3&4
._*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*wattpad user name*
***
---------------
*Arewa book user*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
--------------------
*Sirrinmu* manzon Allah (s.A.W) ya hanemu da gujewa mazajenmu a shimfiɗa yin hakan babban laifi ne kuma tsinuwar mala'iku za ta tabbata akanki. --------------------------------
3🟪4
.. .Dukansu suka haɗa baki wajen ce wa "umma lafiya me ya faru?".kukan ta ƙara fasawa tana ce wa"yanzu har lokacin wulaƙanta ni agidannan ya yi?gaskiya zan bar muku gidannan ku zauna ku da matanku tunda haka kuka zaɓa".
dukansu shiru suka yi sai malik ne ya ce"Umma ki faɗa mana abinda ya faru,don mun shiga cikin duhu wallahi".
"To matarka ce inya mura ita ce ta ɓata min rai,wai ga masifaffiya nan ta iso,don ubanta gidan inyamurai ne nan da za ta tara mana ƴan bariki suna muskuta ɗuwaiwaka kamar gidan maguxawa?to wallahi ni nagaji xan barmuku gidanku".sai ta fashe da kuka sosai har da majina,Hajiya Iklima ta ce"kaka don Allah ki yi haƙuri ki daina kuka"sai kuwa kaka ta Juyo a fusace ta ce"indai na kuka ko?tunda ba uwarki ce taka kukan ba ai dole ki ce haka?ni tashi ma shi ki barni in yi magana da ƴaƴana bana son bare awajen.
wani malulun baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya iklima ta Kalli fuskar hajiya kaka ta harareta,ita ta rasa wacce irin mata ce ba ta ɗaukar zuga ko kaɗan,amman ta yi alƙawarin muddin tana raye sai ta haɗa Hajiya kaka da dukkanin surukanta ta zama ita ce ta gaban goshi.
Tashi ta yi ta fita tana mai ƙara jin haushin cin fuskar da Hajiya kaka ta yi mata,sai kuwa kaka ta ce"to as dai a fita don bana son ina shawara da ƴaƴa na a zo asakamin idanu irin na fulanin daji".
wannan magana da kaka ta faɗa ba ƙaramin mugun haushi ya bawa Hajiya iklima ba,don tasan sarai da ita take don asalinta fulanin daji ce,don itama kafin ta bari a aurota ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba.
"Umma insha Allsh daga yau Zulaihat ba xa ta ƙara yi miki wani abu da zai ɓata miki rai ba,yanzu ma ba sai anjima ba za ta baki haƙuri",yana faɗar hakan ya yi saurin fita.
Usman autan Hajiya kaka ya ce"gaskiya umma ki daina yi wa wannan baiwar Allahm haka,gaskiya ba a ƙyauta mata wallahi saboda ita ba yaranmu ba ce sai kuma ace za abi a tsaneta".
"ah lallai ƙanin Zulai ka ce kaima an jiƙa an baka,kamar yadda sukayi wa ɗan uwanka a da cen baya,yanzu kuwa Allah ya dawo min da hankalin ɗana jikinsa,yanzu muna nan da kai za kaga caccakar da zai yi musu shegu masu cin arziƙi,tunda suka zo ina kula dasu babu abinda suke sai dafa nama daga an sauke wancen a ɗora wannan,ɗana yana ta kawowa suna cinyewa".
dukkansu shiru sukayi har Alhaji Aliyu wato babban ɗan ta don shima ba'a bar matarsa ba,don haka haƙuri kawai ya iya bawa Hajiya kaka yaja bakinsa ya yi shiru.
A ɗakinsa ta samesa yana kaiwa yana kawowa hannayensa ya rungumesu a baya,sallama ta yi ta samu waje ta zauna kanta a ƙasa sai ta ji ya ce cikin zafi"Yanzu Xulaihat abinda ki ka yi wa mahaifiyata ya yi miki daɗi kenan? ki tara ƴan uwanki suna zagar min mahaifiya ta to wallahi ba zan lamunta ba,kowa ya haɗa kayansa ya barmin gidana don ba zan lamunci cin fuskar kowaccenku akan mahaifiyata ba.
Muryarta na rawa zata yi magana da sauri ya ɗaga mata hannu ran tsohon soja ya tashi ya fita yabar mata ɗakin,ya koma wajen mahaifiyarsa ya cigaba da lallaɓa ta,don yana fatan ya gama da ita lafiya.
Kuka sosai ta yi awajen kafin ta tashi ta fita,tana tunanin ta yadda za ta gayawa ƴan uwanta wannan maganar garinsu da sai a yini a kusan ƙwana ana tafiya sannan sai da yamma ta yi sannan za a ce su koma da yamman nan ko kai amarya ba ayi ba sunga gida.
Ɗaki ta koma tasha kukanta sosai,a hankali na buɗe ƙofar ɗakin mahaifiyata halin dana ganta a ciku shine ya ƙara jagula min tuna nina,na ƙarasa kusa da ita hankalina atashe ganin fuskarta ta jiƙe sosai da hawaye cikin daburce wa na ce"Mama lafiya me ya faru da ke?"
Bata iya ce wa komai ba ta tashi ta fita,binta na yi da kallo ina hasashen abinda ya faru tabbas hajiya kaka ce ba wani ba,don tun ina ƙarama na sha kama mama tana kuka kuma ba kowa ne musababin kukanba sai hajiya kaka,sam bata san mama na ban san abinda ta yi mata ta tsaneta haka ba.nima bani da zaɓi daya wuce in fito daga ɗakin don haka na yo waje don ƙawayenmu duk sunci ƙwalliya don kai amarya,ina fitowa Rashida ta ce"lafiya naga fuskar mama duk ta canza?ko ke ce kika yi mata wani abin".
"hmm Rashida ni kuwa me zanyi wa mama da za ta yi fushi dani haka?kawai dai kin san tsakaninta da hajiya kaka ina ganin wannan ne amman ba ni ba ce."
"kin san Allah Khairat matar nab gaba ki ɗaya ta ishemu a gidannan,ni na rasa dalilin daya sa duk iyayenmu suke cikin gidannan kamar dole,ita kuma ba bari take a zauna lafiya ba,kullum sai faɗa ni wallahi matar nan ma na matsu ta margaya mu huta da jarabarta.
Saurin rufe mata baki na yi na ce"wallahi Rashida ki kiyayi wannan bakin na ki kinsan dai matar nan kakarmu ce,babu yadda zamuyi da ita suma iyayenmu haƙuri suke da ita,muma ya kamata muyi haƙurin ko?"
Iman da Salimat da suke juyo hirar da su Khairat suke sai kuwa suka ce"Hmm Rashida wallahi ki cigaba da maganarki kada ki biyewa wannan wacce bata san inda ya ke mata feeling ba,don haka ko muma wallahi mun tsaneta wallahi tunda bata san iyayenmu mu ma dole ne mu tsaneta".
ni dai fitowa na yi babban hall ɗin da ake hidimar bikin abin mamaki duk babu ƴan uwan mama na awajen abin ya ɗaure min kai sosai,yanzu fa na gansu awajen amman har na nemesu ban gansu ba.
Aranar dangin mama na duka suka koma ba tare da sun tsaya sai washe garin ba,hankalina ya tashi sosai na fito na yi sashen hajiya kaka,tana zaune ita da wata ƙawarta Hajiya Inna,na gaisheta tana tsokana ta tana ce wa saura na mu muma,kunya ce ta rufeni sai kuwa na ji Hajiya kaka na ce wa"Hmm Hajiya Inna kema dai kya faɗa wallahi wataran idan na ga yaran nan suna shiga suna fice agidannan su kusan ashirin duk ƴan mata,sai in shiga ɗaki inyi ta kuka sai ta buɗe injirnta ta ce"kinga duk inda na yi ƙashin wuya saboda yarannan duk dun tsotseni wallahi".
duk da ina cikin tashin hankali sai da na yi dariya sannan na ce"Hajiya kaka kina da masaniyar dangin mamana duk sun bar gidannan acikin wannan daren ko kai amaryar basu yi ba sunga gidan brother".
"brozo na ce ungo ƴar nema. to sai me don sun bar gidan ai ni sauƙina ne don wallahi idan na fito naga waɗannan samudawan mutanen har zazzaɓi na ke wallahi don ni bana son ganin ire iren inya murai sam agidannan itama uwar taki darajarku take ci wallahi da tuni ta daɗe da barin gidannan".
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce"haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri'ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga ɗakin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka".
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce"wash".
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce"stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye."
maimakon ya bani haushi sai ma ya ƙara burgeni sosai,abin tausayi wato shi so hana ganin laifi.
Ƙamshin tureransa ya ƙi barin wajen sai da na ɓata minti kusan talatin sannan na tashi na tafi,wajen daya mareni ɗin na shafa hannayensa duk sun fito a kumatuna,ina ta shafa wajen maimakon inji haushi a'ah daɗin marin ma naji don ko babu komai ko madubi na k
Da sauri Hajiya Inna ta kalleta ta ce"haba Ramatu ashe har yanzu baki manta da wannan abin ba?Har sun tara zuri'ah Da Ɗanki yanzu da aurensu ya kai shekara 30 Fa amman ai yakama ta a manta da komai tun sanda malik ya auro yarinyar nan shekararta 13 har yanzu da take kusan shekara 43,amman ace haryanzu ba a manta da komai ba?gaskiya bai kamata ba Ramatu ki sani kema fa ɗiyanki suna gidan miji fa?bakya tsoron ayi musu haka?don Allah Hajiya Ramatu wannan abin ya wuce in banda yarinyar nan tana da haƙuri ne da irin ƴaƴan yanzu ne da babu abinda zaisa ba zasu yi miki rashin kunya ba,don kin zagar mata uwa a gabanta.
Har hawaye ya fara wanke min fuskata na tashi na fita daga ɗakin,wai ita hajiya kaka me take so ne da mamana?wacce irin tsana ce haka".
ji na yi kamar na buge da abu da sauri na juyo saboda buguwar da goshina na ce"wash".
sosai gabana ya faɗi ganin Yaya Bilal,da sauri na take xan gudu ya janyo bayan rigata tas tas ya kifamin maruka har biyu,na dafe ƙuncina hawaye na ƙara fitowa a idanuwa na ya ce"stupid girl kawai ke bakya kallon gabanku ne da zaki bugeni?to wannan shine last warning matuƙar na biyo hanya to ki kada ki biyo don na tsani kallon wannan dirty face ɗin ta ki,don haka ki kiyaye."
maimakon ya bani haushi sai ma ya ƙara burgeni sosai,abin tausayi wato shi so hana ganin laifi.
Ƙamshin tureransa ya ƙi barin wajen sai da na ɓata minti kusan talatin sannan na tashi na tafi,wajen daya mareni ɗin na shafa hannayensa duk sun fito a kumatuna,ina ta shafa wajen maimakon inji haushi a'ah daɗin marin ma naji don ko babu komai ko madubi na duba zan ga tafin hannayensa a kumatuna.
Ban samu kai amarya ba don har sun tafi,sashen Anty ƙarama na je matar baba usman ƙaramin ƙaninsu babanmu.
Turaren wuta ta kunna a burner mai shegen ƙamshi ta kalleni da fara'arta ta ce"ah wata sabon ganin yaushe rabonda na ganki a sashennan har na manta?"
Ɗan murmushi na yi na ce,"to maman arman gani na zo".da mamaki ta kalli kuncina ta ce"ikon Allah ke kuma Khairat wani mugunne ya mareki haka?".
ɗan shafa wajen na yi na ce"am daman faɗuwa na yi ɗazu".
"ƙarya ki ke wallahi Khairat ba faɗuwa ki ka yi ba ki faɗi gaskiya dai?wannsn marine ga yatsu biyu biyar nan sun fito raɗa-raɗa.
Hawaye ne ya fara fitomin na saka tafin hannuna na rufe don kada ta gani,janyo ni ta yi ta rungume ni sannan ta ce"ki faɗa min gaskiya Khairat nasanki da haƙuri da kawaici waye ya mareki haka?".
ban sanda na ce mata ba"maman arman yaya Bilak ne ya mareni waidon na biyo hanyar da ya ke".sai na fashe da kuka don ban san abinda yasa Yaya Bilal ya tsaneni ba".?
"caɓɓi jan lallai yaron nan ba shida mutunci yanzu shi ne ya yi miki wannsn marin na cin kashi da wulaƙanci.? Da sauri na riƙe hannayenta na ce"don Allah maman Ammar kada ki faɗawa kowa wannan maganar wallahi ina sonshi bana son tun yanzu ya ce ina haɗasa faɗa da ƴan uwa.
*Miss green ce*
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
***
Masu tura katin MTN👇
***
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
***
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com