SARAUTAH TAH CE

13.

by @nuceeyluv

👑👑👑👑👑


*SARAUTA TAH CE*





*Free page*





*Wattpad*

@nuceeyluv




By

Nuceeyluv😘






13.....






Wani irin kakkauran yawu yarima yaseer ya hadiye a daidai lkcn da yaci karo da kirjinta Wanda ya Dan hauro izuwa Saman rigar dake jikinta farare Kal har sunfi sauran sassan jikin nata ma haske, da alama bra din data saka ne yyi mata kadan shiyasa suka hauro sama.


Kansa yaji ya Sara tunanin sa na dauko Masa Wani hoto acan kasan kwakwalwar sa me kama da kwatankwacin yyi mu'amala da irin Wannan abin saidai Sam ya kasa tunawa domin ya manta.


Duk yadda zai iya tunowa ya kasa saima jin kansa da yyi yana Masa nauyi alamar ciwo zaiyi Hakan yasa shi kawar da tunanin Yana janye idanun sa dakyar akan kirjin nata yyinda nasa kirjin ke bugawa har yanzu.


Cije kasan lips dinsa yyi yana daukar hijab din ya mike a hankali ya isa gaban kogin dake gabansu, Ruwa ya nado a ciki Yana tangadi domin shima jirin yakeji sama2 Yana zuwa wajenta ya dagota a hankali Yana dorawa bisa cinyar sa dakyar sannan ya matse ruwan akan Inda yaga jinin Yana fita.


Dan kwalin ta da yake kansa data bashi dazu ya warware domin d din daurawa yyi shima sannan ya dawo dashi daidai saitin goshinta ya daure ciwon a nutse domin jinin ya tsaya.


Yana gamawa ya dora jikakken hijab din a saitin wuyanta take bilqees ta sake Jan wata ajiyar zuciyar tana bude ido a hankali.


Ganinta dodar bisa cinyar sa yasa ta zabura da sauri tana kokarin tashi. Rikota yyi da sauri idonsa na lumshewa yace,


"ki nutsu pls"


Janye hannun ta tayi batare data kulashi ba ganin haka shima ya saketa kawai Yana dafe kansa.


Bilqees ta janyo hijab dinta da sauri zata saka sai taga Duk ya jike. Dagowa tayi fuskar ta a hade Tace,


"meyasa ka jika min hijab? Dama Bance kada ka ciremin ba?"


Dagowa yyi a hankali Yana zuba mata ido, beyi mgn ba kawai ya gyara zamansa a tsanake yana Dan kishingida idonsa na Kara rufewa gaba1.


Tsaki tayi tana Hararar sa, tace ,


"Mgn nake maka fa?"


Ganin ya share ta yasa ta tashi daga wajen tana matsawa can gefe ta kama buga hijab din tana dagashi can sama Dan ya bushe da wuri.


Juyowa tayi sai taga kamar Yana bcci. Mmki ne ya kama ta, sannan ta kalli dajin da suke ba motsin mutum ko daya take tsoro ya shigeta tayi sauri dawowa kusa dashi tana jijjiga shi tace,


"Kai....tashi mu tafi Nan ba wajen zama bane."


Gani tayi be motsa ba, ta Kara kamo hannun shi tana jijjigawa tace,


"Wlh idan baka tashi ba Allah zanyi tafiya ta."


Ta furta Hakan cike da takaici tana mikewa tace,


"dama can a daji na ganka Dan haka haduwar daji rabuwar daji."


Tana idawa ta juya da sauri zata tafi. Har lkcn yarima yaseer be farka ba da alama ma besan a duniyar da yake ba tamkar Wanda ya Suma.


Bilqees kuwa Duk tsoro ya kama ta tana ganin gara ta hakura da zuwa gidan yaya Atika kawai ta wuce gida kafin dare yyi mata.


Saida tayi nisa da tafiyar ta juyo har lkcn Yana kwance kamar yadda ta barshi, kwafa tayi tana shirin juyawa taji an damko hannunta ta baya.


A razane ta juya tana kallon gefen nata sai kawai taga wasu maza biyu irin barayin dajin Nan tsaye a kanta Suna dariya sukace,


"Kan uban can yau ga tsuntsu daga sama gasasshe."


Ihu Bilqees tasa a razane tana salati hade da kiran sunan yarima yaseer cewa take,


"bakon gari Dan Allah kazo ka ceceni...."


Juyawa sukayi Nan suka hango yarima yaseer a kwance. Dariya sukayi mata Suna nufar Inda yarima yaseer din ke kwance.


Fisgewa tayi iyakar karfin ta tana isa gaban yarima yaseer ta fada kansa tana jijjiga shi iyakar karfin ta a mugun tsorace tace,


"ka tashi...muna cikin matsala."


"Kai baro kamo min waccar yarinyar."


Dayan ya furta Hakan yana gyara tazugen wando.


A gigice bilqees ta sake dakume yarima yaseer hawayen ta na zuba akan fuskar sa domin ta Rasa mafitar da zatayi yanzu Wanda aka umarta ya taho Yana washe baki yace,


"ilu gani take fa Nan din ta tsira."


Yana Ida mgnr ya kawo hannu zai taba ta bilqees ta sake tsallara karar data Kara karade dajin gaba1.


Yarima yaseer da damshin hawayen ta ya fara tashin sa daga dogon suman da yyi ya mike a firgice sakamakon karar data tsalla yanzu.


Ganin mutum biyu maza yyi a gabansa gasunan murtika-murtika majiya karfi, sai kuma bilqees data sandare Masa akan faffadan kirjin sa yanzu.


Kallon-kallo ne ya afku Tsakanin barayin dajin babban cikin wato ilu ya kalle shi kallo na raini sannan ya watsar kafin yace,


"Kai malam tun muna shaida juna ka sakar Mana yarinyar Nan ka kama gabanka idan ba haka ba Wlh harda Kai zamu tubewa wando."


Gwalo ido yarima yaseer yyi da mugun mmki. Yyinda baro yace,


"ai oga shidin ma ba haka Nan zamu barshi ba, yyinda kke shagalin ka da yarinyar ni Kuma zanyi nawa shagalin da Wannan mutumin Dan kur'ani kana ganin San Nan da alama zaiyi Mai yaseen."


Dariya suka sa gaba1 dayansu. Ilu yace,


"shiyasa nake yinka baro domin kanada dabara Dan haka muje na karbi yarinyar Kai Kuma ka sabule Masa wando."


Izuwa yanzu fuskar yarima yaseer ta hade sosai babu alamar murmushi bare dariya a tattare dashi Yana a yadda yake bilqees na kansa hannayen sa Suna dafe a kasa ya zuba masu ido kawai Yana ganin ikon Allah.


Da isarsu suka Karasa wajen nasu a daidai lkcn da ilu zai sa hannu akan bilqees a Wannan lkcn yareema yaseer ya damke Masa hannu ko Karasa tabata beyi ba ji kke bas ya balla Masa shi take ya sandara Kara,


Karar data fargar da bilqees ta mike a razane yareema yaseer ya dawo da ita kansa kamar yadda take dazun Yana girgiza mata Kai fuskar sa a hade.


Kasa Musa Masa tayi sai kallon ilu take a tsorace lkcn daya ja Baya Yana cije baki. Baro yace,


"Kutmelesi? Oga badai Wannan shafalfal dinne ya gwada maka karfin damtse ba?"


Banza yyi dashi kafin ya sake dawowa be daddara ba zai kamo bilqees yarima yaseer ya Karasa balla Masa dayan hannun karar azaba ya sake saki take ya matsa da sauri baro yace,


"Wlh mu bar Nan nifa nafi tunanin rauhanai ne."


Baro ya furta Hakan yana juyawa zai gudu ilu ya bishi a Baya hannun sa rungume da juna Yana Jan numfashin azaba.


Sauke ajiyar zuciya bilqees tayi a daidai lkcn data daina hango inuwar su ta dawo da kallon ta kan yarima yaseer da shima mmkin karfin sa ya kamata.


Gani tayi itan yake kallo Hakan yasa idanuwan su ya sarke da juna..Dan yake tayi kirjinta na bugawa tayi azamar sauka daga kansa ya rike mata hannu, zaro ido tayi tana dan hade fuska Tace,


"me Kuma zanyi maka?"


Yarima yaseer ya yatsina fuska Yana kawar da Kai yace,


"su waye mutanen Nan?"


Bilqees tace,


"Toh sakeni Mana saina ji dadi fada maka waye su."


Tabe baki yyi yana sakin nata ta sauka lumshe ido yyi yana cije lips a hankali bilqees ta kawar da Kai da sauri Wani Abu na mata yawo a kirji.


"Yes ina jinki."


Yarima yaseer ya furta Hakan har yanzu be bude ido ba. Bilqees tace,


"inata tashin ka dazun kayi banza dani shiyasa nayi tafiyata Nima."


Ta furta Hakan tana turo baki. Gani tayi ya bude ido da sauri Yana zuba mata su yace,


"Pls maimaita banji me kikace ba."


Wara ido tayi da mmki sai taga ya gyada mata Kai alamar cewar lalle baiji ba. Bata kawo komai a ranta ba ta sake maimaita Abinda tace tana Kara turo baki Harya Fi na da din.


"Hmm...!"


Yarima yaseer ya saki ajiyar zuciya yana tsareta da ido sai kallon bakin yake yana Dan murmushi.


Bilqees tace,


"wai har yanzu baka ji bane? Kodai ka samu lalurar Rashin ji ne yanzun?"


Yarima yaseer ya sakar mata murmushi yana mikewa tsaye ya miko mata hannun sa yace,


"Taso mu tafi"


Ba musu ta mike Dan dama ta kagu Subar wajen. Yarima yaseer yace,


"Inane hanyar garin da Zaki je?"


Bilqees tace,


"na fasa zuwa gida zan koma."


Yarima yaseer ya gyada Kai batare da yyi mgn ba Nan suka kama hanyar komawa gidan bilqees na nuna masu hanya har suka koma asalin dajin kauyen su.


Tun a hanya bilqees ke tufka da warwara har yanzu ta Rasa a wanne matsayi zata nuna yareema yaseer a kauyen su...



Duk yadda taso ta samu mafita kasawa tayi Dan haka kawai tasa a ranta gwara ta barshi a dajin kawai kamar yadda ta ganshi anan tun farko.


Sun danyi tafiya me nisa babu meyin mgn a cikinsu har suka Kai Inda bilqees ta fara haduwa da yareema yaseer ja tayi ta tsaya ya juyo da hankalin sa kanta Yana jiran abinda zatace sai ta danyi murmushi tace,


"mun iso Inda kke zama ni zan tafi ka tsaya anan."


Zuba mata ido yyi beyi mgn ba, bilqees tace,


"ko baka ji me nace ba?"


Girgiza Kai yyi a hankali Yana harde hannayen sa ya Kawar da kansa Wani side din.


Numfashi bilqees ta sauke kafin tace,


"Sai anjima."


Juyowa yyi a hankali Yana kallon ta yanayin fuskar sa na canjawa. bilqees ta juya zuciyar ta babu dadi ta wuce a wajen ta barshi.


Har tayi nisa be daina kallonta ba bilqees ta juyo a hankali sai taga har yanzu itan yake kallo be dauke idonsa a kanta ba, kasa daurewa tayi ta dawo gareshi gaba1 tausayin sa takeji ace mutum ba Dabba ba a daji ai babu dadi.


"Ko zaka bini ne?"


Tayi tmbyr batare data shirya Hakan ba. Daga Kai yyi da sauri sai taga ya saki ransa alamar yaji dadi, Wani mugun tausayin nasa ne ya sake kamata tayi kasa da kanta tana tunanin a matsayin da zata nuna shi, sai kuma ta tuna taimakon d yyi mata a wajen barayin dajin Nan Dan haka tace,


"shikenan muje."


Ransa a sake ya biyo Bayanta Suna tafe tamkar Wanda suka dade da sanin juna.


A lkcn har yamma tayi Kuma dole ta wajen dandalin su zasu ratsa.


Hakan yasa tun daga nesa aka zubawa bilqees ido Ana kallo kowa mmki dauke akan fuskar sa. Bilqees dauke kai tayi bata kula da irin kallon da 'yan kauyen ke mata da Wannan bakon ba tayi hanyar gidansu dashi.



"Dakata...dakata...Uban waye Kai?"


Mlm Musa ya furta Hakan lkcn daya fito daga gida, ya hango bilqees tare da Wannan mutumin zasu shiga gidan.


Kallon sa yareema yaseer yyi sai kuma ya dauke kai bece komai ba. Bilqees da tun dazu kirjinta ke bugawa tace,


"dama..dama baffa..."


Baffa yace,


"Wani shegen kika sake kawowa Kuma?"


Girgiza Kai tayi tana janye yarima yaseer daga gefensa yace,


"toh waye shi da zaizo Kai tsaye ya shige min gida?"


Bilqees tace,


"dama a soro zan barshi ya tsaya sai nayi maka sallama dashi."


Mlm musa yace,


"meye hadina dashi dahar zai neme ni?"


Bilqees tace,


"Dan Allah kayi hakuri nayi maka bayani."


Juyar da keya mlm Musa yyi yace,


"inajin Ki."


Juyawa bilqees tayi sai taga dayawan 'yan kauyen su duk anyi curko-curko a wajen Ana jiran abinda zatace.


Bilqees tayi kasa da kanta tace,


"baffa shidin ya ceceni ne"


"kamar ya ceto? Ban gane ba"


Mlm Musa ya furta Hakan yana jiran Karin bayani. Bilqees tace,


"a hanyata na zuwa gidan yaya Atika wasu mutane suka so sace ni harma sunso suyimin mummunan Ilah Allah ya turo Wannan bawan ALLAH ya Cece ni baffah."


Baffah yaja tsaki Yana gyara zaman hular sa yace,


"Toh munji ya ceceki, sai kuma akayi yaya? Ko biyanshi za'ai? Kinsan dai ko kashe ki akayi ba ruwana Dan ban aike ki ba dama."


Ranta ne ya baci irin cin zarafin da baffa ke mata a gaban koma waye ke Bata mata rai gashi kamar Wanda akaga sabon halitta sai Kara taruwa ake.


"Baffa besan waye shi bafa, ya Rasa tunanin sa"


Bilqees ta furta Hakan hawaye na shirin zubo mata. Da mmki kowa yake Kara kallon su.


"Shashancin banza shashancin wofi, ni Zaki maida Dan iska? Kiga mutum zabgege kamar Wannan kice besan waye shi ba? Dodo ne shi? Ko Aljani???"


Mlm Musa ya furta a fusace yana ganin rainin hankali karara bilqees ke shirin yi Masa. Kowa na wajen karyata mgnr yyi, yyinda wasu ke Al'ajabin Abinda bilqees tace game da Wannan bakon da Sam beyi siffa da mutanen kaf kauyen su ba.


"Mlm Musa...haba mlm Musa, lpy kke Wannan fadan a kofar gidan ka haka?"


Kwafa mlm Musa yyi kafin yace,


"Allah gafarta malam Dan Allah ka tayani duban wancan mutumin..."


ya nuna yareema yaseer da a yanzu ya matsa can nesa dasu Yana yatsina fuska domin hayaniyar mlm Musa ta fara damunsa yace,


"wai shine besan kansa ba"


Alaramma Idi yace,


"Ban fahimci abinda kkeso kace ba mlm Musa."


Mlm Musa ya nuna bilqees da kanta ke kasa yace,


"Nima shirmen da yarinyar Nan ta kawo min kenan Dan mgnr Bata fahimta bace."


Alaramma Idi yace,


"Bilqees ko zaki iya min bayani a nutse ta yadda zan fahimta?"


Bilqees ta goge guntun hawayen takaicin daya gangaro mata a kumatu kafin ta Kara sanar dashi yadda ta fadawa mahaifin ta, Sanna ta Dora da fadin,


"Tun a lkcn na tmbyi waye shi? Daga Ina yake? Kuma Ina zaije? Sai ya nuna sam-sam besan waye shi ba, ciki harda sunan shi kuwa, shiyasa na yanke shawarar tahowa dashi Nan asa cikiya a gari ko Allah zaisa a samu Wani bayanin daya dangance shi ko dangin sa."


Alaramma yace,


"tabbas kinyi tunani mekyau bilqees, kamata yyi asa cikiyar sa hadda makotan kauyen mu ko Allah zaisa a dace."


Bilqees ta girgiza kai cike da gamsuwa. Tabe baki mlm Musa yyi yace,


"Tohm duk naji Abinda kuka tattauna, Amma a Ina zai zauna? Dan bazan aje gardi a gidana ba."


Bilqees tace,


"Dan Allah baffa ka bari yyi kwana biyu a soron Nan tare da su yaya sabi'u kafin ya dawo hankalin sa ko kuma a samu Wanda ya sanshi saiya tafi."


Tsalle Mlm Musa yyi ya dire yace,


"Wannan ne Kuma Sam bazan lamunta ba, ai Abinda yasa na yiwa tufkar hanci kenan tun wuri haka kawai na aje mutum da ban sani ba a gidana? Nasan waye shi? Da kikace ya ceceki na sani Duk karyace shima a cikin barayin yake? Haka kawai cikin dare yyiwa 'yan uwansa alama suzo suyimin sata ko su yanka ni? Billahillazi bazan yarda ba kinji na rantse atoh."


Kasa cewa komai bilqees tayi domin a yanzu kam ta Rasa mafita.


Alaramma Idi yace,


"Akwai dakin Almajirai na dake karatu jiya Wani Almajiri na ya koma gida Dan haka za'a samu waje su goma ne a ciki idan ba damuwa saiki kawo shi ya kwana biyu kafin wancan din ya dawo.


Girgiza Kai bilqees tayi hankali ta na tashi ga bikin zuwa babu zanin daurawa...yadda dakin Almajirai yake da wari na tashin hankali da kazanta take hangowa Wannan bakon da har yanzu bata San sunan shi ba, Toh Amma ya ta iya? Ina lefin Wanda ya nemi ya taimaka maka a daidai lkcn da kke bukatar Hakan? Matukar Bata amince da tayin Alaramma ba toh Bata San Kuma Ina zata Kai yareema yaseer ba.


Haka dai tayi yaken dole tana Kara gyada Kai tace,


"shikenan mlm na gode sosai Allah ya Kara Arziki."


"Ameen bilqees muje Kuga wajen koh?"


Bilqees ta girgiza kai tana komawa Inda yareema yaseer ya harde hannayen sa Yana kallon su daga nesa tamkar tv.


Tsaki mlm Musa yaja Yana kallon mutanen da suka zagaye kofar gidan sa yace,


"toh ai saiku tafi ko? Sa'idinawa."


Sum-sum kowa na wajen ya fara darewa Ana gulmar Abinda ya wakana a wajen da haka hirar mutanen kauyen ta canja salo zuwa labarin zuwanta da bako cikin kauyen su, kowa dai da Abinda zai fada.


Kallon shi tayi a tsanake tace,


"muje."


Beyi Musu ba domin dama ya gaji sai yatsina fuska yake tun dazu Dan haka ba gardama ya fara bin bayanta a nutse.


Sun danyi tafiya me nisa acan gaban layinsu gidan Alaramma yake Suna zuwa lkcn Ana kiran magrib Alaramma yace,


"Toh bilqees ki jiramu Anan bari muyi sallah sai na nuna muku dakin."


Bilqees ta gyada Kai tace,


"bari na Karasa gidan naka Nima nayi."


Alaramma yace,


"Toh ba damuwa."


Kallon yarima yaseer yyi yace,


"muje ayi sallah ko?"


Ko kallon sa beyi ba bare yasa ran zai saurare shi. Bilqees tace,


"kuje yanzu Zaku dawo Ina Nan"


ta nuna Masa inda take zaune. Kamar bazai bishi ba saida ta sake nanatawa sannan ya yarda ya bishi Yana waiwayen ta tamkar wacce zata gudu ta barshi.


Murmushi tayi Masa sai ya danyi murmushin shima Yana sakin ransa har suka wuce masallaci tare da Alaramma dake daga wajen Ana iya hango masallacin.


Ajiyar bilqees ta saki tana mikewa a hankali tayi hanyar gidan mlm domin yin tata sallar,


A hanyar ta na shiga gidan daga gefen kofar gida taga window din Almajiran mlm a bude, matsawa tayi domin ta leka,


Tana cusa kanta wajen ta dawo baya a gigice tana toshe hanci saboda Wani irin mugun wari da tsami daya bugi hancin ta lkci guda.





*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number👇🏻



***