Hakuri,tausayi,tsantsar biyayya,makirci

Part8

by @secretwriter1

A secret writer: ๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„๐ŸŽ„

    _WAYE_

  _MAHAIFINA...?_

โ˜˜โ˜˜โ˜˜โ˜˜โ˜˜โ˜˜



    ~Written~

      ~By~

   ~A secret writer~




 forgiveness is the best form of love, it takes a strong person to say sorry and even stronger person to forgive.


    


๐Ÿ…ฟ 8



  Cikin farin ciki Ammi ta tarbesu tana musu lale marhabin.


  Zama sukayi suka sata a tsakiyar su.


 Cikin murna da tsantsar farin ciki take tambayarsu ya gajiyan hanya.


 Bayan sun gama da bangarenta ne suka wuce bangarensu domin su kimtsa.


 Tsab tsab suka tararda bangaren nasu kasancewar jiya Ammi ta sa ummul-khairi ta share bangaren, don tunda sukace a weak din nan zasu gama Exam,Kullum sai Ammi ta tura ta taje ta gaira.


 Bayan sun kammala ne suka fito suka nufi bangaren hajiya, kakarsu.


  Tana zaune a parlour ita kadai tana gairan farce.


  Shigowa suka yi bayan ta amsa musu sallamar da sukayi ba tare da ta dago kanta ba,saboda a tunanita mustapha ne ya dawo daman suna tare muktar din ya kirashi a waya yace mata bari yaje ya dawo.


  "Maigidan har ka dawo....!"


Bata karasaba taji an rufe mata ido ta baya.


 "Kai mustapha sa karmin ido bana son iya shegen kan nan, ko so kake na yanke hannuna dan kaji dadin kawo wata bayan ni."


 Ummul-khairi da ta fito daga kitchen tana rike da tire a hannunta me zatayi in ba dariya ba don itama duk a tunanin ta mustapha ne bata lura da ya Usi dake tsaye a bakin kofa ba.


  Dariyan da ummul-khairi tayi ne yasa muktar yadan juyo domin ya kalli waye.


  Cak ta tsaya da dariyanta tana kallonsa.


"Ya muktar,"ta fada cike da mamaki a fuskarta.


Yakumbo da ke sababin mustapha ya sake mata ido "tace ke ummulu ban son shegantaka fa a ina kika ga muttarin da kike kiransa."


 Muktar jin ta kirashi da sunan da ya fi tsana yasa ya hada fuska ya cire hannunsa daga idonta.


 Ya usi dake tsaya a bakin kofa ya karaso yana cewa.,

"Maganinka kenan baka iya tsokana ba."


  Sai a lokacin ummul-khairi ta ganshi tace.,

 "Ya usi dama harda kai ban......!"

Hadiye sauran maganarta tayi sakamakon wani harara da ya usi ya watsa mata.


 Yakumbo da Sai yanzun idonta ya dawo dai dai,tana ganinsu ta zaro ido cike da mamaki tace.,


   "Kai ummulu Ashe da gaske kike."


 Ta kalli ya muktar da yahada rai yana kallonta,sannan ta juyo don taji kamar da mutum a gefenta.


  Ido ta kara zarowa tace.,


  "Usumanu Kai ne .?"


  Me muktar zayyi in ba dariya ba ganin yadda usi ya kwaba fuska kaman Wanda yaga danyen kashi.


 Sai da yayi dariyarsa San ransa sannan yayi shiru.


 "Kai usumanu yaushe kuka zo bansaniba.."


 Kasa amsa mata yayi saboda takaicin sunanda take kiranshi da shi."


Muktar ne yace ., "ba mu Dade da shigowaba, don ko abinci ma bamu Ciba mukace bari muzo muga yar tsohuwarmu."


Harararsa tayi sannan tace "ka dawo ai dama yanzun za ka ishi mutane da wannan banzan surutun nan naka,shiyasa na fisan usumanu a kanka.


Juyowa tayi ta kalli ya usi da ke zaune ya hada rai yana kallonta tace.,


"To kurma maki maganan mata maji maganan maza Allah ya dawo da kai ya hanya.?"


  Shiru yayi bai ansa mata ba .


Ya muktar y kwashe da dariya yana cewa.,


  "Lallai ma sohuwan nan hakama zakice keda naji labarin lokacin da muka tafi har gadon asibiti a ka kwantar dake, saboda kewar mu."


  Ummul-khairi da tun dazu da ya usi y harareta ta shige kitchen dan ta hada musu wani Abu d zasu sa abakinsu.


  Ta fit daga kitchen din tana rike da tire wanda ta daura dan madaidaicin plate a kai yana shake da snacks danginsu cup cake,da donote.


Ajiye tiredin tayi agabansu sannan ta gaishesu,ta musu sanda zuwa sannan ta mike ta fice daga bangaren.


Sun dade sosai a bangaren suna hira,ko abincima Sai anan Ammi ta turomusu sukaci.

Sai da a kafara kiraye kirayen sallan la'asar sannan suka bar bangaren nata suka nufi masallaci.


 Bayan sun dawo ne kowa ya wuce bangaren mahaifiyarsa.


********


   3:00pm


A dai dai wannan lokacin jirginsu y sauka a garin Abuja.


  Direct gidan Aunty khadija suka wuce, saboda sun tarar da drivern da ta turo.


Cikin murna da farin ciki ta taresu.


Bayan sunyi sallah ne suka zauna suka ci abinci.


  Da kanta ta kaiwa Dady abincinsa shida malam Hashim da aka saukesu a bangaren baki.


Sun sha hira sosai dashi kasancewar akwai shakuwa sosai tsakaninta da mahaifin nata.


  ********

   

  Su amal sun iso a gidan wan mahaifiyarta kuma abokin abbanta da ke abujan suka sauka.







   _*Daga alkalamin*_โœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป

  _*sabuwar marubuciya*_