10.
by @nuceeyluv
👑👑👑👑👑
*SARAUTA TAH CE*
*Free page*
*Wattpad*
@nuceeyluv
By
Nuceeyluv😘
10...
Yadda taga jinin har yanzu be daina zuba akan fuskar sa ba yasa ta hadiye masifar data so yi Masa tana kallon sa cike da tausayawa ta rarrafa gabansa a hankali tana kallon fuskar tashi da kyau.
Idonsa na kallon Wani side din Dan be Wani kalleta ba dukda ta matso wajen Kuma yasan ta zauna kusa dashi.
"A Ina kaji ciwo haka? Su waye suka dake ka?"
Tayi mgnr da tausayi tana wara ido sai kallon wajen take harda keyarsa ma Abinda ya daure mata Kai har yanzu be damu d zubar jinin ba tamkar ba daga jikinsa yake fitowa ba.
Kallon Dan kwalinta tayi taga har yanzu Yana Kai bare ta goge Mai dashi. Numfashi taja kafin tasa hannunta tana kadawa a gefen idonsa tace,
"bawan Allah...kodai Kai kurma ne? Baka ji??"
Tayi mgnr tana Masa alama d siffar kurame.
Kyawawan idanunsa ya zube mata a nata take taji Wani irin faduwar gaba ta sameta Dan haka ta kawar dakai da sauri shi Kuma a lkcn yake mikewa zai tafi.
Da sauri ta kamo hannun sa batare data shirya Hakan ba. Ji tayi hannun da laushi sosai tamkar audiga.
Tsayawa yyi Amma be juyo ba Sbd ta rike masa hannu. Jan hannun nasa tayi zuwa bakin rafin dake gabansu tana kallon idonsa tayi Masa alamar ya zauna kan Wani dakalin Dutse.
Zama yyi kamar yadda tace ita kuma tasa Wannan kokon tana Debo ruwa ta dawo gabansa alama tayi Masa da hannu tace,
"wanke fuskar ka."
Gani tayi ya zubawa ruwan ido Yana kallo. Dan girgiza shi tayi ta sake yi Masa alamar kurame Dan izuwa yanzu ta fara tunanin kurma ne tace,
"wanke fuskar ka"
Dauke kai yyi beyi Abinda tace ba Dan haka ta Dora hannunta kan lallausan gashin kansa da tun dazu take mmkin ganinsa ta Debo ruwan tana zubawa a fuskar sa. Take ya lumshe ido a hankali Yana sauke ajiyar zuciya.
Ci gaba tayi da wanke Masa ciwon har lkcn idonsa a rufe Yana jinta. Hatta gashin kansa daya yamutse da keyar sa Duk Saida ta wanke Masa Sannan ta dawo kan kafarsa daya tutturje Nan ma.
Dagowa tayi da niyyar yi Masa mgn sai taga Ashe ita yake kallo. Kawar da Kai tayi tana mikewa ta kamo hannun sa suka koma wajen daya zauna dazu. Zama yyi sannan ta zauna tana dubansa a tsanake tace,
"waye Kai? Daga Ina kke? Daga wacce nahiyar ka bullo? Dan babu me irin kamar ka akaf fadin kauyikam mu. Kodai ka samu batan hanya ne? Da alama ma barayi ne sukai maka fashi koh???"
Duk ita kadai take ta jera wa'annan tambayoyin batare daya kalli side dinta ba bare tasa ran amsar Sa. Ya fara Bata haushi ta mike a zuciye tace,
"Ko Kai waye ma Kaci kanka"
Tana gama fadin haka ta zari ledar fruit dinta tabar wajen tana mgn ita kadai,
"haka kurum mutum ayita Masa mgn yyi banza dakai nayi alamar kurame ma duk a banza tamkar da Dutse kke mgn mwsss."
Da Wannan maganganun tabar jejin gaba1 batare data sake waiwaiyar Inda yake ba.
*MASARAUTAR MANARAS*
Ba karamin tashin hankali aka fuskanta ba a wayewar ranar da aka nemi yareema yaseer aka Rasa sama ko kasa ba'a fahimci cewar baya masarautar ba Sai wajen karfe 11am anje Kai masa Karin kumallo suhaima taga baya Nan.
Da farko sunyi zaton ya fita ne Saida sukaci karo da wayarsa da system dinsa da komai daya saba fita dashi kafin suka farga da Wannan mummunan Al'amari.
Sun tmbyi duk masu tsaron sashen sa da sauran sassan waje kowa yace bega yareema yaseer ba.
Yadda yareema Yazeed ya daga hankalin sa sosai akai zaka dauka daki daya suka fito.
Soyayyar da maimartaba ke yiwa yareema yaseer Bata bayyana sosai ba Saida aka Rasa shi gaba1 anan hankalin sarki ya tashi Harya so bawa mutane tsoro sbd yadda hawan jini tashi guda ya kama shi.
A bangaren ummi kuwa tamkar mahaukaciya haka ta haukace da dimuwar Rasa yareema yaseer dukka dai masarautar yanzu cikin tashin hankali ake. Take kuwa aka bada umarnin kama dukkan masu tsaron sashen sa aka jefasu gidan sauya hali na masarautar basu zasu fito ba har sai randa yareema yaseer ya bayyana.
A rude ta karaso sashen bayi na mata gaisuwa Bata kulasu ba. Mama sarauniya uwargidan sarki itace Nan ta shigo sashen ummi hankalin ta a mugun tashe kwana biyu bata cikin masarautar sai lbrin batan yareema yaseer taji.
Ummi na cikin daki tana zubda hawaye aka sanar mata da isowar mama sarauniya. Batayi mgn ba saidai gyada Kai kawai da tayi alamar ta bada izini a shigo. Mama sarauniya ta Karasa dakin fuskar ta da alamun tashin hankali tace,
"garin yaya yareema yaseer ya bace a cikin masarauta? Ina masu kula dashi suke?"
Matse hawaye ummi tayi tana girgiza kai Tace,
"Allah shine mafi sani har yanzu babu Wani Wanda ya Amsa cewar yaga lkcn da aka sace yareema yaseer."
"SUBHANALLAH"
mama sarauniya ta furta Hakan tana dafe goshi tace,
"dole akwai maciya Amana a ciki zansa ayi duk Wani bincike da za'ayi domin gani Inda bakin zaren yake."
Ummi ta gyada Kai kawai batace komai ba. Sallama mama sarauniya tayi mata tace,
"bari naje wajen maimartaba ance yana kwance."
Ummi tace,
"Nagode."
Fita mama sarauniya tayi. Yyinda ummi ta bita da kallo tana jin kaunar ta a ranta duk cikin matan sarkin wato kishiyoyin ta babu wacce tafi damuwa da lamarin 'ya'yanta sama da mama sarauniya har kunyar Abinda yareema yaseer keyi mata take, idan ba itace ta turashi ya gaishe ta ba sai suyi satuka basu hadu ba batasan meyasa baya sakewa da itaba mace me kirki tamkar ba kishiya ba Dan har yau Bata taba ganin ta nuna kishinta koda a ido ba.
Sauran matan sarkin da aka karo bisa kanta Suma dai zaman gashi nan dai basa haihuwa shiyasa kowa harkar gabansa kurum yake tunda kowacce da sashen ta.
Saida aka Bata izni Kafin ta shiga sashen sarki cike da girmamawa ta fara gaishe shi. Yana kwance ya mike dakyar Yana kallon ta yace,
"Aisha kin dawo?"
Mama sarauniya tace,
"hankali na ya Gaza kwanciya tunda naji wanann mummunan lbrn daya faru ga danmu yareema yaseer, shiyasa na taho ba tare Dana Ida Abinda ya kaini ba."
Maimartaba yace,
"Nagode Aisha. Kinada kirki kina son Abinda nakeso Wannan kadai ya isa ki samu gurbi a zuciya ta."
Dan murmushi kawai tayi tana dukar da kanta kafin tace,
"ya zama wajibi nayi biyayya akan duk Abinda kkeso Nima na kaunace shi matukar be take shari'ar musulunci ba."
Sosai maimartaba yaji dadin kalamanta. Kafin yace,
"kina ganin wanne me tsaurin idon ne ya samu damar dauke yareema yaseer a masarauta? Kuma wanne irin karfi da madafan iko ne dashi haka daya iya aikata irin Wannan aikin me matukar hatsari?"
Dakyar mama sarauniya ta jawo ajiyar zuciya ta dire tana sake sauke wata ajiyar zuciyar ta dire a jere kafin ta lullube fuskar ta da murmushi Tace,
"tabbas baza'a Rasa makiyan boyen da muke dasu a cikin Wannan fadar ba, sannan bazan iya sanin waye yyi Hakan ba sai dai an bani izinin na Nemo Hakan."
"Na baki wuka da nama sarauniya ta, Zaki iya kula da Wannan binciken...."
Tari ya fara yi a hankali Yana haki. Mama sarauniya ta dubeshi a rude tace,
"ciwon Harya kai haka ne??"
Murmushi yyi cikin kwantar da zuciya yace,
"a'a ba komai..."
Sannan yaci gaba da fadin,
"Amma Dan Allah kisa ayi binciken Nan da wuri Ina bukatar yareema yaseer a kusa dani, shine kadai magajin da nake da burin mallakawa Wannan kujerar da nake Kai domin nasan zai kula da komai bisa tsari sannan Kuma zai kula da lamuran ku inada yakinin yareema yaseer zai zame maku Alkhairi a cikin wannan masarauta kiyi iyakar bakin kokarin ki kinji?"
Yanayin ta ne ya canja tana kokarin yin murmushi dakyar tace,
"Kana dagamin Hankali da wannan maganganun naka maimartaba kada rudewar Rashin yareema yasa ka fara tunanin karshen ka ne yazo, Insha ALLAH baza'a dau lkci ba za'a ganshi so ka kwantar da hankalin ka please."
Murmushi maimartaba yyi yana Gyara kwanciyar sa kawai. Hakan yasa mama sarauniya ta fito bayan tayi Masa sallama.
A waje ta hango jakadiya. Kallon ta tayi a tsanake kafin tace,
"Ina neman ki anjima."
Jakadiya tace,
"an gana ranki shi dade."
Tana gama fadin haka itama ta wuce sashen ta bayin dake biye da ita Suna binta a Baya.
~~~~
Music ne ke tashi a hankali acan Sashen yareema Yazeed, kwalbar giyace a hannun sa daga shi sai gajeran wando Yana zaune kan kujera sai babbaka dariya yake tamkar sabon mahaukaci ga 'yan mata Nan tsala-tsala da aka shigo msa shi daga waje da gani dama karuwai ne sai rawa suke a gabansa Suna turo kirji da mazaunai dama ba kayan kirki ne a jikinsu ba daga su sai bra da pant a haka suke takawa a hankali. Wakar ce ta kare Dan haka yareema Yazeed yayi masu alamar suzo, tahowa sukayi su biyu Yana wara hannun sa kowacce ta fada gefen jikinsa.
Cikin yanayi na maye yace,
"saura next step."
Ya fadi Hakan yana sake rungume su. Kamar jira suke Nan suka fara lashe shi tamkar wasu mayu Suna cire Masa wandon dake jikinsa a haka sukaci gaba da lalume junansu shi Kuma Yana numfashi sama2 hade da kamo duk Inda yyi Masa a jikinsu Cike da Nishadi Yana hango makekiyar kujerar sarautar masarautar MANARAS ta zama tashi domin ba Wani mgji namiji yanzu saishi.
•••••
*KAUYEN JIRAGO*
"Meyake damunki ne wai tun dazu na lura kamar akwai Abinda ke damunki ko duk akan mgnr lauwali ne?"
Shema'u ta tmbyi bilqees lkcn da suka isa dandali da dare yanayin nata yafi na kullum sbd damuwa.
Numfashi taja tana tuno dazu bayan ta barshi a wajen sbd shareta da yyi ita kuma ga zuciya saida tayi nisa sosai sai kuma wata zuciyar take tunatar da ita akan Hakan da tayi Sam bata kyauta ba.
Kuma ga dukkan alamu bako ne a Yankin su, ba mmki kurman ne dgske, kila bayajin Abinda take fada, ko kuma a yanayin yadda take Masa mgnr kurame kila a yaren su ba haka ake kwatanta yadda ta sani ba domin ta fahimci duk yadda akai Wani kabilar ne daga wata nahiyar domin baya kama da irin mutanen data saba gani a wajajen su tamkar dai Wani balarabe dayazo daga Yankin larabawa irin Wanda sukejin lbri a bakin Wanda suka fita wajen kauyikan su ko Kuma idan Ana hira a gidan radio tana iya fahimtar Abinda suke fada koda Bata gani a zahiri ba.
Juyawa tayi tana Kara ganin Rashin kyautawarta ta koma Inda yake cike da dimbin tausayin sa. Saidai me? Lkcn data isa wajen Bata ganshi ba bare me kama dashi.
"Innalillahi"
ta furta Hakan tana waige2 ko kadan babu alamar sa a wajen. Take taji hankalin ta ya tashi Nan ta aje kayan ta fara dudduba kusa da Inda take Nan dai amsar dayace baya wajen.
Ta dade sosai tana zagaye wajen Bata ganshi ba haka dai zuciyar ta babu dadi ta koma gida Toh koda ta koma gida ma hankalin ta kasa kwanciya yyi har izuwa yanzu da suka zo dandali hankalin ta na kansa.....
Girgiza ta Shema'u tayi a karo na biyu tace,
"wai tunanin me kike? Nayi mgn baki bani Amsa ba kin fada tunani Kuma."
Cije kasan lips dinta tayi a hankali tana girgiza kanta tace,
"ba komai."
Kyaleta tayi kawai ta aje tiren goron hannunta a gefenta tana kallon yadda 'yan matan kauyen su ke girgiza kugu a gaban meyin kidan kalangu maza na muru Kari Ana shewa.
Itama bilqees ajewa tayi tana kallon wasan da akowanne dare sai me kidan kalangu yazo yyi abinsa Yana Shan ciniki kowa na nishadi ba Arabi bare Boko.
Wani lkcn Kuma masu garaya ne kawai ke abinsu harda masu hawan bori anayi a Wannan kauyen wasa dai kala2 basu san meke faruwa ma a sauran sassan duniya ba kawai rayuwar su sukeyi a haka.
Ji tayi kamar Ana kallon ta, Dan haka ta juya gefenta a hankali da niyar makawa meyin kallon harara Dan haka samarin kauyen keyi mata sai kuma karaf suka hada ido dashi Yana daga can gefe ta cikin daji a bayan wata karamar bishiya Yana kallon ta direct ko kyaftawa babu,
karaf suka hada ido dashi da sauri ta mike tana sauke ajiyar zuciya haka kurum taji dadin ganinsa Shema'u ta kalli gefenta tace,
"Ina Kuma Zaki?"
Bilqees tace,
"Dan Allah kulamin da kayana yanzu zan dawo."
Wasan da ake yasha mata Kai shiyasa kawai ta gyada mata Kai tana Kara juyawa tace,
,"saikin dawo."
Har bilqees ta tafi sai kuma ta dawo tana diban kankana da sauran fruit din a leda tana kullewa.
Ga mmkin ta tana dagowa Kuma sai taga baya wajen a razane ta fara waige2 tana Dan tafiya a hankali.
Kamar da wasa babu shi babu alamar sa.
"Hasbunallahi wani'imal wakil kodai Gamo nayi ni bilqees?"
Ta furta hakan tana dafe kirji tsoro na fara shigarta a hankali.
Har yanzu bata daddara ba kawai tasa Kai cikin dajin tana nemansa da wata er karamar fitilar ta tana haskawa.
Kusan cin karo tayi da Abu a razane ta bude baki zatayi Kara sai taji lallausan hannun sa a bakin nata Yana rufe mata shi.
Bude ido tayi da sauri tana kokarin kwace kanta hade da jero sakin ajiyar zuciya tace,
"Wai Kai Ina kke tafiya ne? Kayita bacewa saikace Wani Aljani ko tsuntsu???"
Gani tayi yyi murmushi yana riko hannunta alamar su tafi.
Kamar wata sokuwa haka ta bishi cikin dajin a haka suka danyi tafiya kadan sannan ya mata alamar ta zauna kan Wani icce da suka isa wajen.
Zama tayi, shima ya zauna.
"Waye Kai???"
Abinda ya fito daga bakinta kenan bayan ta zauna a daidai lkcn da shima ke furta Abinda take fada kenan sukayi Hakan a tare.
Zaro ido tayi tana hade fuska Tace,
"ni namiji ce da zakace waye ni? Saidai kace wacece ke?"
Wani mmkin ne ya sake kamata a daidai lkcn da taji shima ya maimaita exactly Abinda tace babu karawa bare ragewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihin raji'un"
bilqees ta furta Hakan a rude tana kallon yadda bilhakki da gsky kwaikwayon Abinda tace yakeyi batare daya san kalaman dazai furta da kansa ba saikace sabon jaririn da aka haifo duniya ya fara koyon mgn yanzu.
*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*
It's 300 via... Access bank 1445626295
Nusaiba Mustapha
Then show your evidence ta Wannan number👇🏻
***