SARAUTAH TAH CE

11.

by @nuceeyluv

👑👑👑👑👑


*SARAUTA TAH CE*





*Free page*






*Wattpad*

@nuceeyluv






By

Nuceeyluv😘







11....





Ganin yadda yaga hankalin ta ya tashi sosai yasa shi kamo hannun ta a tsanake yana girgiza Kai yace,


"I don't know who I'm."


Bilqees ta wara ido d mmki, Tace,


"kamar naji kana yaren nasara?"


Dan yamutsa fuska yyi yace,


"meye yaren nasara?"


Bilqees tayi shiru tana tunanin yadda Wani malamin primary dinsu ke koyar dasu yakan danyi masu turanci daga Baya dayaga basa fahimta sai kawai karatun ya koma da Hausa zallah ko fillanci, dukda ba Wani karatun Azo a gani akeyi a makarantar ba. Tace,

 

"Ingilishi."


Gani tayi yyi murmushi kadan Yana kawar dakai yace,


"bansan meye Wannan ba." 


Bilqees tace,


"toh yanzu Kai daga Ina kazo?"


Fuskar sa a Dan hade yace,


"nace maki bansan waye ni ba."


"Oh..."


Bilqees ta furta tana hangame baki tace,


"Ikon Allah, yanzu bakasan waye Kai ba? Amma Toh taya kazo Nan? Kodai fatakai ne sukayi maka fashi? Ko kuwa daga Yankin larabawa ka bullo shine kayi batan hanya? Ba mmki ma kila fadowa kayi ta jirgin sama da yake diban larabawa....."


"Enough... Enough pls."


Taji ya furta Hakan da Dan tsawa Yana toshe kunnuwan sa. Fuskar sa a hade yace,


"what's exactly wrong with you? Kinata min tmby babu coma bare full stop, taya kike tsammanin ni zan iya baki Wannan amsar? I hate noise."


Ya furta Hakan yana juyowa gareta sai kuma yaga bata wajen. Mikewa yyi da sauri Dan harta fara tafiya. 


"Wait..pls wait."


Ya furta Hakan da sauri yana kamo hannun ta. Kwace hannun tayi tana kokarin ci gaba da tafiya ya sake riko hannun dakyau Yana jawota baya kadan ya rage ta fada jikinsa ta gyara da sauri tana juyowa hade da ballo Masa harara...


Kama baki yyi d mmki yace,


"me nayi Kuma?"


Bilqees tace,


"Tmby kke me kayi? Bayan duk irin tsawar daka gama min? Sannan harda Wani na isheka d tmby. Toh sai kayi ta yawo a dajin Kai kadai tunda bakason taimako."


Dafe goshi yyi yace,


"okay srry"


Ya furta Hakan dakyar hade d cije lips dinsa na kasa yanajin kamar Sabon Abu ne a gareshi furta Kalmar hakuri.


Hararar sa tayi tace,


"Soron gidanku."


Tana gama fadin haka ta juya. Harde hannayen sa yyi a kirji yana binta da kallo batare da yyi kokarin dakatar da itan ba sbd 'yan mulkin sun motsa...izzar ta taso shiyasa shima ya juya Baya Yana tafiya batare da yasan Inda zaije ba.


Rintse ido tayi tana cije lips a daidai lkcn data tsaya kikam batare data ci gaba da tafiyar da take ba...tanaji a ranta ya kamata ta saurare shi, ta Kuma yi Masa kyakkyawar fahimta, Da Wannan tunanin ta juyo Dan komawa wajensa. 


Can ta hango shi ya duka kasa Yana taba kafarsa da sauri ta isa wajenshi tana kallon kafar da yake tabawa a hankali. 


Haska fitilar wajenta tayi tana karewa wajen kallo har lkcn be dago ba kansa a duke Yana taba kafar. A hankali ta tsugunna gabansa Nan taga Ashe kaya ya taka ya kasa cirewa. 


"Ya salam" 


Ta furta Hakan a Fili tana Kai hannunta kan kafar taga ya janye d sauri. Dagowa tayi da mmki sai taga fuskar sa a hade Yana shirin barin wajen bilqees tayi kokarin riko shi Amma ya zame Yana ci gaba da tafiya normal tamkar ba kayace a kafar ba. 


Binshi da kallo tayi ranta na sosuwa da irin Wannan kyaluwar daya nuna mata daga Dan zaman da tayi dashi ta fahimci Yana da ji da kansa jifa2 sai ya dinga Wani cizewa tamkar Wani basarake. 


Tsaki taja kawai ta sake juyowa batare data Kara waiwayar sa ba tayi hanyar dandalin su. 


Ana kan yin wasa har yanzu bilqees ta isa wajen zuciyar ta babu dadi. Shema'u data gaji da neman bilqees ta hangota tsaye jikin Wani Dutse ta harde hannu nesa dasu kadan. 


Isa wajenta tayi da mugun mmki take binta da kallo tace,


"dama kina Nan wajen naketa neman ki ban ganki ba?"


Bilqees tayi mata shiru Bata Amsa ba. Shema'u ta girgiza ta tana sake fadin,


"dake nake mgn fah." 


Dan karamin tsaki bilqees tayi kafin tace,


"banajin dadin jikina ne yau." 


"Ai ko baki fada ba Naga alamar haka bilqees, Kuma nasan duk akan zancen lauwali ne. Toh Dan Allah ki daina damuwa Insha Allahu lauwali sai dai Hange daga nesa Amma bazai taba zama mijinki ba kinji?"


Dan numfashi bilqees taja damuwar kam harda ta lauwali dayar damuwa kuwa ta Rasa dalilin dayasa take damuwa akan mutumin da Bata sanshi ba bare asalin sa. 


"Muje mu tafi yadda Zaki samu ki kwanta da wuri kinji?"


Shema'u ta furta Hakan tana daukar turen su ta mikowa bilqees kudin hannunta tace,


"gashi anyi ciniki yau saura kadan."


Godiya bilqees tayi mata sannan suka fara takawa Shema'u na Bata baki akan lamarin lauwali a haka suka isa gidan bilqees dai saidai tace eh ko a'a domin Rabin tunanin ta Yana ga bakon gari.



^^^^

Washe garin ranar da sassafe bilqees ta tashi tana share gidan nasu hade dayin wanka da wuri. 


Inna habi dake gaban wuta tana girki ta Kira bilqees data fito wanka yanzu. 


"Na'am"


bilqees ta Amsa kiran tana juyawa Inda inna take. Inna habi tace,


"Ina Zaki ne da sassafen Nan naga Duk kinyi ayyukan ki da wuri?"


Bilqees ta danyi murmushi tace, 


"yau gidan yaya Atika zan Kai ziyara gabashi."


Inna habi tace,


"haba koda naji naga ne Duk kin shirya da wuri. Amma bayan Wannan meya hanaki bcci jiya?"


Gwalo ido tayi d mmki tana tuna daren ta na jiya, gaba1 rabi da Rabi tayi bcci jiyan nan bakon gari ya tsaye mata a rai matuka. 


Tausayin sa ne ke Kara ruruwa a ranta musamman idan ta tuna cewar ya fada mata wai besan waye shi ba. Besan daga Ina ya fito ba, idan Banda kaddara zabgegen saurayi kamar Wannan ace besan kansa ba? 


Ta dade tana tufka da warwara a daren Nan dakyar da sidin goshi bcci barawo yyi awon gaba d ita saidai asubar fari ta farka da tunanin sa ba shiri ta mike tana tunanin mafitar daya dace..... 


"bilqees" 


inna habi ta girgiza ta ganin tayi shiru Bata Bata Amsa ba saima tunani data fada, bilqees ta saki murmushin yake tace,


"ba komai."


Girgiza Kai kawai inna habi tayi tana tunanin ba komai ke damun bilqees ba sama da zancen mahaifin ta da lauwali.


Mikewa tayi ta wuce daki tana fatan ace ta fice daga gidan batare data ci karo da kowa na gidan nasu ba. Cikin mintuna kalilan sai gashi ta shirya tsaf. Sannan ta Kara wasu fruit din a ledar data Kai masa jiya wacce yaki kulawa bare yaci. 


Inna habi tayiwa sallama bayan ta karbi sakon da zata kaiwa yaya atika.


Fitowa tayi a gurguje tana sauri Bata daina Wannan saurin ba kuwa Saida taga tayi nisa da gidansu sosai kafin ta saki hanyar da take kyautata zaton acan zata sameshi. 



••

"BILQEES...ke bilqees"


Mlm Musa ya fado gidan Yana rafka mata Kira Jim kadan bayan ficewar bilqees din. Inna habi dake tsakar gidan tace,


"lpy mlm?"


Mlm Musa yace,


"Ina Wannan yarinyar take?"


Inna habi tace,


"Bata Nan."


"Ban gane ba."


Cewar mlm Musa Yana hararar inna habi. Inna habi tace,


"na aiketa gidan Atika."


Wani dogon tsaki mlm Musa yaja tamkar bakinsa zai fice ya juya fuuuuu Yana barin gidan izuwa waje. 


Yana tsaye bakin kofar gidan ya iso gareshi. 


"Baffa har an Samo ta?"


Lauwali ya furta Hakan yana gyara tsayuwa. Mlm Musa yace, 


"uwar yarinyar ta aiketa zuwa wajen yayarta saidai ko anjima sai kazo ku gana."


Lauwali yace,


"Kassh gsky naso ace mun hadu yanzu Amma babu damuwa indai akan bilqees ne Ina iya hakuri."


Mlm Musa yace,


"Madallah ya kukayi da magabatan naka jiya?Dan nace kwana uku ma ya wadatar a daura aure."


Murmushi lauwali yyi yace,


"gsky baffa kana birgeni saidai akwai Abu daya."


Mlm Musa yace,


"me kenan?"


Lauwali yace,


"na canja tsarin zuwa Nan da wata daya domin inason duk Inda mabiyana suke lungu da Sako, ramuka da kwazazzabo...mutane da Aljanu....kwari da tumakai... kyankyaso da macijzai...zakuna da Aladu duk susan da bikin sarkin dawa lauwali, lauwali uban dawa Wanda ya gagari mutane tsoho da tsohuwa...yaro da yarinya kai hatta Aljanu ma shayina suke Dan haka nakeson na shirya gagarumin bikin da tunda ake ba'a taba yin biki irinsa a Yankin kauyikan Nan ba."


Zufa ce ta gama jike jikin Mlm Musa tsoro na Kara shigar sa...cikin ransa na Allah Wadai da Wannan haduwar ta lauwali da bilqees. 


A Fili kuwa yace, 


"Wannan shine asalin kalar uban dawa, Hakan zaisa kowa ya Kara fahimtar jarumtar ka lauwali. Muna maraba da Duk bataliyar daka kwaso Mana hatta tsuntsayen dake shawagi ma Ana gyayyatar su."


Lauwali yace,


"shiyasa nake yinka baffa domin kanada matukar fahimta sosai."


Murmushi yyi cikin ransa kuwa takaici na sake kama shi a haka lauwali yyi masa sallama ya tafi Yana tangadi.




*MASARAUTAR MANARAS*



kallon kallo ne ya afku akan hanyar mama sarauniya tare da amaryar sarki Hajia Mairo, kowacce bayinta na take mata Baya. Kai tsaye kowa ya wuce bayan an gama musayar kallo kafin Nan Hajia Mairo ta wuce sashen Gimbiya Falmata Kai tsaye. 


Dan dakatawa mama sarauniya tayi tana juyawa a hankali ta kalli bayanta sai kuma kawai ta juyo gaba tana me ci gaba da tafiya batare data yi yunkurij komai ba. 


Tana Dan kishingide akan lallausar kilisar ta aka sake Aiko baiwa a karo na biyu Hajia Mairo na neman izinin shiga wajen Gimbiya Falmata. 


Kamar bazata amince ba, saidai ta Amsa dakyar tana gyada Kai kamar dole. 


Ita kadai ta shigo parlon nata sauran bayin Suna waje, alama Gimbiya Falmata tayiwa sauran nata bayin dake mata hidima a wajen Suma suka fice. 


Zama hjia Mairo tayi tana karewa yanayin parlon kallo duk an canja Masa tsari ba kamar yadda ta barshi ba last zuwan da tayi. Kafin ta dire kallon ta kan Gimbiya Falmata data daure fuska sosai babu alamar fuska a tattare da ita. 


Dan numfasawa Hajia Mairo tayi tana gyara Alkybbar ta tace, 


"sai kuma mukaji mummunan lbri Dan Lele ya bace?"


Wani irin kallo Gimbiya ta watsa mata tana jin zafi a ranta musamman daga yanayin da tayi mata tmbyr ya Bata haushi akaf matan sarki Abdallah babu wacce sukafi gogawa da ita sama da Hajia Mairo badan komai ba saidan sa mata ido sosai da take akan yaranta especially yarima yaseer duk yabi ya tsole mata ido karara take nuna hasadar ta a Fili shiyasa ko yanzu ma a ranta tana suspecting dasa hannun Hajia Mairo a bacewar yareema yaseer....


"oh.. bafa ni nakar zomon ba Gimbiyar sarki."


Cewar Hajia Mairo data sake gyara zaman ta tana me ci gaba da fadin,


"har gobe dai bazan daina fadar gsky ba, kuma har gaban abadan saidai kici gaba dajin haushina akan fadar gsky keda maimartaba."


Daga mata hannu Falmata tayi a fusace tace, 


"Fice min daga Nan.."


tayi mata nuni da kofa, murmushi Hajia Mairo tayi tace, 


"ko baki fada ba ai zan tafi Amma ki bari na Ida mgnr da nakeson yi...."


"Nace ki fice koh????"


Cewar Gimbiya Falmata da tayi mgnr da tsawa bacin rai karara na sake bayyana akan fuskarta. 


Juya idanuwa Hajia Mairo tayi tace,


"ai shikenan bari na tashi kafin ki huce haushin a Kaina."


Mikewa tayi yyinda Gimbiya Falmata ke aika mata da muguwar harara tamkar idonta zai fice. 


A hanya sukaci karo da suhaima zata shigo. 


"Oh..suhaima kin dawo?"


Hajia Mairo ta furta Hakan tana murmushi, kallon Rashin kunya tayi mata tana dauke kai ta Karasa shigowa ciki. 


Tabe baki Hajia Mairo tayi tana barin sashen nasu gaba1. 


"Ummi me matar Nan takeyi anan?" 


Suhaima ta furta ranta a bace, dakuwa ummi tayi mata tana kokarin saita kanta tace, 


"respect her."


Tura baki suhaima tayi tace,


"ummi ya kamata ki dakatar da ita da zuwa sashen Nan naki gaba1 domin ba komai take karawa mutane ba daya wuce ciwon Kai."


Shiru Gimbiya Falmata tayi tana karajin takaicin Hajia Mairo a ranta.


"Kuma ni Ina suspecting dasa hannunta a bacewar yayana."


Suhaima ta furta Hakan bakinta na rawa. Ita kanta ummi kukan ne yaso kwace mata ta daure dakyar tace,


"I'm suspecting too."



°°°°°°°

Kallon jakadiya tayi a tsanake tana duban cup din hannunta a tsakiyar parlon maimartaba.


Washe baki jakadiya tayi cike d girmamawa tace, 


"a'a Ashe amarya ce da kanta tohm ki jira ai ya samu bcci yanzu na bashi mgni."


"Mgni Kuma?"


Hajia Mairo ta furta Hakan tana sake kallon cup din hannun nata tace, 


"mgnin meye?"


Jakadiya tace,


"eh..toh.. mgnin tari ne na gargajiya."


Tsuke fuska sosai Hajia Mairo tayi tace,


"ban gane ba? Ina likitan sa yake?"


"Dazun Nan ya tafi yace a dinga bashi tarin zai tsaya." 


Kallon ta tayi na wasu mintuna sai kuma ta tabe baki kawai batare data sake mgn ba kawai ta wuce ciki batare data jira anyi mata iso ba.


Yana zaune ya dafe kirji, da mmki ta kalleshi shi da akace Yana bcci?


Zama tayi kusa dashi ya dago kansa a hankali Yana kallon ta. Hajia Mairo tace,


"Allah ya baka yawan rai, Lfy da Nisan kwana maimartaba sarkin MANARAS da fatan kana lpy?"


Girgiza Kai maimartaba yyi yana lumshe ido a hankali. Hajia Mairo tace,


"madallah. Yanzu Ina aka tsaya da binciken Inda yarima yaseer yake?"


Da mmki ya kalleta sai yaga tayi murmushi Tace, 


"Rashin tausayin nawa bekai har haka ba maimartaba, yanzu dai su waye akan binciken nasa?"


"Aisha."


Ya bata Amsa a takaice. 


Gwalo ido tayi da sauri tana dafe kirji tace,


"Whattt....?????"




*KAUYEN JIRAGO*



Duk iya duban da zatayi, tayishi Amma har yanzu bata gano Inda Wannan bakon yake ba. Harta cire tsammani ta juya zata tafi sai kuma taji taku a bayanta, juyowa tayi da sauri tana kare Masa kallo shine dai rungume da hannun a kirjin sa jikinsa duk a jike. 


Wara ido tayi tana isa wajenshi d sauri tace,


 "Wanka kayi?"


Tayi mgnr tana nuna jikinsa daya jike. Murmushi yyi mata Yana gyada Kai. 


Bilqees ta kamo hannun sa suka koma kasan bishiya tace,


"Allah sarki inata neman ka Wlh"


ta Ida mgnr Suna zama. Shima zama yyi kamar yadda yaga tayi ta dauko ledar gefenta tana ajewa a tsakiya tace,


"Dan Allah kayi hakuri ni bansan Abinda zakaci ba kaji? Ga Wannan kasha"


ta bude Masa ledar tana Ciro lemon zagin data yanka gani tayi ya karba da murnar sa Yana kaiwa baki. 


Hakan yasa ta zuba Masa ido cike da tausayawa tana kallon sa. 


Sosai yasha duk ywancin fruit din data kawo Masa fuskar sa wasai tamkar Wanda yakecin dawisu. 


Haka kawai taji dadi ya kamata musamman data ga Yana farinciki sai cin fruits din yake a fuskar sa zaka gane yaji dadi.


Saida ya koshi Sannan ya Daina ci. Kallon sauran tayi yafi Rabi tace,


"bakaso ne?"


Tayi mgnr da damuwa. Girgiza Kai yyi, tace,


"Ka koshi?" 


Sai taga ya gyada mata Kai. Murmushi tayi har hakwaron ta na fitowa ta dauki ayaba daya tana barewa takai bakinta zuciyar ta fari tasss.


Gani tayi ya zuba mata ido kamar ya samu tv tana masa yanayi da Wani Abinda ya Rasa Ina ya taba sani? Dauke idonta tayi daga gareshi domin ji tayi ya mata nauyi. Kafin tace,


"Sunana bilqees. Fadi muji."


Shiru yyi Hakan yasa ta dago. 


_"BILQEES..."_ 


taji ya furta a hankali. Dummm....taji Wani irin Abu ya bugi kirjinta ya soke tashi guda tayi saurin dafe kirjin tana lumshe ido har yanzu Abinda taji be daina yawo a Tsakanin kirjin nata ba, batajin tunda take a rayuwar ta akwai Wani mutum ko ace Wani bil'adama daya iya furta sunan ta cike da sauti me dadi da kayatarwa sama da sautin daya fito daga Wannan bakon garin da Bata San koshi waye ba. 


Bude idon tayi a hankali tana sauke numfashi bayan ta daidaita nutsuwar ta, saita tafa a hankali tana murmushi Tace,


"dakyau ka iya furtawa daidai."


Murmushi yyi yana dauke kai, bilqees Kuma tace,


"tohm tunda Kai baka San waye Kai ba wanne Suna ya kamata a kiraka dashi....???" 


Karshen mgnr ta ce ta makale a tsorace lkcn data jiyo muryar su lauwali na dosowa Inda suke da karnukan su Suna ihu irin na mafarauta...........





*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number👇🏻



***