ZAMANI... riga kowa da irin na shi
01
ZAMANI...
*Riga kowa da irin nashi*
Na
Rahma Kabir mrsMG
Wattpad @rahmakabir
Page 01.
MARUBUCIYAR:-
Rayuwar Suhailat
D'an Amana
Kad'aici
So ne Sanadi
'Yar Shugaba
Mai Hakuri
Karshen Makirci
So Sartse
Da iyayena
Kaddararren Al'amari
Akan Idona
Hantsi
Lubabatu
Kazamin Tabo.
Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. ***
*Idan kuna bukatar a tallatar muku hajar ku a pages ko a daura a status ku tuntubi wannan number ***, zaku samu akan farashi mai sauki.*
_Duk kan Godiya ya tabbata ga Allah Ubangijin mu, shi kaɗai ne ba shi da Abokin tarayya. Tsira da Aminci su k'ara tabbata ga fiyayyen Halitta Monzon tsira s.a.w, tare da Ahalinsa da Sahabbansa._
*Gargad'i*
_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, ko a daurafin shi a wata kafa ba tare da izini naba, dan Allah a kiyaye_
*Sadaukarwa*
_Ga ga duk masoyana, ina godiya Allah ya bar zumunci da kauna-
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
HIBBA.
Unguwar kanawa layin minista, gida mai lamba na uku a jerin farkon layin, babban gida ne mai dauke da dakuna ciki dai dai guda takwas wanda duk yan haya ne ke cikinsu, akwai babban zaure kafin a shiga sannan daga gefen dama akwai bandakin wanka da bayan gida, sai daga gefen hagu akwai babban bishiyar mangwaro sai kicin dake gefensa wanda yake dauke da murhunan mazauna gidan, kicin din yayi baki sosai saboda yawan girki sannan ga shi ba windo ba kofa. A hargitse gidan yake kamar yadda mazauna ciki suke rayuwa cikin latauci duk sun fice hayyacinsu, haka suke yin rayuwa hannu baka hannu kwarya. Hibba ce ta shigo gidan da sauri ta fada dakinsu ta ajiye jakar makarantarta da hijab sai ta fito da gudu ta shiga ban daki tayi fitsari, tun a makaranta ya matseta taki yi saboda kankyamin bayin take duk da na gidansu ba wani mai kyau bane amma ba laifi suna wanke shi kullun. Tana gamawa ta fito tana sauke gauron numfashi saboda dadin data ji akan mararta da ta saki, sai ta shiga dakinsu ta mai da hijab dinta ta dauki wayarta da chargy ta fito ta leka dakin Innansu tana cewa.
Inna zan kai chagyn wayata gidan Haj. Sa'a ta kusa daukewa kuma zanyi karatu da shi anjima.
Hibba har kin dawo, Ina ganin dai malam Hamza ya kusa ya dauke ki koyarwa a makarantarsa, tunda naga ba a sati bai ce kije ki rike masa aji ba.
Kila ya dauke ni amma inna fara karatu kinga hakan ba zai yuwu ba, inna bari naje na kai wayar lokaci yana tafiya karsu dauke wutar.
Amma Hibba ni ko bana son kina shiga gidan matar nan, kinga surutun mutane yayi yawa akanta, amma dai kije karki zauna ki dawo yanzun nan saboda magriba ta kusa kuma babanki yana gabda shigowa, inya so anjima sai ki aika Ali ya amso miki.
Da to ta amsa kana ta wuce. Gida uku ne a tsakanin gidansu dana Haj. Sa'a, nan take kai wayarta chargy duk lokacin da aka yanke musu wutar nepa, dan yau kusan satinsu uku ba su da wuta an yanke musu, sannan mutanan gidan sun kasa hada kudi su biya a mayar musu, shiyasa bashi yayi musu yawa sosai sai wanda yaga dama ya gaji da duhu shi ne yake bawa yan unguwa ɗan hasafi su mayar musu, wata na karewa kuma nepa su zo su kara yankewa, ansha guntule musu igiyarsu akan maida wutar da suke yawan yi ba tare da sun biya ba amma hakan bai sauya zani ba. Hibba ta isa gidan ta tura gate ta shiga ta wuce kofar shiga falo ta kwada sallama, daga ciki hajiyar ta amsa sai ta shiga ciki tare da gaisheta, sannan ta daura da cewa.
Hajiya karki gaji dani yau ma chargy na kawo, zanyi amfani da wayar ne anjima.
Haba Hibba yau da gobe karyata boka ai mun riga mun zama daya karki damu. Amma gaskiya ya kamata ace yan gidanku suna daurewa su hada kudin wuta dan zama a duhu ba dadi.
Kyashi da mugunta ba zai bari su hada kudin ba, abu in dai akace ba naka bane ai sai hakuri, gida ne na haya koya yana zaman kansa.
To Allah ya kyauta.
Ameen. Ummm dan Allah kina da sauran abinci ki bani yunwa nake ji wlh, dan yanzu na bar Innanmu na daura sanwa.
Hibba ta fada tana sosa keya, Hajiya tayi dariya saboda ta san halinta da wuya tazo gidan bata roketa wani abu ba, dan haka shiyasa ta saba da ajiye mata abinci, wataran har sanwa take karawa da ita. Hajiyar ta nisa sai tace cikin wasa.
Ai har kwano nayi miki a gidan nan saboda nasan wajibi ne ki zo.
Hibba tayi yar dariya.
Ai girkin ki ne akwai dadi, ina samun sauyin magi fiye dana gidanmu.
Allah dai ya rufawa kowa asiri ku ci mai maiko.
Hibba tace Ameen tana gyara zama akan cushing din dakin, ta saba sosai da haj. Sa'a saboda kirkinta sannan itama Hibban bata yi mata kuiya wajen aike, sannan kuma duk kawo chargy da take yi hajiyar bata gajiya da sanya mata, duk a unguwar babu yarinyar data saki jiki sosai da ita sama da Hibba, shiyasa itama take kyautata mata sosai. Haka Hajiya ta kawo mata tuwon semo miyar kuka wanda yaji dambun naman kaza, Hibba ta amsa ta soma ci tana santi tare da surutun zata zo ta koyar da ita yadda take girkin zamani, dan ita burinta tana so ta iya girki kala kala wanda in tayi aure tana girkawa mijinta. Hibba ba ita ta koma gida ba sai bayan sallar magrib, tana shiga gidan ta wuce dakinsu suf suf kamar munafuka dan kar Innarsu ta ji yanzu ta dawo, tana bude labule sai ta ganta zaune a gefen gadonsu tana ninke kayan Ali data wanke masa, da wani mugun kallo ta bita kana ta ce cikin fada.
In ba zaki shigo ba ki sakar min labule.
Hibba ta shigo tana rarraba ido tare da cewa.
Inna kiyi hakuri, hajiyar ce ta aikeni kan dam shiyasa ban dawo da wuri ba.
Hibba ina ganin lokaci yayi da zan rabaki da gidan matar nan tunda ke ba mai jin magana bace, saboda kowa ya san ba tada miji zaman kanta take yi, kullun maza ne ke sintiri a gidanta, ina kyaleki ne kina hulda da ita ganin na dauke ki me hankali zaki iya kame kanki, dan da ace na ji ta shawarar mutane da tuni na raba ku. Amma yanzu ya zama dole ki daina kai mata chargy ni zan dauki nauyin baki naira ashirin kina kaiwa Bala me chargyn waya, hankalina zaifi kwanciya.
Amma inna be dace kuna jefarta da mugun zato ba, koda ace mazan take kawowa addu'a za kuyi mata domin kaddararta ce tazo a haka, sannan bamu san dalilin zamanta ita kadai a haka ba, ni dai banga aibin zuwana gidanta ba tunda wlh bata taba nuna min mugun hali ba.
Wato ban isa dake ba kenan.
Ba haka nake nufi ba, Kawai dai ina fada miki raina ne kin san bana iya boye magana.
To Hibba in kin so karki fasa zuwa ni nasan matakin da zan dauka.
Hibba ta turo baki ba tare da ta kuma yin magana ba, sai ta cire hijab ta fito tsakar gida dan tayi alwala, Inna tayi kwafa tana kara jaddadawa a ranta dole ne ta shiga tsakaninsu dan gudun kar ta batawa Hibba tarbiyyar da suka jima suna yi.
Bayan sallar isha'i Hibba ta sidade ta fice da sauri dan ba zata iya jiran Ali ya dawo ba harta aikeshi amso wayarta. Tana shiga falon Hajiya ta samu bako zaune yana shan drink, ta zauna a carpet ta gaishe shi ya amsa tare da sanar da ita hajiyar tana ciki, sai da ta bata minti goma sha daya a zaune kafin daga bisani Hajiyar ta fito sanye da kanunun kaya wanda suka matseta tayi parking gashinta tare da caɓa ado sai kamshinta ya gauraye dakin, Hibba ta bita da kallon mamaki domin bata taba ganinta da irin wannan shigar ba, Hajiya tana ganinta sai duk taji wani irin domin ta san Hibba bata ganinta da irin wannan shigar, da sauri Hibba ta mike ta katse mata tunaninta tace.
Hajiya waya nazo amsa.
Ai Hibba da kin dauka ba sai kin jira ni.
Hibba ta bata hakuri kana ta wuce ta dauki wayar ta fice da sauri duk jikinta a mace, ta shiga tunanin yadda taga hajiyar, kenan duk abinda ake fada akanta gaskiya ne.
Ko me yasa ta sanya rayuwarta a cikin wannan yanayin oho, to Allah ya sa ta shiryu.
Tace a zuciyarta kana ta shiga gida, tun daga tsakiyar cikin gidan ta jiwo fadan baba wanda ta san akanta yake yi, a hankali ta shige daki tana muzurai, ta samu Ali yana cin tuwo ya kalleta yace cikin wasa.
Yau zaki sha dukan tsiya domin baba yace babu abinda zai hana ya dake ki tunda kunnen kashi gareki.
Na shiga uku wai Inna sai da ta fadawa Baba kenan.
Ki je dai ki ji, tace in kin shigo ki same su a daki.
Hibba taja guntun tsaki cike da fargaba ta mike, ta san yau ta shiga uku dan fadan baba ba sauki har gwara ya bigeta akansa. Ta fito ta shiga dakin da sallama, irin kallon da suka bita dashi ya tabbatar mata da ta kade, ta samu gefe ta tsuguna, baba dake cin tuwo ya tsame hannunsa daga kwano ya dago rai bace yana dubanta.
Muhibbatu ke wani irin kunnen kashi gareki, kullun ayita maganar abu guda, na gaya miki da zarar magarib tayi na haramta miki fita amma kin kiji, to Innarki ta gayamin iskancin da kike yi mata, wlh in baki wasa ba zan maidaki can kauye wajen gwaggo ki zauna a gunta in kin samu miji ta aurar dake, ko kuma in katse miki karatunki na bada aurenki sadaka na huta.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Wlh baba na tuba ba zan sake ba.
Hibba ta ce cike da tashin hankali dan ta san muddun Baba ya yanke hukunci tofa ta kade, babu mai iya sauya masa shi dan kaifi dayane.
To karki natsu ki gani wlh ina gabda yanke miki danyan hukunci. Da ina tunanin saki a makarantar gaba da sakandiri ki kara ilimi dan ina so ku samu gishirin zaman duniya fiye damu da bamu yi ba, amma kina niman watsa min kasa a ido.
Kayi hakuri baba insha Allah zan gyara, kuma zanyi karatu kamar yadda kake so nima burina nayi ilimi wanda zan samu abinda zan rufa mana asiri.
Ai mu asirinmu a rufe yake, in kika yi wasa naki ne zai bankade.
Hibba ta cigaba da bashi hakuri har sai da inna ta sanya baki kafin ya yi mata afuwa kana ta dawo daki tana kananun magana a ranta.
To wai duk iya kokarina akan kiyaye bacin ransu amma basa gani, ni banga aibin duk abinda nake yi ba tunda ba wani abun ashsha nake yi ba.
Ta kare maganar tana zama a bakin katifarsu cike dajin haushi.
*****
Da safe Hibba ta gama shirin fita zuwa makarantar bokonsu, wanda za suyi walimar fitarsu na kammala secondary, atamfar sallar bara daya wuce ta sanya fes take bata sha jiki ba, tayi kwalliya dai dai misali, sai dai har cikin zuciyata shigarta bai yi mata ba, burinta bai wuce tayi shigar kece raini ba wanda yayan zamani suke yi masu ji da kansu, sai dai ba yadda zata yi dole ne tayi amfani da abinda Allah ya hore musu domin gutun gatarinka yafi sari ka bani, ta sanya hijab wanda ya wuce guiwarta wanda a cikin ranta take jin ina ma da tana da gyale mai kyau ta sanya duk da ba sawa take yi ba, ta taso cikin sanya hijab sam innarsu bata yarda ta sanya gyale ba kuma a makarantar islamiyarsu malamai suna ja musu kunne akan sanyawa, dole ta saba da hakan duk da a can kasan zuciyarta tana so, amma sabida babu fuska yasa ta saba da hijab sosai. Ta fito sai kamshin turare dan ɗuri take yi, sai ta shiga dakin inna ta sameta tana daura gyada me gishiri a leda na siyarwa, inna ta dago ta kalleta.
Hibba wannan irin turare da kika bubbula a jiki fa sai kamshi ke tashi, kin san dai babu kyau aji jikin mace yana fitar da kamshi haka har ta fita da shi wani na miji yaji yayi sha'awarta, sannan ga wani kwalliya da kika yi sai kace gidan biki zaki, wai ko ba makaranta zaki bane?
Inna meye aibin kwalliyata yau fa muke yin walimar fitarmu secondary, kuma kowa zai yi fitar ke ce raini ne dan har kyauta za a bawa wanda shigarsa yayi zarra data kowa.
To maza kije ki wanke fuskarki bana son iskanci, makaranta zaki ba gidan biki ba.
Hibba ta turo baki tana cewa.
Ni dai Inna ban san meyasa kike takurawa rayuwata ba, kuma ni banga duk aibun abinda nake yi ba tunda ina kokarin kiyaye bacin ranku.
Hibba ni kike fadawa haka? Yanzu ban isa na kula da tarbiyyarki ba sai ya zama takura, to bari kiji bazan taba zuba miki ido kiyi yadda kike so ba tunda kiwonki Allah ya bamu.
Hibba ta wuce fuuu ranta a bace ta ficewarta, inna tana kwala mata kira amma taki dawowa, kwalliyar data ki wankewa kenan ta wuce gidan Hajiya sa'a cike da jin haushin takurata da Inna ke yi.
Ta samu Hajiyar tana sanya lallen gargajiya a hannunta, ganin Hibba yasa ta saki dariya tana cewa.
Mutumiyar wannan kwalliyar fa sai ina haka?
Walimar fitarmu secondary zani, amma sai naga shigata sam bata yi tsari da zuwana wajen ba, kamar ma na fasa zuwa.
Haba Hibba aiko kinyi kyau sosai.
Ni dai Hajiya alfarma nazo nima a wajenki.
Ta me fa Hibba.
So nake ki aramin wannan pink din lafayarki na sanya, ina ganin zanfi kyau sosai.
Eh gaskiya na tabbatar in kika sanya shi zaki hadu matuka, bari na dauko miki harda jaka da takalmi dan zaifi kyau ki sanya me tudu, ina ganin size dinmu daya ne dan 39 nake sanyawa.
Ni ina sanya 38 ko 39 karamin size kila zai yi min.
Hajiyar ta mike da sauri ta isa dakinta, ba jimabawa ta fito rungume da kayan da dayan hannunta mara kunshi, Hibba ta mike tana washe baki ta karbi kayan ta zame hijab dinta ta soma daura lafayar Hajiyar tana tayata sanyawa yanda zai zauna mata sosai a jiki, cikin kankanin lokaci Hibba ta shirya, ta sanya takalmin yayi mata dai dai, ta soma washe baki tana yabawa shigarta, Hajiya sai yaba mata take yi ta dauketa hoto a wayarta saboda kyan da tayi mata sai ka ce kanuri ko shuwar asali, haka Hibba ta fito sai wani sihirtaccen kamshi ke tashi a jikinta domin lafayar an turareshi akan kabbasa da turaren kaya me dadin kamshi, tana fitowa daga gidan ta fara taku dai dai kamar wata sarauniya, ji take kamar ba ita ba, mutanen unguwar kuwa sai kallonta suke tamkar madubi, wani dadi take ji har cikin ranta, ashe haka kyakkyawar shiga ke sanya mutum ya zama tauraro, ina ma zata dawwama da sanya kaya masu daukar hankali mutane haka. Aliyu kaninta yana ganinta sai ya wuce gida da gudu ya sanar da Innarsu da ta soma wanki a tsakar gida shigar Hibba, ya kara da cewa.
Daga gidan Hajiya Sa'a ta fito.
Inna ranta yayi matukar baci sai ta wuce daki ta sanya hijab dinta ta fito tana surfa masifa, matan gidan suna ta ya ta tare da kara zugata akan ta shiga tsakanin Hibba da Hajiya Sa'a, in ba haka ba zata lalata mata tarbiyya, Inna ta fice cike da bacin rai zuwa gidan Hajiyar, Maman Abba wacce dakinta ke jikin nasu Hibba ta zura gyale tabi bayan Inna dan ta tayata fadan, sannan ta samu damar guntsar gulmar da zata fesawa mutane.
Taku
Rahma Kabir