14.
by @nuceeyluv
👑👑👑👑👑
*SARAUTA TAH CE*
*Free page*
*Wattpad*
@nuceeyluv
By
Nuceeyluv😘
14....
Numfashi ta sauke dakyar tana dafe kirji yanzu anan yarima yaseer zai zauna? Dakin Almajirai? Dukda batasan waye shi din ba, batasan asalin sa ba, batasan daga Inda ya fito ba Amma tanaji a jikinta yafi karfin yyi rayuwa a irin Wannan wajen, duba da yadda yanayin jikinsa yake fatar jikinsa a koda yaushe kyalli take ga hannayen sa Duk laushi tamkar audiga har mmki takeyi wai namiji kamar shi Amma da laushin hannu Wannan ko mace Albarka Hakan ya Tabbatar mata da cewar duk Inda ya fito to ba'a wahale yake ba,
Tanajin takaicin Rashin tunanin sa Amma dole a Samo mafita domin tunanin sa ya dawo, ta yadda Zai tuna waye shi? Daga Ina yake? Dan wanne nahiya ne shi?? Ganin sun kusa idar da sallah yasa tabar wajen d sauri tunani fal kanta tana karasawa gidan Alaramma Idi.
Sallama tayi. Matarsa salamatu ta fito daga bayi rike da buta alamar Alwala zatayi. Gaisawa sukayi, kafin bilqees ta sanar mata dalilin zuwanta, salamatu ta karbeta d mutunci kafin ta duro ruwa a wata butar ta bata Nan bilqees ta duka Dan fara yin Alwala.
Suna fitowa yareema yaseer ya fara waige2 ko be furta ba Alaramma ya fahimci bilqees yake nema. Alaramma Idi yayi Masa alamar hanyar da suka biyo dazun yace,
"muje tana can."
Dan sakin ransa yyi kadan Yana gyada Kai suka kama hanyar tafiyar su na komawa gidan Mlm. Tun daga nesa yareema yaseer ya hade fuska tamau tamkar Wanda be taba dariya ba Hakan ya Samo asali ne tun bayan da suka bullo Inda suka bar bilqees be ganta ba yanzu.
Alaramma Idi be lura da canjawar fuskar sa ba yace,
"jirani Anan bari na ware Mana taburma."
Ko ci kanka yareema bece ba bare yasa ran Amsa Alaramma Idi ya Karasa gun taburmar dake jingine da bango batare daya damu d shirun na yareema ba.
Ana haka saiga bilqees ta fito daga gidan Mlm. Yareema yaseer na hango ta ya saki ransa harda boyayyiyar ajiyar zuciya yana zube mata mayatattun idanun sa tun daga nesa.
Murmushi bilqees tayi Masa tana yin kasa da idonta haka kurum taji kirjinta ya buga da karfi, cije lips yyi yana kawar da Kai gefe beyi mgn ba.
"Bilqees har kin fito?"
Alaramma ya furta Hakan bayan ya dago daga shimfidar d yyi, gyada Kai bilqees tayi tana kokarin kallon fuskar yareema daya kawar da kai tace,
"Eh Mlm."
Alaramma Idi yace,
"Toh Bismillah ku zauna."
Dawowa gefen daya kawar dakai tayi tana kallon sa a tsanake tace,
"taho mu zauna."
Juyowa yyi yana kallon ta a nutse ta Kara maimaita Abinda tace, yareema yaseer ya matso Inda take nuna Masa batare d yyi mgn ba ya zauna itama ta zauna acan gefe.
Mlm Idi ya dubesu gaba1 yace,
"dama akwai Abinda zan tmbyeki bilqees shiyasa ma na nemi mu zauna."
Bilqees ta gyada Kai tace,
"Toh ba damuwa mlm."
Alaramma Idi yace,
"Tun yaushe kika ga Wannan bakon?"
Shiru bilqees tayi domin dazu cewa tayi kawai ceton ta yyi Bata nuna cewar ta dade da ganinsa a dajin kauyen su ba. Mlm Idi ya numfasa kafin yace,
"kada ki damu bilqees inason na taimaka muku ne sbd irin Wannan lalurar da yake tare da ita Bata da maraba da ture ko sammu."
Sakin ranta bilqees tayi harga Allah dama tafi bukatar ya samu lpy fiye d ace Yana zama cikin duhu batare daya san Inda kansa yake ba.
A nutse ta fara sanarwa da mlm Idi haduwar su ta farko a cikin daji kusa da kogin data zauna har kawo yau da suke anan.
Sosai Alaramma ya fahimci bayanin bilqees din harta Kai Aya. Kafin ya aje numfashi Yana gyada Kai yace,
"tabbas Zance na Yana bisa hanya bilqees, Wannan bawan ALLAH Yana cikin tsananin bukatar taimako, Allah ne kadai yasan dalilin dayasa taimkon sa ya fado ta hannun ki bilqees domin ni Sam ban taba ganin me kama da irin Wannan mutumin akaf fadin kewayen kauyen mu ba bilqees, zaiyi wahala ace anan kusa damu yake dole akwai Abinda bamu sani ba tattare da lamarin Wannan bawan ALLAH."
Bilqees ta gyada Kai cike da gamsuwa tace,
"Nima Hakan nake tunani mlm."
Mlm Idi yace,
"Toh madallah, yanzu tunda anan Zaki barshi zanyi iyakar bakin kokari na d dan sanin da nake dashi na falalar Al-kur'ani da hadisi muyi Masa Addu'a da mgnin Karya sihiri ko Allah zaisa a dace."
Sosai bilqees tayi farinciki matuka da bayanin Alaramma Idi take ta fara zuba Masa godiya tace,
"Nagode sosai Mlm Allah ya saka da Alkhairi ya biya bukatu na Alkhairi"
"Ameen Yah hayyu yaa qayyum."
Alaramma Idi ya Amsa Yana fuskantar yareema yaseer daya kawar dakai gefe tamkar ba akanshi ake mgnr ba Yana kallon Wani side din.
"Bawan ALLAH tunda bamu san sunan ka ba zamu dinga kiranka da Wani kafin Allah yasa tunanin ka ya dawo kaji?"
Alaramma Idi ya furta Hakan yana kallon sa. Tabe baki yareema yaseer yyi be bashi Amsa ba saida bilqees tace,
"Ayi hakuri mlm haka yanayin sa yake Wani lkcn tamkar kana mgn da Dutse"
tayi mgnr da fillanci sbd kada yaji. Yareema yaseer da har yanzu be kallesu ba yyi murmushi sbd yadda yaji ta canja yare be juyo ba bare su fahimci yaji Abinda take mgn akai.
"Toh shikenan bilqees kina ganin wanne Suna zamu saka Masa?"
Shiru bilqees tayi tana tunanin can tace,
"Annur."
"Lalle kin iya zaben Suna bilqees, haske kenan, tohm Allah ya Tabbatar damu akan haske duniya da lahira."
"Ameen Yah hayyu yaa qayyum"
bilqees ta Amsa tana murmushi.
"Toh saiki sanar Masa sabon sunan ko? Ni bari naje na bude dakin ku gani"
bilqees ta gyada Kai tana amsawa da toh. Tashi yyi ya barsu a wajen. Bilqees ta dubi gefen fuskar sa a nutse tace,
"Annur."
Gani tayi ya juyo a tsanake yana kallon ta. Dan murmushi tayi Masa tace,
"Sunan da zamu dinga kiran ka dashi kenan kafin ka tuna waye Kai sai musan asalin sunan ka."
Gani tayi ya mata murmushi kadan Yana mikewa hade d yatsina fuska alamar ya gaji Kuma.
"Bilqees ku taho"
Alaramma ya furta Hakan yana lekowa daga dakin daya bude.
"Toh Mlm."
Bilqees ta bashi Amsa tana duban yareema yaseer tace,
"Annur muje."
Binta yyi ba musu suka tsaya a bakin kofar dakin, Alaramma yace,
"yauwa bilqees kinga dakin nasu ga gadon dayan can da baya Nan saiya dinga kwana akai kafin ya dawo."
Kallon gadon da aka sassaka shi da Kara bilqees tayi tana kokarin daurewa da warin dake tasowa a hankali ta juya zata yiwa yareema yaseer mgn ta nemeshi ta Rasa.
Sake juyawa bayanta tayi da sauri can ta hango shi hannun sa a saman hancin sa ya toshe shi. Da mmki suke kallon sa. Bilqees ta juya wajen sa da sauri tace,
"meyasa kabar wajen?"
Cire hannun yyi yana Bata rai yace,
"bazan iya tsayuwa ba wajen."
Gwalo ido bilqees tayi tana juyawa Inda mlm ke jiran su kafin ta juyo gefensa a hankali tace,
"meyasa? Inda Zaka dinga bcci kenan fa,"
gani tayi ya gwalo ido d mugun mmki yana Kara ja Baya hade da girgiza Kai yace,
"no..no..I can't....."
saurin dakatar dashi tayi ganin mlm Idi ya taho ta wajen su yace,
"bilqees lpy yake tsaye anan?"
Bilqees ta danyi yake kafin tace,
"Mlm kamar fa bayason zaman wajen."
"Ikon Allah"
Alaramma ya furta Hakan d mmki, yace,
"Toh yanzu Ina yakeso ya zauna? Gashi dakin Almajiran Nan kawai nake dashi Wlh."
Bilqees tayi zuru cike da rashin mafita, ta juya kan yareema yaseer daya daure fuska a hankali tace,
"ka daure ka zauna anan din kaji? Ba dadewa zakayi ba zaka koma gida"
Tayi Hakan d niyyar dabara dukda kasan ranta itama b so take ba toh Amma yata iya? Dole dai dakin Almajiran shine mafita. Girgiza Kai yyi da sauri yace,
"No."
"Kinga bilqees kada ayi Masa dole ya kamata a bishi a sannu mudai ya samu lpy kawai."
Kamar zatayi kuka Tace,
"Toh mlm yanzu ni Ina zan kaishi? Kana ganin yadda baffa yaki karbar sa fa."
Alaramma Idi yace,
"haka Zaki koma ki Kara lallaba shi ko za'a dace domin Nima babu mafita ta wajena."
Bilqees ta Rasa abin cewa duk ta damu murya na rawa Tace,
"shikenan Mlm. Nagode da kulawa."
Alaramma Idi yace,
"karki damu bilqees, Kuma har yanzu Ina kan bakana zamuyi Masa Addu'a da kuma mgni Insha ALLAH za'a dace."
"Toh Allah ya yarda."
Bilqees ta furta Hakan Suna Kara sallama da Alaramma Idi suka bar wajen nashi gaba1.
Yareema yaseer ko a jikinsa kamar an gutsiru kakkausa sabanin bilqees da a yanzu tarin tunani yyi mata yawa tana neman mafita.
A hanya kuwa sai kallon su ake Ana nuna su bilqees sai dauke kai kawai tayi dama tasan dole Hakan zata faru.
Mlm Musa Yana kofar gida tare da Wani makocin sa ya hango bilqees lkcn duhu yyi tare da Wannan bakon Hakan yasa ya mike da wuri Yana komawa kofar gidansa ya tsaya. Bilqees tace,
"Baffa mun dawo."
Baffa yace,
"da kuka dawo sai akayi yaya? Me zanyi Masa?"
Bilqees tace,
"yanzu zuwa nayi na roki Arziki."
Dauke kai mlm Musa yyi yana juyo keya yace,
"Inajin Ki"
Sauke ajiyar zuciya tayi tace,
"baffa dama Aron dayan dakin zauren can zaka bani"
a harzuqe ya juyo yana masifa yace,
"kekam dai d ace mayya ce Wlh d tuni kin gama cinye ni, nace bazai zauna min a gida ba dole ne? Ko shidin kanin ubanki ne da Zaki ishi mutane da Nema Masa taimako? Ki sakeshi haka Nan man ya kama gabansa."
Bilqees ta dukar dakai zuciyar ta ba dadi saidai ba yadda ta iya a Hankali tace,
"haya zan kama Masa."
Dariya Mlm Musa ya fashe da ita Yana kallon bilqees sama da kasa yace,
"Eh kwarai yau ga hajjaju wato Ashe haka kuke da kudi keda uwar taki munafukai kukayi lumi daku? Haba ai dama barewa baza tayi gudu danta yyi rarrafe ba duk Wannan mugun halin na uwarki ne habiba Wlh."
Fitowa inna habi dake jiyosu tayi zuwa kofar gidan tana kallon yadda mlm Musa ke kare masu tanadi ga mutane sai kallon su ake dama tun dazu ta kasa tsaye bare zaune tana jiran dawowar bilqees din sbd lbrin Abinda ya faru ya risketa tun dazu sai yanzu data jiyo muryar mlm Musa ta taho d sauri.
"Dakata Mlm...ya isa haka Kuma"
Inna habi ta furta Hakan tana janye bilqees daga gabansa. Bilqees ta fashe da kuka tana fadawa jikin inna habi, rungume ta inna habi tayi sai ga yareema yaseer daya matsa can gefe ya taho da sauri hankalin sa a tashe tun bayan da yaji fashewar kukan bilqees din.
Ganinta jikin wata mata ya sashi tsayawa gefensu kirjinsa sai bugawa yake ransa na fara baci d ace ba matar ce ta rungume ta ba toh kuwa ba Abinda Zai Hana shi yareema yaseer ya rungume bilqees din.
Inna habi ta dago tana kallon mutumin daya kasa tsayuwa waje daya tun bayan daya iso garesu sai Nan...Nan yake kamar ya kwace bilqees din a hankali tace,
"Shine bakon?"
Tayi mgnr lkcn data maido da hankalin ta kan bilqees data dago kanta. Juyowa tayi bayanta Nan taga Ashe shine a kusa d su, gyada Kai tayi tace,
"Shine inna."
"Ku biyoni."
Inna habi ta furta Hakan tana yin gaba.
Mlm Musa ya tabe baki yace,
"can umma ta gaida Aysha, Shegen son 'ya'ya kamar kyanwa shima bakon a hada dashi dama ba'a taba samun namiji ba."
Maganganun sun soki inna habi Amma haka ta daure Bata juyo ba domin halin sa ne kowa ya sanshi da Rashin daraja iyalinsa musamman ma ita din da yake aibata 'ya'ya matan da take Haifa.
"Bilqees..."
Yareema yaseer ya furta hakan a nutse yana kokarin kama mata hannu ta zame d sauri tana kallon gefenta yadda mutane ke kallon su,
Hakan ya Kara daga hankali Yareema yaseer da a yanzu ji yake dama shi dinne ya rungume ta ko zata daina kukan Nan da take yi yanzu domin ba karamin daga Masa hankali kukan nata yake Masa ba.
Binta yyi d sauri har Yana kokarin gogar jikinta Bata kulashi ba, Saida suka bar cikin mutane bilqees ta dakata yareema yaseer ya Kara kawo hannu Yana rike mata su yace,
"why are you crying bilqees? Me kika yiwa wancan mutumin yake maki ihu a koda yaushe?"
Ya furta Hakan yana matsa hannunta, bilqees ta kwace hannun d sauri kirjinta na bugawa tana waiwaiyar Inda inna habi take ta hango Harta sha kwana.
"Ka daina tabani bana so"
Ta furta Hakan tana Dan hararar sa. Ji yyi kamar shi yyi lefin Hakan ya sashi jawota jikinsa yana riketa gam yace,
"I'm sorry pls, Dan Allah Kiyi hakuri."
Kokarin kwacewa tayi ta kasa ya riketa sosai, hakan yasa da sauri tace,
"Naji...naji... shikenan Dan Allah sake ni."
Sakin ta yyi yana sauke ajiyar zuciya d sauri2, hade d cije lips. Bilqees ta harare shi kasa2 tana kawar da Kai batare d tayi masa mgn ba ta juya Dan zuwa Inda inna ta tafi.
Binta yyi d sauri yana sake Bata hakuri bilqees tace,
"Ba Abinda kamin ya wuce."
Yareema yaseer yace,
"Toh ki daina zuwa wajen mutumin pls."
Juyowa tayi da sauri tana kallon sa, yareema yaseer ya gyada Kai yace,
"Yess Yana maki ihu, nikuma banaso...gashi ya saki kuka dazu Yana jawowa Nima Hankali na Yana tashi."
Ya furta hakan har cikin ransa hade d yatsina fuska.
Janye idonta tayi daga gareshi tana sauke ajiyar zuciya a hankali kirjinta na harbawa da sauri2.
A haka suka isa Inda inna habi take, tana kofar gidan data je tana jiransu.
*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*
It's 300 via... Access bank 1445626295
Nusaiba Mustapha
Then show your evidence ta Wannan number👇🏻
***.
*Zaku iya turo katin 300 MTN ta Wannan number ****
*DATA...🗣️DATA...🗣️🗣️DATA...🗣️🗣️🗣️*
*INA MASU SON SIYEN DATA AKAN FARASHI ME SAUKI? YAU GA GARABASA TA SAMU💃🏻 DATA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA🥰👌🏻 NUCEEYLUV NA MUKU MARABA DA SIYEN IYA KUDIN KA IYA SHAGALIN KA🤸🏻♀️🤸🏻♀️💃🏻*
*500MB - N200*
*1GB - N300*
*2GB - N600*
*3GB - N900*
*5GB - N1500*
*1 month validity*
Call👇🏻 or cht me private👇🏻👇🏻
***
*ANA TURO KUDI TANAN👇🏻*
Via....1445626295 Nusaiba Mustapha Access bank.
*BANA KARBAR KATI PLS👏🏻😁*
*KUNA TURO KUDI ZAKU JI ALERT DIN DATA INSHA ALLAH BABU BATA LKCI🙅🏻♀️ KO BANA ONLINE KU KIRA DIRECT A SAKO MAKU DATA😹👌🏻*