AMANA TA

Book 1 (Farko)

by @takori

FARKON LABARIN

Garin Dukku, dake cikin jihar Gombe, gari ne na Fulani masu asali da tushe, gari ne da Allah Ya yiwa albarkar kasar noma da ciyayin kiwo, Ya kuma azurta Fulanin wannan gari da shanu da tumaki masu albarka.

A wannan lokacin za ki samu saurayi dan shekaru ashirin da biyar da garken shanu buka-buka nashi na kashin kansa, sai dai a wancan lokacin babu wutar nepa babu ruwan famfo a Dukku, sai dai albarkar rijiyoyi, fadamomi da koramu da Allah Ya bamu, dasu ne muke gudanar da al’amuran rayuwarmu na yau da kullum, cikin wadatar zucci da godiyar Allah.

Ni da mahaifinki Umaru, ‘yan asalin garin Dukku ne, anyi mana aure tun ina da shekaru sha biyu.

Aure irin na iyaye da kakanni, wanda babu sanayya ko wata soyayya a cikinsa. Ban sanshi ba, bai sanni ba, sai ranar da aka kai ni.

Umaru dan sarauta ne a Dukku, mahaifinsa ke rike da sarautar San-Turakin Dukku. Fulani ne usul, wadanda suka gaji Sarautar San-Turaki tun daga kakannin-kakanninsu.

Yayin da ni na kasance diyar talakawa, mahaifinshi shi ya nemi Babana Malam Sajoh da ya ba shi ni ya aurawa dansa Umaru, saboda kaunar da yake yiwa mahaifina, da irin tarbiyyar da yayi mana.

 

Zamani ne farkon zuwan boko, lokacin da duniya ke kwance; abin nufi, laifuffuka basu yawaita ba, haka boko bai fantsama ba. Sarakunan gargajiya sune suke mulki ba Gwamnati ba.

Umaru da ‘yan tsirarun ‘yan’uwansa sune kadai suka samu damar yin ilimin boko a Dukku, yayin da Turawan wayar da kai suka kawo ziyarar wayar da kai fadar Sarkin Dukku.

Umaru shi ya fara cewa zai shiga, suka bude makarantun firamare da sakandire wadanda basu samu goyon baya sosai ba daga al’ummar garin, musamman malaman addini, sai daidaiku irin su Umaru, da suke ‘ya’yan masarauta.

                                                   

Sunana Halimatus-Sa’adiyyah, mahaifina Malam Sajoh manomi ne mai rufin asiri, domin ya fi karfin abincin da iyalinshi za su ci, da sutturar da za su daura. Mahaifiyata Innayo, (Habibah), ta rasu wurin haihuwar kanina Bello.

A lokacin ina da shekaru hudu, amma duk da karancin shekaruna ni ke kula da Bello, har zuwa lokacin da Baffanmu ya auri Inna Baddo, a lokacin ita ma mijinta ya rasu ba ta taba haihuwa ba.

Don haka ta kama mu ni da kanina Bello ta rungume tamkar ita ta haife mu. Don haka zan iya ce dake ban tashi tare da mahaifiyata ba, amma kuma ban san maraici ba.

Da zuciya daya Inna Baddo ke rike damu, har zuwa sanda mahaifina ya aurar dani ga mahaifinki.

Rana ta farko da ya shigo dakina ya fada min cewa shi fa ba sona yake yi ba, saboda ni jahila ce, yana da wadda yake so a birni mai ilimi ‘yar’uwarsa.

Don haka zai zauna dani ne kawai don ya zauna da mahaifinshi lafiya, don haka in na ga zan zauna, in zauna, in ba zan zauna ba in koma gidanmu in ce bana son auren. Amma ya ja kunne na kada in sake sunan shi ya fito a ciki.

Ban yi magana ba, har ya gama rashin arzikinshi ya tafi. Daga ranar ban kara ganin keyarshi ba, ya tattara ya koma birni, inda ya ke karatu.

Sai da aka share watanni uku rannan sai gashi. A lokacin na yi nisa da sana’ar saka da nake yi na kayan sanyin yara da huluna, don tun bayan tafiyarsa mahaifina ya bani jarin sakar ya ce in riki sana’a kada in dogara da miji ko zaman banza.

Don haka ne duk wannan dadewa da Umaru ya yi bai waiwaye ni ba, ko a jikina. Sakata da ibaduna kawai nake yi, kuma Allah ya sa min nasibi a ciki, ina samun ciniki sosai.

Don in na gama a take ake sayewa, daga baya ma har kamu ake yi cewa da na gama ana bukata.

Tunda Umaru ya dawo na aje saka gefe na shiga kula da al’amarinshi tsakanina da Allah. Kamar yadda kowacce mace ta gari ke yiwa mijinta. Amma bana burge Umaru ko kankani. Rashin arziki da rashin albarka iri-iri babu wanda ba ya yi min.

Abu kadan zan yi ya yi min gorin jahilci da kauyanci. Ke kya ce shi ba asalinshi kauyen bane. A haka Allah ya nufe ni da samun cikin ki, inada shekaru sha shidda. Na yi shiru ban fadawa kowa ba. A lokacin Baffanmu ya kai kanina Bello almajiranci hannun wani babban malami a Maiduguri.

A hanyarshi ta dawowa Allah ya saukar da ajalinsa, domin mota ce DAF ta danne karamar motar da suke ciki babu wanda ya tsira a cikinsu.

Tunda na samu wannan labari ne na fadi. Ban farfado ba sai a hannun Inna Baddo. Tana kuka ina yi kamar ranmu zai fita. Babban tashin hankalinmu bamu san inda Baffa ya kai Bello ba, ya dai ce da Inna Baddo Maiduguri zai kai shi. Maiduguri a ina? Bamu sani ba.

Bayan Inna Baddo ta gama takaba ta koma garinsu Billiri. Amma ta yi min alkawarin kawo min ziyara a duk lokac in da ta samu dama.   Wani abin haushi irin nawa ko Inna Baddo ban taba gayawa irin zaman da muke yi da Umaru ba, ba don komai ba sai don wata nasiha da Baffa ya yi min a lokacin da za a kaini gidan miji, cewa in yi hakuri, shine jigon zaman aure, domin shi hakuri baya baci, kuma shine babban jari a rayuwa.

Bayan rasuwar Baffanmu, San-Turaki (mahaifin Umaru) ya dauki dukkan kulawarshi ya dora a kaina. A lokacin ne cikin dake jikina ya fito kowa ya gani.

Mahaifiyar Umaru kullum cikin yo min dafe-dafe take. Irin wadanda masu ciki ke sha’awa. Watan Umaru biyar a birni bai zo ba, don haka har cikina ya cika watanni bakwai bai sani ba.

Da ya tashi dawowa ya dawo da kyankyasheshiyar matarshi Hafsatu. Kwanan shi uku cikin gidan bamu hadu ba, don bai neme ni ba, bai zo inda nake ba.

Na dai ga ana ta shiga da kaya daya sassan dake rufe. Iya Ramatu (mahaifiyar Umaru) ta aika na zo. Ta fara da bani hakuri da kalamai na kwantar da hankali, ta gaya min Umaru ya kara aure in yi hakuri mu zauna lafiya, suma basu san da neman auren ba sai Baffannin shi ya aikowa su je su karba mishi aure a birnin Kano.

Na ce da Iya babu komai, Allah ya bamu zaman lafiya, ya hada kan mu. Ta ce, “Amin, Allah Ya yi miki albarka Halimah”.

Bayan kwanaki bakwai da zuwan amarya Hafsatu, kamar yadda addini ya tsara, na danne zuciyata na yi wanka na yi kwalliya na nufi turakar maigida, na yi sallama na tura kofa na shiga.

Dukkansu su biyun suka zubo min ido kamar sun ga wani sabon abu, idanun Umaru kyar a kan cikina, ita ma amaryar kallo na take.

Ban yi aune ba sai saukar wasu gigitattun mari na ji a kuncina dama da hagu. Na rude na gigice na kidime, na nemi ji da ganina na wucin gadi na rasa.

Cewa yake, “Me zan gani haka? Ciki a jikinki Halimah? Uban wa ya yi miki?”

Na durkushe a nan ina dafe da kuncina ina kuka, yasa kafa ya yi fatali dani daga cikin dakinsa zuwa waje, na kifa a kan dutsen da muke rufe rijiya da shi, a take na ji wasu abubuwa sun tsinke a idanuna, suka fara zub da jini, ya yin da marata ta daure tam!

Bai ji tausayina ba balle ya ji tsoron aika-aikar da ya yi, ya tankadani waje da kafafunshi yana fadin.

“Ki tafi gidan ubanki ki nemi uban shegen cikinki, amma ba ni ba. Sau daya na taba kusantarki kuma ban zuba kwai na a jikinki ba (azlu). Muddin kika sake kika doshi iyayena sai kin yi nadamar zuwanki duniya, kuma sai na tona miki asiri. Ki san inda za ki kai shegen cikinki tun wuri, amma ba gidana ba, bana iyaye na ba.

Na sake ki.... na sake ki.... na sake ki.....!” Ya maimaita har sau uku.

 Da yake dare ne kowa yana cikin gidansa. Babban tashin hankalina bana ganin gabana bare bayana, face wani irin duhu. Ga ruwa da jini suna ta bulbula daga idona. Ga tirtsetsen ciki ga ciwon mara da ya turnike ni. A haka na ci gaba da jan-gindi na bar kofar gidan.

 

****

 

“Wane ne a nan?”

Malam Tanko makwabcinmu yake tambaya, yana haskani da cocilan dinsa.

“Subhanallahi! Halimah ce?”

Ya fada a hankali.

“Halimahh.....!”.

 

Daga wannan ban kara sanin inda kaina yake ba.

 

Sai bude ido na yi na ganni rungume a jikin Ta-Birni matar Mal. Tanko.

Fadi take, “Ta farka Malam, maza kawo ruwa!”.

Na shafa cikina na ji wayam, babu, ai sai na fashe da kuka.

Ta-Birmi ta miko min wani abu kunshe cikin tsumma yana wutsil-wutsil ta ce,

“Karbi kyautar da Allah Ya baki Halima, ‘ya mace ce, mai kama da Ubanta. Rungume ta sosai, ta ji dumin jikinki, bakwaini ce”.

Ta kwance tsumman da Mal. Tanko ya daure idanuna dasu ta ce, “Yanzu kina gani?”

Na kara rikicewa da kuka na ce, “Bana ganin komai sai inuwa”.

Malam Tanko hankali tashe ya fita ya dinga bugawa Umaru kofa kamar zai balle ta. Daka ciki Umaru ya amsa.

“Wai wane mahaukaci ne ke buga min gida da asubahin nan?”

Malam Tanko ya ce,

 “Ka bude sai ka gani”.

Jin cewa makocinshi ne ya san kwanan zancen. Ya bude kofar a fusace ya ce, “Mene ne?”

Don takaici Malam Tanko kasa magana ya yi. Baram! Umaru ya doko kofa a kan fuskarsa ya ce,

“In dai Halima ce na sake ta saki har uku, saboda ba zan karbi cikinta ba, ban san wa ya yi mata ba.

Sannan ina gargadinka kada ka sake ka doshi iyayena a kan maganarta. Idan ba haka ba wallahi-wallahi sai zaman garin nan ya gagare ka”.

Malam Tanko ya ce, “Iyayenka kamar sun ji sun gama, sai in bana numfashi. Mugu azzalumi. Ilimin Nasaran bai amfane ka da komai ba sai tabewa, insha Allahu sai wata rana ka nemi ‘yar Halima da kanka. A lokacin da nadama ba za ta yi maka amfani ba”.

Ina jin Malam Tanko yana gayawa Ta-Birni yadda su kai da Umaru. Ya kara cewa, “Jira nake gari ya dan yi haske sai mu kai wa San-Turaki jaririyar, ita kuma Halima mu kaita asibiti a duba idanunta. Har yanzu bakya ganin mu Halimah?”

Muryata ta dushe saboda kuka da bakin ciki na ce,

“Bana ganin kowa sai inuwar ku, na rokeku, ku bar min ‘yata, ku bar Umaru da halinsa, in aka rabani da ita wa nake da shi a duniya?

Tunda ya ce ba ‘yarshi ba ce, suma iyayen babu amfanin sanar dasu. Na yarda ni ‘yata ce ni kadai, kuma ina so. Na gode da taimakon ka, na gode Malam Tanko”.

Na mike rungume da jaririya, ko mayafi babu a jikina. Ta-Birni ta ce, “Me kike nufi Halima? Ina za ki je da jaririya bakwaini da danyen jego haihuwar fari? Ki yi hakuri in yi muku wanka ko na sati biyu ne, lokacin kun ji kwarin jikinku, sai mu zauna a san abin yi. Yanzu miko min ‘yar in goyata muje nan asibitin Dukku a duba idon ki”.

Ban yi mata musu ba na mika mata ‘yar, ta sa zani ta goyata. Ta janyo mayafinta jikin kyaure ta yafa, ta kama hannuna Mal. Tanko yana gaba muna binshi a baya har dakin shan magani na garin Dukku.

Ya duba idon ya wanke da magani, ya like da bandeji, ya ce bayan sati daya a cire a dawo ya kara sa maganin shi kenan zai washe.

Mal. Tanko ya biya kudi muka dawo gidansa. Ta-Birni ta tada wuta nan da nan ta gargasa ni ta yi min wankan jego da runhu, sannan ta zuba min wanda zan zauna a ciki, ta fito ta barni ta dawo kan jaririya ta yi mata wanka duk da kankantarta kuwa.

Sai dai an rasa suturar da za a sanya mata. Ta-Birni ta aika gidan ‘yarta Lami da yake goyo take ta ba da kayan ‘yarta kala biyu aka sanyawa jaririyar, aka kunshe ta cikin zani bayan ta yi mata gashin cibi.

Nan take ‘yar bakwaini ta yi barci. Ba ta ajiye ta ba, rungumeta ta yi a kirjinta har na fito ina bin bango.

Ba zan taba mancewa da Ta-Birni ba, har ranar da na daina numfashi. A take ta kama zabbinta biyu ta bararraka min farfesu.

Bayan magariba sai ga Mal. Tanko shi ma da gasasshen nama fal leda. Ta-Birni ta shirbine shi da yajin daddawa ta sa min a gaba sai da na cinye shi tas sannan ta kyale ni.

Ranar da muka yi kwana bakwai Mal. Tanko ya kama tikeken ragon sa da yake kiwatawa na babbar sallah, ya yanka da sunanki dana zabar miki, sunan mahaifiyata Habibah, nake kiranki MUHASIN. Wato (mai kyautatawa)

Haka bayin Allahn nan suka ci gaba da kula damu har tsayin sati biyu. Ido kuwa an yi jelen asibiti har an gaji ba abinda ya canza.

Don haka na rungumi kaddara ta da hannu bibbiyu, idan jarrabawa ce Allah ya bani ikon cinye ta.

Ranar litinin ita ce ranar da Malam Tanko ya yanke cewa zamu je gidan San-Turaki don ga dukkan alamu basu san komai ba, domin babu wanda ya biyo baya.

Ba yadda ban yi da shi ba a kan ya bar zancen a tsakaninmu amma ya ki amincewa. A cewarsa hakkin su ne ya sanar da su. Koda kuwa bazasu dauki wani mataki ba. Ni kuma na kudire daga wannan rana na bar garin Dukku kenan har abada!

Ba don komi ba sai don in tsira dake, domin na tabbata muddin San-Turaki da Iya Ramatu suka ji karbar ki za su yi, tunda saki uku Umaru ya yi min, babu zancen a gyara.

Burina kawai in bar garin Dukku in yi nisa da duk abin da zai raba ni dake Habiba-Muhasin. Don haka Mal. Tanko na fita Ta-Birni ta shiga wanka na lalubo ki a shimfidarki na goya ki, na yafa mayafin Ta-Birni, na dauki sandar da Mal. Tanko ya saya mini ina dogarawa da ita na lallaba na fice.

Ina zuwa zaure na ji almajiri yana bara, na yi kiran shi na tambaye shi ko ya san tasha? Ya ce, “Eh, ya sani”. Na roke shi ya taimake ni yai min jagora ya kai ni ya sanyani a motar Billiri.

Niyyata in je in nemi Inna Baddo, in gaya mata abin da ya same ni, ta taya ni jimamin rashin Baffa, ta taya ni rainon ki. Idan kika yi kwari sai in kara gaba zuwa duk inda Allah ya kai ni.

Cikin sa’a muna zuwa motar Billiri saura mutum guda. Yaron nan ya sanya ni, alhalin na san bani da ko sisi.

Sai da mota ta fara tafiya mai mota ya lura ni ban ba da kudi ba, ya ce, “Baiwar Allah ina kudinki?’

Ban san sanda kuka ya kwace min ba, na ce, “Ka barni in je Billiri a motar ka sadaka fisabilillahi. Bani da ko sisi”.

“Zancen banza kike Hajiya, kin san baki da kudi kika shigo mana mota?”

Gaba daya jama’ar motar suka maido hankalinsu kan mu. Ya soma kokarin tsai da motar yana cewa.

“Wallahi sauke ki zan yi. Ku nakasassun nan kun dauka kowa ma mai matacciyar zuciya ne irinku? To ni na abinci nake nema halalina ba masu bara nake taimako ba”.

Yana kokarin bude murfin motar. Daga can baya wani mutum da ban san ko wane ne ba ya ce.

“Haba bawan Allah, ka dubi jaririn dake bayanta, ka dubi lalurarta, zaka sauketa a wannan kungurmin dajin? Wai me yasa mutane da yawa bamu da tausayi ne?”

Ya kirgo kudi a aljihunsa ya bashi. Mai mota ya amshe ya kalmashe yana cewa.

“Yanzu na ji magana, kai da kake da tausayi baka san zafin nema bane. Sai ki yi hattara, in yau wani ya biya gobe babu mai kallon ki”.

Ya ja motar aka ci gaba da tafiya.

Na juya ina yiwa mutumin godiya, duk da ba ganinsa nake ba. Ya ce babu komai. Mutanen motar babu wanda ya sanya mana baki, har aka iso kauyen Billiri.

 

“Baiwar Allah ki fito an zo”.

Muryar wanda ya taimake ni ne. Na daddogara na fito ya kama karshen sanda ta yana cewa, “Ina kika nufa ne?”

Na ce, “Gidan su Inna Baddo”.

Ya yi dariya ya ce,

“Ai ba a sanin sunan mace, da dai kin san sunan maigidanta ko mahaifinta ko samarin gidan”.

Wata sabuwa! Na ce,

“Wallahi ban sani ba. Don Allah ka taimaka ka sama min makwanci cikin tashar nan inda ba zamu cutu ba, zuwa wayewar gari sai in shiga gari in yi ta tambaya”.

Tausayi ya kama shi, ya ce, “Kawo ‘yar kina ji tana ta kuka”.

Kememe na ki sakkota na ce,

“Nono take bida, ka samar min inda zan zauna sai in ba ta”.

A raina na ce, in baka ka yi kwallo da ita? Kamar yadda Umaru ya yi kwallo da ni, itama ta makance?

Ai babu ni babu namiji, gaba daya na hada na yi musu jimillah, basu da adalci da imani cikin zukatansu.

Ya ce, “To wuce muje in kai ki gidan Mai-gari, za su baki makwanci har zuwa lokacin da za ki ga wadda kike nema, amma bai kamata ki kwana a tasha da wannan jaririyar sabuwar haihuwa ba”.

Na yi masa godiya har da hawayena, ya kama gefen sandata yana yi min jagora har gidan Maigari.

A zaure Maigari ne tare da wasu dattijai guda biyu. Mutumin ya umarce ni da in tube takalmina mu shiga.

Sai a lokacin ne na tuna ashe kafata ko takalmi babu. Ya zube yana kwasar gaisuwa, nima na yi yadda na ji ya yi.

Sannan ya yiwa maigari bayanina yadda muka hadu daga Dukku har zuwa nan, da cewa da na yi zan kwana a tasha. Shi kuma shine ya ga dacewar ya kawo ni nan gare shi don kada na fada mugun hannu.

Maigari ya ce, ya kyauta kwarai. Sannan ya juyo gare ni.

“Jini ya taru cikin idanunki, me ya same ki? Ga idanunki a bude, amma ga dukkan alamu ba kya gani”.

Na yi shiru ban amsa ba.

“Sakko yarinyar”.

Na sauke, amma na kankame ban baiwa kowa ba, na soma kici-kicin sanya mata nono a baki, ta kama a hankali.

Suka ci gaba da tattaunawar da suke yi da jama’arsa, daga bisani ya sallame su, shima mutumin da ya kawo ni sallama ya yi mana zai tafi.

Ya ce, in an kwana biyu zai bullo ya ji ko na samu ganin Baddon. Shi kuma maigari ya ce in tashi mu shiga ciki.

 

Babban gida ne mai sassa daban-daban, wanda ke kunshe da matan aure hudu da ‘ya’yansu, jikokinsu da surukansu.

Wajen uwargida Hajiya Tafisu maigari ya kai ni, ina ji yana yi mata bayani da rokon ta taimake ni kamin a binciko wadda na zo gurin ta. Ya kuma ce dani in saki jikina in yiwa Haj. Tafisu bayani sosai, kada in ji ko dar, a kyakkyawan hannu nake, inda ba za a cutar dani ba.

Hakkinsu ne taimakon jama’a ba nice ta farko ba. Na yi musu godiya ina hawaye. Tafisu ta ce, “Bani ‘yar”. Ita da yake macece na mika mata ke.

Ta ce, “tubarkallah, Kyakkyawa da ita”. A take ta mike ta saki labulaye ta rufe kofa, ta baki ruwan dumi ta goya ki ta fita ta dafa ruwa ta yi min jagora ta dinga zabga min ganyen dalbejiya wadda suke da bishiyarta a nan cikin gidansu, amma mu can Dukku da runhu akeyi.

Sannan ta barni ta ce in yi na sabulu. Kema ta wanke ki da sabulun salo data aika jikanta ya sayo mata, ta lullube ki cikin kayan saki ta miko min ke, ta ce in ci gaba da baki nono.

Ta fita ta kawo min tuwon dare, tuwon dawa mai sulbi da miyar karkashi, ta wadata da yajin daddawa da man shanu.

Na kuwa kama ci kamar Allah ya aiko ni. Don har na manta rabona da abinci. Na ci na koshi na sha ruwa, hankalina ya dawo jikina.

Wani daddadan barci ya soma fizgata, daga ni har jaririyata, ta yi min umarnin in hau gadon bononta in kwanta ita za ta kwanta a na katakon, da yake gado biyu ne a dakin. ‘Yan jikokinta kuma ta yi musu shimfida a kasa.

Bayan mun yi sallar asubahi da duku-duku Haj. Tafisu ta sake yi min wanka, ta kara gasani ta bani kayan ‘yarta nasa.

Haka baiwar Allahn nan ta ci gaba da kula damu ba tare da ta san ko ni wace ce ba, har na fita wanka wato kwana arba’in.

A ranar ne kuma muka zauna na ba ta labarina, na kuma kwatanta mata Inna Baddo. Ta ce,

“Baddo da yawa a garin nan, ba zan iya ganewa ba.

Amma bari Dillaliya Dije ta zo, ba wanda ba ta sani a garin nan ba. Ki yi hakuri kuma ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari.

Ni na gaya miki wata rana sai Umaru ya nemi abin da kika haifa da kafafunsa da hawayensa”.

 

Muna zamanmu mai dadi a gidan Maigari kowa ya shigo gidan nan sai ya tanka ki saboda kyau da koshin lafiya.

Haj. Tafisu tana shan tambaya a kanmu, amma ta ce ni din ‘yar’uwarta ce.

Rannan muna zaune tsakar gida da yammaci, kina zaune jikin Asabe daya daga cikin yaran gidan, aka yi sallama ana cewa, “Gafaranku dai masu gida, ga ‘yan kunnaye da awarwaro ko da mai saya?”

Na yi saurin dagowa na dubi sashen da maganar ta fito, ko mutuwa na yi na dawo ba zan mance muryar Innata Baddo ba.

Baddo na Baddon Bello, mai son mu mai kaunar mu. Ban san sanda kuka ya kece min ba. Na ce,

“Inna Baddo!!!”

Ta yi hanzarin dubana da mamaki da tsoro, ta ce, “Halimahhh?”

Na ce, “Na’am Inna”.

Ta sauke kayan dake kanta ta iso ta rungumeni ta ce, “Ke da wa kika zo?”

Sam-sam Inna Baddo ba ta lura bana gani ba, saboda idanuna a bude suke tas. Jinin da ya kwanta cikin su har ya washe. Ina kuka sosai nake gaya mata “yau watannina uku a Billiri ina bulayin neman ki Innata”.

Na juya ga Haj. Tafisu na ce,

“Hajiya Alhamdulillahi, yau Allah ya takaita mana wahala, ga Inna Baddo da na zo wurinta”.

Ta ce, “To, Alhamdulillahi, bari in je in fadawa Maigari”.

Tare suka dawo da shi, Inna Baddo ta gaishe shi cike da girmamawa, ta yi ta zuba mishi godiya shi da mai dakinshi.

Ya ce, “babu komai”.

 

Sai kuma kewa ta kama mu ni da Haj. Tafisu, ta ce, “To yanzu Halima in kin tafi sai yaushe?”

Inna Baddo ta ce, “Kada ki damu Hajiya, Halima bazata bar garin nan ba ta yi miki sallama ba”.

Suka hada min sha tara ta arziki, muka fito muna hawaye Haj. Tafisu ta kasa rabuwa da ke da kyar ta yadda ta baiwa Baddo ke ta goya ki.

Ta ce da Inna Baddo, “Ki kama ta ki yi mata jagora, ba ta gani”.

Inna Baddo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta kamo ni ta rike ta soma kuka. Nima sai ta karya min zuciya muka yi ta yi.

Ban taba jin tashin hankalin da ya same ni a kan idanuna ba sai yau. Hannuna ta ja muka tafi, muna yiwa jama’ar gidan bankwana.

Tun bayan rasuwar Baffanmu Inna Baddo ba ta kara aure ba, tana tare da gyatumar ta Inna Larai a gidansu na gado, don uban ya dade da rasuwa, tana saide-saiden ta don samun na abinci.

Ta yiwa Larai bayanina, sannan ta nemi labarin abin da ya rabo ni da gida. Na kwashe kaf na gaya mata ban rage komai ba.

Ta ce, “Bai cuce ki ba Halima, Umaru kansa ya cuta. Da sannu za ki ga sakayyar da Allah zai miki, insha Allahu tun daga nan gidan duniya.

Gara da kika taho, dan nima ban laminci a rabaki da ‘yarki ba sanyin idaniyarki, da kika ci wahalarta ke kadai ko sannu baki samu ba. Nima ba wata wadata ke gare ni ba, amma ba zan gaza komai a rikon ki ba.

Allah Ya iya mana, bani ita nan in soma gwada mata nonon Akuya, yana sa yara saurin wayo da saurin girma, musamman in kin hada shi da waken suya”.

Nan ta shiga hidima da mu da iyakar iyawarta.

 

Zamanmu a Billiri tare da Inna Baddo, zama ne mai dadi da fahimtar juna da taimakekeniya.

Domin dai duk da na rasa idanuna, ban kwanta a daki na ce sai Inna Baddo ta min komai ba. Da safe tana sai da waina da taushe, ni nake taya ta ayyukan, gashi tana samun ciniki sosai. In yamma ta yi kuma ta tafi tallan kayan koli da ‘yan kunnaye gida-gida haka take bi.

Yayin da za ta goya ki ta tafi dake. Tsakanina da ke sai shan nono. Inna Baddo ta dauke min komai na rainon ki.......”

Ta tsaya tana share hawayen da suka tsatstsafo mata da gefen mayafinta. Muhasin ta kasa shiru ta ce.

“To yanzu ina Baddo ne muke kwana a karkashin gada?”

Ta yi wata ajiyar zuciya mai karfi ta ce, “Kin fiya ci da zuci Muhasin, a sannu ai zan gaya miki”.

Ta ci gaba da cewa.

“Shekararki takwas da haihuwa Allah ya yiwa Baddo rasuwa, ta dawo daga cin kasuwar Ladin Makoli, wata motar shanu ta bige ta a wajen ta rasu.

Mu dai muna zaune tare da Larai aka dinga sallama, aka shigo da gawarta. Jina na yi kawai ana zuba min ruwa saboda sumewa na yi. A lokacin har an hadata an kaita gidanta na gaskiya.

Tun daga wannan lokacin abubuwa suka tsaya. Na yi burin a ce da idanuna in ci gaba da sana’ar Baddo ta sai da waina, (masa) haka Allah yake ikonsa.

Ga jinyar Larai da ta hau kaina, don ita ma tun daga lokacin ba ta kara lafiya ba. Yau ciwon kafa gobe hawan jini, har ya zamanto Inna Larai sai dai a kwantar a tayar, tunda babu kudin zuwa asibiti.

Dan jarin da Baddo ta mutu ta bari aka tattara aka bawa Larai, dasu muke samu mu ci abinci.

Kan ka ce meye wannan babu ya kare, aka koma cin gayan tuwo. Wata ran ko gayan ba za a samu ba sai a sha ruwa ayi hakuri.

Gashi ke baki san babu ba, kin saba ki ci waina da taushe da koko kullum ta Allah, haka za ki sani a gaba ki yi ta ihun ba za ki ci gayan tuwo ba.

Daga karshe ma shi kansa gayan tuwon gagara ya yi. Wata ranar litinin na tatso nonon akuya wanda ya zama abincinmu, na tada Larai zaune ina ba ta.

Sai na ji ta yi nauyi a hannuna, sannan madarar tana dawowa ta hancinta. Na kura mata ido duk da ba ganinta nake ba, na dora hannu na a kirjinta, na tabbatar ba ta numfashi.

Na kwantar da ita na rufe mata idanunta, na yi lullubi na tafi gidan maigarin Billiri na sanar da shi rasuwar Larai.

Haj. Tafisu ce ta wanke ta, maigari ya sallace ta aka yi jana’izarta.

Bayan rasuwar Larai da kwana uku Haj. Tafisu ta zo gidan ta samu a gaba ta ce mu koma wajen ta, ko mu yi mata bayanin inda dangina suke ta kai ni.

Nan kuka ya dawo sabo. Na ce da ita bani da kowa, sai kanina Bello da aka kai karatun almajiranci Maiduguri.

Daga ita har maigidanta suka ce, to mu zauna tare dasu. Na ce, “A’a, tafiya zamu yi”. Suka kada suka raya amma na ki. Don na san rikon mutumin da ba naka ba a wannan zamanin ba karamin abu bane. Gara in nemi na kaina in dogara ga Allah in tafi duk inda Allah Ya kai ni.

Haj. Tafisu tana kuka ina yi muka rabu. Ta ce, “To yanzu Halima ina za ku je? Yadda duniyar nan ta lalace, satar dan mutum ta zamo kamar satar kaza, ke ba ido ba, ke ba dangi ba”.

Na yi murmushi na ce da ita,

“Kada ki damu Hajiya, duk inda na fada ba zan manta daku da alkhairin ku gare ni ba.

Wata rana insha Allahu zan zo mu gana muddin ina raye”.

Ta tattara mana ‘yan tsummokaranmu cikin Ghana Must Go, ta kawo naira dubu uku ta bani ta ce in yi kudin mota, Allah ya hada fuskokinmu da alheri.

Kika kama sandata kina yi min jagora, da yake tuni ke kike min jagora zuwa duk inda zamu. Yara sa’o’inki a Billiri kin sha kuka a kan su, kan kiranki da suke yi ‘yar makauniya, don ke kam baki yarda a kirani da wannan sunan ba, dalili kenan da kullum kike cikin hawaye a yawancin lokuta.

Da muka zo tasha muryar ‘yan kamasho na ji suna fadin, “Ina za ku je? Gombe, Kano, Katsina ko Bauchi?”

Ban san sanda bakina ya furta Gombe ba. Don na sha jin labarin karamcin mutanen garin wajen girmama bako. Na biya su kudin su na karbi canji muka fada motar Gombe. Aka sauke mu a nan tashar Dukku muka fara bara.

Ke kika sama mana wannan karkashin gadar muke kwana. Ganin muna samun na abinci bamu taba wuni bamu samu abin da za mu ci ba, da abin da zamu batar ba, na yanke shawarar mu yi zaman mu a nan.

Ga kuma bayan gida (toilet) da masallaci a nan din na matafiya, ke kike min jagora ki shigar dani bayan gida ki sama min ruwa, mu yi lalura mu yi alwala mu je masallacin mata mu yi sallah. Zancen wanka dama babu shi, mun ma manta yadda ake yin sa.

Ba tsana ba tsangwama, don duk wanda ke cikin tashar nan ya sanmu, yau shekaru biyu kenan. Haka duk sanyi duk ruwan saman da ke zuba, bamu fasa kwana karkashin gadar nan ba. To kin ji wannan shine tarihinmu”.

 

Muhasin da ta yi shiru tana sauraron mahaifiyarta, ta ce,

“Insha Allahu Umma sai nima na yi karatun boko na zama soja, nasa an kama Baba Umaru. Sai na zama likita, na baki maganin ciwon ido. Sai na zama Alkali, na hukunta Baba Umaru wata rana.....”

Umma Halimah, ta yi murmushi ta ce, “A’a, Muhasin, ni tuni na yafewa Baba Umaru. Ina rokon Allah nima Ya yafe mani, ko ba komai ya zamo silar da na same ki.

Don haka bana bakin cikin komai a rayuwa, tunda ina da ke. Ki yi hakuri ki yafe masa Allah yana son bayinsa masu afuwa”.

Muhasin ta yi shiru, ba ta ce da Umman komai ba, wanda ke nufin, ba ta dauki nasihar ba.

Tayi suntum cikin fushi, zafin rai da kunar zuci, jikinta har rawa yake, idanunta sun kada sun yi jawur. Ta cokano baki, tayi kankan da ido, kamar Baba Umarun na gaban ta.

****

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Y

a kai gwauro ya kai mari a tsakiyar kayataccen falon sa, yana rike da waya yana ta faman kira amma ya ki shiga, shegiyar matar nan mai sanyin murya ke ta gaya masa (is switch off). Kamar ya yi kuka a lokacin da Haj. Maimuna uwargidansa ta shigo tana rike da tata wayar tana turo ‘troller’ din kayan abinci.

Ta isa ga ‘dining’ wanda aka yiwa mazauni a gefe guda na falon ta soma jera ‘warmers’ da farantai da cokulla, da sauran kayan da ke cikin ‘troller’ din a kan ‘dining’ din.

Ta juya ga maigidanta a hankali ta ce, “Har yanzu bai bude wayar ba?”

Ya ce, “Kyale ni da ja’iri, yana sane ai ya kashe wayar saboda kar in neme shi. Karo na uku kenan suna kama min kaya suna jawo min asara, sannan gashi duk ya hana kananan ma’aikatan karbar cin hancin da nake aika musu, na kuma gargade shi da ya fita harkar kayana in har ya na so in shirya da shi, amma kin gani.

Yanzu Inspector Nura yake cewa sun kara kama min kaya a Lagos. To wallahi wannan karon ba zan dauki asara ba, ke da danki za ku biyani naira na gugar naira har naira miliyan goma.

Tunda ai ke kika daure masa gindi ya tafi (Custom) din, maimakon (Air Force ) da na ce ya je. A kaina aka soma shigo da Tobbacco Nigeria?

 Ko su mutanen da suke shanta, basu san illarta ba suke sha?

Da sana’ata ya tashi ya ganni, ban ga dan abu kazan da ya isa ya hanani ba…..(ya lailayo ashar ya kunduma)”.

Ita dai Haj. Maimuna sum-sum ta lallaba ta fice, domin idan Alhaji Suraj ya soma irin wannan bala’in nasa, ba ta tanka masa, don sai ya huce a kanta ko ya ce tasa danta a gaba su bar masa gida, tunda dan ya nuna aikinsa ya fishi muhimmanci a gare shi, bayan da kwabon Tobbaccon aka yi karatun da ake tinkaho dashi, amma ake kuma son a kawo masa rainin wayo.

Yana jira ya ga uban dan da zai iya hana shi shigo da Tobbacco Nigeria. Balle dan sa na cikinsa.

Ko kallon inda abincin da ta jera masa yake bai yi ba, ya suri hularshi ya fita. Direbansa Danlami ya taho da gudu ya zube a gabansa yana fadin.

“Ranka ya dade fita zamu yi ne?”

Ya ce a fusace, “In ba fitar zan yi ba me zai fito dani a daren nan?”

Ya mike a sukwane ya jawo mota gabansa, da alama yau Oga na cikin bala’in nasa da kowa ke gudu a cikinsu.  Ya fito ya bude masa. Bai tsaya tambayar sa inda za su je ba don ya san hali, ya sukwani motar aguje. Buzu maigadi ya wangale musu girgijejiyar get din suka fita.

Sai da suka hau titi sosai sannan ya ce da Danlami, “Dau hanyar damanka, Airport zamu, Lagos zan wuce”.

 

****

Y

ana zaune a kayataccen ofishinsa, sanye cikin ‘uniform’ dinsa na ma’aikatan Custom din Najeriya. Da farin gilashin PRADA a idanunsa. Zarkadeden saurayi Bafulatanin Kumo, ta jihar Gombe.

Bai yiwuwa ka kintata shekarunsa a lokaci daya, saboda ya yi kuruciya ainun da matsayin Controller na Custom din Nigeria gaba daya.

A jikin aljihun gaban ‘uniform’ din sa, cikakken sunan sa ne wato ALIYU SURAJ KUMO.  A kan kafadarshi ta dama ‘rank’ din sa ne na (controller). Fari sol, ma’abocin gargasa ta gashi a ido, sumar kai da gefen fuskarsa. Haka kuma suka bi duk wata gaba suka kwanta linkif a fatar jikinsa.

Yana da wasu irin idanuwa tamkar an diga musu silber. Dan shekaru talatin da daya, wanda ya dama ya kutsa cikin ilimummukan zamani daban-daban.

Da farko dai ‘Engineer’ ne, wanda ya karanci (Electrical Engineering). Tun daga Digiri har Masta, daga nan ne ya yo ‘course’ din aikin yaki da fasa kwauri a Jami’ar ‘Lancaster’ da taimakon mahaifin shi Alhaji Surajo, kuma yana dawowa ya soma aiki da hukumar Custom ta kasa baki daya.

Yau shekara guda kenan da ya hau kujerar (Controller), ba don shekarun shi sun kai ba, sai don kwarewa, rashin wasa, jajircewa da sadaukar da kai ga aikinsa wanda (Controller) na baya Alh. Tajuddeen Olayemi ya fuskanta. A shekarar da ya yi ritaya ya dora shi a kan kujerarsa, ya kuma ci gaba da koyar da shi dabarun sanin makamar aiki, kuma dama shine ubangidansa a Custom.

 

Matsala ta farko da Controller Aliyu Suraj ya fara cin karo da ita da hawa kujerarsa shine; bribery and corruption, (matsalar karbar cin hanci da rashawa), daga kananan ma’aikata har manyan su.

Wannan ce matsalar da ya fara kokawa da ita daga hawa kujerarsa. Ya tsaya tsayin daka kan aiki da gaskiya da amana, babu sani babu sabo babu sanayya. Ya kau da cin hanci da rashawa, yana aikinshi da zuciya daya babu sani babu sabo. Ciki kuwa har da kalubalantar mahaifinsa a kan sana’arsa ta shigo da Tobbacco, wanda hatsari ne ga lafiyar al’umma.

Yana so Daddy ya fahimce shi ya sauya sana’a, amma Daddyn ya ki tsayawa ya fahimci abin da Aliyun ke son fahimtar da shi, a ganinsa kawai Aliyu ya raina shi ne saboda ya yi ilimin zamani mai zurfi.

In ban da haka ba da kudin Tobbacon aka yi dawainiyar karatun nashi ba? A ganin Daddyn, babu wanda ya isa ya sa shi sauya sana’ar da ya riga ya saba da ita, har ta zamo hanyar cin abincinsa.

Taba ba giya ba ce, ba ‘cocaine’ ba, ba kayan maye ba, ba sholisho ba. Sai dai abu ce wadda ke da hatsari ga lafiyar al’umma. Duk da dai hukuma ba ta hana shigo da Tobbacon.

Aliyu, a nashi tsarin, ya hana. Don abu ce da ke wanzar da cututtukan huhu, take kuma kashe matasa da kuruciyar su.

A jikinta baro-baro ma’aikatar lafiya ta kasa (Federal Ministry of Health) ta rubuta cewa; ‘smokers are liable to die young…..’  Amma ya rasa me al’umma ke ji a cikinta, suna wasa da rayuwarsu suna sane? Da gangan? Shin menene a cikin Taba ne da ya wuce hayaki da daci?

 

Ya maida kai ga tarin ayyuka cikin ‘file-file’ din dake gabansa. Aka bankado kofar ofishin aka shigo babu ko sallama.

Ya cira kai a hankali ya dubi mai shigowa, Daddy ne.

Ya nuna shi da dan alinsa ya ce,

“Wallahi-wallahi Aliyu ka fita daga idona, ka sakar min kaya, ni sa’anka ne ko abokin wasanka?”

Ya mike yana cewa,

“To Daddy yi hakuri ka zauna tukunna”.

Ya jawo masa kujerar da ke fuskantarsa ya ce,

“Zauna Daddy”.

“Ba zan zauna ba”.

Ya yi murmushi ya nufi dan karamin firjin da ke gefe ya dauko gongonin Coca-Cola, ya dauko kofin gilashi garai-garai da shi ya bincire hancin, ya juye lemon ciki.

 Ya isa ga Daddy ya durkusa a kan gwiwoyinsa, ya mika mishi yana kallon shi yana murmushi.

“Amshi Daddy!”. Ya fada, cikin sautinsa mai sanyi.

Sai da ya yi kwafa sannan ya amsa, ya zauna ya ce,

 “Lumbu-lumbu wutar kaikayi, ai ka iya munafuncin da dole mutum ya karbi lallashinka”.

Ya sha lemon, Aliyu yana durkushe gabanshi, ya kwantar da kai a cinyoyin Daddyn ya ce.

“Ka yi hakuri Daddy, zan biyaka kudin kayanka, amma ba zan bada kayan ba!”.

Alhaji Suraj, ya aje kofin bisa tebur ya dube shi sosai ya ce.

“Wai meye illa a sana’ar Tobbacco ne da ka bi ka sawa kahon zuka?”.

A raunane ya ce,

“Daddy it is harmful ga lafiyar matasan mu. Wadanda sune iyayen gobe, kuma shuwagabannin gobe. Kai kanka in ka yi tunani ai ba sha kake ba, sabida ka san tana cutarwa, amma kana sayarwa.

 Abinda kasan bazaka ci ba, ai bai kamata ka bari wani yaci ta hanyarka ba. Bayan kana sane da cewa illa ce ga lafiyar al’umma”.

Ya yi shiru, yana kallon dan nasa. Wai ka haifi da a cikin ka ya fika hankali. Ya gaza cewa komi, sabida yadda Aliyu ke magana cikin sanyi da girmamawa, tare da lallashi mai sanyawa dole ka yarda da shi.

Ya mike, Aliyu ma ya mike, ya kama hannun Daddyn har gaban motarsa kirar ‘Opel-Astra’ baka wuluk, sai sheki take, ya bude mishi ya shiga shima ya zaga ya shiga mazaunin direba, ya ja motar suka fita daga harabar ma’aikatar suka harba kan titi.

 

Gidanshi dake Bictoria Island ya nufa kai tsaye, suna tafe yana jan Daddyn da hira mai ban dariya, tun yana kumbure-kumburen, har ya ware suka rika hira da dariya.

Suna isa ya tarar kukunsa Jim ya kammala hada abinci bisa ‘dining’. Sai da suka fara yin sallah tukunna suka ci abincin, Daddy ya huta.

Aliyu bai gushe ba yana lallashin Daddyn a kan ya canza sana’a, shi kuma ya kafe kan cewa sana’ar da ta amshe shi kenan, kowa yana da hanyar abincinsa, to shi tasa kenan.

In kuma shi din yana da wata sana’ar da yake ganin za ta karbe shi to ya samo. A take Aliyu ya ce.

“Daddy mu gwada sana’ar fata man da kasar Italy? Ana samu sosai”.

Ya ce, “To zai yi tunani”.

A haka suka rabu ya kai Daddy Airport din Murtala Mohammed ya bi jirgi ya koma gida.

Aliyu ya girgiza kai yana murmushi, ya koma office yana mai godiya ga Allah da Ya daura shi yau a kan mahaifinsa Alhaji Surajo Tobbaco.

Ya dade yana kyamar sana’ar Daddyn, sai yau Allah Ya sa ya samu kan birkitaccen Daddyn nasa.

Ya soma addu’a cikin zuciyarshi kan Allah Ya sa sana’ar da Daddyn zai canza ta zamo mafi alkhairi a gare shi, kuma mai albarka.     

****

S

aukar Aliyu kenan daga Lagos ranar Juma’a da yamma, ya bude waya yana kiran Mamanshi ya ce,

“Ina Airport Mama a turo Danlami ya zo

filin jirgi ya dauke ni”.

Mama ta ce, “Ya tafi Kumo dauko Gwaggon Kumo ba ta jin dadi, gani nan da kaina ka jira ni”.

Ya ce, “A’ah Mama ki zauna kawai zan yo shatar tadi, bana so kina ‘dribing’ dinnan, ina Hanifah?”

Ta ce, “Hanifah ma ta je bikin kawarta a Mubi, ni kadai ce a gidan”.

“To yi zaman ki Mamana, ba zan iya jira ba gani nan”.

Ya rufe wayar ya sanya a aljihun coat dinshi, yana rataye da karamar bakar jaka mai dauke da ‘Ipod’ da sauran muhimman abebaden shi.

Ya fito daga filin jirgin ya tadda tadi-tadi masu jiran mai daukan su shata, ya samu daya ya hawo ya ce “Shango Estate”.

Sanda suka iso, Mama na harabar gidan, kamar ta rungume dan tilon dan da Allah Ya bata. To saidai fillancin, ya hana.

Hannun su cikin na juna suka isa cikin gidan, fuskar Hajiya Maimuna fal far’a kamar wanda ya shekara bai zo ba.

Rabon su da juna yau watanni uku kenan, shima ya yi kewar Mamansa. Yadda ba’a zato. Abinci kala-kala Maman ta shirya mishi har kala biyar, duka babu wanda ba fabourite dinshi ba;

Ga dai Sinasir da miyar ganye, ga Kisra da miyar bindin saniya, ga beef sausage, da stuffed atomy. Duka babu wanda ba zabinsa ba, ya fita masallacin dake makale da gidan ya yi sallah, can suka hade da Daddy suka taho gida tare.

Mama ta yi serbing dan lelenta tana ta zuba mishi hira, sannan ta yi serbing Daddy. Shi dai yana kallon ta yana dariya a cikinsa, kaunar Hajiya Maimuna da danta Aliyu Haydar sai Allah, sam ta manta da Daddy balle ita kanta. Sai shi Daddy ne ya cika filet ya tura mata, ya ce,

“To kowa ya kula da nashi”. Aka sa dariya gabadaya.

Bayan sun kammala Asabe mai aikin Maman ta fidda komai ta gyara ‘dining’. Daddy da Aliyu na bisa ‘cushion’ suna tattauna lamarin da ya shafe su.

Daddy ya ce,

“Har gobe ina alfahari da haihuwar ka Haydar, kai din nan kwaya daya ka fi min gayyar ‘ya’ya goma. Shi yasa aka ce da daya kwakkwara, ya fi taron dubu yuyuyu.

Duk shawarar da ka bani in nabi ina ganin fa’idarta. Yaro da tunanin manya.....ina alfahari da kai da haihuwarka ALIYU-HAYDAR. Allah ya yi maka albarka.

Sai dai kuma alfaharin nawa ba zai cika ba, sai na ganka da iyalinka, kamar kowanne managarcin mutum, kullum addu’ata kenan Aliyu-Haydar, Allah Ya nuna min’ya’yanka kamin ya dauki raina”.

Aliyu wanda kansa ke sunkuye bai dago ba, sai dai kuma da zai dago din, da Daddyn ya ga yadda fuskarshi ta sauya zuwa wani kwantaccen bacin rai.

Shi fa sam, babu aure cikin lissafinsa, domin a ganinsa duk ‘yammatan zamani halinsu daya (yaudara, kwadayi da rashin sanin darajar da Allah ya yi musu ta ‘ya’ya mata uwayen al’ummah, tareda rashin ganin darajar soyayyah ta hakika) irin tsohuwar masoyiyar shi (Shareekah).

Don haka har Daddy ya gama maganganun shi bai ce komi ba. An sosa wa Mama inda ke mata kaikayi.

Ta muskuta ta ce,

 “Ga ‘yar’uwarshi ma Hanifah ta ki kowa sai shi, ta dauki soyayyar duniya ta dora a kansa. Amma ya yi shakulatin bangaro da ita.

Meye laifin Hanifah saboda Allah Daddy? Yarinya mai kyau, ilimi da asali. Sannan gata ‘yar’uwarshi wadda ta san ciwon sa.

Ni kam in har kana son albarkata da farin cikina to ka aje waccen kabilar daga ranka ka auri ‘yar’uwarka mai so da kaunar ka saboda Allah”.

Kanshi dai na kasa bai dago ba, sannan bai ce komi ba har suka yi shiru. Ya mike yana cewa,

“Zan je in huta Mama, ruwa zan watsa in kwanta zuwa maghriba. Amma idan har Gwaggo ta iso, to a taso ni”. Ya sa kai ya fita.

Uwar da Uban suka bishi da kallo. Kafin da su saki ajiyar zuciya a tare. Sun rasa mece ce matsalar dan nasu ta kin aure.

Mama ta kasa shiru ta ce, “Nifa ina tsoron anya haka Bayerabiyar nan ta barshi? Tunda suka rabu ya daina zancen aure, ya kuma tsani ayi masa.

Gashi ni Allah bai bani yawan ‘ya’ya ba, burina kadai in ga ‘ya’yanshi na yawo cikin gidan nan”.

Daddy ya yi murmushi ya ce,

“Ki bishi a hankali, komai lokaci ne. Idan lokacin aurensa ya yi ko yana so ko ba ya so dole zai yi. Ki daina turasasa shi a kan zancen Hanifah, ko don ki saya mata mutunci a idanunsa.

Gobe in Allah Ya kaimu zan ga liman Halilu a fara yi mishi addu’a. Insha Allahu kwanan nan Aliyu zai yi aure, ina ji a jikina”.

Mama ta ce, “Toh, Allah Ya yarda”.

Suna haka suka jiyo tsayuwar mota, Danlami da Gwaggo sun iso kenan. Daddy ya mike ya fita ya shigo da mahaifiyarsa, Mama kuma ta nufi dakin da take sauka ta duba an gyare ko’ina.

Ga katifar gado an sauke mata ita kasa. Kasancewar bata yarda ta hau gado. Anyi shimfida ta alfarma. Dan firjin dake gefe cike yake da ruwan FARO da fresh milk din Oldenburger, da madarar Hollandia, an saki labulen, an kashe fanka da A.C,  duk don Gwaggo ba ta son ko daya daga cikin su.

Ta kunna ‘burner’ ta zuba turaren wutar bakhour, ta jawo kofar ta fito tana lale da Gwaggo.

Gwaggo Hassana ta zauna cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon suka gaisa, gaisuwa ta mutuntawa da ganin girman juna da sirakuta. Sannan suka shiga labarin ‘yan’uwa da abokan arziki dake Kumo. Sannan ta tambayi Maman Hanifah Innani, da dan lelen ta, jika kwaya daya ya tsoka daya a miya, Aliyu-Haydar.

Nan Mama take gaya mata yadda su kai da shi yanzun nan, kan cewa zai je ya kwanta ya huta, idan ta iso a taso shi.

Gwaggo ta yi dariya ta ce, “Haydara Zakin Manzo kenan. Kyale shi dai ya yi barcin shi ai ina cikin gidan duk sanda ya tashi ya ganni”.

Mama ta ce, “Gwaggo hawan jinin ne dai har yanzu?”

Ta ce, “Uhm! Bari ke dai Maimuna, jikin girma sai a hankali. Ga hawan jini, ga ciwon kafa da baya, sannan ga tarin fika, duk ni kadai”.

Ta yi tarin kuful-kuful, ta ci gaba da cewa, “To ya za a yi? Girman kenan!”.

Mama ta ce, “Allah Ya kara sauki Gwaggo, bari ya fito sai ku tafi asibitin”.

Ta ce, “Ni kam ba inda zan iya zuwa a yau dai, sai ko gobe in Allah Ya kaimu, kafin nan na huta daga jijjigar motar nan da ta kara min ciwon jiki”.

Cike da tausayawa Hajiya Maimuna ta ce, “To Allah ya kaimu goben. Da yau da goben duk daya ne. Ta so muje ki kintsa, ki sha ‘panadol’, zaki ji saukin ciwon jikin”.

Ta kama hannunta ta mike suka nufi dakin saukar tata. Mama ta koma ta kawo mata abinci, ta fiddo ruwa da madara. Ta zauna tana zuba mata abincin suna hira.

Da ta kammala ta sha ruwa da madarar, ta kishingida ta ciro goro cikin ledar kayanta tana ci.

Mama ta hada kayan ta fita dasu da kanta ta kuma fara aikin tuwon acca miyar kubewa danya, wanda Gwaggon ta ce shi take so ta ci da dare.

Karfe biyar dai-dai Aliyu ya tashi daga daddadan barcin da ya sure shi. Ya kai idon shi ga agogon bango, da sauri ya tashi yana “Subhanallah! Lokacin maghriba, ya fita, ban yi sallah ba”.

Ya fada ‘toilet’ ya sakarwa kanshi ‘shower’. Daman kuma Aliyun ba daga nan ba. Dan gaye ne danye sharaf (fresh) na karshe, wanda ya san sirrin kula da jiki da daukan diresin. Ma’abocin parmanent (tabbataccen) kamshin turaren American-Crew. 

Ya zuba wata sassalkar shadda ‘filted’ fara tas mai santsi kamar boyel, ya taje kwantaccen gashin kansa. Bayan ya yi sallah ya sunkuya yana daura bakin sandal a kafarsa na fatar damisa.

Wayar shi na ta ruri amma bai kula ba, sai da ya gama abinda yake. Ya dauki wayar ya duba ya ga missed call din na Hanifah ne, ya yi tsaki ya jefa wayar aljihu yana kunkuni......

“Yarinyar nan na nema ta uzzura min don ta ga Mama na bayanta. To ana so dole ne?” Ya ja wani matsiyacin tsaki, ya fito ya nufi cikin gida.

Ba kowa a falon, Mama na kicin, sai mai aikinta tana goge ‘tiles’ din falo. Ya wuce dakin Mama ba ta nan, don haka ya bi ta kicin.

Ya tadda tana tukin tuwo, kamshin turarensa ne ya sanya ta juyo ta dube shi. Ita kanta Aliyu yana mata matukar kwarjini a lokutta da dama, har ta dinga tambayar kanta anya! Ita ta haifi wannan sardidin Balaraben?

 

Kyakkyawa ne na karshe, ma’abocin ado; dana ce ado a nan, ina nufin; na suttura da na zuciya. Babu komi cikin zuciyarshi sai alheri ga kowa. Wato dai; Babu kyashi, babu hassada. Ba shi da abokin fada, ba a taba kawo mata karar shi ba tun yana yaro.

Yana jin kanta, kamar diya mace ke gare ta. Shi din nan har girki yake taya ta, da sauran ayyukan cikin gida, tun yana karami har girman sa.

A wannan zamanin samun da mai halayyar Aliyu-Haydar da wuya. Bai dauki rayuwa da zafi ba, yana bin komi a hankali. Duk da cewa ya tashi cikin gata, amma bai taba daukar gatan nasa a matsayin tabbataccen abu ba.

Ta juyo ta dube shi idanunta cike da kauna irin ta Uwa ga dan ta. Ya amshi muciyar zai tuka mata tuwon, ta yi dariya ta hana shi.

Ta ce, “Goggo ta iso”.

Ya ce, “Kai Mama shine baki taso ni ba, gashi har na makara sallah”.

Mama ta ce, “Ita ta ce in kyale ka, ba ta yarda a katse maka hutu ba, don ta san in ka tafi kai da hutun kun yi hannun riga kenan”.

Ya yi dan murmushi ya juya ya fita ya nufi dakin saukar Goggon.

Ya yi sallama Gwaggo ta amsa tana daga kishingide a gefen katifarta, ya idasa shigowa dakin ya zauna kusa da ita.

Ta ce, “Sai da ta taso ka ko?”

Ya ce, “A’a, ba ruwan Mama ni na tashi da kaina. Kun iso lafiya?”

Ta ce, “Alhamdulillahi, ya ya aikin?”

Ya ce, “Komi lafiya, ya ya wajen su Malam Sani (Kaninta)?”

Ta ce, “Kowa lafiya”.

Ya ce, “Daddy ya ce baki da lafiya, gashi kuma na ganki ragas, kin dai ki mutuwa mu ci gumba”.

Ta yi dariya ta ce, “Dan nema, dani da kai wa ya san gawar fari? Ka ganni nan daram, sai na goya ‘ya’yanka insha Allahu”.

Ya basar ya ce, “Me ke damun ki ne Gwaggo? Ki yi briefing dina (takaita min) abin da ke damun ki don in san me zan gayawa likita in mun je”.

Gwaggo ta ce, “Meye wani birifil? In za ka yi min Hausa ka yi min, in ba za ka yi min ba to ka yi min yarena (Fulfulde)”.

Ya dara sosai ya ce,

“Ina nufin ki takaita min abin da ke miki ciwo, ni ban iya wani Fulfulde ba”.

Ta ce, “Kowa ya bar gida Aliyu.....’

Ya ce, “In gidan zai yi adalci, to kada ya barshi…..”.

Ta soma gaya mishi nan na ciwo, can na ciwo. Ya ce,

“Dakata-dakata, ai cewa nai ki takaita”.

Suna haka Daddy ya yi sallama a kofa. Gwaggo ta yi mishi izinin shigowa. Ya shigo yana cewa, “Ke da maigidan naki ne?”

Ta ce, “Sam, ai ni tuni na guntule auren tunda ya ki ya yi min kishiya”.

Nan da nan ya sauya fuska. Daddy ya gyara zama ya ce,

“Ban da abun ki Gwaggo, wacce mace ce take son kishiya? Gara da Allah Ya kawo ki, ki tambaye shi dalilin sa na kin aure, don mu har yau mun kasa gane kansa”.

Nan da nan ya mike yana cewa,

“Daddy zan leka wajen Al-Ameen ya min (tedt) cewa ya iso kasar yau, mun jima bamu hadu ba”.

Ya ce, “Za ka gudu dai, saboda kada ayi maka zancen aure, Allah Ya shirya. Manzo (S.A.W) dai ya ce, “Aure sunnata ne, wanda ya ki sunnata baya tare dani”.

Kamar zai yi kuka ya ce,

“Daddy ku yi min auren, da duk yarinyar da ta kwanta muku, ni bana son kowa!”.

Ya sa kai ya fita. Farin ciki ya kama Daddy, haka Gwaggo.

Ta ce, “Kaga ga Safara’u ‘yar gidan Sani, bana ta gama sakandire, yarinyar na da nutsuwa, gata son kowa kin wanda ya rasa. Ka yiwa Kawun naka magana”.

Dariya Daddy ya yi ya ce,

“Gwaggo, dan birni ai sai ‘yar birni, ‘yar kauye sai dan kauye. Mamarshi ta yi mishi mata tuni, diyar yayarta da ta ke riko, Hanifah.

Kinga ita a jami’a take, sannan ta san dukunkunannen halinsa za ta iya fin kowa hakurin zama da shi, tunda ta san halinsa. Gida daya suka tashi”.

Gwaggo ta ce, “To Allah Ya tabbatar da alheri, kada a tsaya bata lokaci tunda dai an samu ya yi na’am”.

Ya ce, “Haka ne Gwaggo, bari in kira Maimuna”.

Ya yi waya ya kira Mama. Ta baro aikin wajen mai aikinta ta taho. Ta samu waje gefen Gwaggo ta zauna.

Nan Daddy ya ba ta daddadan albishir cewa Aliyu ya basu wuka da nama, su aura mai wadda suka ga ta dace, shi kuma ya zabi Hanifah.

Mama kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don murna. Ta ce,

“Masha Allahu, abu ya yi dadi. Na ji dadi sosai, sai a aikawa mahaifinta can Darazo”.

Haka suka ci gaba da tattaunawa. Su wane ne wadannan ‘family’ din ne?????????

 

****

 

 

 

 

 

ASALIN SU

S

un bullo daga Kumo, ta jihar Gombe. Malam Sama’ila malamin buzu ne, kuma daya daga cikin dattawan garin Kumo, wadanda ake ganin kima da mutuncin su, shine mahaifin Alhaji Surajo.

Duk   da cewa ba halinsu daya ba, domin Surajo mutum ne mai wuyar sha’ani wasu lokutan, gashi da fada da rashin barin ko ta kwana. Duk da haka ya tsaya ya yi karatun addini sosai a wurin mahaifinsa kamin Allah ya dau ransa. Ya kuma ba shi babban jari ya ce ya je ya gwada duk irin kasuwancin da ya kwanta masa.

Surajo bai yi karatun boko ba, sanda ya shigo garin Gombe neman na kai Allah ya hada shi da wani Alh. Sule Mai-Taba, suka fara sana’ar sayar da taba.

Kanti guda gare su a babbar kasuwar Gombe suna sayar da taba nau’i-nau’i, kuma suna samu sosai, babu irin tabar da basa shigowa da ita Gombe daga Lagos.

Da abin yai gaba suka soma rarraba ta ga kananan ‘yan kasuwar taba dake sauran garuruwa. Da suka yi karfi suka koma safarar ta da kansu daga kasar Amurka da Ingila.

Sanda Surajo ya fara karfi mahaifin shi Malam Sama’ila ya rasu, shi kadai ya haifa tare da mai dakinsa Gwaggo Hassana, duk haihuwar da ta yi bayan ta Surajo mutuwa suke tun basu shekara ba.

Shi kadai Allah ya bar mata, suka gaji abin da Malam Sama’ila ya mutu ya bari. Tangamemen gida da gonaki biyar, garken shanu da sauran dabbobin kiwo.

Surajo ya ci gaba da kula da gyatumarsa bayan rashin Malam Sama’ila, har zuwa lokacin da Allah ya hada shi da Maimuna.

Maimuna diya ce ga ubangidan shi Alhaji Sule, ta kammala karatunta na sakandire, Alh. Sule ya wanke ta ya ba shi auren ta. Mace mai ilimin addini da na boko kwarai da gaske, mai kyau matuka. A lokacin ya gama ginin katafaren gidanshi da yake gini a unguwar Shango Estate.

Shekaru biyu da auren su Maimuna ta haifi santalelen danta Aliyu Haydar, gata na duniya Aliyu ya gani a wurin iyayensa da kakanninsa; Gwaggo Hassana da Alh. Sulaiman.

Idan aka yi hutun makaranta wani lokacin yana Kumo wajen Gwaggo, wani lokacin yana wajen kakanninshi na wurin uwa. Sai dai kuma tun haihuwar Aliyu, Maimuna ta samu matsalar da dole aka juya mata mahaifa, haihuwa sai dai ta ji ana yi a makota.

Amma hakan bai sa Alh. Surajo ya taba tunanin kara aure ba, domin Maimuna jarumar mace ce, wadda ta sadaukar da kanta ga mijinta da danta.

Tana mishi biyayya da soyayya ta gaskiya kamar ta kwanta ya bi ta kanta.

Gwaggo Hassana ce ma ta taba dosar shi da zancen ya kara aure, ya ce,

“Na roke ki Gwaggo, kada ki kara wannan tunanin. Maimuna ta wuce in mata kishiya don in tara ‘ya’ya, wanda Allah ya bani na gode, Allah ya albarkace shi”.

Daga ranar ita ma Gwaggo Hassana ba ta kara tayar da zancen ba har inda yau ke motsi.

 

Hanifah, diyar Yayar Hajiya Maimuna ce wadda ke aure a garin Darazo, ta ba ta rikonta tun tana shekara biyar don ta dinga debe mata kewa, don Aliyu halinsa sai shi.

Kai shi magana ma wannan aiki ce ja a wurinsa. Baya furuci sai wanda ya zamo lazim, ba ya magana mara ma’ana ko mara muhimmanci.

Lokacin da Hanifa ta dawo gidan su yana da shekara goma sha biyar, aji biyar a sakandire. Ita kuma aji uku na firamare. Ba ruwan shi da ita harkar karatun shi kawai ya sa a gaba.

In ko ta sake ta shiga shirginsa yanzun nan za ta ci dan banzan duka. Don haka take dari-dari da shi, tun tana kankanuwa.

Aliyu ya yi dukkan karatunshi a jami’ar Maiduguri, kafin ya tafi zuwa ‘Lancaster’. Sanda ya soma aiki da hukumar ‘custom’ ne suka hadu da Shareekah, diyar ubangidansa Controller Tajuddeen Olayemi.

Mahaifinta Bayarabe ne, mahaifiyarta mutuniyar Bendel, dukkansu Musulmi ne. Sun dade suna soyayya, sun aminta da juna, daliba ce a jami’ar Lagos mataki na uku.

Da abin yai nisa har iyayenta sun sani. Ba karamin jin dadin hakan Controller Tajuddeen ya yi ba, saboda yadda yake kaunar Aliyu kamar dan da ya tsuguna ya haifa, saboda hazakarsa da kyakkyawar zuciyarsa.

To amma kuma me? Bayan ya kai zancen gida Mama da Daddy duk da basu so ba, amma suna kaunar Controller Tajuddeen, saboda rawar kaunar da yake takawa a rayuwar dan nasu wajen ciyar da shi gaba kusan kowanne lokaci a kan aikinsa, ba za su iya cewa basa son hada jini da shi ba.

Aka kai kudin gaisuwa ga mahaifinta da tambaya kamar yadda yake a al’adar Hausa-Fulani, aka sa lokaci kowa cike da ganin girman dan uwansa.

Shareekah kyakkyawa ce, baka (black beauty), don sai an tona sosai cikin mata kafin a samu mai kalar fatarta. Kullum kanta cikin karin gashi yake, don haka ba za ka iya sanin tana da gashi ko ba ta da shi ba.

Ta ce da shi za ta yi tafiya zuwa Muzambikue an tura su “edcursion”

 kasancewarta dalibar ‘geography’ daga makaranta za suyi sati daya.

Tun dai da suka dawo Shareekah ba ta kara zama lafiya ba, ciwuwwuka iri-iri, haraswa, kasala, zubar da miyau da sauran alamomin mace mai juna biyu, ta kuma ki yadda kowa ya kaita asibiti har shi din kuwa.

Don ita a tunaninta sauyin waje ne kawai ya janyo mata. Ba ta ankara ba daga ita har iyayen sai ga ciki ya bayyana tororo wata shida, kowa yana gani.

Ashe ba wani ‘edcursion’, da uban ya rufe ta da duka kamar ya halaka ta kan sai ta fadi inda ta samo cikin, ba ta rufe ba ta ce,

 “Michell ne (tsohon saurayin ta) suka fita hutawa kasar Johannesburgh ya yi mata fyade.

Tana kuka sosai tana rokar mahaifinta ya rufa mata asiri kada Aliyu ya ji, zai fasa auren ta, za ta je a zubar da cikin ko ta wanne hali.

Controller Tajuddeen har kuka ya yi, ya kuma kira Aliyu ita ma ya kira ta ya gaya mishi komai a gabanta.

Sannan ya kirgo kudin gaisuwa da na tambaya da iyayenshi suka kawo ya ba shi. Ya ce ya je Arewa ya nemi wata cikin kabilarsa. Ba zai aura mishi baragurbi ba.

Aliyu ya ce, “Ba zai karba ba, ya barwa Shareekah duniya da lahira”.

 

Wannan ne dalilin da yasa Aliyu ya tsani ‘ya’ya mata, ya alkawarta ma ranshi ba zai kuma son mace ba. Tunda su din mayaudara ne, maha’inta ne.

Duk soyayyar da Shareekah ke nuna mishi ashe a fuska ne kawai. Shin ya ake soyayya ta gaskiya? Ya ya take? Shin ma akwai ta ko babu? Does it really edist?

 

Wadannan sune tambayoyin da Aliyu-Haydar ke yiwa kanshi a kullum.

Ya tattara ‘file’ din mace da al’amarinta da ita soyayyar kanta ya aza a gefe, ya fuskanci al’amuran ci gaban rayuwarshi.

Muhimman abubuwan da ke gaban Aliyu-Haydar sune, aikinsa, kula da iyayen shi da gyatumar kakarshi Goggo Hassana.

Duk wata kankanba da giringidishin da Hanifah ke yi a kansa ya sani, bai taba daga ido ya dube ta da sunan so ba, share ta yake kamar bai san Allah ya yi ruwan tsirar ta ba.

Har kuma zuwa yau da ya yi furucin da ya zo ya dame shi, wato baiwa iyayenshi dama su aura mishi duk wacce suka ga dama, don ya ga farin cikinsu. Wanda ko kaffara ba zai yi ba, idan ya rantse cewa Hanifah za su zaba masa ba wata ba.

Ba zai iya dorar da komai a kan Hanifah ba, wato kyawun halinta ko akasin haka. Don ta tashi a gabansa, tunda ba sakar mata fuska yake ba balle ita ma ta saki jiki da shi.

Mama dai ta sha gaya masa cewa shi Hanifah take so, tun abin yana ba shi haushi har ya koma ba shi mamaki. Allah ya kawo mu wani zamani da wai mace ce za ta budi baki ta ce tana son namiji, a ganinsa karshen wulakantar da kai kenan ga ‘ya mace.

Duk feleken da ta ke masa dai na nuna ‘caring’ ba ta taba tarar shi fuska da fuska ta ce ‘ina sonka ba’. Sai dai ya ji a bakin Mama. Wannan ne ya bar mata dan guntun mutunci a idanunsa.

A wannan daren dai Aliyu barcin shi gashi nan ne, rabi da rabi. Bai ankara ba ya ji kiran asubahi a kunnuwan sa. Ko masallaci bai iya ya je ba, yana ta tunane-tunane kan subutar bakinsa, ya ba da farali ya koma ya kwanta, sannan ne ya samu barci mai dadi ya yi awon gaba da shi.                                                 

****

 

               

 

 

WASHEGARI

A

 makare Aliyu ya tashi misalin karfe tara na safe, shaf ya manta zai kai Gwaggo asibiti. A gurguje ya yi wanka ya kintsa cikin shirt da wando samfurin ARMANI, ya fesa turare ya yi cikin gida a gurguje.

Bai tadda kowa a falo ba sai Mama tana waya, ga dukkan alama da Hanifah take wayar, don yana jin yadda Mama ke lallashinta wai ta baro gidan bikin haka nan ga Yayanta a gida kuma akwai albishir.

Wani haushi ya kama shi, ya yi gaba dakin Gwaggo. Ya taddata ta kintsa shi take jira, ya zauna a gefenta kamar yadda ya saba. Ta dora hannu a kan kafadun shi ganin yana ta huci shi kadai.

Ta ce, “Wa ya tabo min Zakin Manzo? A’ah, saki ranka, wannan fushin bai yi maka kyau ba”.

Ya ce, “Tashi muje Gwaggo, I got lot to do....”

Daddy ya shigo shima cikin shirin fita, ya zube ya gaida Gwaggo ta amsa fuskarta a sake. Ta ce, “Zamu wuce asibitin”.

Ya ce, “To, sai kun dawo, a yiwa likita bayani sosai, ku je General Hospital can ne ‘file’ din ta yake”.

Ya kai duban shi ga Aliyu ya ga yana ta huci amma bai fasa gaida Daddyn ba. Ya ce, “Gwaggo ya ya ne ke da angon naki? Wa ya tabo miki shi?”

Ta ce, “Haka nan nima na ganshi”.

Da yake Daddy lallabashi yake kada ya botsare ya ce ya fasa auren, sai ya dube shi da murmushin lallashi, yana son ya ji damuwar shi.

Aliyu ya mike ba tare da ya ce komi ba, ya doshi kofa, ya ce, “Gara mu tafi Gwaggo rana tana yi”.

Ta yafa mayafinta ta mike da kyar, Daddy ya yi saurin riko hannunta har jikin mota. Aliyu ya bude mata kofa ta shiga baya ya rufe, ya zaga ya shiga mazaunin direba suka fita a harabar gidan.

Shima Daddy tasa motar ya shiga ya nufi inda za shi. Gidan ya rage daga Mama sai mai aikinta Asabe.

Bayan sun fito daga asibitin gudu sosai Aliyu ke yi a kan titi, Gwaggo ta soma fada, ita fa idan ba zai daina gudu ba to ya sauke ta ya sa ta a Keke-Napep.

Bai daina gudun ba, kuma bai ce komi ba. Wannan halin shiru din na Aliyu na matukar ba ta haushi, yana ji kana magana amma ya yi kamar bai san kana yi ba.

Tsautsayi....wanda an ce...ba ya wuce ranarsa!. Wata yarinya ce ta tsallako da gudu da kwanon bara a hannunta, ta baro uwarta da takewa jagora a daya titin. Duk kokarinsa na kauce mata, da kwarewar sa wurin sarrafa sitiyari sai da ya kwashe ta ya watsar a gefe.

Gwaggo ta yi salati ta sanar da Ubangiji, ta ce, “Ka gani ko?

 Ka ga abin da nake gaya maka amma ka yi kunnen uwar shegu dani. Maza samu wuri ka tsaya”.

Ya yi parking a gefen titi, shi kansa zuciyarsa ta tsinke da ganin yarinyar jina-jina kwance a gefen titi, har mutane sun rufe ta.

Ya fito shima ya keta jama’a ya isa gare ta. Wani daga cikin mutanen dake wajen ya hau sirfa masa zagi yana cewa,

“Ku masu kudin nan kun mai da jinin talaka kamar na kiyashi, ku sanya hancin mota ku buge wanda kuka ga dama saboda takamar za ku saya mishi magani. To Allah Ya isa....!”

 

Aliyu ya daga kai ya dube shi, bai ce da shi komi ba. Ya dauki yarinyar ya sanya a bayan mota. Wani tausayi ya kama shi ganin yadda kanta ya fashe jini na zuba, ga alamar karaya a kafafunta da ke reto.

Ba tare da hankalinshi ya kai ga mahaifiyarta ba, wadda ke tsaye har zuwa lokacin a daya titin tana jiran diyar tata, ba tare da ta san abin da ya faru ba.

A guje ya ja motar ya nufi wani pribate hospital da ita. Don ya san na gwamnati ba za su karbe ta ba har sai sun bata lokacin neman ‘report’ din ‘yan sanda da sauran su. Likitoci uku ne suka rufu a kanta suna kokarin ceto numfashinta.

Aliyu da Gwaggo suna zaune a harabar asibitin, kan wasu kujerun siminti. Kar ka so ka tona fargabar dake zuciyoyinsu. Idan yarinyar ta rasu a dalilin su yaya za su yi?

Gwaggo ta ci gaba da yi mishi fada a kan gudu da mota kamar ta ari baki, amma bai tanka mata ba. Don ya fita shiga damuwa.

Awanni uku cur suna zaune sannan likitocin suka fito, aka turota a keken tura marasa lafiya zuwa dakin aminity wanda Aliyu ya biya.

Likitan ya kira shi ofishinsa, ya yin da Gwaggo ta shiga dakin da aka kwantar da yarinyar  tana ta hirji cikin ranta. Haka kawai tsautsayi ya afka musu, suna neman tasu lafiyar.

Ta zubawa yarinyar ido, duk kafafunta anyi dori, ga plasta a kanta. Ta ce,

 “Na shiga uku ni Hassana, yau ina za mu nemo iyayenta?”

Ko da yake ga dukkan alamu, almajira ce, ko daga annakiyar daudar ta, da ratattakakkun kayan jikinta, da himilin gashin kanta da aka yiwa wata irin tufka kamar ciyawa.

Doctor Misau ya dubi Aliyu ya ce,

“Kai Yayanta ne?”

Kawai sai ya samu kansa da cewa “Eh, mota ce ta bige ta”.

Ya girgiza kai ya ce, “Ta samu karaya har biyu a kowacce kafa, sannan ta ji mummunan rauni a kanta, wanda muke addu’a Allah ya sa kwakwalwarta ba ta tabu ba, ta tashi cikin hayyacinta.

An dora dukkan kafafun anyi mata dinki a kan. Sai mu ci gaba da addu’a Allah Ya takaita ya kuma tashi kafadunta”.

Ya ce, “Ameen”.

Doctor ya ce, “Sai ka je ka biya ‘bill’ din ka”.

Ya mike ya fita. Ya shiga dakin da aka kai yarinyar ya ce,

 “Gwaggo taso in kai ki gida in yaso sai Asaben Mama ta zo ta zauna da ita kamin a sami iyayenta, zan je in biya ‘bill’ in zo mu tafi”.

Ta ce, “To, Allah ya kiyaye gaba”.

Ya ce, “Ameen”.

Da suka shiga gida Mama na kicin tana kiciniyar hada abincin dare. Jin shigowar su ta fito falon ta ce, “Lafiya kuwa? Ina kuka makale ina ta kiran layinka a kashe?”

Gwaggo ta zauna tana cewa,

“Tsautsayi kawai Maimuna, yarinya muka bige duk ta karairaye, kai ya fashe, kuma ba a san daga ina take ba balle iyayenta”.

Mama ta ce, “Subhanallahi! Garin ya ya?”

Gwaggo ta ce, “Garin gangancin sa mana? Kin ga irin gudun da yake yi kamar ya tashi sama, ina ta fada amma ko ya kalle ni. Kai wannan halin miskilancin na Haydara bai yi ba wallahi”.

Shi dai bai tanka ba, ya nufi ‘side’ din sa ya sakar ma kanshi ‘shower’, ya yi alwala ya rama sallolin da bai yi ba, ya canza zuwa caftan na wata jikakkiyar shadda rini, mai ratsin baki da toka-toka (grey).

Ya taje sumarsa wadda ke kwance linkib tana sheki saboda samun kulawa. Yana taje sumar, hoton yarinyar da ya buge dazun nan na gilma  mishi, hankalinshi a tashe yake kwarai, don dai bai nuna bane kada Gwaggo ta samu gangara ta ci gaba da yi mishi bala’i, shi yasa kawai ya yi shiru, amma ko kiyashi ba ya fatan ya kade balle dan mutum bani Adam.

Cikin gidan ya shigo lokacin Gwaggo na dakinta tana sallar isha. Ya tadda Mama da Asabe a kicin, ya gayawa Mama zai koma asibitin ta ba shi Asabe ta dinga kwana da yarinyar kamin ta ji sauki ta fadi inda iyayenta suke a kaita.

Tuni Mama ta hada abinci cikin dan karamin kwando har da fulas din ruwan zafi da kayan shayi, da duk abin da maras lafiya zai bukata ta fannin abinci mai ruwa-ruwa da maida kuzari, ga su ‘lucozade’ da sauransus. Asabe ta dauka suka tafi.

Har zuwa lokacin da suka shiga dakin yarinyar bata farka ba. Ya danna kararrawa Nurse ta shigo ta canza mata ‘drip’, za ta fita ya ce,

 “Har yanzu ba ta farka ba?”

Ta ce, “Nan da karfe goma na dare insha Allahu za ta farka”.

Asabe ta shimfida dardumar da ta taho da ita a kasa ta zauna. Shi kuma ya karasa jikin gadon, ya zubawa yarinyar ido. Bery cute da ita, fara tas mai yalwar gashin ido, giran ido da sumar kai.

Hatta a hannayenta gashi ne kwance lambam kamar ta hada jinsi da Lebanese. Sai dai kuma dukun-dukun take, kamar an tsamo ta daga kwatami. Wata daudaddiyar atamfa ce a jikinta duk ta kekkece, riga da zani da kallabi, suma din wari-da-wari.

Ya ja kujera ya zauna, ya dauki magazine ta asibitin a nan kan ‘side drower’ yana dubawa. A lokacin Dr. Misau ya shigo suka yi hannu, ya ce, “Sun yi hoton kwakwalwarta dazu komai normal, insha Allahu lafiya za ta farka nan da awa daya, idan allurar barcin da a kai mata ta sake ta.

Karfe goman kuwa ta bude ido. Ta dade tana nazarin inda take. Ta ji ta kasa motsa komai na jikinta, radadi da zugi da kafafunta ke yi suka shige ta.

Ta soma kuka tana kiran “UMMA! Wayyo Umma-wayyo Umma.........”

Kuka sosai, da ta lura duk mutanen da ke dakin babu Ummanta, kuma bata san su ba.

Asabe ta taso ta iso gareta ta ce,

 “Ki yi hakuri ki yi shiru, kinga baki da lafiya.

Ina Umman take aje a kirawo ta?”

Ya aje ‘magazine’ din yana kallon ta. Asabe nata lallashin ta amma ta ki yin shiru, musamman da ta tuna ta baro Umma a gefen titi ta tsallaka don ta karbo sadaka wajen wata mai fanke, daga nan ne kuma ta ji anyi sama da ita an watsar, daga nan ne kuma ba ta kara sanin abin da ke faruwa ba, sai yanzu da ta farka ba ta ga Ummanta ba.

Ai kuwa ta zabura za ta mike, ta kwalla kara saboda azabar da ta ziyarce ta har cikin kwakwalwarta. Ta koma ta kwanta tana kuka da nishin azaba sabin gwanin ban tausayi.

“Hada shayi ki ba ta”. Ya ce da Asabe. Karo na farko kenan da yayi Magana tun farkawarta.

Cikin sauri ta hada shayi mai kauri wanda ya ji madara da bombita. Ta sa mata kofin a baki bayan ta tallabo ta, ta jingina mata filo.

Ta kuwa kama sha sosai yana warware dunkulallen hanjinta da ya dunkule waje daya saboda yunwa. Kan Asabe ta farga sai kofin a hannunta.

Ya ce, “Zuba mata abinci mai ruwa-ruwa”.

Ta zuba faten dankalin turawa wanda ya ji hanta da ganyen alayyahu da tumatur, ta zauna a bakin gadon tana ba ta da cokali tana shan faten hannu baka hannu kwarya kamar kunnen ta ya tsinke.

In ba ta yi kuskure ba tunda uwarta ta kawo ta duniya ba ta taba cin abinci mai dadin wanda ta ke ci yau ba. Nan da nan ta cinye.

Ya ce, “Kara mata!”.

Asabe ta kara ta ba ta tana ci da kanta. Ta balle hancin lemon ‘Mountain Dew’ ta ba ta, suma nan da nan ta share su. Ta koma ta jingina da filo tana ajiyar zuciya, nutsuwa ta zo mata. Ta ci gaba da kukan neman Umma.

 

A nutse Aliyu ya taso ya tsaya a gabanta. Ya fiddo hankicinshi mai kamshi da tsafta fari sol da shi daga aljihunsa ya mika mata.

“Ungo share hawayenki”.

Ta daga kai tana kallon ma’abocin wannan lallausar murya, lallausar kamshi, da bayyanannen kwarjini, sai ta ji ta kasa yin musu, ta karba tana share hawayen da sauri da sauri.

“Ya ya sunanki?” Ya tambaye ta.

“ Habibah, amma (MUHASIN) Ummana take ce mini”. Ta ba shi amsa.

“A wace unguwa kuke?”

“Can karkashin gada”.

“Wace gada?”

“Ta cikin tashar Dukku”.

Ya boye mamakinsa ya ce, “Idan aka je gobe za a samu Umman a can?”

“Ban sani ba”.

“To ki yi hakuri, ki daina tada hankalinki. Gobe in Allah Ya kaimu zan je na taho miki da Ummanki, in har tana can. Ki daina kuka, tsautsayi ne, nine na buge ki ba da sani na ba. Yanzu ma dan dare ya yi ne da na je karkashin gadar. Ki yafe ni kin ji Muhaseen? Insha Allahu zamu kula da lafiyarki har sai kin warke, kwanta ki huta”.

Ta koma ta kwanta, ta lumshe idanunta. Shi kuma ya yiwa Asabe sallama ya tafi.

Washegari Aliyu ya koma dai-dai inda ya kade Muhasin, ya yi ‘parking’ ya fito daga mota. Ya doshi wasu matasa dake sayar da rake a gefen titin ya yi musu sallama suka yi hannu.

Ya dubi mai raken ya ce,

“Don Allah dan’uwa tambaya nake”.

Ya ce, “Allah Yasa na sani dan’uwa”.

“Tashar Dukku nake nema?”

“Ai ko ka baro ta can baya”. Ya kwatanta mishi.

Aliyu ya yi godiya ya koma motar shi ya ja.

Lokacin da ya isa cikin tashar, kowa na harkar gabansa babu wanda ke kula da wani.

“Alhaji ina za ka? Hajiya ina za ki?’

Abin da yake ta ji kawai kenan, shi kuma bai ga wata gada ba balle karkashin ta.

Ya matsa ga wani shagon aski a nan cikin tashar, mutane hudu a ciki ana yiwa na biyar din aski.

Ya yi sallama suka amsa duk suka yi hannu, ya ce, “Don Allah tambaya nake?”

Mai shagon ya ce, “Yi tambayar ka”.

Ya zura hannayenshi cikin aljihu ya ce, “Shin akwai wata gada ne cikin tashar nan da mutane ke zama karkashin ta?”

Mai shagon ya ce, “Eh, akwai gada a can gaba da almajirai suke zama, musamman in ana ruwa”.

Ya ce, “Don Allah a nuna mini, don wata yarinya na buge jiya ta ce mahaifiyarta a can take, shine nake so in je in dauke ta in hada su da ‘yar ta”.

“Kwarai, akwai wata almajira makauniya da suke tare da ‘yar ta, wasu farare tas dasu, suna yawan zama a wajen. Don ana cewa ma a nan suke kwana, duk zafi, duk sanyi”.

Hankalin Aliyu ya kwanta, ya ce,

“Don Allah a raka ni”.

Dayan ya ce, “Haladu raka shi don Allah”.

Haladun ya mike ya wuce gaba suka tafi. Tunda suka doso wajen gaban Aliyu ke faduwa, don da alama babu kowa a wajen sai kullin kayansu cikin buhu.

Dan rakiyar ya ce, “Nan ne wurin tambayi mai sai da abincin can ko ta ganta, don idan ba ‘yar, ba ta fita bara ita kadai”.

Aliyu ya karasa gurin mai dan wake ya yi mata sallama, ya kuma tambaye ta almajira babar Muhasin.

Ta tabbatar mishi tun jiya ba ta gansu ba, don wani almajiri ma yake gaya mata an kade ‘yar, uwar kuma wani mai katuwar mota ya sace ta, don yana ganinta ya danna ta a mota ya tafi da ita.

Hankalin Aliyu ya kai kololuwar tashi, ya yi mata godiya, kafafunsa a salube ya koma karkashin gadar ya dauki kullin kayan nasu, ya yiwa Haladu ihsani ya nufi motarsa.

Ko da ya iso asibitin jikinsa a sanyaye yake, yana cewa cikin ransa shi ya shiga uku, yarinya ta rasa uwarta a dalilinsa, ta rasa kafafunta dalilinsa, yanzu ya ya za su yi da ita? Ina za su kaita?

 

Ya tura kofar ya shiga cikin sallama. Asabe ta amsa, ya shiga. Muhasin din na barci, amma jin muryar wanda ya ce zai je ya kawo mata Umma ai tuni ta  watstsake, ta kafa mishi kananan idanunta.

Ya ja kujerar robar da ya zauna jiya ya zauna, yana kokarin zakulo murmushin dole a kan siraran lebbansa.

Ga mamakinshi sai ji ya yi ta ce da shi, “Ina wuni?”

Ya amsa “Lafiya lau kanwata, ya ya jikin? Ina ke miki ciwo yanzu?”

Ta runtse ido, “Duka jikina yana ciwo”.

“Ki yi hakuri kin ji, za ki ji sauki bery soon insha Allahu”.

Ta rufe ido hawaye suka ziraro. Kafin ta amayo da abin da ke cin ta a zuci,

“Baka ga Umman ba ko?”

Ya girgiza kai cikin tausayi,

“Sun ce wai wani mai mota ya tafi da ita. Yanzu haka garinku zai kaita, ina ne garin ku?”

Ta rushe da kuka tun karfinta, “Wayyo Umma! Wayyo Allah Ummana!! Shi kenan an sace ki, ba zan kara ganin ki ba”.

Duk dauriya irin ta Aliyu sai zuciyarshi ta tsinke, kwalla ta cika kyawawan idanunsa. Ya yi kokarin mai da su.

“Take it easy kanwata….., zamu ga Umma in Allah Ya yarda. Nima ina da Ummata mai kirki kamar Ummanki, za ta rike ki Muhasin kamar Umman ki, har zuwa sanda Allah zai sada mu da Umma.

In kuma kin san garinku ki gaya min yanzu in je in binciko”.

“Ni ta gaya min sunan garin amma na manta. Ta ce ita har abada ba za ta koma garin ba saboda abin da Babana ya yi mata. Ta ce sunan sa Umaru, ta ce ni jikar San-Turaki ce. In suka ganni za su kwace mata ni”.

Ta ci gaba da kuka.

Daga Aliyu har Asabe sauraron ta suke, muryarta mai kumaji (husky), lafuzanta masu taushi. Ga irin abubuwan da take fadi cikin kuka, za ka fahimci ba karamar kauna take yiwa mahaifiyarta ba.

Asabe ta rungumo kafadunta tana lallashin ta, shi kam ido ya zuba mata. Can ya ce,

 “Ba za ki iya tuna sunan garin ba? Ki yi kokari ki dan tuna”.

“Ni fa na manta, amma idan na tuna zan fada maka”.

“To shi kenan, fatana yanzu shine Allah ya baki lafiya, zan kai ki wajen Mamana ki zauna har zuwa sanda za mu ga Umma, zan ba da cigiyarta cikin radio da talabijin, za a ganta in Allah ya so, kwantar da hankalinki Muhasin, kuka kara ciwon zuci yake, sannan baya baka abin da Allah bai baka ba. Sai dai ki yi ta addu’a Allah ya bayyana mana ita da sauri”.

Ta ce, “To”.

Ya duba agogon hannunshi ‘swatch’, “Bari in je in kawo muku abinci. Zan iya tafiya ba matsala MUHASEEN?” Ya fada da wata irin tattausar murya, mai kwantar da hankalin karamin yaro.

Daga mishi kai ta yi alamar ya tafin. Ya juya ya fita. Da ya kai bakin kofa sai ya kara juyowa, suka kuwa hada ido, don ita ma bayan shi ta bi da kallo.

Ta yi murmushi ta ce, “Sai ka dawo”. Ya fita ya ja musu kofar.

Yana zuwa gida ya tarar da Hanifah ta dawo, tana mike cikin ‘sofa’ da ‘Ipod’ a kan cinyarta.

Budurwa baka, ‘yar gaye, mai masifaffen gayu irin wanda ya zarta hankali. Dalibar ‘Law’ a jami’ar Tafawa Balewa dake Bauchi, tana kokarin hada LLB dinta shekara mai zuwa.

A fuska kam ba ta da makusa sai a ‘structure’ ta yi siranta da yawa, sai dai akwai tsayi irin wanda MANYAN MAZA ke rububi a wannan zamanin.

Ya yi sallama, ita kadai ce a falon. Ta dago cikin slow tana kallon sa da fararen kwayar idanunta, kirjinta ya shiga harbawa da sauri da sauri, kamar yadda ya saba duk sanda ta yi tozali da Yayan nata.

Namijin da yasa ta raina sauran maza, da duk abin da suke takama da shi. Namiji daya da zuciyarta ke so. Shi kadai ne a duniya take jin za ta iya aura, ta kuma iya yin rayuwar aure dashi, don in har yana raye, to ba za ta iya auren kowa ba.

Kallon maza take with contempt (a raine) a duk lokacin da ta daga ido ta dube su; a ganinta babu kamar shi, ta fannin komai; shine kadai cikakken mutum a idanunta da duniyar zuciyarta.

Amma abin takaicin bai taba yi mata wani kallo bayan na kanwar shi ba. Ita kadai take sha’aninta.

 Ciwon kana so ba a son ka, matukar ciwo ne da shi, amma a yau ji take ta fi kowa farin ciki da sa’a a duniya, tun sanda Mama ta shaida mata cewa ita din dai zai aura ba wata ba. Addu’arta ta shekara da shekaru, ba ta tashi a banza ba.

 

Ta amsa sallamar tashi muryarta tana rawa, bai tsaya ba kai tsaye ya wuce ‘bed room’ din Mama, don bai ganta a falon ba.

Tana daura kallabi a madubin dogon yaro, ya yi sallama tana kallon shi ta cikin madubin ba tare da ta juya ba ta ce.

“Ina ka shiga ne? Ga abincin su Asabe tun safe na rasa mai kai musu”.

Ya ce, “Bari ke dai Mama, ina tashar mota tun dazun”.

“Tashar mota? Me ka je yi tashar?”

Ya zauna a kujera cike da gajiya ya soma warware mata yadda abin yake. Mama ta nutsu tana ji, ba ta katse shi ba.

“Babarta makauniya ce, almajirai ne masu kwana a tasha. Babu wanda ya san daga garin da suka bullo. Yanzu kuma uwar ta bata, bai san ya zai yi da yarinyar ba, don ba zai iya barinta ta fada mugun hannu ba.

Ya kare da cewa, “Mama sai kinga yarinyar wallahi za ki ji ta shiga ranki. Naibe and Innocent.....”

Ta yi murmushi, “Tunda ka yaba nima ina sonta, in ta warke ka kawo min ita tunda dama duk gidan za ku bari, ni kadai za ku bari, sai in samu bokiyar debe kewa”.

“Da gaske kike Mama za ki rike min Muhasin har in nemo mata babarta?”

Ta baro jikin madubin ta zauna kusa da shi.

“Na taba yi maka wasa ne? Ina nufin abin da na ce, zan rike ta har gaba da abada idan akwai. Da na kowa ne, sannan tsautsayi yana kan kowa.

Ka daina dorawa kanka damuwar cewa kai ne ka yi sanadin rabuwarta da babarta, haka Allah ya rubuta mata. Babu kuma wanda ya isa ya kankare mata kaddarar rayuwarta”.

Ya ce, “Thank you my dear Mum, na san za ki yi min fin haka. Kullum na kalli uwar wani sai in ce tawa ta fi ta kowa.....”

Ya bawa Mama dariya sosai ganin ya kama hannayenta ya rungume.

Ta ce, “Baka ga Hanifah bane?”

Nan da nan ya yi fuska, “Na ganta”. Ya mike, “Bari in kai musu abincin in dawo”.

“Ka tafi tare da Hanifah ta zauna da mara lafiya din zuwa dare, ka taho min da Asabe, akwai ayyukan da za ta min in yaso da daddare sai ta koma ku dawo da Hanifah”.

Bai ce komi ba ya fita. Tana nan a inda ya barta, ta nutsa cikin yanar gizo.

Ya ce, “Ki dauko abinci a kicin ki biyo ni”.

Da hanzarinta ta mike ta yafa mayafin doguwar rigar dake jikinta, ta yi yadda ya ce din, ta bi bayansa.

A darare ta bude kofar motar gidan gaba ta zauna. Ta aza kwandon kayan abincin a baya. Zai ja motar ya tuna bai gaida Gwaggo ba yau, kuma sam bai ganta ba.

Ya juya ga Hanifa ya ce, “Ina Gwaggo?”

Tana kallon gefen titi ta ce, “Sun fita da Daddy tun safe wai za su Dukku gidan abokin Daddy Dr. Omar, matarshi ta rasu”.

Cikin ranshi ya ce, “Allah ya ji kan rai”. Ya ja motar suka tafi.

Sanda suka murda kofar suka shiga, Asabe na sallah, maras lafiyar na jingine da filo tana shan ‘tea’ a dan kankanin kofi.

Ta yi kuka har ta gode Allah. Idanunta sunyi luhu-luhu sunyi jajir. Ita dai Hanifa tana kallon ikon Allah, tana kuma cewa cikin ranta “wace ce wannan almajirar kuma ni ‘ya su?”

Da sauri ya karasa ya zauna a kujerar da yake zama, ya ce cikin damuwa,

“Kuka Muhaseen, why? Ban ce ki daina kukan nan haka ba?”

Ta ja shessheka, ta ce cikin rishin kuka, “Mafarki na yi wai sun yanka Umma......”

Ya girgiza kai,

“Mafarki ne kawai, don kin sa hakan a ranki. A duk lokacin da kika tuna Umma addu’a za ki yi Allah ya bayyanata da gaggawa.

Ina ji a jikina ita ma tana kyakkyawan hannu. Tashi ki ci abinci”.

Hanifa dai na tsaye jikin gado, hannaye rungume a kirji. Uffan bata cewa mara lafiyar ba.

Asabe ta shafa addu’a ta tsuguna tana gaishe shi, bai amsa ba ya ce,

“Maza zuba mata abincin”.

Ta jawo kwando tana budawa. Yau da kanshi yake ba ta abincin a baki tana karba tana ci, ya cika mata kofi da kunun gyada ya bata ta soma sha.

Ya mikawa Asabe filet din ya ce ta kintsa su tafi Mama na kiran ta, ga Hanifa nan za ta zauna.

Ya dube ta ta gefen ido, kamar an barota daga cikin kwai saboda kyau da gayu, amma ba ta ko dada shi da kasa ba.

Ya ce, “Yarinya ce na bige da mota ba a ga Mamanta ba, ki kula da ita mu zamu tafi, sai bayan isha zamu dawo”.

Ta turo baki gaba ko uffan ba ta ce ba. Suna fita ta ja tsaki tana kunkuni,

“ni na zaci ma ‘shopping’ zamu shine za a kawo ni jinyar almajira. Mts!”

Ta kara jan tsakin. “Dubi yadda ya ware wannan kulalliyar fuskar tasa yana tarairayarta, ni ko murmushinsa ban taba gani ba. Na ga wadda za tai jinyar”.

Ta juya tai ficewar ta ta zauna a ‘reception’ tana faman kiraye-kirayen wayar kawayenta.

Ba ta koma dakin ba sai da aka yi sallar magariba. Muhasin na so a cire mata ‘pampers’ din da Asabe ta sa mata, ta cika taf kuma ta dameta.

Hanifa ta shigo ta ja kujera gefe tai zaman ta tana faman ‘chatting’ da waya. An ce wai ‘wargi ma wuri shi ka samu….’, tana so ta gaya mata ta cire mata amma babu fuska, tilas ta yi shiru.

Allah ne ya kawo Nurse Habiba mai kula da ita. Ta cire mata ‘drip’ ta ce ta huta zuwa anjima sai a mayar.

Ta ce, “Cire min kunzugun nan, na yi bayan gida”.

Ai da jin haka Hanifah ta gudu. Sister Habiba tasa ‘tissue’ da ruwa da sabulu da ‘dettol’ ta wanke mata, ta fita da ‘pampers’ din waje. Ta dawo ta sa mata wata ta ba ta magani da ruwa a cup ta sha ta fita.

Tana fita Asabe na sawo kai niki-niki da ledoji. Ya biyo bayanta rike da wasu ledojin bai ga Hanifah ba.

Ya ce, “Ina mai jinyar taki?”

Ta ce, “Ta fita”.

Sai gata ta shigo. Ya balla mata harara ya ce,

“Abin da nasa ki kenan?”

Ta ce, “Ba fa wani waje na je ba, nan din ne ba serbice and I wanna mek a call, shine na dan fita”.

Bai kara bi ta kanta ba ya mai da duban shi ga Asabe.

“Ga ruwan dumi a filas ki zuba Dettol kadan da wannan ‘bath-gel’ din ki goge mata jiki sosai da wannan karamin tawul din, ki dauki daya cikin kayan nan ki sa mata. Amma ki yi da kula, kada ki fama ta”.

Cike da ladabi ta ce, “To”.

Ya juya ya fita Hanifah ta bishi, don dama dai duk ta gundura da zaman.

Da suka iso gida suka tarar da Gwaggo sun dawo. Gwaggo ta ce, “Ya ya mai jikin?”

Ya ce, “Ta ji sauki sosai”.

A nan Gwaggo ke bawa Daddy bayanin abin da ya faru.

Ya ce, “Allah ya kiyaye gaba. Ba tun yau ba nake hana ka gudu da mota amma ba ka ji”.

Shi dai ya mike zai gudu don barci yake ji sosai, gashi gobe zai yi sammako ya koma Lagos.

Gwaggo ta ce, “Ina za ka ne? Ka zauna magana zamu yi”.

Ta dubi Hanifah ta ce,

 “To bamu waje, kin zauna kina rabawa mutane ido, ko a gabanki kike so ayi zancen auren naki?”

Da sauri ta tashi ta yi dakinta tana murmushi. Ya koma ya zauna yana sauraron su.

Daddy ya ce, “Mun je Dukku yau, ganin kan hanya ne kawai muka shiga Darazo. Alhamdulillahi tafiya ta yi kyau, don Alh. Abdullahi (mahaifin Hanifa) ya karbi lamarin sosai.

A take muka gabatar da komai har sadaki, muka yanke lokacin aure farkon watan April mai kamawa, zamu je can a dauro aure. Yaya? Ya yi maka?”

“April Daddy? Ai ni zuwa lokacin ban shirya ba. A bani nan da watanni shida, don kuwa ko gidana ban yi tsarin shi da mace ba, yana bukatar gyare-gyare”.

Daddy ya ce,

“Wannan ba matsala ba ce, ai itama karatu take ba binka za tayi ba, za ku zauna a nan a ‘side’ dinka zuwa sanda za ka gama gyaran gidan a nutse, kafin sannan ita ma ta hattama karatun ta, tunda saura shekara daya ya rage mata.

Maganar lefe kuwa wannan an dauke maka nauyinsa, za su je Italy ita da Mamanku ta zabi duk abin da take so sati mai zuwa. Sai me ya rage na shirin?”

Aliyu ya mutu a zaune, ya rasa abin cewa. Sai ya dukar da kai ya ce, “Shi kenan Daddy, hakan ya yi, Allah Ya kara girma”.

Gwaggo da Daddy suka ji dadi har cikin ransu, suka fara sanya mishi albaka.

**       **