Hakuri,tausayi,tsantsar biyayya,makirci

Part 3

by @secretwriter1

 secret writer: ๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„

     _WAYE_

  _MAHAIFINA..?_

   

    ~Written~

       ~By~

  ~A secret writer~

   

 _*A new story by a new writer a new style*_


   _*This is my first novel happy reading...!*_


๐Ÿ…ฟ 3


   Juyi Kawai takeyi ta kasa bacci, Sai tunanin abinda yafaru da ita a bangaren mama takeyi,duk da cewa itama abun na Damunta sosai.

   

    Tana mamakin meyesa mahaifiyarta ta hanata tambayar labarin MAHAIFINTA..!

  

 To ko dai ni shigiyace banda Uba kamar yadda ake fada Shiyasa Ummi Batason na tambayeta abu game da MAHAIFINA.?

 Gabanta ne yayi mugun faduwa a Dallin wannan tunani da tayi. 

  

  To idan ni ba shegiya bace meyesa Ummi bata son na mata maganar mahaifina.?


  Haka dai ta cigaba da yiwa kanta tambayoyin da batada amsarsu kuma batada mai amsa mata,karshe da baccin ya ki zuwa mikewa kawai tayi ta sake dauro alwala tafara kaiwa Allah kukanta.


_*WACECE UMMI.?*_


  Alhaji hassan ba fulatanin garin Adamawa ne, aslinsa dan garin mubi ne, yabaro garinsu ne shi da iyalansa da kuma kanwarsa Asma'u (ummi) adalilin fadarda akayi a garin mubi.

 A dalilin haka suka rasa iyaye da kuma yan'uwansu.


 A cikin wani kyauye mai suna mutum biyu dake cikin karamar hukumar gassol a cikin jahar taraba anan suka yada zango.


Mutm biyu babban garine wanda ya tara manya manyan yan boko maza da mata manya da yara duk da kasancewar sa kyauye amma mutanen cikin garin suna neman ilimi sosai kuma suna saka yayansu.



 Alhaji hassan yanada yara uku Hapsat,maryam da kuma umar (khalifa).

Hapsat na aure a jahar Adamawa, maryam kuma a cikin taraba take da zama.

  

  SUMAYYA (Isamat) shine asalin sunanta yarinya ce kyakyawa,fara ce sosai,ita ba doguwa ba ba kuma guntuwaba tanada diri mai daukan hankali.

  Tanada yalwar gashi akai irin na fulanin asali,tanada hanci sosai,idan tana magana gefen kumatunta lotsawa suke (dimple),tanada sexy eyes farare tas,hummm bari dai na barku haka kar na cikakaku da surutu lol.


 Tanada matuqar kokari a makaranta, islamiyya da kuma boko,hakan yasa ta zama popular a cikin makarantarsu da kuma kyauyen nasu gaba ษ—aya.

 Hakan ya jawo mata bakin jini sosai a gurin ษ—alibai.

 Sun sha tareta a lungu sumata ษ—an banza duka,kuma su mata warning akan ta daina bada answer idan malami ya tambayeta abu a makaranta tace bata iyaba,amma ta ki ji kumabata fasaba, saboda haka kullum sai sun bugeta.

  Umar ne ya fahimci abinda ke faruwa ya faษ—awa malamansu aka ษ—au mataki sannan suka fita hanyarta.

  A lokacin da ismat tafara girma a lokacin ne kuma duk wani baiwar kyau da Allah yabata yake daษ—a bayyana.

   A lokacin ne kuma abubuwa suka daษ—a da gulewa a cikin kauyen nasu, bata isa ta fitaba sai samari sun bita, abu fa yayi tsamari har fasa aure akeyi ta dalilinta.

  Hankalin umminta ya tashi sosai dan yanzu har gida ake zuwa aci musu mutunci itada Inna,abubuwa sun daษ—a tsananta wanda har ya jawo Ismat ta daina fita ko kofar gida,saboda matsa mata da samari sukayi da kuma yan matan garin.


  Amma duk da haka bata tsiraba har gida iyayensu ke zuwa.

   Sai da manyan gari suka shiga maganan sannan a ka kashe maganan, saboda yan matan garin da iyayensu sunce sai dai a maida Ismat gidan ubanta ko gun dangin ubanta in kuma ba hakaba sai dai gaba ษ—ayansu subar garin,ba yadda za'ayi suna baki ta dalilinsu yayansu suki auruwa.


Lokacinda ummi taji wannan magana hankalinta yayi mummunan tashi saboda idan suka bar garin nan basu san ina zasu nufa ba,kuma bata san mai zai kuma faruwa ba idan suka je wani gurin tunda duk wannan tashin hankalinda akeyin nan anayinsa ne akan yarinyarda bata wuce shekara 13 ba, idan tafi haka kuma mai zai faru.



    Dakyar aka kashe wannan wutan, sannan ko wata uwa tayiwa ษ—anta kashedi akan Ismat ษ—in.

  Wannan shine dalilinda yasa Ismat ta tashi batada friends  





_*Daga Alkalamin*_โœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป

 _*Sauwar marubuciya*_