ZAMANI... riga kowa da irin na shiFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

ZAMANI... riga kowa da irin na shi

  • 1views
  • 11chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

Ongoing

No synopsis yet.

About the author

Marubuciyar littafin hausa

More from @rahmakabir13

Sample · 01

ZAMANI...  *Riga kowa da irin nashi*NaRahma Kabir mrsMGWattpad @rahmakabir Page 01.MARUBUCIYAR:-Rayuwar SuhailatD'an AmanaKad'aiciSo ne Sanadi'Yar ShugabaMai HakuriKarshen MakirciSo SartseDa iyayenaKaddararren Al'amariAkan IdonaHantsiLubabatuKazamin Tabo.Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. *** kuna bukatar a tallatar muku hajar ku a pages ko a daura a status ku tuntubi wannan number ***, zaku samu akan farashi mai sauki.*_Duk kan Godiya ya tabbata ga Allah Ubangijin mu, shi kaɗai ne ba shi da Abokin tarayya. Tsira da Aminci su k'ara tabbata ga fiyayyen Halitta Monzon tsira s.a.w, tare da Ahalinsa da Sahabbansa._*Gargad'i*_Ban yarda ayi afmani da wani b'angare na wannan labarin ba ko kuma satar fasaha, ko a daurafin shi a wata kafa ba tare da izini naba, dan Allah a kiyaye_*Sadaukarwa*_Ga ga duk masoyana, ina godiya Allah ya bar zumunci da kauna-BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMHIBBA.Unguwar kanawa layin minista, gida mai lamba na uku a jerin farkon layin, babban gida ne mai dauke da dakuna ciki dai dai guda takwas wanda duk yan haya ne ke cikinsu, akwai babban zaure kafin a shiga sannan daga gefen dama akwai bandakin wanka da bayan gida, sai daga gefen hagu akwai babban bishiyar mangwaro sai kicin dake gefensa wanda yake dauke da murhunan mazauna gidan, kicin din yayi baki sosai saboda yawan girki sannan ga shi ba windo ba kofa. A hargitse gidan yake kamar yadda mazauna ciki suke rayuwa cikin latauci duk sun fice hayyacinsu, haka suke yin rayuwa hannu baka hannu kwarya. Hibba ce ta shigo gidan da sauri ta fada dakinsu ta ajiye jakar makarantarta da hijab sai ta fito da gudu ta shiga ban daki tayi fitsari, tun a makaranta ya matseta taki yi saboda kankyamin bayin take duk da na gidansu ba wani mai kyau bane amma ba laifi suna wanke shi kullun. Tana gamawa ta fito tana sauke gauron numfashi saboda dadin data ji akan mararta da ta saki, sai ta shiga dakinsu ta mai da hijab dinta ta dauki wayarta da chargy ta fito ta leka dakin Innansu tana cewa.Inna zan kai chagyn wayata gidan Haj. Sa'a ta kusa daukewa kuma zanyi karatu da shi anjima.Hibba har kin dawo, Ina ganin dai malam Hamza ya kusa ya dauke ki koyarwa a makarantarsa, tunda naga ba a sati bai ce kije ki rike masa aji ba.Kila ya dauke ni amma inna fara karatu kinga hakan ba zai yuwu ba, inna bari naje na kai wayar lokaci yana tafiya karsu dauke wutar.Amma Hibba ni ko bana son kina shiga gidan matar nan, kinga surutun mutane yayi yawa akanta, amma dai kije karki zauna ki dawo yanzun nan saboda magriba ta kusa kuma babanki yana gabda shigowa, inya so anjima sai ki aika Ali ya amso miki.Da to ta amsa kana ta wuce. Gida uku ne ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters11
premium4
08

13

Premium
Updated 5 months agoAvailable now
09

14

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
10

Page 15 and 16

Premium
Updated 6 months agoAvailable now
11

17

Premium
Updated a year agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play