JANNAH

9

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......9



Saboda cewar da yai da wuri zamu fita yasa tunda nai sallar asuba sai ban koma ba, naita tazbihi ina gyangyad'i har sadda takwas da rabi tayi sannan na tashi ja shiga wanka.


Ban dad'e ba na fito ina duba kayan doguwar rigace irin wadanda ake sawa tare veil din nan irin ta yan gayu amman ba kwalliya jikinta ko kadan, kalar blue black ce mai dogon hannu iyakar wuyan hannun, tun asuba daman na wanke pant din dana saka jiya na shanya sa inda zai bushe,sadda na dauko sa yabushe don fanka na kunna masa duk da sanyin da aka tashi dashi saboda ruwan jiya,rigar tayi mun kyau sosai ni kaina na shaida hakan, nagama kintsawa sannan na fito zuwa falon lokacin tara daidai tayi, kamshi ta ko ina ya baibaye gidan na turaren wuta mamaki ya kamani ba dai shike da wannan aikin ba, ina cikin wannan tunanin naji motsi daga hanyar da zata kai kai kitchen waigawa nai naga wannan kukun nashi yana shirya dining, ga boner a jone jikin socket risinawa yai yana gaidani,


"Good morning madam"


Sai na jinjina masa kai kurin na samu waje na zauna ina kallon tv dake kunne, tunanin su innamu kurin nake ko yasu? Sunyi kewata kamar yadda nake cikin tasu kuwa? Bazan iya ganewa ba ahaka banda waya balle na kirasu wanda ya daukoni har yau bai had'ani dasu ba, wannan kamshin dake shigar mun har zuciya naji ya bakunci hancina nai saurin dago kaina ina dubar hanyar danasan tanan zai b'ullo, saman labbana nake furta "Tabarakallah masha Allah"


Don kuwa yai kyau ainun suit ne dai yasaka amman navy blue rigar cikin fara sai yar falmaran din da coat din da wandonsa sune navy blue din, kafafunsa sanye cikin bakaken sawu ciki hannunsa daure da dankareriyar agogo wanda daka kalla kasan akwai tsada, kunsan yan ball suna son aje suma shid'inma gata nan ya tara gwanin kyau datasha gyara, waya yake yana isowa inda nake zaune ai sai dan danan naji xuciyar zata fito waje, ban yaudari kaina ba duk sadda na gansa gefena gudun zuciyata karuwa yake, bansan dalili ba nasan dai yana mun kwarjini ainun, yana da cikar haiba sosai idanun sa kamar wani mai mai ne aciki idan muka had'a ido jinake idona yana tara ruwa,wani irin kwayar idone Allah yai masa mai daukar hankali, bansan ni shashasha bace saida naji wayarsa bisa kunnena yana cewa, "kibar kallona kiyi magana yayankune"


Wata yar ajiyar zuciya na sauke ina sadda kaina k'asa wayar na hannunsa yasamun ga kunne naji yayanmu na magana, cikin sanyi da doki nace "yayanmu kaine? Ashe zaku tuna dani"


Dariya yayi yana cewa, "kullin yallab'ai yana gaya mana kina lafiya shiyasa bamu tada hankalin mu ba"


Mamakin sa nake don yana gaya masu ina lafiya hakan na nufin sun yarda koda ace ba hannu na gari nake ba, meyasa kudi sun rufe ma yan gidanmu idanu har haka?


"Amman yayanmu duk da haka ai saikace kana son zuwa ka ganni da inda nake din ko"


"Kiyi hakuri murja, ni yanzu bana da ma lokaci sosai kullin ina makaranta course din da aka bani wahala ne dashi dole saina dage, nasan yallab'ai bazai cutar dake ba rayuwarki zatai kyau"


Sai nace masa, "sai anjima ka gaida su innamu"


Raina ya b'aci yadda yake nuna bai damu da inda na tafi ba, dauke kaina nayi daga wayar kurin shi kuma ya kashe yasa aljihu, baice mun komi ba ya wuce dining yana cewa "kizo mu karya"


Har muka gama break din kamar kurame bamai magana, tunda ya sadda kansa bai dago ba saida ya gama kamar bana wajen, ayadda na lura fuskarsa kamar ta canza kamar ransa ya b'aci, to me akai masa? Na tab'e baki na kurin ina daukar tissue kamar yadda naga yayi ya goge bakinsa ya mik'e yace, "ki jirani wajen mota"


Na tashi na wuce wajen motar na jingina da ita ina kallon harabar wurin, ko nan kadai zaka tabbatar gidan yana da kyau, an kawata sa ta ko ina da abubuwan kawata waje, ga flowers nan kala daban daban ruwan da akai yasa sun kara haske, garin da lillami aka atashi yau.


Ina nan tsaye ya fito cikin natsuwa yake tafiya cike da mazantaka yanayin jikinsa kadai zai tabbatar maka shidin dan kwallon kafane, driver ne ya iso cikin sauri gana isowa wajensa ya risina cikin bayar da hakuri,


"Agafarce ni yallab'ai na makara"


Da hannu yai masa nuni da yashiga mota yana jifa masa key din kawai, duk nasha jinin jikina yadda yaketa cin d'acin nan dole akwai abunda yafaru, shigarsa motar yasa nima na bud'e na shiga daga can bangaren sa driver yaja muka dauki hanya hanya kurin yake kallo ta glass din gefen sa, duk banjin dadin wannan abun da yake ko nice nai masa laifin to? Na tambayi kaina sai nasamu kaina da cemasa,


"Yallab'ai nayi wani abunne?"


Yadda ya juyo yana kallona dole na sadda kai kasa, "mikike son ya zarga da kike gaya masa ya kamata yazo ya ganki da inda kike? Idan kinsan baki yarda dani ba meyasa zaki yadda ki biyoni? Ni a tsarina bana son rashin yadda haka bana son zargi, don haka zan maidaki gida shine kawai"


Hankalina tashi yayi cikin duburcewa nake cewa, "Yallab'ai baka fahimceni bane magana ba haka take nufi ba, wallahi ko kusa bana zargin ka da komi, kuma na yarda dakai kayi hakuri don Allah idan ka maidani ban san wani kalami inna da baba zasuyi mun ba, kaji yallab'ai don Allah"


Idona ya cika da kwalla har sun fara zuba, baice mun komi ba hakan ya sake tada mun hankali na saka kaina cikin cinya ina kuka,na dauki lokaci ina kukan sannan naji yace,


"Please............."


Shashsheka nake tayi ina kokarin daina kukan, saboda yadda ya dauki maganar har raina ba haka nake nufi ba, sake mun magana yayi cikin sassauta murya,


*"JANNAH please"*


Dagowa nai ina kallon sa hanky ya mik'o mun yana cewa, "ni fa bance kiyi kuka ba"


Yadda yai maganar kamar wani dan yaro ansa nai ina goge fuskata ina shakar kamshin dake jikin hanky d'in, na mik'a masa kin ansa yai yana jingina bayansa sosai da kujera,


"Ka juya yanzu mun fasa gida zamu mannir"


Ya amsa cikin girmamawa sannan ya jiyo yana dubana yatsuna kurin nake ta tsifa, d'an matsowa yai kusa dani har saida gabana ya fad'i murya kasa-kasa yake magana,


"Duk abunda kikaji na fad'a idan mun isa karki sake ki nuna ba gaskiya bane, sannan zaki cigaba da karatu insha Allah Amma lokacin na tafi zan dora nauyin hakan akan usman"


Jinjina kai nayi bance komi ba yaja iska kadan sannan ya dan kallan yace, "fushi kike?"


Saurin kallon sa nai nace, "Aa fa"


Lumshe idonsa yai daga nan har Allah ya iso damu nasarawa bamu sake magana ba,

Girman gidansu yallab'ai kadai dole ya baka mamaki, babbane katon gaske harda bene asama saidana kilga get uku ne garesu, gidan fa ba karya duniya kenan bed'e mana akai muka shiga cikin harabar gidan, anan na fahimci bangare bangare garesa gidan, ga motocinan sai numfashi suke dirma dirma babu wadda tasha jiki acikin su, jinai gabana yana fad'uwa sosai sai na tuna maganar anty jamila da tace nayi addua, dan danan na kamayi inajan ajiyar zuciya.


"Are u OK?"


Ya tambayeni firgicin daya gani tare dani yasa bai fita ba yace mun, "ki natsu pls babu abunda zai sameki insha Allahu kinjiko"


Na d'aga kaina kurin sannan ya bud'e yafita na bisa abaya adduar nake tayi ina biye dashi har zuwa babbar kofar da zata sadaka da cikin gidan, gaba daya bangwayen tayils ne mai dan karen sulb'i, kofar ma da maddanni ake bud'eta muka shiga saida muka wuce wani karamin falo da kujeru guda uku harda tv a wurin, sannan muka sauka daga wani dan bene hawa shidda sannan muka shigo katafaren falon mai dauke da set din kujeru guda biyu, ga faskekiyar tv nan da kayan kallo, kai idan na tsaya fayyace gidan bazan gama ba gidansu yallab'ai karshene..........."zauna anan ina zuwa"


Yace dani, zama nai cikin daya daga cikin kujerar mai laushi inata cigaba da kallon falon, shi kuma yabi wata hanya ya b'ace ma gani na.................







Sai kunyi hkr dani akan posting, banda lafiya isassa ba kullin zan ringa typing ba ina fatan zaku mun uziri, na yau ma karfin haline ngd da kaunarku




Mom muhseen✍🏻