JANNAH

8

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......8


Muna hanya akai sallar isha'i saboda tukin da yake kamar wanda bashida kuzari atattare dashi, nidai tunda na shigo bance uffan ba kamar an rik'e harshena ko gaidashi kasawa nai, munyi nisa da tafiya ne naji yace mun,


"Kin kalli madubi kuwa?"


Yana kallon hanya yai mun maganar, kaina k'asa nace cikin sanyin murya "ehy na kallah"


"Mekika gani to"


Dan kallonsa nai a sace na maida kaina kasa nai shiru bance komi ba, shima din kamar bazai magana ba sai kuma yace,


"Kema kinga yadda kika canza ko?"


Can kasan mak'oshi na ansa da "uhm"


Daga haka bamu sake magana ba har muka iso gidan nashi, muna fitowa iska ya taso ashe hadarine kwance garin, cikin sauri ya dauko ledojin dake baya ganin sun masa yawa yasa na anshi guda, ya bude gidan muka shiga.


Zubewa yai cikin kujera ya aje ledojin k'asa yana d'age kanshi sama, nima gefe naja na zauna injin yadda gabana yake fad'uwa, a duk sadda muka kasance nida shi agidan daga jiya zuwa yau sai inji gabana yana mugun fad'uwa, tsoro yana kamani na takure waje guda inajin yadda ruwa yake sauka kamar zai keta rufin ya shigo, jinai kamar zan fashe da kuka dama can tsoron ruwa gareni, in ana ruwa zainab nake kwakumewa har agama.


Fuskata na sanya cikin kafafuna ina shashshekar kuka ahankali, saboda ruwa ake inajin harda kankara, ko jiyai ina kukan yai saurin tasowa,


"Jannah, jannah kuka kike? Me akai miki? Akwai abunda nayi maki ne?"


Girgiza kai kurin nayi saboda ban san me zance masa ba, ayadda naji muryarsa duk a kid'ime yake,


"Don Allah kigaya mun, baki son gidan nan ko? Bakijin dadin zaman nan ko? Kiyi mun magana don Allah"


Cikin shashshekar kukan murya na rawa nace, "Ruwa nake jin tsoro"


Bai san sadda yaja gefe ya dafe kaiba, murmushi yana kubce masa ya dau lokaci yana murmushin kafin yace, "please Jannah stop crying, ruwan nan fa bazai miki komi ba,"


"Idan akayi tsawa har suma inayi, don Allah ka kaini inda bazanji karar sosai ba"


Dariyarsa yake dannewa yace, "ok saikin daina kukan sannan"


Shiru nai inajan majina da ajiyar zuciya, hakan baisa na daina jin tsoron ba mik'ewa yai yace "biyoni"


Haka na bisa kamar jela har zuwa dakin danai baccin rana, bude mun yai na shiga ya shigo yana rufe tagogin na sliders, ya Saki labulen da yake manya ne labulayen dakin, sannan ya kunna na'urar dumama daki ya jiyo yana kallona, har sannan fuskarsa da murmushi yace "kinajin karar sosai har yanxu"


Girgiza kai nayi yace, "kiyi salla bari na kawo miki abinci"


Yaja kofar ya fita wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, agidan mu na saba kwano ne ko silin babu idan ana zuba wannan ruwan jinake har cikin yan cikina, akwai ranar da akai wata tsawa agarin mu har gidaje suka fad'i da bishiyoyi, tun ina shekara goma lokacin, a sannan har suma nayi daga lokacin Allah ya sanya mun matsanancin tsoron ruwan sama, saboda in anayinsa da wuya ba'ai tsawa ba.


Yadda naji bana jin karar ruwan sosai yasa na sauke ajiyar zuciya, na rab'e baki gadon ina haka sai gashi ya dawo, tire ne dauke ga hannun sa saurin tashi nayi na ansa cikin sanyi nayi masa sannu,


Ya amsa mun da "yawwa, kinyi sallar kuwa?"


"Zanyi in nagama ci"


Saboda yunwa nakeji sosai alokacin, kamar bazai tafi ba yai tsaye jikin k'ofa ni kuma ina tsakurar soyayyen dankalin turawa da aka soyasa tare da kwai, ga yar miya mai dadi a saka asaka, sai nama balago sai kamshi yake sai lemu da ruwa kasa sakewa nai ganin bai tafi ba, zuwa can yace mun a sanyaye "daga gobe ba lallai mu sake had'uwa time to time ba"


Ahankali nake kallonsa na had'iye abunda nakeci nace, "zakayi tafiya ne?"


Lumshe mun idonsa yai sannan ya bud'e yana cemun, "Daman ba mazauni bane ke kika zaunar dani"


Sake kallonsa nai cikin mamaki zanyi magana ya rigani, "I mean hidimar ciwon baba da kuma daukarki zuwa gida Yasa ban koma da wuri ba"


Rausayar da kai nayi bance komi ba duk da inada tambayoyin da nake son nayi masa, na kasa ne idan na kallesa yana mun kwarjini sosai sai inji na kasa fadar abunda ke bakina,


"Talk to me"


A d'an karatun da nayi inadan jin wasu words din na turanci, cikin rashin fahimta nace "me zance?"


Kallona yake tayi sannan ya cigaba da magana, "kina son tambayata na gani a idonki"


Ai saiya sake sani zaro idanun nawa har naso kwarewa, nasha ruwa sannan na ji sauk'in d'an guntun tarin danai,


"Im sorry nasa kin kware"


Jinjina kaina nayi kurin sannan yace, "zanje inyi salla naci abinci, in kin gama zan sake dawowa"


Ya fice ba tare dana oya fad'ar koda A ba, wannan mutum shu'umi ne na jima ina nazarin maganganunsa haka dai naci na koshi na tashi na shiga toilet don yin alwalla, nazo na fara sallar magriba nai isha'i na had'a sa shafa'i da wutir, na daga hannuna ina rok'on ubangijina neman sa'a da dacewa, da neman kariya daga dukkan masu sheri, don sosai nake cikin zullimin zuwana cikin mutanen da ban tab'a ganin su ba, ina shafa adduar naji yai knocking tashi nai na bud'e masa duk da abud'en take,da alama kayan bacci ne jikinsa don naga masu taushi ne rigar hannunta dogo wandon har wuce guiwa yake, yai kyau sosai duk abunda yasa yana masa kyau ainun,hanya na bashi duk da inajin gabana yana fad'uwa ba abunda ke tada mun hankali irin mu kadaice nidashi agidan nan, bakin madubi yai tsaye yana rubugume hannun sa bayan ya ajiye wata leda mai kaya aciki,


Gefen gadon na koma na zauna ina jin yadda zuciyata take bugawa da karfi, duk munyi shiru kamar ba zamuyi magana ba, jinjina kai yayi yana dan murmushi mamakinta kurin yake yadda kusan halinsu guda.


"Injinki fa"


Na kallesa ahankali ina sassauta muryata, "nifa ba abunda zance maka"


"Aa ni nagani cikin idonki dazun"


Girgiza kai nake kamar kadangaruwa, "Aa ba haka bane"


Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauki ledar yazo ya ajeta gabana duk fuskarsa ta canza, sannan ya juya mun baya yana magana a sanyaye cikin yana yinsa,


"Na dauka akwai tambayar da kike son kiyi mun shiyasa na dawo, saboda daga yau zuwa gobe ba lallai ki sake ganina a kusa ba, ga kaya nan kiyi amfani dasu goben ki tashi da wuri 9:30 zamu fita"


yana gama fad'ar haka ya bud'e k'ofar yasa zai fice............."kaji"


Lumshe ido yayi yana jin sanyi a ransa, sai yai kamar baiji ba zai rufe k'ofar da karfi na sake cewa,

"Yallab'ai *ASAAD* "


murmushi yake son yayi amman ya danne ya dawo baya idonsa sun lumshe kamar bacci yakeji ya tsira mu idanun sa wanda nakejin suna addabata tun ranar farko,


"gani Rakiyadad'e *JANNAH* "


ban san sadda murmushi ya kubce a fuskata ba, na sadda kai kurin saboda ni dariya ma yabani, nice ma rankishidad'e din nadan jima ina murmushin ina wasa da yatsuna sannan nace ahankali,


"Aa niba ita bace, ban kai haka ba"


Gyara tsayuwar yayi don so yake yajata da magana duk da yaga itama miskilarce irinsa, baisan meyasa yake son suyi fira ba,


"Inji wa?"


Ban sake kallonsa ba kaina kasa na bashi ansa da cewa, "inji ni kuma inji kowa ma"


"Aa injikin dai, don abakin ki akaji"


Daga haka ban sake magana ba tsawon lokaci ban son na dago in kamasa yana kallona,hakan yana samun jin ba dadi kallon yana yin yawa.


da gaske bazai magana ba sai na daure nace masa,

"Yallab'ai idan ka tafi taya zan ringa ganawa dasu baba? Sannan inajin tsoron kasancewa da mutanen da zaka sadani dasu tun kafin naje d'in, bayan nan har yanzu ban san komi a kanka ba"


Ajiyar zuciya ya sauke yana nan a tsayen yace, "tafiyata ba yana nufin mancewa dake ba, duk abunda zanyi inayinsa ne akan tsari koda bana nan indan lokacin zuwanki wajensu yayi zakije, zan sa akaiki"


"Meyasa kikejin tsoron kasancewa dasu bacin baki sansu ba, baki tab'a haduwa dasu ba?"


"Haka nan nakejin fad'uwar gaba, kamar wani abu zai iya samuna"


Ya lumshe idonsa yace, "Insha Allahu muddin ina raye bazan bari wani abu ya cutar dake ba, saidai idan *KADDARA* wannan kuma ban isa in hana ta faruwa ba"


Jikina yai sanyi sosai na kasa magana, ya cigaba da cewa "tambayarki ta karshe kuma naga baki damu ki sani ba shiyasa, amman tunda kin buk'ata yanzu zakiji kin shirya ko?"


Na jinjina kai,saida ya dan huta sannan yafata cewa, "Sunana Asaad Abdullahi galadima, ba lallai kinsan babana ba tunda ba nan kuke ba amman duk wanda kace ma Audu galadima da yawa zasu gaya maki waye,babana d'an siyayasa ne shiyasa yai suna sosai As ne na governor maici ayanzu, ma'ana mai ba gwammana shawara, momyna sunanta Hafsatu ita yar niger ce babanta commissioner ne, nine babba agidan mu inada kanne maza biyu mata biyu akwai Hisham shine mai bimun yana da matarsa ma harda d'a, sai Farida itama tayi aure sai usman da Hindatu, karatuna duka nayisu a Spain yanzu haka na kammala PhD dina shekara guda kenan, tun ina karami nake sha'awar kwallon k'afa bayan na gama degree dina na farko akaimun cuku cuku na fara shiga harkokin kwallon, yanzu haka shekarata ta biyar kenan cikin sana'ar kwallon k'afa ina daya daga cikin yan wasan spaim a club din arsenal, duk month inasa albashi mai yawan gaske mun samu d'an hutu ne nazo gida mafarin na had'u daku office din abokina ashir, inajin wannan hutun shine silar had'uwata daku,kinji ko waye ni ba d'an shan jini bane"


Murmushi nayi ina cewa, "Ai zuciyata bata tab'a gaya mun haka ba"


Shima yana murmushin yace, "anya zan yarda"


Ina cigaba da murmushin ban dai ce komi ba,


Mun dade ba mai magana har sannan ana ruwa amman ya rage karfi sosai, kafin naji muryarsa yana cewa,


"Abunda Zan gaya miki shine idan munje gida babu ruwanki da shiga harkar wani, abunda aka baki matsayin aikinki shine zaki maida hankali kiyi, ba ruwanki da duk abunda zaki gani akwai abunda saikinje zaki fahimta, don haka please Jannah ki kula da kanki koda bana nan inajin tsoron wannan Kyan naki, please ki tsare kanki kinji"


Ya fad'a da sanyin murya dagowa nai ina kallonsa shima yana kallona mun tsare juna da ido, kamar an bugan akai nai saurin dauke idona inajin sadda ya sauke ajiyar zuciya cikin sanyi yace,


"Zanje na kwanta dare yayi sosai good night"


Daker na amsa masa da cewa "uhum"


Yaja mun k'ofar ni kuma na silale na kwantar da kaina bisa filo, na rufe idanuna ina ta tunanin maganganun da mukai dashi, da alama cikin gidan nasu akwai rud'ani.


"Ya Rabbil'alamin ka kareni don ikonka, karka ba wani mahaluki damar cutar dani nayi tawassuli dakai da alqur'ani maigirma nayi tawassuli da sunayenka tsarkaka guda casa'in da tara, ka tsareni daga dukkan sharri"


Na fad'a a sarari sannan na cire hijabin najawo bargo nai addua na shafa na kwanta, daker bacci b'arawo yazo ya saceni cike da mafarkai.............









Mom muhseen✍🏻