Book 1 (Farko)
by @takori
A BARI YA HUCE...-1
Gurin-gawa karamin kauye ne mai tsohon tarihi da ya kunshi al'umma masu sana'o'i daban-daban, amma duka tushensu daya. Galiban malamai ne da manoma, kuma kauye ne da manyan malaman da a halin yanzun suka barwa duniya abin da ba za a mance da su ba suka fito. Gurin Gawa na nan cikin karamar hukumar Kumbotso, yankin Fanshekara ta jihar Kano. Karamin kauye ne, wanda ya samu tallafin gwamnati ta hanyar wutar lantarki, ruwan sha mai tsabta, da takin zamani, wanda ke taimaka musu kwarai wajen bunkasa harkar nomansu.
Akwai sanannen hadin kai tsakanin al'ummar garin mazansu da matansu. Sai dai kuma babu titi mai kyau a Gurin-Gawa. Idan mota ce zata shiga kauyen sai ta yi futuk da kura, mutanen cikinta sun gwaggwara kawunansu sabida rashin kyawun birjin.
Duk da haka wannan bai hana al'ummar cikinta jin dadin zamanta ba, motar haya ba ta shiga cikin kauyen, sai dai ta aje ka a titin ka hau achaba ko bayan akori-kurar Rake ta mutanen garin ka karasa ciki. Don haka da wuya ka ga mutanen birni na shiga kauyen, don a ganinsu ba su ga mai zasu tsinto cikin wannan kalataccen kauyen ba.
Samarin garin Gurin-Gawa kan fita cikin Fanshekara da wajenta domin neman kwabo, ta hanyar ga-ruwa, sayar da rake, dukanci, dako da sauransu. Don kalilan ne suka damu da makaranta wadda dama idan dai ta boko ce, to ba a zancenta cikin garin Gurin-Gawa. Makarantun allo da na Buzu su ne Allah Yai yawa da su a garin.
Malam Bedi, yana daya daga cikin dattawan garin Gurin Gawa, haifaffen nan ne iyayensa da kakanninsa. Sana'arsa shi ne noma, yana da gonar rake da gyada, sannan yana nome dankalin Hausa, makani da gurjiya.
Bedi da matarsa Hure, fulanin Gurin-Gawa ne na usul. Mutanen kwarai ne da duk Gurin Gawa ba wanda bai sansu ba, tare da yi musu kyakkyawar shaida. Babban dansu shi ne Habibu, wanda tun yana karami Malam Bedi ya dankawa kaninsa mai bi masa a haihuwa ya ke taya shi sana'ar fataucin goron da yake yi daga Shagamu zuwa Kano, wanda daga baya shi Habibu ya shiga makarantar horas da malamai (SAS) tun daga wancan lokacin kuwa ya koma Kano kwata-kwata. Shi da Gurin-Gawa sai dai yazo da yawo idan ya zo gaida mahaifansa wanda yakan dauki dogon lokaci bai yi hakan ba.
Su ma su Malam Habibu ba su wani damu da shi ba, don ba wata cikakkiyar shakuwa ce a tsakaninsu ba. Duk wani burinsu na duniya yana kan 'yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu.
Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe 'yar lelen ce zaune bisa tabarma tana dandasawa 'yar bebin karanta kwalliyar juma'a da wani tsalelen yankin yadin mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga 'yar bebin tana cillawa tana cafewa tana wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu a gaba dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke samu daga Innarta.
"Ke kam 'yar gata ce, Ta-Ummule.
Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki.
A taba ki a tabo bala'i,
A duke ki, in rama miki.
Innata ta tsaya min,
Ni kuma na tsaya miki........"
Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa 'yar bebinta, cikin zazzakar muryarta kamar gyare. Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa,
"Yaya Habibu oyoyo!"
Ya ce "Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko, hanci duk busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su duka a jikina. Wallahi duk sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da kazantarki nake, shashashar banza an girma ba a san an girma ba".
Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba. Inna Hure ta cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala'in da ke cike taf a bakinta, sabida wannan tijara da yake yiwa autarta.
A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da matsananciyar kaunar da Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da dukkan zuciyarta.
Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce
"Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?"
Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce "Lafiya kalau". Cikin danne bacin ranta.
Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai daina kyarar mata auta ba, to ya daina zuwa, babu dole.
Cikin kasada ya ce "Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana wakar 'yar bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana haramar tafiya islamiyya, amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa duk wasu abubuwa na yara masu hankali, ba ta san shi ba............"
A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce "Kai saurara. Wai me ye gaminka da yarinyar nan ne? Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata, amma wannan sababin da kake yi mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta sai ka dauketa ka kai ta".
Ya sunkuyar da kai ya ce, "Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku".
Ta ja tsaki, "Tsuuuu!" Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai kuma tashi daga durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da alama a gajiye ya ke likis, sai gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya fadada far'arsa, amma jin Inna Hure na ta sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan Habibu ba zai daina tsangwamar mata Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba.
Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce "Ai gara da ka zo, dama binka zan yi yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a gidansu ta ke zaune ba, balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce".
Malam Bedi ya ce, "Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya zo gaishe ki? Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne majibincin al'amarin ta nan gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata ranar da babu mu, wane ne zai shiga?
Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya daina cewa 'yar ki ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar mu rasa jam'i".
Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa, "Yaya Habibu ni ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba".
Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, "To mu je, amma sai ki tsaya a wajen masallacin daga gindin bishiya kina bin jam'in, don mata ba sa zuwa masallacin maza".
Ta ce "To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi yake dora ni, kai kuwa ka ma fishi tsawo".
Ya kama baki, "Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?"
Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce
"Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto ta fado tim! Ta karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar 'yar Birrai nake. Bana fadowa, sai dai in ciko bujena da goba da tsamiya........."
Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to ita me ye laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi.
Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da malamai ta Kano, wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake ma abin da ya kawo shi Gurin-Gawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa.
Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da Habibu da hidimar karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga makaranta da ranakun karshen mako.
Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu da 'ya'ya bila adadin maza da mata. Saidai ‘ya’yanshi kanana ne da ake haifa akan idon Habibu. Cikinsu duka babu mai shekaru goma. Babbar diyarshi Ladidi sa’ar mairo ce. Don haka Habibu tamkar wani jigo ne ga iyalin Alh. Abbas wanda duk suke kauna sabida zumuncinsa da rikon amana.
A rayuwar Alh. Abbas bai taba ganin yaro mai kwazon neman na kai da amana irin Habibu ba. Tunda ya ke tare da shi, kwandala wannan bata taba bata cikin lissafinsa ba, kimanin shekaru ashirin ke nan. Watau tun Habibun yana dan shekara biyar. Wannan ne dalilin da ya sa ya maida Habibu dan cikinsa ba Dan dan uwansa ba.
Taimako dai-dai gwargwado Alh. Abbas na yi ma yayan shi Malam Bedi, kamar ta samar mai ingantaccen takin zamani, da taimaka mai da motocin noma a yayin girbi, wadanda yake dauko masa haya daga KNARDA.
Bayan wannan sallah da azumi shi ne sutturarsu, haka ta fannin abinci lokacin azumi, tun daga kan sukari, lipton, madara, da su taliya ba abin da ba ya taso Habibu ya kawo musu, sai dai idan suna nomansa a nan Gurin-Gawa.
Zumunci ne mai karfi a tsakaninsu, wanda iyayensu suka dora su a kai, har gida Alh. Abbas ya sayawa Mal. Bedi a Yakasai ya ce ya dawo su zauna tare, inda shi kuma ya ce shi da rabuwa da Gurin-Gawa sai dai mutuwarsa. Ko ita ba ya fatan a fitar da gawarsa daga Gurin-Gawa, su je can su tsinci abin da suke tsinta a birnin, shi kam a gareshi kwanciyar hankali shi ne komai.
To amma wannan zumunci na mazan ne banda matan. Babu shiri ko kadan tsakanin Inna Hure da matan Alh. Abbas wato Habiba da Hajara. Tun sanda daya daga cikinsu ta taba cewa a bata Mairo ta dinga taimaka mata hidimar ‘ya’yanta ta kulla gaba da su. Ta ce kuma wadda duk ta kara tako mata gida, Allah Ya isa. Ta rasa dalilin da 'yar tata ta tsolewa kowa ido. Ba abin da ta ke so a rayuwarta irin ta budi ido ta ga Mairo na wasan 'yar tsanarta a tsakar gida, suna harkokinsu gwanin ban sha'awa.
Don haka ne ko makarantar firamare da ake sa yara a kauyen taki yarda ta sakata, ita dai su zauna abinsu.
Sai da Mal. Bedi ya yi da gaske kamin Mairo ta dinga zuwa karatun allo a makwabtansu, daga takwas na safe zuwa sha biyun rana. Nan din ma ba wani abin arziki ta ke tabukawa ba da ya wuce tsokana, jan fada, surutu da guduwa idan Malam ya soma gyangyadi.
Abin da Mairon Hure ta kware akai shi ne hawa bishiya. Yadda kasan kadangaruwa koko Gorilla haka ta ke makalewa a jikin bishiya. kusufa-kusufa ta iya kurdawa ta tsinko abinda ranta ke so ta cika bujenta. Duk girman bishiya Mairo zata iya dafe ta, ko tsoron irin aljannun nan da ake ce suna zama a bishiyoyi ba ta yi. Ta tsinko musu su ci abinsu, ita da Innarta, wannan ya fi komai dadi ga Hure.
Mairo yarinya ce 'yar kimanin shekaru takwas cif. Amma kaifin bakinta ya fi na dan shekaru ashirin. Kyau kam ba a magana, tsurarshi na Inna Hure, doguwa shafal-shafal da shafaffar mara gami da lafiyayyen kugu, wanda tun tana jaririya haka yake. Sumar kai yalwatacciya, yalo-yalo kamar ta hada jinsi da Larabawa. Sai dai fa dankare take da kwarkwata da amosani wanda ya bi ya cinye rabin gashin.
Wani aiki sai Hure Innar Mairo, don tunda Mairo kukan kitso ta ke, aka shafe yi mata kitso a doron kasa. Kai wata kila ma ta manta akwai suma akan Mairo, don kullum kulle ta ke tamau cikin wani bakin dankwali mai masifar dauda. Sai idan kwarkwatar ta ishe ta da cizo ne ta ke tube dankwalin ta samu gefe guda ta yi ta susa da hannu bibbiyu har sai jini ya bubbugo.
Wannan shi ne babban takaicin rayuwar Habibu, yana matukar bakin-ciki da tsarin rayuwar kanwarsa tilo, wadda kuma Allah Ya sanya masa matsananciyar kaunarta da tausayinta. Ta wani bangaren ba ya ganin laifin Inna Hure, domin haihuwar ce Allah Ya ba ta a tsufanta, bayan ta riga ta fidda rai da samunta.
Sannan yawan aiyukan gida da ke kanta ba zasu barta ta kula da irin wadannan kananun abubuwan game da yarinyar ba.
Duk ba wannan ya fi damunsa ba, kamar jahilcin Mairo. A ganinsa Mairo jahila za a kirata kai tsaye, ba arabi ba boko. A ganinsa da tana zuwa makaranta, wannan duk wani abu ne da ita kanta zata yi wa kanta nan gaba, ba tare da kowa ya sata ba.
Bayan sun fito masallacin ya duba inda ya ce Mairo ta tsaya ta yi sallah, ba ta ba alamunta, balle dardumar karauninta. Ya juya gabas da yamma, Kudu da Arewa babu Mairo. Ransa ya sosu, ya kira wata 'yar yarinya mai tallan rogo, ya ce "Don Allah ko kinga Mairon Hure?"
Ta ce, "Na ganta ta mika kwanar gidan su".
Ya ce, "To madallah. Ta yi gaba abunta dai-dai sanda Malam Bedi ya cimmasa da cazbaha a hannunsa ya ce, "Mai kake tambaya ne?"
Ya ce "Mairo mana, sama ko kasa na nemeta na rasa?"
Dariya ya ba wa Malam Bedi, ya ce "Mairon ce zata zauna maka waje daya? Ai yadda kasan tsuntsuwa haka ta ke. Idan dai ba gaban Innarta ba ne babu inda zata zauna. Ai jin ku kawai nakeyi da ka ce wai ta zauna nan mu fito".
Ya girgiza kai suka ci gaba da tafiya yana ba shi labarin Mairo. Wanda duk mai bakanta zuciya ne ga Habibu.
Ya ce "A rana in ba a kawo min kararta sau hudu ba, a kawo sau shida. Malaminsu ya gaji da sulalewar da ta ke yi, ya ce ta yi zamanta gida. Ni al'amarin Mairo ai sai addu'a. Kuma duk Hure ce ta jawo".
Habibu ya yi kankan da murya ya ce "A gaskiya Baba kai ma da naka laifin. Mai yasa idan Innar ta yi hukunci akan Mairon ba ka ketarewa? Yanzu sabida Allah kamar Mairo ace har yanzu ba ta shiga makarantar boko ba, sai yaushe? Sai karatun ya wuce lokacinta? Fisabilillahi ina matukar takaicin rayuwar Mairo. Ina tausaya mata, domin dai ita 'ya mace ce, gidan wasu zata je ba da jimawa ba.
Babu mijin da zai iya zama da ita da wannan rashin tarbiyyar wadda ni ba haka aka yi mun ba".
Ya yi shiru kamar zai yi kuka, zuciyarshi na matukar kuna.
Malam Bedi da alama zancen Habibu na shigarsa. Ya ce "Yanzu ni me zan iya akai Habibu? Ba karamin abu ba ne Hure ta amince akai Mairo makarantar book ba. Ni kuma bana son tashin hankali balle abin da zaya bata mini rai, ina zamana lafiya".
Habibu ya dubi mahaifinsa cikin ido, ya ce "Shin Baba kai ko Inna wa ke auren wani?"
Malam Bedi ya ce
"Ni ne".
Ya ce "To matukar kai ke da iko da ita dole ka ba ta umarni. Kuma dole ta bi idan dai ita matar kwarai ce. Ka daina tsoron sababinta, kai ma ka bude mata murya. Ita ma ta iya ta bude maka makogwaro balle kai?"
Ya yi murmushi ya ce "To yanzu me za a yi?"
Ya ce, "Ni zan je na samu hukumar makarantar in musu bayani har halayenta duka zan fada musu, don su yi hakuri da ita, su kuma san matakin da za su dauka a kanta idan ta gudo ba tare da sun yi la'akari da fadan Inna ba. Ga kuma makarantar islamiyya da na ga yara suna zuwa da hijabinsu da uniform, nan ma zan je in ba da sunanta su sanyata ajin da ya dace da ita.
Kai kuma aikinka shi ne ka tabbatar tana zuwa akan lokacin, da son ranta da na Innar ko babu?"
"Malam Bedi ya ce "Sha Allahu za a yi kokari. Allah dai Ya yi maka albarka Habibu, idan ban da kai dan uwanta wa ya damu da ita balle har ya ce a sanyata makarantar?"
Habibu ya ce "Sai abin da ya kawo ni, amma ina ganin mu samu gindin bishiyar can mu zauna, maganar ta zaune ce".
Malam Bedi ya ce "Inji dai ALHERI ne?"
Ya ce "Alheri ne, idan Allah Ya so Ya yarda, kai ma ka yarda".
Suka samu kututturen bishiyar wata goriba mai duhu da inuwa mai sanyi suka zauna. Malam Bedi ya tattara dukkan hankalinsa akan Habibu, yana zake da son jin mai zai fito daga bakinsa. Shi kuwa Habibun in banda addu'ar neman rinjaye babu abin da yake dannawa Malam din daga zuciyarsa.
Malam Bedi ya ce
"Kai na ke saurare, kuma ka yi shiru".
Habibu ya ce "Eh to, dama Alhaji ne ya ce in zo in shawarce ka, ko kuwa in nemi izninka, idan ka yarda shi ke nan. Idan ma ba ka yarda ba babu damuwa sai na hakura".
Ya ce (a dan kufule) "Wai mene ne ka ke ta kwana-kwana? Daga ji ba abin arziki ba ne, don abu idan na arziki ne ba a kumbiya-kumbiyar fadarsa".
Ya yi murmushi ya ce "Yi hakuri Baba. Wani abu ne na zamani ya shigo mana cikin na'ura mai kwakwalwa wai shi yanar-gizo (internet). Ta cikinshi babu inda ba zaka sadu da shi ba a duniya. To rannan ina lalube na, sai na ci karo da tallan wata makaranta a Malaysia suna neman dalibai. Kamar da wasa na cike form dinsu na tura musu.
To kwatsam har na manta, shekaran jiya sai ga sako sun turo cewar sun dauke ni, na zo na biya kudin makaranta na fara karatu. Na samu Alhaji na fada masa, ya tayani murna kwarai, to amma shi kansa ba ya da kudin da zai iya daukar nauyin karatun, amma yace zai yi min hanyar da zan mika neman taimako daga gwamnati ta hanyar wani abokinshi mai baiwa gwamna shawara akan harkokin matasa wai shi ALHAJI GAMBO ADO, kuma ya tabbatar min za a samu insha Allahu, ragowar shi Alhajin ya yi alkawarin cikasawa daga aljihunshi.
Shi ne ya ce na zo na fada maka tun kamin komi ya yi nisa, kada sai an gama wahala ka zo ka ce ba ka yarda ba. Yanzu kuwa ba abin da aka yi, sai da amincewarka".
Shiru Malam Bedi ya yi kamar ruwa ya cinye shi, yayinda Habibu ya ci gaba da jifansa da, "Innahu ala raja'ihi la-kadir". Bai gushe ba yana maimaita addu'arsa sai jin muryar malam Bedi ya yi tana tambayarsa har tsayin shekaru ko watanni nawa za a yi ana karatun?
Ya yi godiya ga Allah a zuciyarsa, domin da alama akwai nasara, ya ce "Abin ya fi karfin watanni. Shekaru shidda ne zan yi ina karatu akan na'ura mai kwakwalwa".
Malam bedi ya ce "To daga nan kuma fa?"
Habibu ya murmusa ya ce "Sai na dawo gida na nemi aiki".
Malam Bedi ya ce "A'ah, ba haka nake son ji ba, sai ka dawo ka yi aure ka tara min 'ya'yan da ni Allah bai bani da yawa ba".
Habibu ya sunkuyar da kai yana murmushi, ya ce "Insha Allahu Baba".
Malam Bedi ya ce "To ka je, Allah Ya tabbatar da ALHERI……....."
Dai-dai nan Habibu ya ji “tim!” A tsakiyar kansa an nannako masa katuwar goriba a tsakar ka. Kwakwalwarsa ta daure, kansa ya yi dumm!! Kamar an kwala masa dutse. Wata azaba ta ziyarce shi tun daga tsakiyar kansa har yatsar kafarsa. Kamin ya gama farfadowa daga takaitaccen suman da ya yi, sai jiyo zazzakar muryarta yayi kamar zata tsige masa dodon kunnuwa tana fadin "Yaya Habibu sanya min a aljihunka, nawa aljihun bujen ya cika……..".
Suka daga kai su duka biyun suna kallonta, Mairo ce kwance abinta akan reshen bishiya, a kalla ta fi karfin awanni biyu akan bishiyar. Tunda liman ya tada kabbarar sallah ta yi raka'a daya ta dago, ta hango goshin kowa a kasa, babu mai kallonta, ta yayibo tabarmarta da zummar tahowa gida. Sai kuma ta hango nunannun goriba ai kuwa ta daka tsalle ta dare.
Duk abin da suke cewa akan kunnenta, sai dai ba wani fahimta ta ke yi ba sabida hankalinta ba ya jikinta. Ita dai tana tsinkar goribar ta gutsira ta ji idan da zaki ta sa a buje, idan ba zaki ta cillar. Sai da bujen ya cika ne ga shi kuma ba ta iya barin wannan zazzakar, ta cillowa Habibu ajiya.
Ya bude baki da kyar ya ce "To sauko mu tafi".
Ta ce "Bari na tsinkowa Baba".
Ya ce "A'ah, shi baya da karkon hakori".
Ta kamo reshe bayan reshe tana bin jikin bishiyar cikin kwarewa har ta sauko suka taho gida.
A ranar da ciwon kai ya kwana, amma bai daina yi wa malam Bedi magiya da naci akan makarantar Mairo ba, ko baya nan. Malam din ya yi masa alkawarin kada ya damu, da yardar Allah kamin ya dawo Mairo ta kimtsu.
Washegari ya je ya ba da sunanta a makaranta aka sata aji uku. Ya yi musu bayaninta dalla-dalla wani malami da yake makocinsu ne ya ce ya san Mairo farin sani, ko shi yana takaicin rashin sa ta makaranta, to amma kowa ya san sababin Inna Hure, idan dai akan Mairo ne, shi yasa kowa ya sa mata ido. Amma insha Allah zai tsaya a kanta kamar yadda zai tsayawa 'yar cikinsa.
Habibu ya yi godiya mai tarin yawa, ya nemi taimakonshi a kan ya taimaka ya bayar a dinka mata uniform, ya kirgo kudi ya ba shi har na littattafai da jakar makaranta. Sannan ya nufi islamiyyar yaran Gurin-Gawa, nan ma ya ba da sunanta. Sun tabbatar mishi ba komai ai irin su Mairon ake son a gyara.
Hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya ga Mairo ranar litinin cikin kayan makaranta da jakarta a rataye ta tafi makaranta. Duk da Inna Hure na kumbure da shi, bai damu ba, tunda ya cika kudurin da ya dade yana damun zuciyarsa. Don haka koda ya je yi mata sallama zai komo Kano ta yi masa kunnen uwar shegu.
Hure ta ga tijarar Malam Bedi irin wadda ba ta taba gani ba, ba ta kuma taba tsammanin ya iya ba, domin cewa ya yi idan Mairo ba zata je makaranta safe da yamma ba, to dukkaninsu su zo su fice masa a gida, su tafi duk duniyar da za su.
Ba ta yi magana ba, amma a cikin ranta tasan wannan aikin Habibu ne, don yadda Malam din ke jin maganar Habibu ko ubansa sai haka. Abin da ta ce da shi kawai shi ne, "Saboda ka tabbata tsohon bakauye ka zauna dan ka ya fi karfin ka".
Ya ce "Eh, koma mai zaki ce ki ce, amma Mairo da uwarta ba su zama min cikin gida muddin Mairo ba zata nemo ilimi ba. Me ye marabarta da dabba? Babu! Dabba ce aka sani da hawa bishiya da cin abincinta daga 'ya'yan itace, amma ba dan mutum ba".
Habibu ya karkace kai ya yi ta ba Innarshi hakuri, ya ce "Inna ku yarda da ni, ba ni da nufin cutarku, sai dai ma na yi kokarin ganin duk abin da zai zamto cuta a gare ku na yake shi iya karfina. Ina nufin Maironki da alheri ne, bayan wannan ba wani abu. Ke da kanki wata rana za ki gane gata na yiwa rayuwar Maryam. Don Allah Inna ki sauko ki yafe min, kisa min albarka!".
Zuciyarta ta yi sanyi lakwas, ta ce "Ai shi ke nan, nasan iyakar gaskiyar ke nan, laifina shi ne, ina son Mairo da yawa".
Ya yi murmushi ya ce "Hakan ma ba laifi ba ne. Sai dai ki yi kokari kada son da kike mata ya sa ki kasa lankwasata. Ni ma ina son Mairon ki, son da bana yi wa kowa a duniya, amma idan har da gaske ina sonta, dole in inganta mata rayuwa da gishirin zamani, wanda idan babu shi miya duk dadinta lami ce. Wannan gishirin kuwa ba komi ba ne, face wannan ilimin dana ke so Mairo tayi. Shi ne zai haskaka mata ragowar bangarorin rayuwarta, tasan kanta, tasan inda ta sa gaba.
Amma a yanzu wallahi Mairo ba ta da maraba da 'ya'yan birrai".
Dariya Inna ta yi, ta ce "To Allah Ya taimake mu ta kimtsu".
Ya ce, "Amin--amin, ko ke fa Innata? Ni ma karatun zan tafi..." Ya warware mata zare da abawa.
Ga mamakinsa sai ya ga damuwa karara ta bayyana a kyakkyawar fuskarta, ita da a kullum, ta ke nuna ba ta damu da shi ba. Ya shiga kwantar mata da hankali cikin tausasan kalami, yana nuna mata shekaru shida kamar yau ne, idan da rai da lafiya. Da kyar ya samu ta sa ma abin albarka.
Da wannan Habibu ya koma Kano ya ci gaba da shirye-shiryensa, da taimakon Baffansa. Cikin watanni uku kacal komi ya kammala, ya zo wa iyayenshi sallama.
Ya ji dadin yadda ya ga Mairo cikin wankanta fes! Ba ta kuma yi masa wannan damuken oyoyon ba, an fara nutsuwa ke nan.
Ya yi murmushi, ya ce, "Mairon Inna 'yan makaranta, ya ya dai?"
Ta yi murmushi ta kawar da kai ba ta ce komi ba. Ya kamo hannayenta ya ce "Ba ki ga yadda kika soma sauyawa ba? Ina fatan duk runtsi za ki dage da zuwa makaranta? Zan tafi karatu Mairo, sai Allah Ya dawo da ni kimanin shekaru shidda a nan gaba. Ki kula da Innarki, ki dinga tayata aiki, ba wasan 'yar bebi ba kin ji Mairo nah?"
Ta shiga damuwa sosai, nan da nan sai ga hawaye rau-rau a idanunta. Ta ce "Yanzu Yaya Habibu shekaru shidda zan yi ban ganka ba? Ina zaka je? Mai yasa ba zaka ci gaba da zama gidan Baba Abbas ba kana zuwa makarantar a can?"
Ya ce "Kamar yau ne Mairo za ki ga na je na dawo, idan dai da rai da lafiya. Ki kula da kanki, ki dinga wanka kullum, ki dinga yanke akaifarki ta kafa da hannu duk sati. Ki kuma dinga wanke gashin kanki shi ma duk sati, kin ji?"
Ta ce, "Na ji Yaya Habibu, Allah Ya dawo da kai lafiya".
Ya ji dadi sosai, bai zaci Mairo tana da dan hankali ba ko yaya ne, har ta yi wa mutum addu'a. Ya sa hannu a aljihunsa ya ciro naira ashirin ya bata, ta yi ta murna ta je tana nunawa Innarta.
Haka Habibu ya tafi cike da tunanin Mairo. Yana addu'a, Allah Ya sa ta dore da hakan. Watau turbar da ya sanyata.
Washegari ya tashi zuwa Malaysia, inda ya samu gurbi a Unibersity of Malaya.
Ya sha wuya matuka kamin ya samu ya mance da tunanin gida. Da taimakon abokinshi Amiru wanda shi ma dan Kano ne ya samu ya soma fuskantar karatun, amma babu ranar Allah da zata fito ta fadi bai tuna Mairo ba.
***
BAYAN TAFIYAR HABIBU
Malam Bedi tsaye yake akan kafafunshi kan karatun Mairo don cika alkawarin da ya daukarwa Habibu. Da taimakon Allah Mairo ta saba da zuwa makaranta, kuma lokuttan makarantar sai ya shafe lokacin da ta ke samu ta hau bishiya ko ta yi wasan 'yar tsana.
Idan ta dawo makaranta karfe daya na rana wanka zata yi ta ci abinci, ta yi sallah. Karfe biyu cikin ajinsu na islamiyya ya ke mata. Ba kuma za su taso ba sai goshin magriba, don haka ranakun alhamis da juma'a da yamma kadai ta ke samun hutu. A cikinsu kuma tana tare da Innarta suna ayyukan gida wadanda ta alkawarta wa Yaya Habibu taimakawa Innar.
Rannan Mairo na surfen masara Inna Hure tana bakacewa, Mairo ta aje tabaryar ta ce "Oh Inna, Yaya Habibu yau watanninsa bakwai ke nan, yana can a cikin Turawa".
Inna ta ce "Wa ya ce miki a Turai yake? Kasar Larabawa ne".
Mairo ta yi murmushi, ta ce "A'ah Inna, rannan na tambayi malaminmu na makarantar book, a ina Malaysia ta ke? Ya ce min Asia ne, can wajejen India da Pakistan".
Inna ta kama baki ta ce "Ke Mairo, yaushe kika iya Turanci haka?"
Mairo ta ce "Ba Turanci na yi miki ba Inna, sunan kasashe na fada miki".
Wani dadi ya kama Inna Hure, ba tasan sanda ta ce "Kai Allah Ka sakawa Habibu da alheri”
MARYAM BEDI, ta ci gaba da karatunta cike da himma da kwazo. Takan sanya wa ranta cewa, kawai Habibu na kallonta, yana jin dadin kwazonta. Yana kara mata karfin gwiwa. Ba ta yarda wai shekaru shidda zai yi bai dawo ba. A ganinta shi ne Habibu na iya dawowa yau, ko gobe, don kawai ya rutsa ta, ya ga irin kwazonta.
Saboda haka cikin shekara guda kacal, Maryam Bedi, ta zama zarrah a ajinsu na boko, kan gaba a ajin islamiyyah, wadda ke da haddar izfi ashirin na Alkur'ani a cikin kanta.
Sauran littattafan addini kuwa idan ta bude su tana karantawa tana fassarawa Inna tsarki da alwala, da irin sallar khashi'ai da sallar da ake dunkulewa a jefowa bawa kayarsa, tun kamin ya tashi akan dardumarsa. Sai Inna ta sa habar zaninta tana share hawaye, ta ce "Ba karamar cuta na so na yi miki ba Mairo".
Shekaru uku ke nan cif da tafiyar Habibu, kuma a yau ne ranar saukar su Mairo. Ta sha wanka da sabon dinki na atamfa (hitarget) da suka yi anko gaba dayansu. Ta dora wani sabon farin hijabi akai, wanda ya tabo har gwiwarta. Ta azalzali Innarta ta yi sauri ta gama shiryawa su tafi kada wajen zama ya cika ta rasa inda za ta zaunar da ita. Innar kuwa sai sake murza kwalli ta ke a idanunta yadda zata fito radau!
Ta kuwa fito din, sai kyallin wanka da basilin ta ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu'ar samun nutsuwa cikin zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al'ummar kauyensu wadanda ake nufin ta yi karatu a gabansu.
Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba, yana ta ware ido don ganin ta inda Mairo zata bullo.
Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar da ita, sannan ta karasa cikin 'yan group dinsu suka yi sansani.
Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu'a, daga limamin garin Gurin-Gawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur'ani cikin daddadar kira'arta kai ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi, wato ayar nan ta "Muhammadurrasulullah…...."
Gaba dayan jama'ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa aya aka dauki kabbara kowa na cewa "Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi".
Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce babar Mairo, sai gaisawa suke da ita. Yayin da 'yan bakin-ciki, wato wadanda ke da 'ya'ya a makarantar ba a kuma kirawo 'ya'yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai an tsikari kakkausa.
Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban karamar hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi tiryan-tiryan cikin kira'ar da ta fi ta malamin.
Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da'a a gaba dayan daliban shekararsu. A sa'ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin gabatar da jawabinsa na babban bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi
"Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren 'yammata ta gwamnatin tarayyah da ke Minjibir".
Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa kansa don farin ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da Chairman.
Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara daurewa. Ta shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu. Malam Bedi ya gabatar musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da zana jarrabawar fita firamare. Ya kare da cewa.
"Amma fa makarantar ta kwana ce".
Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce "Haba Inna, wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san Lanto ma ta gidan Kado tana makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke. Sannan bayan kowanne wata ana zuwa ziyara".
Inna ta ce "To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?"
Ta ce "Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki".
Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi hakuri har ki zo hutun".
Mairo ta yi murmushi ta ce "Shi ke nan Inna".
Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin dan uwansa. Bai sani ba ita a ra'ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su sake yin yunkurin rabata da Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna gida zaman jiran sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman. Cikin sati uku sai ga takardar daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na shekarar.
A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa ya kuma gaya masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya kuma ba shi katifar Mairo da filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe.
Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta daka mata kuli-kuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta yi sha'awa ta kwada ta ci, kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki da sabulun wanka. Man shafawa da man kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya sun hadu sai tafiya.
A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun dama cikin dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne.
Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta Minjibir, don haka tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman ya cika shi da abin arziki duk don ya kula da karatun Mairo.
Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo, malam Bedi rike da dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce da Bedi daga wannan zuwan da zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don haka ka dinga kula da duk abin da na yi".
Malam Bedi ya ce "To, angode dai".
Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar Bata/Kuroda. A nan suka hau motar Minjibir, Mairo a maleji su kuma a kujerun gaban motar. Tafiyar awanni biyu ta kawo su Minjibir, aka sauke su a tasha. Daga nan suka hau tasi aka kai su har kofar FGGC. Suka gaisa da maigadi, suka ba shi ajiyar kayan su suka karasa cikin makarantar. Jikin Mairo ya yi sanyi matuka ganin irin tsaleliyar makarantar da aka kawo ta.
Ta daga ido tana hangen dalibai cikin kayan makaranta iri daya, cikin tsari da nutsuwa. Kowacce a nutsenta ta ke tsaf, tana tafe cikin kamala. Ba ka jin hayaniyar komi sai sautin malamai suna koyarwa cikin azuzuwa, shi ma din a tausashe.
Mairo ta kalli kanta sama zuwa kasa, ta hango bambanci a farrake tsakaninta da irin jefi-jefin daliban da ta ke ganin suna wulgawa.
Gabadaya sai ta ga kanta kamar wata almajira, duk da kuwa ta kure adaka, ta sha lalle. Ga jambaki jawur ta rambada ta yi kuma jagira da digo a tsakiyar goshinta. Duk da hakan ba ta ji ko dar na zama a wannan makarantar ta yi karatu ba. Ta yi tunanin cewa, ba wannan ne abinda ya kawota ba, darasin da za a koya mata ne, Yaya Habibu ya dawo ya yi alfahari da ita.
Suka tambayi ofishin shugaba aka nuna musu. Kai tsaye can suka dosa, Mairo na kallon yadda daliban wani aji da babu malami a ciki suka yi cincirodo a taga suna kallonta. Sai hankalinta ya tashi matuka, don haka har ta riga Hedimasta tura kai ofishin shugaba, don dai ta tsira daga kallon wadannan yara.
Shugaban makarantar Halima Dukku, ta yi tsai da ranta ta cikin gilashinta tana kallon harbatsatstsiyar dalibar da aka kawo mata. Ta jinjina kai ba tare da ta tofa ba, ta karbi takardun hannun Hedimasta ta sa hannu bayan ta duba ta kuma shigar da sunan Maryam Bedi cikin jerin daliban da makarantar ta karba a wannan shekarar. Ta sa aka ba ta uniform, house-wear da sauransu. Ta kalli takalmin da ke kafar Mairo ta ga silifa ne, wani bakikkirin da shi, ya kuma hadu da wata kafa jawur kamar gauta. Ta ce ba sa ba da takalmi don haka aje a sayo mata sandal ko cambus.
Hedimasta ya ce su yi masa alfarma ya bada kudin a siya mata, su baki ne a garin ba su san ko ina ba. Ta kira leburanta, ta hadasu dashi, ya gaya masa sandal dari takwas ne, kambas dubu daya da dari biyar mai saukin kudin kenan. Gabadayan su shi da Malam Bedi suka hada baki suka ce, "Mai ka ce?"
Ya sake maimaitawa. Malam Bedi ya hau salati amma shi Hedimasta da yake da dan karatunsa na yaki da jahilci sai ya ce"Au to, ba mu sani ba ne, domin yanzu a aljihuna kwata-kwata naira dari hudu ne, ga shi a ciki zamu hau mota. Amma ga wannan". Ya mika masa dari biyu, ya ce, "Ko irin na dankon nan ne mai igiya a saya mata idan zata dawo sai a nemo".
Haushi ya ishi leburan ya juya zai fita abinsa, shugaba ta yi gyaran murya ta dauko gudar naira dari biyar guda hudu ta mika masa, ba tare da ta ce komi ba.
Malam Bedi ya dinga zuba mata godiya, ta ce, "Babu komi, ai da na kowa ne". Ta sa aka kira mata wata prefect ta hadata da Mairo da kayanta gami da littattafai wadanda suke cikin kudin makarantarta, amma babu jaka, ta ce su sayo mata daga baya, ta ce ta kai ta hostel.
Sai a lokacin ne kuka ya zo wa Mairo, shi ma Malam Bedi duk da dauriyarsa sai da ya sa habar babbar rigarsa yana share hawaye. Suna dagawa juna hannu har su Mairo suka kule cikin hostel.
Bayan prefect din nan ta damka Mairo a hannun house-captain dinsu sai ta koma aji. House-captain ta nunawa Mairo dakinsu ta ba ta gado ta shimfida katifarta ta ce, to ta sanya uniform ta tafi aji don kowa yana aji. Sai dai fa a ranta tana mamakin yadda aka yi wannan bakauya ta zo makarantarsu.
Mairo ta tube kayanta ta sanya na makaranta ta bi bayan captain har ajin da aka ba ta, wato JSS 1A. Ta je staff room ta nemo class master dinsu ta hada shi da Mairo, ta koma nasu ajin.
Mairo ta yi tsuru a gaban allo, a lokacin da Uncle ke gabatar da ita a matsayin sabuwar daliba a ajin. Abin da Mairo ta lura da shi shine, gabadaya 'yan ajin wani irin kallo suke mata na raini da kyama, suna kyabe baki duk sai ta ji ta muzanta.
Uncle ya nuna mata kujerar zama gefen wasu fararen yara 'yan gayu guda biyu, da ba su fice tsaranta ba. Ai kuwa suka soma matsawa jikin junansu suka takure suka ba ta katon fili.
Malamin ya lura da irin karbar da Mairo ta samu a ajinsa, duk sai ya ji tausayinta ya kama shi. Ya dube ta ya ce, "Sake gaya min sunanki, ban gane abin da principal ta rubuta sosai ba".
A hankali ta bude dan kankanin bakinta ta ce
"Maryam Bedi".
Ya ce "What a nice name, maryama, saki jikinki ki zauna a inda na umarce ki. Ba ruwanki da kowa sai abin da ya kawo ki, kina ji na?"
Ta gyada kai, amma ba ta amsa ba.
Ta karasa inda ya nuna mata ta zauna a darare. Yarinyar kusa da ita ta ja tsaki, tsuuu! Ta murguda baki ta juya mata keya. Ta dauki tulin littattafanta ta zura su cikin lokar kujerarta tunda ba ta da jaka.
Uncle ya fita cike da tunanin wannan yarinya. Yana daga cikin malaman da ba sa son ganin rashin walwala ko yaya daga dalibansu. Abin da ya lura shi ne, Maryama ta shigo makarantar da ta fi karfinta. Ya fi kowa sanin girman kai da ji da kai na daliban FGGC don haka ya samu kansa da tausayin 'yar yarinya, Maryama.
Ya alkawarta wa ransa taimaka mata iyakar iyawarsa, har sai ya ga ta saki jikinta tamkar sauran dalibai ‘yan uwanta.
Da aka tashi daga aji Mairo ba ta san dawar garin ba. Ta dai ga kowa na fita da littattafansa babu wanda ya kulata, kai ba ta ma ishi kowa a ajin kallo ba. Sai ta kwaikwayi yadda suka yi, wato ta kwaso littattafanta masu yawa da matukar nauyi ta nufi hostel kamar yadda ta ga sun yi.
Tana shiga dakin sai ta ga wadannan fararen yaran sun rigata isa har sun tube uniform sun sa na hostel, ashe su ma a dakin suke. Suna ganinta ta shigo suka kara yin kicin-kicin da fuska kamar an aiko musu da sakon mutuwa, musamman da suka fahimci a kusa da gadonsu ta ke.
Dayar ta yi tsaki ta canza harshe tana cewa da kawarta, "See this girl, i donno what she is looking for here..."(kalli wannan yarinyar bansan me take nema a nan ba).
Kawar ta ce, "Kaddararmu ke nan, daki daya, aji daya, mts!"
Jikin Mairo ya kara yin la'asar, amma sai ta dasa wa ranta ta rabu da wadannan yaran ta yi abin da ya kawo ta. Ta ajiye litattafanta ita ma ta tube uniform tasa na hostel irin wanda taga sun sanya, ta nufi famfunan da ta ga ana alwala, ita ma ta yi ta nufi masallacin da ta ga ana shiga da sauri ta samu jam'in sallar azahar.
Da aka fito yunwa ta addabe ta, ta soma tunanin ta je ta kwada kwadon kwaki sai ta ji wata senior na fadin a fita ‘dining’ za’a rufe hostel. Ta dinga maimaita kalmar 'dining' a ranta, ko mene ne? Ta ga dai kowa fita yake yi sai ta bi bayan wasu yara ba tare da sun san binsu ta ke ba, har zuwa wani katon dakin cin abinci inda ta ga dalibai a zazzaune kowa da filet dinshi ana ta cin abinci.
Yawun bakinta ya tsinke, ta bi layin da ake bi a karba ita ma ta karba, jallof din shinkafa ce da yankan nama biyu da soyayyar ayaba (plaintain) sala uku. Ta zauna ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta yi hamdala ta mike ita ma ta nufi hostel ta kwanta a gadonta don ta huta zuwa la'asar.
Da aka yi sallar la'asar kuma suka koma aji zuwa karfe shida. Haka dai ta yi ta bin abin da ta ga ana yi, har lokacin barci.
A sannan ne ta samu damar kwashe kayanta da ke cikin (Ghana Must Go) ta jera a loka, kamar yadda ta ga kowa ya yi. Yaran nan makotanta suka fito da wani irin abu cikin kwali da ba ta taba gani ba suna ci, suna korawa da lemon gwangwani suna hira da Turanci, suna kallonta, ita da kullin kayan kuli-kulinta suna ta dariya. Duk ta bi ta sha jinin jikinta, amma ba ta daga kai ta kalle su ba, ta jika ramarta cikin 'yar robarta ta ajiye akan lokarta tana jira ta jiku ta kwada da kuli.
Tana ganinsu har lekowa suke da kai suna leka robar ta, amma ragowar jama'ar da ke dakin ba ruwansu da ita, kowa gararin gabansa yake yi. Ta rasa dalilin wadannan yara na sa mata ido da wulakanci a gare ta, daga baya ta fuskanci daya sunanta Nabilah, daya kuma Kausar.
Ta kwada ramarta ta ci ta koshi, ta sha ruwa ta kwanta a katifarta da ko zanin gado babu. Ta rufa da zanin atamfar Innarta, wadancan yaran kuwa irin bargonta da hedimasta ya cinye suka rufa da shi. Hatta filon ya dauke ya cinye saboda rashin tsoron Allah irin nasa. Aka yi (light-off) na gabadayan hostel din, ta shafe jikinta da addu'o'i ta kwanta.
Washegari da aka yi sallar asubah ta ga kowa yana bin layin wanka, don haka ita ma ta bi ta yi wankanta ta yi sallah a masallaci tare da Imam. Daga nan aka tafi aji.
Suna shiga aji ta ga mutanenta sun dauke bencin gabadaya sun maida shi wurin da ba kowa sun zauna, sun kuma kira wata yarinya sun zaunar da ita a wajenta. Ta rasa inda za ta zauna, ta koma karshen ajin ta sanya littafinta daya a kasa ta zauna akai. Zamanta da kamar minti biyar Uncle din ajin ya shigo. Yana ta jefa ido ya hango Mariaman da ya kwana ya tashi da tunaninta jiya, amma bai ganta ba.
Gabadaya ajin aka mike, ita ma sai ta mike kamar yadda suka yi, suka hada baki gabadaya suka ce "Good morning Uncle".
Ya ce, "Morning class, how are you all?"
Suka sake hada baki gaba daya suka ce "We are fine Uncle". Sannan ya yi umarni da a zauna.
A sannan ne ya hangota makure a can layin karshe kamar mujiya, kuma a dandaryar kasa. Bai ce komi ba ya bude rajista ya yi kiran lambar kowa, ya amsa, sai a karshe ya ce "No. 40". Shiru ba a amsa ba, a lokacin ya gane lambar Mairo ce, sai ya ce, "Mariama daga yau ke ce no.40".
Ta ce "To".
Ya rufe rajistar ya dinke fuska sosai, ya ce
"Kausar!"
Ta amsa, "Yes Uncle".
Ya ce "mene ne dalilinki na janye benci ki hana Mariama zama?"
Ta yi shiru ba ta amsa ba.
Ya dubi dalibar da suka zaunar a wajen, "Ke Laila ina wajen zamanki? Me ya kawo ki nan?"
Ta yi saurin mikewa ta koma wajenta.
Ya ce "Kausar fito nan".
Ta fito tana gatsina ita a dole ga 'yar masu kudi. Saura kadan ya zabga mata mari, sai dai ya yaki zuciyarshi ga yin hakan, ya ce ta fita waje ta yi kneel down, har zuwa lokacin break.
Ta cika ta yi fam, kamar balam-balam, dama ga ta buleliya. Ta zobara baki, ta ce "Ai ba ni kadai na janye bencin ba, har da Nabilah".
Nabilah ta ce "Wallahi Uncle babu ruwana, ita ce ta ce wai ba zata zauna da billager ba".
Bai yi mamaki ba, sai ya bude murya yana tambayar 'yan ajin "Shin dama akwai banbanci tsakanin musulmin kauye da musulmin birni?"
Suka ce "A'ah Uncle".
Ya ce "To me ye laifin wannan yarinya da kuke kyamarta?"
Wasu daga ciki suka hau matsawa suna cewa "Ta zo ta zauna a kusa da mu".
Amma Uncle sai cewa ya yi, babu inda zata zauna sai bencin su Nabilah, don haka idan Nabilah da Kausar baza su zauna tare da Maryama ba, sai dai su koma gidan ubansu.
Mairo dai na sauraron ikon Allah. Tana tunanin yadda ta ke abar so a wurin Innarta da Babanta, amma wai yau ake takaddama akan inda za ta zauna sabida ita an ga alamar ba ta da arziki.
A lokacin ta ji wata zuciya na shigarta (determination) akan rayuwa. Ta alkawarta wa ranta idan ilimi na kawo arziki, to zata neme shi ko don 'ya'yanta. Za ta nemi ilimi har sai ta ga karshensa, idan har ana gani. Ba zata so a yi wa danta irin wannan wulakancin ba. Uncle ya lura Mairo kuka ta ke yi, sai zuciyarsa ta karye. Don haka tunda ya gama kiran lambar sai ya fita, bayan ya tabbatarwa Kausar kada ta sake ta bar kneel down din da yasa ta har sai ya dwo.
Malamin maths ya shigo ya fara ba su darasi, Mairo ta tattara hankalinta akan malamin gabadaya, ba ta damu da hararar da Nabilah ke mata ba. Ya gama ya fita, sai ga Uncle ya dawo wanda kuma shi ne yake daukarsu darasin Turanci.
Yana koyarwa, amma rabin hankalin sa na kan Mairo. Ya lura sabanin ragowar ‘yan ajin, Maryama ta ba shi dukkan 'attention' dinta, da wani muradi cikin kwayan idanunta. A zahiri wannan yarinya bakauyiya ce lakadan, amma ga dukkan alamu, ba haka Allah Ya yi nufin barinta ba.
Ya kammala darasinsa ya ba da aiki 'Essay Writting' mai take guda uku, ya ce kowacce ta zabi wanda za ta iya yin sharhi a kansa. A rubuta a kawo masa washegari. Hankalin Mairo ya tashi, domin dan ilimin nata bai kai nan ba. Magana ce ake so su rubuto da harshen Turanci akalla shafi daya da rabi na littafi.
Aka kada kararrawar fita break, amma Mairo ba ta yi niyyar fita ba. Ta kurawa aikin 'assignment' dinta ido tana tunanin ta inda za ta bullo. Ba ta ankara ba ta ji wani sassanyan kamshi na dukan hancinta da kuma alamun zaman mutum a bencin gabanta. Ta dago a hankali tana kallonsa, Uncle ne.
Ya ce "Yaya dai Maryama, kowa ya fita cin abinci, amma ke ban ga alamar kina da niyyar fita ba?"
Ta sadda kai cikin kankanuwar murya ta ce
"Ina tunanin yadda zan yi aikin da ka bayar ne".
Ya yi murmushi ya ce "Aiki ne kuwa mai sauki, amma ga wanda ya gane tambayar. Wacce tambaya kika dauka a ciki?"
Ta sunkuya tana kara nazarinsu, ta ce "Ina ganin ta daya za ta fi mun saukin amsawa, tunda daga karkara na ke, 'Yadda ake bikin sallah a karkararmu".
Ya yi murmushi, ya ce
"Ni kuwa sai na ga tambaya ta biyu zata fi dacewa da ke 'Ranata ta farko a sakandire', za ki kawo 'points' sosai wanda zai taimaka ki yi 'scoring' maki mai yawa. Kinga sauyin abubuwa da dama, a zuwanki babbar makaranta. Haka ne ko ba haka ne ba?"
Ta yi murmushi, wanda ya lotsa kumatunta hagu da dama. Akwai wani asirtaccen kyau a tare da Mariama, wanda rashin gyara da rashin gogewa ya boye shi. Yarinya ce kamar diyar Larabawa, sai dai fatarta a dafe ta ke, kamar an shafa mata shuni, wanda kai tsaye ya banbantata da sauran yaran makarantar.
Ta ce "Haka ne Uncle. Na gane cewa, ashe mu ba mutane ba ne, ababen kyama ne ga wasu jinsin al'ummah. Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni 'yar talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma idan da ace ni ce a matsayin mai shi din, ba haka zan yi wa mara shi ba!".
Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke tun daga karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne.
Ya ce "Mariama!"
Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba.
Ya ce "Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da kika gani a duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san darajar kansa ba, bai san ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi tunani ko ya ya cewa, kai wani ne, to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji.
Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda da cewa, sai wun fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su gare ki. To akan me za ki yi tunanin sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron Allah!”.
Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce "Uncle kana nufin ni ba abun kyama ba ce?"
Ya girgiza kai "Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga gyara kanki, sai kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo nema ba, ilimi kika zo nema, irin wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa ba su fi ki kokari ba".
Ta yi murmushi ta ce "Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka yake yi min irin maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da zai yi ba".
Ya ce "Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta".
Ta washe baki ta ce "Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai in yi ta ganin kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta".
Ya ce "Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi alfahari da ke, amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba ne da ya wuce perserbearance (jajircewa) da ba da himma".
Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce "Na gode Uncle, kuma na yi maka alkawarin I'll persebere".
Ya yi mata tafi guda daya ya ce "Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya Habibu",.
Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce "Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?"
Murmushi ya yi, "A'ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi".
Ta ce "Galadanchi?"
Ya ce "Eh, kin santa ne?"
Ta ce "A'a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?"
Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka da yawan tambayarsa (curiosity).
Ya ce "Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga Kanawa. Duk wani Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu 'ya'yan cikinta muna alfahari da ita da kasancewarmu 'ya'yanta.
A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan 'yan bokon Kano, da mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin jihohi 'yan uwanta, to duk 'yan Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a cikin kansu".
Ta ce "Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi".
Murmushi ya yi "Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran dalibai, idan kun fito 'pref' da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani".
Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta.
Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu ya kara sanya mishi jin son taimakonta.
Mairo da ta fito 'pref' ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta 'essay' dinta mai taken 'My first day in secondary school'. Da jagwalgwalallen turancinta mara 'tenses' har haduwarta da Uncle a aji ta rubuta, inda ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce “shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba ra'ayinta ke nan ba.
Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta.
Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi 'assignment' din shi ba sai da period dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama Bedi. A zahiri duka 'yan ajin sun fi ta iya Turanci, da kula da 'tenses' sabida su sun sami kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To amma idea da ke cikin rubutun Maryam fasaha ce tsagwaronta.
Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana nuna mata kura-kuranta, tare da cewa "Matsalarki daya ce a Ingilishi (tenses), don haka darasinmu na yau tenses ne".
Nan da nan ya fara darasi inda Mairo ta dauki dukkan hankalinta ta likawa Uncle. A yau da aka fita break ma ba ta yi saurin fita ba, ta zauna ne tana aikin lissafi (maths). Uncle Junaid ya kwankwasa desk dinta, ta yi hamzarin dagowa kamin ta yi murmushi ta ce "Uncle dama ba ka fita ba ne?"
Ya ce "A'ah na fita, dawowa na yi. Tun daga staff room na hango ki kina rubutu, zuwa na yi na gaya miki ki daina zama cikin aji yayin da kowa ya fita. Komi na makarantar nan cikin tsari yake, yanzu lokaci ne na cin abinci ba na yin aiki ba. Idan wani bai ga abinsa ba yana iya cewa ke ce".
Ta rufe littafin ta mike ba tare da ta ce dashi komi ba. Ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ya ce, "Maryama".
Ta juyo cikin damuwa, ya ce, "Ina fatan ba ranki ne ya baci ba?"
Sai ta koma dariya, ta ce "A'ah Uncle".
Ya ce "To mai yasa kika yi shiru?"
Ta ce "Ka yi hakuri Uncle Junaidu".
Ya yi murmushi ya bi hanyar kofa shi ma ya na kissimawa a ranshi Maryam na daga cikin miskilan yara.
Cikin sati biyu kacal Mairo ta fahimci tsarin komi na makarantarsu, sai dai ma ta nuna wa wani. Babu ruwanta da su Kausar, duk kuwa da basu fasa yi mata izgilanci ba, a daki ne ko a aji. Sai dai su kansu sun san akwai wani aminci, ko kuwa shakuwa ta musamman tsakanin Maryam da Uncle, don haka basa yi mata a gabansa. Saboda Maryam Uncle Junaid ya kirkiro tutorial class da yamma da yake yi akan darasinsa English da darasin Uncle Wahhab (mathematics), wanda ba karamin taimakawa Mairon ya yi ba.
Duk wasu matsalolinta akan karatu Mairo ba ta shayin gayawa Uncle Junaidu shi kuma ya tsaya mata kamar Yayanta. Shi kansa bai san mai yasa ya tsani Kausar da Nabilah ba, tun daga ranar da ya lura sune kawai matsalar Maryama cikin makarantar.
Ita kuwa kullum kokarinta shi ne, ta boye abin da suke mata, kada ya gane. Don duk ranar da ya hora su sabida ita, idan sun koma daki akanta suke hucewa. Rannan da ya sa su noma sabida sun karya bencin ta karfin gaske, duk don kada ta zauna kusa da su, da suka komo hostel suna ta digar da gumi. Sun yi jawur sabida wahala, Kausar ta yi kuka ta ce "Wai Nabilah wannan bakauyar kanwar uban Uncle ce ne?"
Nabilah ta ce "A'ah, ina jin tare aka haife su, don shi ma da alama dan talaka ne ya soma daukar albashi ya je ya sayo gwanjo yana zanzarewa".
Kausar ta ce "Uban wa ya gaya miki? Abokin Yayana ne tare sukai karatu, dan chief justice Atiku Galadanchi ne. Har gidansu na sani sanda muka zo Kano daga Jos da Yaya Yusuf bikin wani abokinsu, abin da na kasa ganewa shi ne, mai wannan billager din ta ke gaya masa yake damuwa da ita? Ni kam da nasan har da irin wadannan a makarantar nan ai da ban yarda Daddy ya kawo ni ba".
Nabilah ta ce "Ke kika ga zaki iya, amma ni nan idan an yi hutu bazan dawo ba, Edcel collage zan koma. Minjibir ta rube, ta zama ta yaku-bayi".
Suka kwashe da dariya, Mairo dai na jinsu ba ta dago ta dube su ba, sai rubutunta ta ke kamar alhudahuda.
Ranar ziyarar 'yan makaranta, wato bisiting day ta zo. Kowanne dalibi ya sha wanka ya yi fes, ya fito neman nasa. Mairo dama ba ta sa a ka ba, tasan Babanta da Innarta duka ba su san da wata ranar ziyara ba. Tunda ko radiyo ba su damu da su saurara ba, don haka ta samu can wani gefe gindin wata bishiyar goba mai inuwa ta zauna akan benci tana nazarin littafin the boy slabe da ta karbo a library.
Can anjima ta daga kai ta kalli motoci na gani na fada da ke ta fakin yara na rugawa su rungume iyayensu, sannan a soma kokawar fito da manyan ma'adanan abinci da katon-katon na kayan masarufi ana ajiyewa.
Waje ya cakude kowa na nemawa 'yan uwansa wurin zama, babu wanda yasan da ita, a lokacin ne ta ji babu dadi, ta ji kewar Innarta. Idanunta suka cicciko da kwalla. Kamar daga sama ta ji muryar Uncle a kanta ya ce. "Mariama".
Da sauri ta dago tana kokarin boye kwallar idonta, Uncle ne rike da manyan ledoji guda biyu, a bayansa wata yarinya ce budurwa da akalla zata girme ta da shekaru biyu da kuma wani yaro da zai yi tsara da ita, su kuma niki-niki da manyan kulolin abinci da picknick cooler wato irin kular nan da ake zuba lemuka da kankara mai hade da dan famfo a jiki. Ko ba ta tambaya ba tsabar kamanninsu da juna ya gaya mata wadannan yaran kannen Uncle Junaid ne.
Ta zame kasa tana gaishe shi, ya ce "Kuka kike ko Maryama, sabida mene?"
Ta share kwallar idonta dai-dai lokacin da shi da budurwar suka zauna akan bencin nata, ta ce "Lah Uncle ba kuka nake yi ba".
Ya ce "Mai yasa 'yan gidanku ba su zo ba?"
Ta ce "Ba su san ana yi ba".
Ya ce "To ki fada min adires na garinku ni da kaina zan je na taho da su a bisiting na gaba. Yanzu dai ga kannena Ilham da Sagir sun zo miki bisiting, are you o.k?"
Farin cikinta ya gaza boyuwa, bakinta ya gaza rufo don dadi. Ba tasan mai zata ce da Uncle Junaid ba, sai ta kama hannun Ilham tana murmushi, ta ce, "Na gode Ilham".
Ilham ta ce "Ba komi Maryam, yadda Yaya Junaid ke ba ni labarinki sai na dauka zan ga wata babbar budurwa, ashe kamar Sagir ce Maryama?"
Ya mike yana cewa "Ki tabbata ta ci abincin, kuma ba ta yi kewar kowa nata ba, I know you Ilham. Zan dawo nan da awa daya mu tafi".
Ta ce "To Yaya Junaidu". Tana murmushi.
Ilham ta ce "Amma ko kannenki ba su zo ba Maryam?"
Ta ce "Ba ni da kanne, ni ce auta a wurin Innata".
Suka ci gaba da hira, Ilham na kokarin cika umarnin Yayanta na ganin cewa, ba ta bar Maryam da kewa ba kamar yadda dan uwanta ya umarce ta. Ta zuba mata abinci mai rai da motsi cikin filet da kirjin kaza ta mika mata tana cewa "Ci maza kamin Yaya Junaidu ya dawo ya tuhume ni da barinki da yunwa".
Dariya ta yi, da ta lotsa kumatunta, tana tambayar kanta ko wane matsayi Uncle Junaid ya ba ta haka a wurin 'yan uwansa? Girmansa da kimarsa ya karu a zuciyarta. Tana ganin bayan Baba da Inna da Yaya Habibu ba ta da kamar Uncle Junaidu.
Ya dawo da wata leda mai dauke da ruwan (Faro) roba uku masu sanyi ya mikawa Ilham. Suka sha dukkansu sannan suka yi haramar tafiya, Mairo ta ji babu dadi.