fuskarta ya matse kumatunta da ya sakata buɗe baki ya tura mata bakinta ya ce. "Dalla cinye."

Dolenta ta tauna ta haɗiye, tana ɓata rai tace. "Ai wannan ƙazanta ne."

Ya harareta ya ce. "Kazanta kuma ke lokacin da kike yarinya ki ke bani abun bakinki nasha, duk abinda da nake sha haka ki ke saka hannunki a bakina ki ciro ki sha, nima kuma haka kike cire na bakinki duk yawunki ki bani nasha to me kuma ya rage."

Zaina rai ta ɓata tana turo baki ta fara ci don yunwar da take ji, idanu kawai ya zuba mata yana kallonta ko wani daƙika sonta ƙaruwa yake a cikin zuciyarshi, ta ya zai iya rayuwa babu ita, ko ya barta ta auri wani, sai dai bayan mutuwarsa da yake fatan su tafi tare.

Kaɗan taci tace ta ƙoshi, ya ɗauki exotic ya miƙa mata ta karɓa tasha ta ajiye sauran tace ta ƙoshi, ya kunna motarshi suna barin gurin.

A kofar gidan su yayi parking, tana shirin fita ya dakatar ta ya ce. "Bani wayarki."

"Na ƙi." Tace ta saka wayar cikin hijabinta ta tura rigarta. Yana kallonta yayi murmushi yace. "Kin kai inda bai dace na saka hannuna ba, da babu abin da zai hanani kwata, ko in gwada ne?" Ya ce yana matsawa kusa da ita.

A tsorace ta watsa mishi harara cikin duhun da hasken lantarki na waje ya hasko motar, wanda ya ba shi damar ganinta, ya yi murmushi yace. "Ki daina hararata da wannan idanuwanki zasu kashe ni."

Rai ta kuma haɗawa tace. "Ka buɗe min in fita."

Lock ɗin motar ya cire ta fita da sauri, ya ɗaga murya yadda za ta ji ya ce. "Sai an kawo ki gidana."

Sai lokacin abubuwan da suka wuce suka dawo mata, ta juya da sauri sai kuma ta shige cikin gida.

 Nan ta samu matan gidan cirko cirko Mama Hadizatu sai surfa ruwan bala'i take, Inna tana zaune gefe ranta ɓace duk da an nemi Zaina an rasa abun ya ɓata ranta amma zagin da Mama Hadizatu take yafi komai ɓata mata rai, tana jifan ƴarta da munanan kalamai, anya in aka yi auren za ta bar Zaina ta samu kwanciyar hankali cikin gidanta.

Mama Hadizatu da ta hango tahowar Zaina tace. "Dama na faɗa za'a cuci ɗana a ba shi ragowar wasu, in banda lalacewa daren washegarin ɗaurin aurenki ki saka kafa ki fita, wannan yarinyar sai ta jawo mana abin kunya a zuri'a."

Jinta kawai Zaina ta yi ta wuce ɗaki, don ba ta da lokacin amsa mata su, duk da dama ba amsa mata take ba idan tana yi.

Can saman gado ta hau ta duƙunƙune guri ɗaya, wasu hawaye masu zafi suna sauƙa saman fuskarta. Tana tunawa shike nan sun rabata da abin sonta, yaushe hakan zai daina faruwa cikin danginsu, auren dole, wanda an jima da daina yi, zasu kaita gidan da mahaifiyar shi ba ta sonta, basa duba da halin da za ta shiga.

Kuka taci gaba da yi, ta ciro wayarta ta ƙira Musa, wayarshi yana ta ringin bai ɗauka ba, haka tai ta yi ba'a ɗauka ƙarshe ma ya daina shiga, ta ajiye wayar ta fashe da kuka.

Haka daren ranar ta kwana hawayen idonta ya kasa daina zuba, tana gani kowa yana shirin kwanciya har dare yayi sosai kowa ya yi bacci amma ta kasa.

Sai wajajen ƙarfe uku daren ɓarawon bacci ya ɗauketa. Ba ita ta farka ba sai ƙarfe goman safe shi ma hayaniyar mutane ya tasheta, da mugun ciwon kai ta farka da ƙyar take iya buɗe idanunta.

Wanka ta fara yi ta gyara jikinta, tana shirin saka kaya Surayya ta shigo ɗakin ta sameta.

Ganin haka Surayya ta ce. "Ki saka sabi mana Zaina, ko har yanzu ba ki fauwala lamuranki ba?"

Idonta ne ya cika da hawaye ta ce. "Matar Yaya ba za ki gane ba, ina son boyfriend sosai shi ne abin sona, wai har yaushe za'a daina wannan al'adar cikin zuri'ar mu."

"Babu rana, amma idan har hakan zai iya jawo tashin hankali ga rayuwar masu zuwa Allah ya kawo sauƙin cikinta." Surayya ta ce mata don kwantar mata da hankali.

Zaina cikin kuka ta ce. "Bai kai har zuwa ga masu tasowa ba, ni kaina sun cuceni sun cuci rayuwata da wannan abin da suke yi."

Shuru Surayya ta yi don ta fara ganin gaskiyar Zaina, cikin lallashi tace. "Haka ne, yanzu ki daure ki sa shaddar nan ko don maganar mutane."

Zaina ba ta ce komai ba ta ɗauki doguwar riga na shaddar da yasha aiki ta saka, ta koma ta kwanta ta ce. "Matar Yaya in kin fita ki aiko min abinci yunwa nake ji kuma kaina ciwo yake."

To Surayya ta amsa mata da shi ta fita, ta zubo mata masa da miya da aka yi ta aika yaro ya sayo mata Panadol kafin ta koma ɗaki ta ba ta abincin.

Kwaya biyu ta ci tace ta ƙoshi, tasha ruwa da maganin da aka kawo mata ta koma ta kwanta, tuni wani bacci ya ɗauketa da ba ta san lokacin ba.

...


Ɓangaren Musa yana komawa gida ya wuce ɗakinshi ko damar amsa ƙiran da Momy take mishi bai yi ba, ya fara haɗa kayansa sai da ya deba akwati biyu da duk abinda yake buƙata kafin ya fito ya nufi kofar fita, Momy ta tare shi da sauri.

"Ina za kaje Musa?"

Sai lokacin ya dubeta yace. "Garin zan bari Momy, ba zan iya zama ko rayuwa gari ɗaya da Girlfriend tana auren wani ba, kar ki hanani Momy Please."

Momy ta ce. "Yanzu akan mace za ka bar iyayenka? Kar ka ga laifinta dole aka mata, kuma wannan shine ƙaddarar ku Allah ya yi ba zaman aure tsakanin ku, ka yi haƙuri ka zauna, idan ka gyara paper naka ni da kaina zan nema naka visa ka tafi wani ƙasar ka karo karatu. Allah yasa haka shine mafi alheri a rayuwarku."

Ire-iren kalaman da Momy ta yima Musa tana mishi nuni da ƙaddara ce daga Allah don ya kwatanta imanin su, idan har ya karɓa hannu bibbiyu Allah zai biya shi da mafificin alheri.

Nutsuwa ce ta shiga Musa kafin ya haƙura amma ƙasan ransa yasan da wuya ya so wata bayan Zaina. Kuma yana godewa Allah da ya aikota cikin rayuwar shi ta zamto silar shiriyarsa.

Masu ɗaurin aure fa?

Ko me yasa Mama Hadizatu ba ta son Zaina?