SARAUTAH TAH CE

20.

by @nuceeyluv

👑👑👑👑👑


*SARAUTA TAH CE*





*DATA...🗣️DATA...🗣️🗣️DATA...🗣️🗣️🗣️*



*INA MASU SON SIYEN DATA AKAN FARASHI ME SAUKI? YAU GA GARABASA TA SAMU💃🏻 DATA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA🥰👌🏻 NUCEEYLUV NA MUKU MARABA DA SIYEN IYA KUDIN KA IYA SHAGALIN KA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️💃🏻*



*500MB - N200*

*1GB - N300*

*2GB - N600*

*3GB - N900*

*5GB - N1500*



*1 month validity*


Call👇🏻 or cht me private👇🏻👇🏻


***


*ANA TURO KUDI TANAN👇🏻*


Via....1445626295 Nusaiba Mustapha Access bank.


*BANA KARBAR KATI PLS👏🏻😁*



*KUNA TURO KUDI ZAKU JI ALERT DIN DATA INSHA ALLAH BABU BATA LKCI🙅🏻‍♀️ KO BANA ONLINE KU KIRA DIRECT A SAKO MAKU DATA😹👌🏻*






*LAST FREE PAGE*




*Wattpad*

@nuceey





By

Nuceeyluv😘





20....




Fuskar sa a hade yace, "wai bada ke nake mgn ba?" Yyi mgnr d Dan karfi. Hakan yasa bilqees ta bude ido a hankali tamkar bada itan yake ba ta fara waige2 tana hade rai kafin ta juyo kansa daya zuba mata ido tana Dan wara idonta kadan tace,


"Wai dani kke mgn ne?"


Ta furta Hakan tana Kara juyawa kamar me neman Wani Abu, Kutt..., Yareema yaseer ji yyi kamar ya make ta Dan haushi Wannan rainin wayon da tayi Masa ba karamin tokare Masa wuya yyi ba, Yana huci tamkar Wani Zaki ya damko hijab dinta data sunkuya Hakan yasa bilqees ta dago a razane tana kallon yadda Duk yanayin sa ya canja gaba1 ta tsorata matuka saidai tayi kokarin danne Hakan tana kwace kanta dakyar Amma ta kasa Hakan yasa tace,


"Dan Allah malam sakar min hijab dina..."


Wani banzan kallo daya watsa mata a take ta hadiye duk Rashin kunyar nata d takeyi Masa tana kauda Kai da Sauri.


"Kina kokarin kure hakuri na ne a kanki?"


Yareema yaseer ya furta Hakan ransa a mugun bace idan akwai Abinda yafi tsana ya biyo bayan raini,


"Duka nawa kike da har Zaki dinga min magana a tsatsaye??? Ni sa'an ki ne?? Ko kuwa Dan kinga Ina kyale ki shine Zaki dinga min Abinda kika ga dama???"


Ya furta Hakan duk cikin bacin rai. Bilqees ta kume ta hade fuska tayi shiru ta tsuke baki ko tari batayi Masa ba bare ta bada hakuri sai ajiyar zuciya kurum da take tana Hararar sa kasa2 kwafa yareema yaseer yyi yana janye hannun sa daga gareta Yana hura iskar bakinsa a hankali bilqees ta dago da niyar yi Masa mgn ta hango mutane dayawa a bayansu sun nufo su kowa dauke da Adda a hannun sa, Wani ta gani zai sarawa yareema yaseer ta Baya ta buga Kara me karfi tana fadin,


"Annur...."


kafin ya Ankara ta fada jikinsa akokarin ta janye shi. Juya bayan nasa yyi d sauri Nan yaga manyan maza ne majiya karfi suka tunkaro su, Hakan ya bashi mmki matuka Toh meye hadinsu da wa'annan mutanen. Bilqees tayi kokarin tashi yareema yaseer ya riketa kam a jikinsa Yana duban mutanen da suka zagaye su fuskar sa a hade yace,


"Suwaye ku? Daga Ina kuke?"


Dariya suka kwashe Masa dashi, Hakan ya batawa yareema yaseer rai, daya daga ciki yace,


"Eh lalle d alama baki ne, ko daga batan hanyar da sukayi ya nuna lalle basusan Inda suka kawo kansu ha."


Bilqees ta dago da kanta tana kallon yareema yaseer daya dawo da hankalin sa kanta jikinta na rawa Tace,


"Mun saki hanya tun farko banan ya kamata mu biyo ba"


"What???"


Yareema yaseer ya furta Hakan yana zaro ido. Bilqees ta gyada Kai da sauri tace,


"Ni Wlh bansan inane Nan muka biyo ba Kuma d farko yamin kama da Wani Kogi da ake hayewa Saida muka karaso na fahimci mun saba lamba...."


"Amma meyasa tun farko baki fada min ba?"


Yareema yaseer ya furta Hakan yana Kara dagowa yaga mutanen zagaye dasu Suna babbaka dariya. Bilqees ta turo baki kamar wacce zatayi kuka Tace,


"Toh ba fushi kke dani ba?"


Hmmm...! Yareema yaseer ya saki a jiyar zuciya yana janye idanuwan sa daga gareta a hankali.


"Kai saki Wannan yarinyar ku matso Nan wajen inason ganin gwiwar ku a kasa."


Harara mekyau yareema yaseer ya watsa Masa Hakan yasa sauran suka hayyako Suna me zaro bindigar dake boye a wandon su suka nuna yareema yaseer da ita. Ba karamin mmki ne ya kama yareema yaseer ba ya fahimci tabbas bindiga ce a hannun mutanen Nan, Kuma idan yyi gardama babu Abinda zai Hana su harbe su Dan yaga alamun Hakan. Hakan yasa ya dage hannayen sa sama.


Bilqees ta dubeshi da sauri tana kada Kai tace,


"Annur meyasa ka saddakar da wuri haka?"


"Ke rufe Mana baki kafin na dagargaza kanki yanzun Nan."


Ba shiri bilqees taja bakinta ta tsuke yyinda yareema yaseer ya cije lips a hankali Yana zube gwiwowin sa a kasa bayan umarnin da ogan ya basu. Bilqees na ganin haka itama ta duka kamar yadda tayi daidai gefen sa ta zube nata gwiwowin tana zubar da hawaye cikin rada-rada tace,


"meyasa zaka saduda da wuri haka? Ina karfin ka yake? Ina jarumtar ka take? Meyasa zaka bari wa'annan kananun mutanen suci nasara a kanka????"


Bilqees ta furta Hakan tana fashewa da kuka, a Hankali yareema yaseer ya lumshe ido Yana cije lips da karfi.


Ji sukayi a. hankado wasu mutanen wajen su sai koke-koke suke Hakan yasa yareema yaseer ya bude ido da sauri idon Nan Harya kada sbd tsananin bacin rai, bilqees itama ta juya d sauri Nan taga maza da mata ne yara da tsoffi aka kawo kusan goma Suna koke-koke.



"Ku hadesu waje guda anjima motar zata iso mu wuce dasu dajin KARE KUKAN KA."


Wata irin muguwar faduwar gaba ce ta dira a dukkanin zuciyoyin mutanen wajen, kama daga bilqees, yareema yaseer, hatta da sauran Wanda aka kawo daga Baya duk Saida zuciyoyin su ta tsinke tashin hankali karara ya bayyana akan fuskokin su, except yareema yaseer daya dake tamkar Wanda zuciyar sa Bata tainke ba daga can ciki....


Sai a yanzu yareema yaseer ya fahimci bangaren d yake ciki a Nigeria, sai yanzu ya gano cewar ba karamin nisa yyi da mahaifar sa ba wato Adamawa...lalle tafiyar ba Karamin nisa ne da ita ba...,


Suna Nan zaune gabansu saiga wata katuwar mota me shiga gonakin Nan ta cakke a gabansu buuuu... Kkeji take na cikin motar suka fito fuskar su duk a daure da kyalle hannayen su rike da manyan bindigu Suna matsowa Inda suke. Alhafis babandi shine shugaban tafiyar tasu Yana isowa wajen ya dubi Wanda suka tsare su yareema yaseer daya dukar da kansa kasa Yana tunanin mafita.


"Assalamu Alaikum..."


Ya furta Hakan yana daga hannu.


"Ameen wa'alaykas salam"


Suka Amsa Masa ya karaso wajen nasu Yana karewa su yareema yaseer kallo. Har lkcn yareema yaseer be dago ba kansa a duke.


"Iya Wannan kuka Samu yau??"


Ya furta Hakan yana dagowa a fusace. Cike da girmamawa sukace iya Abinda muka samu kenan Amma akwai wasu jiragen da suka koma ko za'a samu Karin wasu. Mtwssss mutumin yaja tsaki Yana kallon yaran dake biye dashi yace,


"Ku kaisu mota."


Bilqees ta rarrafo da sauri tana dafa cinyar yareema yaseer da be dago ba a hankali take girgiza shi tace,


"kasan kuwa Inda za'a kaimu? Ka taba jin dajin kare kukan ka? Kasan me Hakan ke nufi kuwa? Meyasa wai har yanzu baka iya cewa komai bane?"


"Waye wancan??"


Ogan ya furta Hakan lkcn daya juyo yaga

Bilqees ta dafa shi. A tsanake yareema yaseer ya dago fuskar Nan a tamke.


Tsura Masa ido alhafi yyi yana tunanin kamar ya taba sanin fuskar a Wani waje Amma ya manta. Dauke kansa yyi d sauri Wanda ya tmby din yace,


"Tsuntsu ne daga Sama gasasshe dazun Nan suka bullo ta waccar hanyar d alama batan Kai sukayi mu kuwa mun samu banza muka kame su."


"Aikin ku na kyau."


Alhafis ya furta Hakan yana bubbuga bayan mutumin a hankali kafin ya juya a nutse yace,


"Ku turo mana su a mota."


"An gama oga."


Mutanen suka furta Hakan Suna karewa Yareema kallo.


"Oya muje ku shiga mota"


Aka bawa su yareema umarni, sauran suka mike jiki na rawa yyinda yareema yaseer yyi tsaye kikam hannayen sa a kirjin ko motsawa beyi ba saima kallon bayan mutumin kawai da yake.


"Kai kurma ne da bazaka bisu muje ba?"


Ya furta Hakan yana Kai hannu jikin bilqees zai tura ta, yareema yaseer ya janye ta da sauri zuwa jikinsa hade da banko Masa harara.



"Bur* ub*n can kayyasa Wannan fa shege ne"


Ya furta Hakan zai Kai masa duka yareema yaseer ya dauke shi da Mari, take ya rike fuska d sauri sauran suka dago bindigar su oga Alhafis ya dawo baya a nutse yana kallon yareema yaseer dake binsu da mugun kallo, fuskar sa a hade yace,


"ko ka bimu mu tafi, ko kuwa mu harbe ka anan wajen."


Jiki na rawa bilqees tace,


"kuyi hakuri zamu Biku, Wallahi zamu Biku kada ku kashe mu."


Kallon ta yyi da sauri bilqees ta gyada Masa Kai alamar ya amince janye idonsa yyi d sauri rai bace Yana kallon mutumin yace,


"Idan naki saika kashe ni? Kai kayi ni? Ko Kai kke d raina? Jibeka babban mutum kamar gske Amma a zahiri kare ma ya fika Daraja sbd baka dauki rayukan bayin Allah a bakin komai ba. Toh bari kuji...."


Ya furta hakan yana kallon su daya bayan daya yace....


"Babu Dan iskan daya Isa ya dauke mu daga Nan wajen idan kuwa kuka kuskura kuka Tako koda Inda nake ne sai kun rainawa Aya zakin ta...."


Mgnr karshe ce ta makale a makogwaron sa lkcn daya ji bilqees ta kankame bayan sa hade da kiran sunan sa d karfi, sai kuma karar bullet d yaji ya fita.


A firgice yareema yaseer ya juya bayansa Nan yaji bilqees tayi kasa a sume...zaro ido yyi a gigice Yana dukawa kasan bakin sa na furta sunan ta a rikice sai yaga ko motsi batayi...


Bilqees ta tare Harbin da akaso yiwa yareema yaseer, ta saka rayuwar ta a hatsari domin ta ceci tasa rayuwar, ta lura da Harbin ne tun bayan da yake ta jaraba ogan yyiwa na bayan signal ya harbeshi sai akan idonta basu san ta gansu ba, ta matsa d sauri zata ture shi batare data sanar dashi ba sai kuma aka samu akasi bullet din ya sameta....


"BILQEES..."


Ya furta Hakan a karo na biyar Yana jijjigata hankalin sa a mugun tashe..., Dagowa yyi yana kallon su a hargitse kafin yyi mgn tuni suka harbeshi a damtsen hannun sa,


"oucchhh..."


yareema yaseer ya saki karar azaba Yana kama hannun nasa sai kuma yyi saurin taro bilqees dake shirin faduwa daga rikon d yyi mata, kafin yyi aune tuni sun sake Harbin sa a kirji Hakan yasa yareema yaseer ya zube a wajen cike da tsananin azaba Yana faduwa kasa sumamme.


"Ku zuba su a mota."


Ogan ya furta masu haka Yana hararar yareema yaseer ya kada Kai yyi gaba. Hakan kuwa akayi, batare da yareema yaseer yasan Inda kansa yake ba sbd suman da yyi haka zalika bilqees dake ta zubar da jini tun dazu suka kwashe su suka watsa cikin mota ba tausayi bare Imani.


A take mejan motar ya kwasa a guje Yana ratsaaa cikin dazuka da kwazazzabo. Sunyi tafiya me Nisan gaske kafin suka isa asalin sansanin nasu.



Mutane ne dayawa himili-himili zango-zango a Wannan sansani yara da manya, mata da maza, tsoho da tsohuwa ke Wannan waje wasu Suna can Fili Ana horas dasu dabarun yaki, wasu Kuma Suna wasu aiyukan daban.



Bilqees da yareema yaseer basu dawo cikin hayyacin su ba Saida suka kwana biyu a kwance Ana musu mgni. Yareema yaseer ne ya fara farkawa a firgice bakin sa dauke d salati Yana neman bilqees saiya ganshi a cikin Wani daki me duhun gske Hakan ya sashi fara mgn d sauri yana lalumen kofa yace,


"Inane Nan? A Ina nake waii?? Su waye suka kulleni anan?"


Ya furta Hakan cikin fushi. Bude kofar akayi Nan yaga gari tarwaii haske ko Ina mutumin daya bude kofar yace,


"Fito."


Hararar sa yareema yaseer yyi yana damko wuyan sa d sauri yace,


"Ina yarinyar da kuka kawo mu tare??"


Dakyar na bakin kofar ya kwace kansa Yana haki yace,


"Ni bansan Abinda kke mgn akai ba."


Yareema yaseer zai sake mgn yaga an hankado bilqees ta fado ta Inda yake d azama ya Karasa fitowa daga dakin duhun Nan Yana tarar bilqees d sauri kafin ta fadi kasa sannan ya dubi me turo ta din sai yaga Wannan mutumin ne me rawani da dogon gemu tsaye a kansu sai kuma daya daga cikin yaran da suka fara kamasu a bayan sa. Fuskar su a murtuke, yareema yaseer shima ya daure fuska Tamau aka shiga kallon-kallo.


"Kai da alama taurin Kai zaka nunawa kungiya ko?"


Mutumin ya furta Hakan yana sake daure fuska. Yareema yaseer shima ya sake Bata rai sosai yace,


"Ni nace maka Ina cikin kungiya???"


Mutumin yace,


"Ko kace, ko baka ce ba toh dolen ka kana cikin kungiya tunda ka fado Wannan sansanin."


Juyawa yareema yaseer yyi yana karewa sansanin kallo sai yanzu ya lura da yadda mutane zango-zango ke shawagi a wajen, wasu na koyon fada da kuma koyon harbi wasu Kuma sai zagaye suke da manayan AK47 a jikinsu Suna safa da Marwa. kafin ya juyo da kansa wajen su yaga shi suke kallo, ransa a hade yace,


"Sbd ubana ne Kai shiyasa zanyi Abinda kace?"


Na bayan ne ya gwale ido d mmki, kafin ya dubi ogan nasu daya hade fuska sosai yace,


"ba shakka so kke nasa ayiwa yarinyar Nan dake gaban ka fyade anan wajen yanzun Nan.."


A razane yareema yaseer ya dubi bilqees da take lumshe ido a hankali, sai yaga har yanzu tangadi take gabansa ne ya fadi Yana dubansu d sauri yace,


"Me kukayi mata?? Nace me kukayi mata??"


Gani yyi Sunsa Masa dariya Suna kallon junan su. Jikin yareema na rawa yaja bilqees cikin dakin da niyyar dage mata zani ya duba sai kuma yaga dakin duhu yyi yawa bazai iya ganin komai ba, tsananin bugin kirjinsa ne ya tsananta ya fito a harzuqe Yana damko wuyan dayan me dariyar har yanzu yace,


"Ko ka gayamin me kayiwa yarinyar na ko kuwa Wallahi na murde kanka."


Tari mutumin ya fara yi dakyar Yana haki ogan dake tsaye a wajen ya damko hannun bilqees Yana kallon yareema yaseer yace,


"Sake shi"


yareema yaseer hankalin sa ya rabu gida biyu, bacin rai ne karara ya sake bayyana akan fuskar sa sbd rikon hannun bilqees din d yyi Dan haka ya saki mutumin Yana dawowa kan bilqees ogan ya maida ta bayan sa Yana daga bindiga, dayan ma bindigar ya daga...suka sa yareema yaseer a tsakiya.



Cikin kakkausar murya Alhafis Yace,


"Nan wajen ba wajen wasa muke kawo mutane ba, idan baka San inane Nan ba toh ka sani Wannan shine dajin KARE KUKAN KA, Dajin da tunda ka riga ka shigo ba zaka taba barinsa ba saidai mutuwar ka, domin ka dawo cikin Ahalin Wannan daji, yanzu baka da izinin yin komai batare da umarnin mu ba idan kuwa ka musanta Hakan Toh Abu daya ne zuwa uku zai faru.


Kodai ka amince da cewar lalle ka zama Dan kungiyar dajin kare kukan ka, ko Kuma nasa a yiwa yarinyar Nan fyade a gabanka tun tana numfashi harta mutu kafin a sauka a kanta. Daga karshe kaima nasa a kashe ka, kisa mafi Muni da wulakanci kamar yadda zansa ayi mata fyade harta mutu.


Dan haka yanzu zabi ya ragewa me shiga rijiya.


Tsananin firgici da tashin hankali ne sosai ya bayyana akan fuskar yareema yaseer karara...duk dauriyar sa na son dannewa Saida Hakan ya nuna a fuskar sa, bawai mutuwar yake tsoro ba, a'a Abinda za'a yiwa bilqees din shi yafi komai daga Masa hankali da jefa shi shiga rudani, toh Amma a dayan bangaren idan ya amince da shiga kungiya Hakan na nufin yyi bankwana na har abada kenan da MASARAUTAR MANARAS??? Iyaye fa ba abin wasa bane, ummin sa, abban sa, sister suhaima and d rest.....Toh koda yyi taurin Kai ma kashe shi zasuyi bayan sun gama tozarata bilqees a gabansa, tozarci mafi Muni da wulakanci idan kuwa hakan ta kasance har gaban abadan bazai taba yafewa kansa ba Never.... wannan shi hausawa ke cewa TSAKA ME WUYA.......





*LALLE KAM WANNAN SHINE TSAKA ME WUYA...*



*KO YA YAREEMA YASEER ZAIYI?*


*ZAI AMINCE NE YA HAKURA DA MASARAUTAR MANARAS KO KUWA ZAI CECI BILQEES DAGA HANNUN WANNAN AZZALUMAN? WANDA HAKAN NA NUFIN ZAMAN SU NA DUNDUN KENAN A DAJIN KARE KUKAN KA??*




*INA BURIN SA YAKE? NA SON GANO MANYA-MANYAN JIGA-JIGAN MUNAFUKAN DA SUKA SAMU DAMAR FITO DASHI DAGA MASARAUTA??? WANDA HAR YANZU YA RASA GANO TA YADDA AKAYI YA SAMU MANCEWAR TUNANI? WATO MANTAUU*



*TAYA ZAI TAIMAKAWA BILQEES TAYI KARATU DAGA KARSHE YA SAKETA KOWA YA KAMA GABANSA🤔*


*TOH WAI MA INA LABARIN MASARAUTAR MANARAS???, SHIN YAREEMA YAZEED DA KWARKWARA SA'ADIYYA BURINSU YA CIKA NA HAYEWA KARAGAR MULKI NE?*




*TSAKANIN MAMA SARAUNIYA DA HAJIA MAIRO MEYA JAWO HADDASA TAKUN SAKA A TSAKANIN SU??*





ABUBUWAN FAH DA YAWA WALLAHI😄 TARIN TAMBAYOYI DA AMSOSHIN SU NA CAN A CIGABAN LITTAFIN SARAUTA TAH CE. HAKAN BAZAI SAMU BA SAI MUN BIYA 300 DINMU DUMIN KASANCEWA A CIKIN 'YAN PAID GROUP💃🏻💃🏻💃🏻


*MUN GAMA FREE PAGES, MESON CI GABAN YA BIYA 300 A SASHI A PAID GROUP*




*TUNI AKA FARA BIYAN KUDI FAH🗣️, MAZA KUYI SAURI KADA AYI BA KU🗣️🗣️🗣️ 300 kacal👌🏻 ta Wannan account din 1445626295 Nusaiba Mustapha Access bank, ko katin MTN ***. Saina jiku masoyan kwarai🥰.*