Fajaruddeen

8

by @fadimafayau

Sun ɗan jima suna hira farida duk a takure take daurewa kawai take can tace Yah jikin fa patient ya motsa a rikice yace sannu meke damunku ta ɗan ya mutsa fuska ba komi to shikenan Allah ya ƙara afuwa bari in gudu se munyi waya ta daure tace bazaka shiga ku gaisa da mami ba bari se na kuma zuwa.


  Ta ɓata rai so kake tace na kwace mata ɗa ace kazo bazaka shiga ku gaisa ba gaskiya inbaka shiga ba zamu ɓata a'a to baza'ai haka ba muje tai gaba ya bita abaya ji yake kamar yace tazo su jera sedai yana tsoron kar aljanun masifar ta su motsa ta butse masa.


  Sosai mami taji daɗin ganinsu tare fatan ta Allah yasa Fatahun yayi nasarar shawo kan faridan.


 ************


Shi kuwa Faruk tun daga wannan ranar kullin kome yake duk yadda aiki ya run ca ɓe masa se ya yakice yaje inda Fatiha ke saida awarar ta ya siyo.


  Tun yana siyan ta ɗari biyu yakoma ɗari uku yanzu kullin ta ɗari biyar yake siya duda kuwa ko da wasa baya koda ɗan ɗannawa burin sa kawai ya ɗora idanunsa kan yarinyar duda kuwa magana ko kaɗan bata haɗa in ka ɗauke ta nawa tashi se anjima mungode shima se in Ibrahim me zubawa baya nan.


  Sosai tsarin yarinyar yake birgeshi sana'arta kawai take gashi da wuya kazo gun ka tadda maza da sunan cin awara sedai ta zuba maka ka tafi da ita sa'annan da wuya kazo babu wani ƙaninta ko wanta agurin azaune.


  Tun yana ƙaryata kansa da maganar kamis har ya fara jin tabbas kamis gaskiya ya ke faɗa masa sedai yakasa yadda anya kuwa tayaya kamar shi zuciyarsa zata so wata yarinya yarinyar ma wai me talla a hanya anya kuwa to anman me yasa nake kasa samun sukuni in idanuna basu ganta ba ya tambayi kansa.


  Wayarsa ya ɗauka ya kira kamis bugu biyu ya ɗauka a'a mutumin yadai kira da sassafe haka Faruk yace matsalata dakai gajen haƙuri inkayi shiru baka tambaya bama ai zan faɗa maka to shikenan inajinka.


  Daman maganar yarinyar nan zanma kamis yai saurin cewa me awara faruk yaja tsaki Fatiha sunanta malam kamis yasa dariya lalle an tafi dakai wato har sunanta ka samo tsaki faruk yai ni bansan shiririta wallahi.


  To naji na dena shiririta me kake san faɗan tambayarka zan inajinka pls da gaske san yarinyar nan nake kuwa kamis yasa dariya lallai naka wasa ne wallahi kaga ni ba iskanci nace kamin ba kawai kaban amsa.


  Sorry sir inji kamis ya faɗa cikin dariya kaga in bazaka faɗan amsata ba shike nan cikin sauri kamis yace gaskiya ban sani ba ko santa kake anman ka jira zuwa anjima zan zo kanon se muyi maganar in kuma ban samu zuwan ba zan kuma kiran ka ok se mun haɗu faruk ya kashe wayar gami da miƙewa dan zuwa ya kintsa.


****************


Tafe take cikin nutsuwa tai kyau sosai kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin nishaɗi sanye take da doguwar riga abaya baƙa mai adon duwatsu ja sai mayafin rigar da ta naɗa akanta Faiza kenan ta fito ne zuwa gidansu malam fajar dan duba ƙanwarsa Fatima kuma ƙawarta.


  Kamar ko yaushe da faɗuwar gaba ta ƙarasa cikin gidan da ummansu Fatiman ta fara cin karo a tsakar gida tana wanki har ƙas ta durƙusa ta gaida ta gami da mata ya me jiki da fara'a umman ta amsa ai me jiki ma taji sauƙi ta ma fita ayya.


  Shiru yaɗan ratsa kamin Faiza tace umma kawo wankin in tayaki umma tai murmushi a'a yarnan ki barshi kije ɗakin ƙawar taki ki jirata nasan tana hanya ba nisa taiba a'a gaskiya umma ki kawo in taya ki kinga indai aiki kike san tayani to ga kwanukan nan wanke min farin ciki ya kama faiza tai ɗakin Fatima ta ɗauko zani ta ɗaura saman rigarta ta hau wanke wanke.


  Sama sama suke fira da umman wanda duk dai kan karatune sosai umma kesan yarimya dan akwai hankali tanaiwa Fajaru sha'awarta matsayin mata dan tasan zai ji daɗin aurenta sedai ganin shi baya tunanin haka kuma tana tunanin ko yarinyar nada wanda take so yasa take barin komai cikin ranta.


   Fa'iza na wanke wanken ne Abbansu fajar ya shigo a'a yau su Faiza ne agidan tai murmushi ta gaidashi aiki ake haka ne eh to Allah yayi albarka ta amsa amin umma ta cika da mamaki yadda taga sun gaisa faram faram da Abban su Fajar tai mamaki sosai dan sanin da tai masa tun bayan abinda ya sameshi na biyu ko yaransa bai damu da shiga sabgarsu ba tai mamakin har sunan yarinyar ma yasani.


   Se taji tabbas yarinyar nan ta kuma kwanta mata anman zatai ƙoƙarin tambayarta inta gane bata da wanda take so itakam zata sa fajar ya nemi aurenta in anyi sa'a sun dedai ta itakam zatai farin ciki dan ta gaji da ganinsa ba aure da uzirin da yake bata mara kan gado.


  ******************


Duk yadda farida takai ga ɓoye damuwarta ta gaja duk ta rame hankalim iyayanta duk ya tashi musanman mahaifinta da Allah ya ɗora masa santa.


  Mubasshir ne ya shigo ɗakin nata dan sanar mata da kiran Dad sedai yadda yaganta yasashi ruɗewa yai sauri ƙarasawa jikinta zafi rau alamun zazzaɓi se rawar ɗari take ba shiri yai waje ya faɗawa Dad da gudu Dad ɗin yai ɗakin Faridan hankalinsa ya tashi sosai mubasshir yasa ya kira likita yadda Dad ya tada hankalinsa ko mami bata damu haka ba.


  Koda likita yazo ya dubata ya bata magani a falo yake faɗawa su Dad ai jininta ya hau sai malaria kuma hankalin Dad ya tashi da jin yarinya kamar Faridan sanace jininta ne yahau itakam meke damunta.


 Abakin gadonta Dad ya zauna yana shafa kanta tausayinta duk ya cika masa zuciya ji yake kamar yasa kuka gani yake duk lefinsa ne.


  Koda ta farka kan dad ɗinta ta fara ɗora idanunta tausayinsa ya kamata tasan dad ɗinta nasanta taji sauƙi bakamar ɗazu ba nan dad yasata agaba yana tambayarta damuwar me tasa aranta haka tai ta ce masa ita bata sa komi aranta ba seda ya bata abinci taci suka ɗanyi hira kamin ya fice zuwa nasa ɓangaren.


  Yana shiga kukan da yake ɓoyewa ya kwace masa akullin baya jin sukuni in baiyi kukan nan ba sedai yau duda yanayinsa zuciyarsa bata dena masa ɗacin takaici da danasani ba damuwarsa bata ƙara ƙaruwa ba seda yaga farin cikin faridansa ya fara yin ƙaura tun alokacin damuwarsa ta fi ta da sedai tayau tafi ta koyaushe.


  Farida yake gani abaya yaɗanji sanyi sedai baisan kuskurensa ya shafeta.


 Mami ce ta shigo ɗakin danjin Alhaji shiru yadda ta ganshi ya ɗaga mata hankali tasan lokaci lokaci yakan keɓe yayi kuka sedai baya bari ta ganshi sedai fa yau kamar damuwarsa tafi ta kullin.


  Da hanzari ta ƙarasa sedai me makon ya dena kuka kamar yadda ya saba in yaganta sedai yau kamar an tinzirashi.


 Daƙyar ta samu yai shiru haba Dadyn Farida yanzu in farida tazo taganka ahaka yakake jin zata ji dan Allah ka daure ka mance da abinda ya faru dan Allah.


 Haba Bilkisu taya kike gani zan mance bacin nasan yana rubuce a littafina haka ne anman ai Allah gafururrahimu ne anman baya yafe haƙƙin wani kema kinsani hakane anman yasan yadda kayi nadama.


 Ni tsoro na kar abinda nayi ya juya kan yarana ina tsoron ko shike bibiyar Farida bama shi bane Allah ba ya zalunci baya kama wani da lefin wani ka ci gaba da neman yariyar sa su kuma karka kaza wajen musu sadaka tunda....se kuma tai shiru ka tashi kaje kayi wanka ta miƙe zata shiga toilet ɗin.


  Hannunta ya ruƙo ta jiyo yace nagode Bilkisu nagode Allah da besa nayi kuskure biyu ba kuskuren rabuwa da ke alokacin da idona ya rufe nagode da haƙurin da kikai dani ta murmusa karkaji komi har abada ni mesanka ce ya saketa ta shigo toilet ɗinta.


  Tana shiga ta share kwallar da ta tawo mata dan mikin da ya daɗe a zuciyarta takejin kamar ya warke ya taso ji take kamar tasa ihu sedai tanasan kwanciyar hankalin mijinta dole ta shanye damuwarta ta fito tana murmushi oga ruwa ya kammala ya shiga ita kuma tai nata ɗakin.


  Nikam na fito cike da tunanin ko mene suke kokawa akai oho


💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞


  Wajan biyu na rana kamis ya iso kano saida yaci abinci sa'anan suka fara tattauna maganar da suka fara ɗazu a waya.


  Faruk ne ya fara magana da faɗin ple kamis ka faɗan meke damun zuciyata game da Fatiha nakasa na kasa ganewa shin santa nake ko kuwa, dariya sosai kamis yasa cikin fushi fatuk ke faɗin kaga malam bansan iskanci dan kawai na tambayeka bayana nufin na zama shasha ba da zaka tisa ni aga kana faman min dariya.


  Cikin dariya mai ƙular da tai kamis ke magana ai kai ɗin ne dole ama dariya ace kaida zuciyarka bakasam me take ciki ba ina kuma gani da ba'a jiki na take ba.


 Mtsss faruk yaja tsaki gami da miƙewa zai bar ɗakin kamis yai saurin kamo hannunsa haba nawan da wasa nake ai kai kasan hakina sai slow zauna mu tattauna ya fara ƙoƙarin kwace hannunsa kamis ya marairai ce haba nawankayi haƙuri mana kazauna in faɗa maka me na fahinta.


  Fuska a haɗe faruk ya koma ya zauna yayin da kamis ya fara da azahirin gaskiya faruk banajin san yarinyar nan kake faruk ya ɗago cike da fara'a haba koda naji nisan ba san ta nake ba wallahi shiru ya ɗan ratsa kamin faruk ya ɗago ya dubi kamis to anman faɗan meke damuna game da ita da kullin nake san ganinta da san jin muryarta.


  Fakar idon faruk kamis yai yaɗanyi murmushi dan yasan yanayin dariya abu zai zama rigima.


Eh to nima gaskiya bansan meke damun zuciyar ka da ita ba ina ganin kai zaka fi kai zaka fini sani cikin fushi faruk ke faɗin inda na sani ai da bazan kiraka neman shawara ba.


  Kasanme inji kamis duk alamu sun nuna zuciyarka ta kamu da santa cikin fushi faruk ke faɗin Allah ya kiyaye tayaya ma hakan zata yiwu eh shi yasa nace aɗazun nace gaskiya bansan meke damun burnin zuciyar ka ba sabida ita soyayya ba ruwanta da asali masoyi baya kyamar masoyinsa sai dai kai kana kyamar ta tunda bazaka iya cin abin ta ba ni bansan meke damunka ba dole ka yadda bansani ba gaskiya kai zaka zauna ka gano da kanka in yaso sai mu gano mafita ya miƙe zai bar ɗakin.


  Har yakai bakin ƙofa ya dawo kasan me kamar yadda na faɗa ɗazun inajin ajikina kamar kuma yadda alamu ya nuna santa kake sedai ego ɗinka ya hanaka fahinta bai bi ta cewar faruk ba yai ficewarsa yayin da faruk ɗin ya bishi da mugun kallo cike da takaicin cewar da yai wai santa mai awarar nan yake.


*****************


Umman Fajar ce zaune suna hira da mai gidanta cikin dabara ta bijiro masa da abinda ke ranta Abban fatima ta faɗa murya ƙasa ƙasa a nutse ya kalleta na'am umman fajar cikin nutsuwa take faɗin daman maganar Deeni ce nan da nan ya sauya fuska kardai kice wannan zsncen zaki kuma min bashi bane saidai zai iya shafar sa to indai bashi bane inajinki.


  Eh to daman gani nake yaron nan ya girma ya kusa talatin da biyu ka duba ka gani duk suna da yara shine nake ganin ko zaka sa baki ya daure yayi aure ina ganin zaifi jin Maganarka tinda ni bai ɗauki maganata da mahimmanci ba.


Cikin fushi da faɗa yake faɗin ba nace miki ki dena sani cikin harkar yaran nan ba inyaga zai yi aure yayi in ma bazaiba ni babu ruwa na ya miƙe zai fice.


 To shikenan naji zanyi iyayi na har ya yadda yayi auren kasan baida inda zai zauna ka bashi izini koda iya ɗakinsa na yanzu ne se ya zauna kafin Allah ya hore masa inma kinaso ni sai in dawo ɗakinki ya haɗa da nawa ɗakin kawai asani ciki ne bana so yai waje tai saurin cewa dan Allah ka dawo mu ƙarasa wallahi bazan saka ka ciki ba.


  Dawowa yai ya zauna ita kuma ta ɗora da daman na yanke wata shawara ne nasan baida wata budurwa shine nake neman shawarar ka kan inasan ya auri yarin yar nan ɗalibarsa fauziyya matsayin ka na uba nakesan ji daga gareka inka amimce.


  Indai yarinyar ta amince ai ba komai nima na yaba da tarbiyyar ta shikenan tace eh ya tashi ya fice yai ɗakin sa ransa a tunkushe shikadai yasan meke damunsa alwala yai yayi nafila gami da roƙon Allah inda alkairi a abinda da Salima kesan haɗawa Allah ya tabbatar.


  ******************


Duk yadda faruk yakai ga daurewa zuciyarsa kan bazai kuma zuwa gurin yarinyar nan mai awara ba sai dai hakan yaci tura kusan kullin sai yaje yake samun sukuni sai ya dawo takaici da haushin kansa duk ya cika masa rai.


 Yau kusan kwana uku kenan yana zaryar zuwa gurin saidai babu ita babu dalilinta hankalinsa duk ya kasa kwanciya.


  Sannu a hankali ya yardarma zuciyar sa tabbas tabbas ta kamu da san yarinyar nan so mai tsanani sai dai rashin ganin ta gurin sana'ar ta shi yafi komai ɗaga masa hankali gashi ko ƴan matasan da ke zama gurin baya ganinsu bare ya tambayesu.


  Kamis ya kira awaya kuka riris yake masa wai yai gamo sosai kamis yai dariya wallahi faruk kanada matsala na rasa yaushe zaka girma wataran in ina ma kallon gentle kawi se ka dawo sha..... Yai saurin rufe bakinsa dan yasan halin faruk da fushi ya sauya maganar da faɗin dan baka ganin ta ai ba yana nufin kayi gamo bane malam kaje area ɗin ka tambayi address ɗin gidansu cike da farin ciki sukai sallama faruk ya kashe wayar.


💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞