7&8
_*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
---------------------
*Wattpad user name*
***
---------------
*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
-------------
*Sirrinmu*
manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da saka turare idan zamu tafi don yaɗa xinar idone,don haka mu kiyaye.
------------------------
7🟩8
. . . .Tun ka fin ta ƙarasa bakin gate ɗin taga duk babu motocin gidan,ta ce"oh mu dai Allah ya tsaremu da mugayen mata yanzu tsabar baƙin ciku don zanje nemawa jikata ƴanci shine za a ƙwashe motocin gidan a ɓoye."
Ammar ta hango ɗan gidan Baba ƙasim me bin baba auwalu,da sauri ya fara neman wajen Ɓuya tunda yasan halin kakar ta su,da sauri ta ce"Zo nan Ammaru ko Ƙasimu ubanka bai isa ina masa magana ya ƙi zuwa ba,saboda uwarka ƴar borno tasha ruwan babur na baƙin hali shine ina magana zaka ɓoye?".
ɗan shafa kansa ya yi sannan ya ce"haba kaka wane ni na'isa kina magana in ɓuya,ai ban isa ba yanzu dai me ki ke so?".
"ayyo to na ɗauka rashin mutuncinne ta motsa tunda kasha nonon babur ƴan maiduguri".kallon kakar ta sa ya yi sannan ya ce"wai ke kaka me yasa kullum sai kin zagar mana iyaye sannan ki ke jin daɗi ne?don Allah ki daina yadda ki keson ƴaƴanki muma haka mukeson na mu".ta ɓe baki Hajiya kaka ta yi sannan ta ce"to rasai ai dole inyi zagi tunda kasha nonon rashin kunya,yanzu dai ni dai ina duka motocin ƴaƴana aka kaisu"?.
kallon ɓangaren da Bilal ya ke Ammar ya yi yana jingine a jikin gate ɗin yana kallonda dramar da kakar ta sa ta ke yi,Ammar ya ce"to kaka ni kuma da ba ma hawa motar na ke ba Dady ya hanani ta ina kuma zan san wanda ya fita da motar ni motar Hajiyata kawai na ke hawa a gidannan".
"to me Hajiya tunda dai bakasan inda motocin suke ba shikkenan ba sai ka gaya min kai ɗan hajiya bane,tunda ni dai ba ƴar hajiyar ba ce to shikkenan,bari inje in hau motar haya in tafi abuna ni dai yau babu me hanani zuwa ƙwatarwa jika ta ƴanci duk baƙin cikin mutum ma sai dai ya yi don ya yi ta banzar.
Tana fitowa waje ta dinga tsare adaidaita amman suna ƙin tsayawa,cen ta hango Bilal yana ɗaga mata hannu cikin motarsa ya yi gaba abinsa.
"Kai amman yau muguntar fulanin bauchi ta tashi ai Bilal kasha a maman ruƘayya uwarka dole ka Ɗagomin hannu a mota,yau zanga wanda ya Ɗaure maka gindi a gidan,cikin gidan ta koma tana ta banbaminta ta wuce saahen Mahaifiyar Bilal tana zuwa kuwa ta sameta a farlo tana cike wasu takaddu,da sauri ta ajje aikin da ta ke Rashida da Nusaiba suna tayata aikin da sauri suka kalli kakar ta su don sunsan aƙwai abinda ya kawota.
"Yanzu Ruƙƙaya ke ce kika bawa ɗanki Bilal damar wulaƙantani a idon duniya ko?ki ka sakashi ya ƙwashe motocin gidan ya ɓoyesu don kada inje in karɓarwa jikata ƴancin ta ko?".
"haba Umma ta yaya zance ya aikata hakan?wallahi ban san komai a game da hakan ba,don Allah ki yi haƙuri idan ya dawo zan samesa muyi maganar".
"ikon Allah ki ma samesa kuyi maganar ba ma ki hukuntasa akan ɓata min ɗin da ya yi ba ko Ruƙayya?tunda shi Bilal ɗin shine ya haifeki ba ke ce ki ka haifesa ba ko? to shikkenan idan shi Abdullahi ɗin ya dawo ya yi masa faɗan tunda ke tsoronsa ki ke ji?".
tana faɗar hakan ta yi tahowarta,Rashida ta ce"ni fa daman nasan ba alkhairi ya kawo wannan tsohuwar ɓangarenmu ba?ke dai umma kada ki yi magana don wallahi idan ki ka ce wa yaya Bilal hajiya kaka tazo nan kin san zuwa zaiyi suyi ta ɗauki babu daɗi don haka kawai ki saka musu idanu,idan ba haka ba wa ke shiga tsakanin kaka da Yaya Bilal?.
shiru dai Hajiya Ruƙayya ta yi kanta na yi mata ciwo ta ce"Nusaiba ɗakkomin paracetamol insha kaina ciwo ya ke".da sauri nusaiba ta ɗakko mata a wani ƙaramin kid tasha sannan ta haɗa kayan ta koma ɗaki.
Nusaiba na ganin mahaifiyar ta su ta tashi ta ce"Anty Rashida gaskiya kaka ba ta ƙyautawa wallahi kawai daga abu ya haɗota da Yaya Bilal sai ta ƙare akan Mama ai bai kamata ba wallahi,ki ga fa abinda ta kewa mamansu Khairat kulli yaumin sai ta goranta mata wai ita tuba ce?ai bai kamata ba tunda har ta musulunta."
"hmm ke dai bari nusy wallahi matar nan ta tsayamin a ƙahon zuciya jira kawai na ke wataran ta taɓoni tasan ta taɓoni don abinda ta kewa iyayenmu ya isheni wallahi".
"hmm Anty Rashida gwara dai abi a sannu mu rabu lafiya tunda ta kusa sheƙawa ma kowa ta huta wallahi da jarabar mafaɗaciyar tsohuwa,ai Yaya Bilal ɗin shine dai dai ita kaf gidannan,yanzu ba ta ce wai za ta faɗawa Baba ba wallahi muna nan da ke baza ta faɗa masa ba,don ni nasan irin son da takewa Yaya Bilal,suna cikin hirar ya shigo don haka suka tsuke bakinsu suna yi mai sannu da zuwa,yasha mur ya ce"ina Mama take?".da sauri nusaiba ta ce"tana ɗakinta yanzu ta shiga don kanta na ciwo".
Shigewa ɗakin mahaifiyar ta sa ya yi ya barsu anan,Nusaiba ta ce"Anty wai me yasa Yaya Bilal ya fimu ƙyau ne?shiyasa magana ma sai ya ga dama ya ke mana mu dai sai fari kamar zabaya amman kuma ya fimu ƙyau."
"Ke ni dai rabani da maganar wannan bawan Allah kinfi kowa sanin kunnensa yanzu ya iya dawowa ya ɓata mana rai don haka ni dai ki bar maganar".
hajiya kaka ranar har kuka ta yi wai Soja ya hanata fita a gidan don yasan shi soja ne,duk wanda ya shigo ɓangarenta sai ta faɗa masa ai soja ya wulaƙanta ta.
An sallomoni daga asibiti na yi garau dani kamar ba ni ba,Baba kuma ya kafa musu tsauraran sharuɗa akaina don haka kowacce ta kama mutuncinta arabu lafiya.
Sanda aka sallamo ni Yaya Bilal ya koma da daddare na nufi sashensu ina zuwa na tarara da Abba da Hajiya na gaishesu na wayance na shige wajen Rashida har ta fara bacci na tasheta tana mitar waye ya tashe ta sai ta ganni ta ce"gaskiya Khairat ba ki da mutunci kinsan yau yini na yi aiki sai da wannan ɗan wahalar ya tafi sannan muka huta".
mamaki ne sosai kam fuskata na ce"waye kuma ɗan wahala Rashida?".banza ta yi min ta shiga banɗaki ta fito tare da ɗauro alwala ta kalleni sannan ta ce"wa ye kuwa daya wuce yaya Bilal?".harararta na yi sannan na ce"gaskiya Rashida wallahi baki da kunya yanzu yayan namu shine ɗan wahala?ni zuwa ma na yi in gansa inji sanyin a zuciyata ashe kuma ya tafi".?
sheƙeƙe ta yi tana kallona sannan ta ce"lallai khairat wai ke haryanzu yaya yana ranki baki ciresa ba?gaskiya idan har zan baki shawara ki haƙura da yaya don wallahi aƙwai matsala babba idan har ki ka ce zaki so yaya,saboda idan ma baki sani ba yau ki sani yaya ya wuce duk yadda ki ke tunanin mata da yawa suna kawo kansu waɗanda suka amsa sunansu mata masu ji da kuɗi da mulki amman wallahi ko kallo basu ishesa ba,wai shi har yanzu bai ga macen da ta ƙwanta masa ba,don haka ina mai baki shawara khairat ki yi haƙuri ki ciresa daga zuciyarki,ga maza masu mulki masu komai suna sonki ammanke kin dage sai yaya gaskiya ki yi haƙuri ki zaɓi ɗaya a cikinsu musha biki".
wasu hawaye ne masu zafi suka zubomin,nasa bayan hannuna na sharesu sannan na tashi zan tafi duk jikina a saɓile,janyo hannuna Rashida ta yi sannan ta ce"yi haƙuri khairat wallahi ban san abin zai ɓata miki haka rai haka ba ƴar uwata,insha Allah daga yanzu bazan ƙara faɗa miki haka ba,zan taya ki da addu'ar Allah ubangiji ya baki Yaya Bilal".tana faɗar hakan ta rungumeni tana kukan tausayina i'tama.
****
Kamar yadda kuka sani part 12 ne agidanmu kuma duk ƴaƴan Hajiya Kaka ne su da ta haifa da mijinta,Baba Abdullahi shine na farko sai Bananmu Abdulmalik,Baba Tijjani,Baba Kamalu,Baba Sagir,Baba Bashir,Baba Ali,Baba Auwalu,Baba Ƙasim,Anty Zulaiha,Baba usman,Anty Aisha.
Waɗannan sune Ƴaƴan Hajiya Kaka,Abdullahi yana da yara biyar ya aurar da biyu mata saura mata biyu namiji ɗaya
Yaya Bilal,Babanmu kuma yana da Yara 8,Tijjani 9,kamalu 6,Sagir 5,Bashir 10,Ali 4,Auwala 9,ƙasim 6.Zulaihat 7,Usman 2,Aisha uku.
Waɗannan sune jikokin kaka waɗanda adadinsu ya kai 74,dukkansu mazan a gidan suke da ya ke gidane mai yalwa sosai kuma daman tun kafin mahaifinsu ya rasu ya riga daya ta nadar musu waɗannsn filayen kowa da nasa,matan kuma sun ce sun barwa yayyinsu,amman duk da haka sai da suka basu kuɗi masu yawa saboda suna tausayin ƴan uwansu saboda tun suna ƙanana an koya musu tausayin ƙannensu saboda haka tunda suka taso da son junansu suka tashi shiyasa babu wani talaka acikinsu don dukkansu duk wanda ya ke samu zai janyo ɗan uwansa a kusa dashi sosai,kuma kaf ɗinsu mutum biyu ne masu kuɗin,Malik da kuma Abdullahi amman duk sai da suka ja ƴan uwansu a jiki duk abinda suka samu na ƴan uwansu ne.
Hajiya kaka ita da mijinta ƴan asalin jihar baushi ne fulanin usul,amman mahaifiyar Hajiya kaka ƴar zaria ce babanta ne ɗan Bauchi.
Mijin Hajiya Kaka sojane tun zamansu a bauchi sukayi sa,amman ana yi musu transfer sosai daga gari gari,har Allah ya kasu garin kano suka fara zama a gidan haya daga baya ya yi na sa,amman zaman kano ɗin ya fi yi musu daɗi,don unguwar da suke unguwa ce mai ƙƴau unguwar jan bulo,Allah ya azurta su aƙwai filaye sosai a kusa dashi ya dinga siya yana ajjewa har Allah yasa ya siya filaye a kusa dasu sunfi 15,kuma a waje ɗaya suke kusa da gidansa suna zaune a kano ƙwatsam aiki ya mayar dasu a kaduna unguwar malali.amman suna zuwa kano akai akai.
Hajiya kaka tafi son zaman kano don haka ya barta anan ya ɗakki mata ƙanwarta suke zama tare,ƴaƴansu sun fara girma yanzu don haka ma bata fiya zuwa kaduna ɗin ba.
Waɗannan filaye da ya siya ya siyawa yaransa ne,ko kafin yabar duniya ƴaƴansa sha 11,sanda ya mutu bata ma san tana da ciki ba sai daga baya ta haifi autarta Aisha.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin rayuwar Hajiya kaka.
*Washe gari*
babu wacce bata shirya a cikin mu ba,saboda ayau za a mayar damu boarding daman kusan duk ƴan matan gidan kusan mu goma duk boarding muke kuma muna a shekarar ƙarshe yanzu.
Duk jikina a sanyaye ya ke bayan na haɗa kayana na nufi sashen hajiya kaka,tana ganina ta hau kuka tana ce wa"Allah sarki jikata bana son rabuwa da ke wallahi,ke kaɗai ce a cikin jikokina baƙya yimin rashin kunya,ABIN CIKIN ƘWAI ya fi ƙwan daɗi haƙiƙa Allah ya bani jikar da nake alfahari da ita,sai ta rungumeni tana kuka na riƙo hannunta muka fito inda motar da za ta ɗaukemu take,motar gidanmu ce wacce daman an ajjeta ne don kai yara skull.
Hararar hajiya kaka suka fara yi,Nadiya da Samira Karaf a don kaka ta ce"to amman dai ba ni kuke harara ba ko?fulanin daji da sadakar yalla kukewa amman ni ba ni ba.Nadiya ta ce"wai ke kaka waye ma ya kalle ballanta na ma a harareki?kema da wani idon har kika san ana kallonki idan baki kallemu ba"?.
"shut up"!
yaya abeed ya ce wanda muke uba ɗaya dashi kuma yayan nadiya, sannan ya cigaba da ce wa"wallahi ban san rashin kunyarki har ta yi tsamari haka ba,ki dinga iya bakinki idn ba haka ba kuma jikinki zaiyi tsami."
"a'ah ɗan nan da a uman take da bata isa ta yimin haka ba,da na haƊa ta da askarawa sunci ubanta malik".Dariya aka sheƙe da ita don abu kaɗan sai kaji ta ce da a uman kake da baka isa kayi mata abu kaza ba,kawai don ta yi zaman cen shikkenan.Ko da muka shiga motar sai da aka so ayi faɗa don su iman da nadiya waje ɗaya suke zama Rashida ta zauna kusa dasu don haka sukace sai ta tashi, yaya abeed ya ce"wallahi duk shegen da ya yi min rigima zan saukesa ne a duk inda naga dama don haka kada kowa ya dameni,ku baƘwa ko yi da ƴar uwarku khairat tana zaune baka jin bakinta amman ku sam baku da nutsuwa.
Ai fa wannan maganar da yaya abeed ya faɗa sosai abin ya bawa su Nadiya haushi,suke ta hararata ni kuwa ban ma san suna yi ba,Rashida ce taso biye musu amman na hanata don suna sane suke hararata don sun san halin Rashida ba tada haƙuri kuma ba za ta bari a zageni ko aci mutunci na ba.
Tunda daga lokacin babu wanda ya ƙara magana,ni Rashida,iman,nadiya,samira,unaisa,khalisat,intisar,raudat,Amina.
Duk babu wanda ya ƙara ce wa kanzil don sun san halin yaya Abeed bai da mutunci sun sansa kamar wutar cikinsu.
Muna zuwa makaranta kowa ya yi hanyar ɓangarensu tunda muka koma skull hankalina ya koma kan karatu wani lokacin Rashida har tsokana ta take wai yanzu na dain tunanin yaya Bilal hankalina ya koma kan karatu,sai dai kawai inyi dariya don na san son yaya Bilal a zuciyata ya ke bazai taɓa gogewa ba har abadan.
*Miss green ce*
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
***
Masu tura katin MTN👇
***
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*