15&16
_*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_
📃Littafi na 1
By🪶
*Ummu maher(Miss green)🍏*
*GAWURTATTU 5*
-----------------------
*Wattpad user name*
***
-------------------------
*Arewa book user name*
https://arewabooks.com/u/rabiattu0444
----------------------
masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi.
*Sirrinmu*
mata mu kasance masu tsafta,ladabi,biyayya,haƙuri,juriya.domin shi namiji ba ta ƙarfi ake samunsa ta lallami da lumana.Allah yasa mu dace amin.
----------------------------------
15⬜16
. . . .Ina ƙwance duk abin duniya ya isheni tun jiya Yaya Bilal ya i'so gidan amman tsoron fita na ke don bana son abinda zai janyo mana tashin hankali dashi don matuƙar yazo to fa tabbas sai an ɗebi ƴan kallo,shi yasa ma na rufawa kaina asiri na yi zamana a ɗakin,ina jin tafiyar mama ta taho na yi saurin lulluɓa da bargon don bana son ta aikeni gun kaka don yau ita ce da girki.
"Khairat!Khairat!! Mama ta fara tashi na, na buɗe idanuwa na gaisheta sannan ta ce"kalli garin mana rana ta fito sosai amman kina cikin ɗaki kina bacci?yanxu Khairat kin lalace da bacci wallahi da tun kafin in tashi zaki shiga kitchen ki girkamin abinci?amman yanzu sai na tashi da kaina na yi sannan kuma ki ƙi tashi da wuri?ni dai gidan miji na ke jiye miki don wannan salon da ki ka ɗauka ba mai ɓullewa ba ne?yanzu ki tashi ki kaiwa kaka abinci don ya zama ready".tana faɗar hakan ta fita nasan halin mama ba ta san jira don haka na tashi da sauri na shiga ba yi na yi brush sannan na wanke fuskata,daman na yi sallah tun asuba gabana yana ta faɗuwa don bana son na haɗu da Yaya B,don nasan ko ban kulasa ba dole ne na yi laifi,don idan na gaishesa ma ba ya amsawa ko kallon inuwa ta bayayi,ni na rasa wannan wacce irin tsana ce haka?.
ina fitowa farlon na iske Amira ƙanwar su iman tana homework,da murmushinta ta juyo ta ce"la Anty daman ke na ke jira ki tashi wallahi".murmushi na yi mata sannan na ce"to little sis me kuma ya faru?".shagwaɓe fuska ta yi sannan ta ce"assignment aka bani kuma wallahi na kasa yi guda 3,ne na yi ɗaya sauran ban iya ba,kuma na bawa su Anty iman sunce wai baza su iya ba aikin na da wahala"?.
"To Meeraty bari dai yanzu in kaiwa Kaka abinci in dawo sai in yi miki kinji?"da to ta amsamin ni kuma na wuce don kai aiken kaka.inason Amira don kaf cikin ƴan uwanta ta fita zakka ita kaɗai ce take sona acikinsu sauran duk sunbi layin iyayensu mata.
Tun daga ne sa na ke jiyo ƙamshin turarensa gabana yana ta faɗuwa na tsaya cak sai da na karanta addu'ar tsoron mutune sannan na yi hanyar.
Ƙamewa na yi kawai ina kallonsa yadda ya haɗu cikin wata farar jallabiya farar fatarsa sai shining take kamar ta mata,sak balarabe haka ya fito,shima tun daga nesa ya hango ta yaga ta kafesa da idanuwa azuciyarsa ya ce kai wannan yarinyar kamar mayya take wallahi ƙwata ƙwata ba tada kamun kai irin na mata,shi fa arayuwara na fi son mace mai kamun kai,tun ba yau ba yasan Khairat na sonshi irin son nan na ƙarshe,shi kuma tun daga ranar yaji ya yi wani irin muguwar tsanarta wadda ko ganinta ya yi sai yaji gabansa yana faɗuwa ainun,ga ta wata mummuna da ita don kaf gidan kamar ita Aka ɗorawa muni.
Har ya wuce ta kusa dani ban daina kallonsa ba,ya yi tsaki ya wuce shima sashen kaka ɗin ya shiga,cikin faɗuwar gaba nabi bayansa muka shiga atare.
Kaka tana sharar ɗakinta ta ce"kai!"cikin tsawa duk sai da muka tsorata ta ce"duk ku tsaya anan shara na ke ko mijina yasan idan ina shara tsayawa ake har sai na gama don bana son ju shigarmin da datti".
"to in koma kenan ko?"ya ce wa Hajiya kaka kawai sai na ji ta ce"kai soja ni na i'sa in ce ka koma?jiya ma fa haka ka aikomin da abin arziƙi lodi lodi,yauma ka ga kayan shayin da ka lodomin shi na haɗa da safen nan nasha abina,kafin a kawomin makararren abincin da aka saba kawomin".ta kalli abincin hannuna ta yi wani gyatsine.
Shiga ɗakin ya yi ni kuma naja na tsaya har ta gama sharar ta sai kuwa ta ce"to dogariya ke ko kunya ma baki ji ba?ina ta aiki ko ki taya ni?kema kin fara ɗakko hali irin na su Nadiya ko?to kuwa wallahi wahala zakisha,agidan miji don ni har na fara tausayin jikokina da aka haɗasu dasu Nadiya don babu abinda suka iya sai rashin arziƙi".
ni dai bance mata ƙala ba na wuce zuwa ɗakin cikin nutsuwa na ajje abincin sannan na gaisheta,na wuce ɗakinta don na tuno duk ranar asabar ni ke mata gyaran kayan cikun sif ɗinta.
Ina jin kaka bayan tafiya ta ce"Allah sarki Abin cikin ƙwai yarinya kirki yanzu haka fa gyaran ɗakin za ta yimin abinda kaf jikokina basa yin hakan,Allah ya baki miji nagari yarinya ga haƙuri ga kunya".ta faɗi haka tana buɗe abincin dana kawo mata.
Azuciyarsa ya ce lallai bakisan yarinya mai kunya ba abinda idan taga maza kamar za ta cinyeshi take,ita wannan maitar ta ta ma har tafi tasu Nadiya ma.yana cikin wannsn tunanin yaji kaka ta fashe da kuka ta ce"ikon Allah yau kuma abincin inyamurai akayi agidan,ka duba fa ka gani Bilal?wai ruwan shayine da wannan soyayyiyar ayabar,ayabar da tunda na ke ban taɓa cinta ba ko da na yi zaman cikin yare,shine ni za'a kawomin ni wallahi bazan ci ba".ta faɗi hakan tana ajje abincin a gefe.
Rarrashin kaka ya dingayi har ta ɗan ɗauki plaintain ɗin ta fara yaga kamar kashi,abinda aka kawo mata cikin flask sai ga kaka ta kusa handumeta ta ce"ikon Allah ɗannan ashe dai daɗine da wannan abar?shiyasa ka takuramin naci gaskiya tana da daɗi,ita ba doya ba ita ba dankaki ba gata nan dai.
Ana cikin haka na fito na ce"Kaka na gyara miki ɗakin ni zan tafi zanje islamiyya ne,ko aƙwai abinda ki ke so"?.murmushi ta yi sannan ta ce"wallahi ga ɗakin nan sai ƙamshi ya ke Allah dai ya yi albarka ya baki miji nagari abin son kowa".da Amin na amsa mata na ɗan daure na ce wa Yaya Bilal"sai anjima".ko kallona bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa yana dariya,kaka ta kula da hakan sai dai bata yimai faɗa ina nan ba sai da na fita ta ce"haba Bilal wai me yasa ka kewa yarinyar nan haka ne?ina fa lura da kai ko gaishe ka ta yi baka amsawa me yasa haka ne?".
Ɗago kansa ya yi sannan ya ce"kai kaka ni fa idan damuna zaki yo sai in fita?kawai daga shigowarta sai ta haɗamu".?ganin irin mirmisisin da ya yi da idanuwa bata ƙara ce masa komai ba suka cigaba da hirarsu kaka na ɗarsa wani abu azuciyarta.
Ina fitowa na samu wani ɗan lungu na fashe da kuka mai ƙarfin gaske,na yi mai i'sa ta sannan na juya xan tafi sai muka ci karo da yaya Aliyu da Yaya Mukhtar.da mamaki suke kallona sannan suka haɗa bakinsu wajen ce wa"a'ah little sis me kuma ya sameki haka?me ya faru agidan?".saurin goge fuska ta na yi to me zance musu?ce musu zanyi inason yaya Bilal shi kuma yana wulaƙanta ni ko me?no ai abin da kunya.
Ganin bance komai ba suka sakani agaba wai sai na gaya musu abinda ya faru?bakina yana rawa na ce"kukan rabuwa ta na ke yi da Rashida".na faɗi hakan cikin shagwaɓa.dariya sukayi dukansu musamman yaya Aliyu ya ce"to ikon Allah kukan kuma tun yanzu?ai haƙuri zakuyo dukanku don ku daman rayuwar mace ƙanƙanuwa ce daga gidan iyayenta sai gidan miji,don haka ki share hawayenki kinji?"da to na bisu sannan na wuce.
Yaya Mukhtar ya ce"bro ni fa na samu mata agidannan Tun khairat bata kai haka ba na ke matuƙar sonta har yanzu,amman na rasa ta inda zan faɗa mata".?dariya yaya Aliyu ya yi sannan ya ce"bro me gaskiya kada ka yi sakaci kamar yadda na yi akan Rashida ka gabatar mata da kanka ka ga kawai sai a haɗa bikinmu asha biki".ya faɗi hakan yana kallon mukhtar wanda shima shi ya ke kalla.
***
Har na isa sashenmu jikina duk a sanyaye ya ke,ban kula da mutanen da ke farlon ba na yi wuce wa ta sai kuwa naji anty Hamdala ƴar Mama wato uwargidan su maman mu wacce take aure a Abuja ta ce"ikon Allah ita kuma wannan ƴat baƙar yaushe ta fara raina mutane har haka?".mata ce"hmm Hamdala ta gaisheki tana ganin kakarta da uwarta sun ɗaure mata gaba agidannan sai wanda taso ta gani da mutunci a gidannan sannan take gani da gashi,ai kinga gwara mutum ya kama kansa kafin kuma a koma dukanka".cikin jin kunyar maman nawwara wato antyna Hamdala na ce"mmn nawwara ina yini?wallahi ban kula da zuwan ki bane amman don Allah ki yi haƙuri".na kama kunnuwa na alamar ban haƙuri,sai kuwa ta ce"ai ke dai kam Khairat kin shiga ukunki da iya haɗa munafunci yanzu da ki ka saka za'ayi wa su Nadiya auren dole me ye ribarki?baki da wata riba sai ta munafunci da iya haɗi,to wallahi ni dai kada ki yadda gulmarki tazo kaina don ba Hajiya kaka ba ko Hajiya wacece agabanta zanyi maganinki ehe don ni ba kunyar wata tsohuwa na ke ji ba,idan su Baba ita ta haifesu to mu ba'ita ce ta haifemu ba".
Sosai na yi mamakin abinda Anty Hamdala ta faɗa na rasa me yasa iyayensu suka koya musu rashin sanin darajar mutane,Daman Hajiya kaka sun saba yi mata rashin kunyarsu da fitsararsu abin yana yimin ciwo don duk zagin da Hajiya kaka ke yi wa mahaifiyata bai saka ko kaɗan na raina ta ba,shiyasa sam bata bari a cuce ni ko kaɗan sai dai idan bata wajen don takan faɗa ce wa wai ni banyo mai sunan na ta ba,don ni ba mutum ce mai faɗa ba,sai ka yi min abu ban taɓa nuna maka ka yi min ba sai dai inyi kuka in share hawayena ko mama ba ta sanin komai idan ba ni ce na gaya mata ba.
Ban sake ce wa komai ba na wuce ɗaki raina babu daɗi,a rasa me yasa ƴan uwana suka tsaneni haka?ko don suna ganin son da Baba ke nuna min ne oho?ko kuma fifita ni ɗin da kaka ke yi ne?don ita Hajiya kaka babu ruwanta ko agaban waye sai ta nuna min ƙaunar nan daga Allah take.
Mama ta sameni aɗakina lokacin na fito wanka na gaisheta ta ce"yauwa Khairat ɗazu yayanki Aliyu yazo ya ce gobe zakije gidansa Khadija babu lafiya ga shi kuma zaiyi tafiya kinga sai ku zauna a atare".?to na ce mata amman ba don raina yazo ba don sam bana son zuwa gidan babban yayan nawa wanda shine babba awajen mama shine ɗan farin ta,abinda yasa bana son zuwa saboda Khadija aƙwaita da shegen son jiki sannan ba tada jan dangin mijinta ajiki,duk da itama ƴar uwarmu ce don auren dangi a ka yi musu Babanta baba faruku Ƙanine awajen babanmu kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke.
Babu yadda na iya washe gari da wuri na haɗa kayana bayan na gama gyara ɗakina harda babban farlonmu duk sai da na gyara sannan na nufi kitchen inda mama take aiki,na samu Nadiya tana cin ayaba sai zubar da ɓawon take,mama kuwa ko kallon ɓangaren Nadiyan bata yi ba,tana ta aikinta na rasa mama wata iriyar macece sam babu ruwanta da wani faɗace faɗa ce rayuwarta so simple ce,babu yadda za ayi inyi wa mahaifiyarsu Nadiya haka don mama bata taɓa bani ƙofar raina wani cikinsu ba,nima ko kallon Nadiyan banyi ba don nasan neman jaraba take na wuce wajen mama,da fara'a na ce"mama aƙwai abinda za'a ƙarasa miki ne?"ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"a'ah na gama komai ɗauki abincin Kaka ki kai mata anjima kuma Boy zai zo ya ɗaukeki"?in dai kaji mama ta ce boy to yaya Aliyu take nufi ɗan farin mama don tana matuƙar ji masa kunya don ko hira sosai basu cika yi ba.
Tsaki naji Nadiya ta yi sannan ta fita,nasan sarai dani da mahaifiyata take amman bance komai ba na girgiza kaina na wuce.
Ina zuwa sashen Hajiya kaka na same ta tana kallon labaran safe a tv ɗinta,da fara'a ta amshi basket ɗin kayan karya kumallon na ta sannan ta ce"ABIN CIKIN ƘWAI Lafiya naga kin rame haka ko wanine ya taƁaki yanzu in saƁa masa".
Girgiza mata kaina na yi kafin in bata amsa naji sallamar Yaya Bilal,a take naji gabana ya yi wani mugun faƊuwa don tsabar tsoronshi da na ke ji,hajiya kaka ta kalleni ta daka min harara don tasan abinda na ke wa tsoron.
hajiya kaka ta ce"ke kuma me ye kika wani firgita kamar kinga wani namijin zaki"?.ɗan dai dai ta nutsuwa ta na yi sannan na ce"babu komai kaka bari inje mama za ta aike ni ne".
Hajiya kaka ta ce"hmm kyaji dashi dai da kin gansa sai ki kama wani rarraba idanuwa kamar mujiya yo sojan har wani abu ne da zaki dinga tsoronsa haka?Ni fa kakanku nasha yi masa kuka akan ya kaini barrek Ɗinsu don a tafi filin daga dani saboda rashin tsorona,yo me aka yi aka yi wani soja".
baiyi niyyar dariya ba amman sao da ya yi ya ce"to ke hajiya idan akaje naushi Ɗaya za'ayi miku ki baje awajen".
ni dai raƁewa na yi a gefe kamar wata munafuka ya buga min wani banzan kallo sannan ya ce"ke tashi ki fita ni sa'anki ne da zaki zauna kina kallon bakina ina magana,comon dalla tashi ki fita Ƙazama kawai me shegen kallo kamar mayya".
*Miss green ce*
*GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE*
1, *MU GANI A ƘASA..🔥*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
_Mrs Bukhari_
5_ *AUREN WATA TARA👩❤️👨*
_Miss Hajo_
Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k
*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇*
Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.
Shaidar biya tanan 👇
***
Masu tura katin MTN👇
***
...........🥚👩❤️👨💥🌎....
*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇
+227 84 50 64 76
*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*