Fajaruddeen

11

by @fadimafayau

Kamar yadda kamis ya tsara masa kuwa haka yai yau ya shirya cikin shigarsa ta mutunci kai tsaye unguwar su fatiha yai sai dai baiyi sa'ar samun mahaifin nata ba hakan yasa ya nemi ko zai samu number ɗin sa kasantuwar babu kowa gida sai umma batai wani tunani ba ta rubuta number ta baiwa yaron da aka aiko shi kuwa ya kaiwa faruk.


Faruk ya amsa gami da baiwa yaron hamsim yaja motarsa inda yaron ya tafi yana murna.


Seda yaje office sannan ya kira bugu ƙaɗan aka ɗaga cikin girmamawa faruk yake masa magana kai kace yana ganinsa daman naje gida ne baka nan shine nace bari in kira inji yaushe zaka zo inasan yin magana da kai daga ɓan garen baban yace yanzu ma ina hanya anman inajin kamar yau zan koma in zaka iya se mu haɗu a gidan nawa ok Inji faruk yana kashe wayar ya fice nan ya bada Sallallahu ga sakataren sa kan kowa yazo ace ya jira inba sauri yake ba.


I lai kuwa yana zuwa ya tadda har yazo dan yana ƙoƙarin shiga da mashin ɗinsa ya isa nan yace ya jira ya shige.


A nitse gami da girmamawa Faruk ke masa bayanin abinda ya kawoshi yayin da shi kuma yai shiru yana jinsa saida ya gama yace eh to naji zan cenka sai dai yarinyar ce ban shirya yi mata aure ba Faruk yai saurin kallonsa kafin yace eh ai yanzu izini zaka ban in dinga zuwa kafin mu fahinci juna nasan insha Allahu ka shirya lokacin.


Bawai auren ne bazan mata yanzu ba azahiri kai ɗin ne bazan bawa ba a tsorace faruk yace cikin rawar murya yake faɗin dan Allah baba bai bari ya ƙarasa ba yace karka damu baka da wani aibu in zaka iya auren ƙanwarta zan baka ko yau kake so sai a ɗaura anman Baba me yasa bazaka ban fatihan ba sabida ina tausayinka banasan abinda ya samen ya sameka baku dace ba ba irin ka nake san ta aura ba inka shirya ka amince zan baka ƙanwarta indai har da gaske santa kake inaganin jininta ma zai zama abin sanka yai shigewarsa gida.


Faruk ya dafe kansa cike da tausayin Fatihansa wannan wace irin masifa ce ace abinda ake faɗe a masu yadda harda mahaifinta ya jima a mota kamin ya iya jan motarsa ya bar unguwar.


************


Soyayyar Fa'iza da Fajar tai nisa dan har manya sun shiga duda kuwa koda wasa mahaifinsa bai taɓa maganar auren ba balle yaji yana neman aure bare kuma yasa baki abin na damunsa sai dai alƙawarin da yaima mahaifiyarsa kan bazai kuma maganar da ta shafi mahaifinsu da rashin kulawar sa gare su yasa yabar damuwar sa a zuciyar sa.


Umman fajar da kanta taje ta samu yayanta kan ya nemawa fajar ɗin aure sai dai fafur yace shi bazai jeba daƙyar ta shawo kansa ya amince dan cewa yai shi ya gaji yaro da ubansa anman sai dai dangin uwa suyi masa tace yayi haƙiri ai yasan dalilim da yasa ita kuma bata san ta taso da abinda ya wuce musan man da ya kasance Abban fajar ɗin baida cikakkiyar lafiya tuna hakan yasa kawu bukar ya yadda suka je shida ƙaninsa da amininsa.


Karɓa sosai ta mutumci suka samu aka musu daga ɓangaren su Fa'izan hakan yasa sukaji daɗi dan tabbas sun san tabbas fajar yayi sa'ar surikai.


Ba wani lokaci mai nisa akasa ba wata huɗu e shima dan fajar ɗin bai gama shiryawa ba dan inta mahaifin Fa'iza wata ɗaya tal za'a sa dan tun lokacin da Fajarudden ya sameshi kan ya bashi izinin zuwa zance yasa ya fara shirin sa dan yasan yaron da gaske yake yadda yasan nutsuwar yaron.


Umman fajar ce zaune da Abban fajar suna hira ya miƙo mata leda ta amsa kuɗi ta gani a ciki na mene ta tambaya rabi ki bawa fajar ya rage wani abin rabi kuyi hidimar abincin biki tace anman baka ganin ka bashi da kanka zaifi jin daɗi.


Cikin faɗa yake magana ba nace ki dena sani cikin maganar yaran nan ba bazan bayar da kannawa ba yanzu ma na baki ne ki bashi matsayim ke ko wani cikin danginki ya bashi ko kaɗan banasan yasan ni na bayar shiru kawai tai ranta na mata suya itakam ta gaji kawai dan tai alƙawarin bazata ƙara kulashi suyi faɗa kan yaran nan bane da wallahi yau kam ba abinda zai hanata magana.


Tunda aka fara batun bikin Fa'iza farin ciki yabar bashir duk yabi ya rame ji yake tamkar yafi kowa rashin sa'a arayuwa ko abinci ma se an masa dole yake ci duk umman sa tabi ta damu ta tada hankalin ta ganin yadda tilon ɗanta namiji ya koma.


Ada farin ciki take ganin yarimyar ta samu miji dan batasan alaƙarta da ɗanta anman yanzu duk hanyar da zata bi na hana auren tabi anman mahaifin Fa'iza yaƙi yace ina bazai zama ƙaramin mutum ba.


Hakan yasa tsanar yarinyar ta ƙaru aranta dan gani take asiri suka masa yasota suka kuma bata wani dan su lahanta mata yaro.


Kwanci tashi ba wuya ankai kayan lefe yau sauran kwana goma cif ɗaurin auren Fajarudden da amaryarsa faiza inda za'a ɗaura a masallacin tsohuwar jami'ar Bayero.


Tuni ɓangaren biyu suka kammala rabon kati inda ta ɓangaren fajar ya rasa ta inda zai faɗawa fatiha auren kusan kullin sai sun haɗu sai dai ya rasa me yasa yakejin kamar in ya faɗa mata zata iya jan baya baya dashi ya rasa me yasa yake tsoron hakan.


Sannu a hankali yanayin fatiha da tunaninta ya fara sauyawa kan fajar kan ta ankara ta tsunduma tsundum cikin kogin soyayyarsa.


Tun tana gaza yadda da tunaninta da zuciyarta harta amimta da tabbas sansa take aranar da ta tabbatar sansa take tai kuka sosai dan tasan tai kuskure babba ta ina zata kamu da san wani bacin da tasan ita wace ta ina zata karya alƙawarin kanta na soyayyar wani sai dai kashi ta manta da shaƙuwa kan haifar da ƙauna bama so ba tasan tai kuskuren shaƙuwa da fajar da har ɗa bi'unsa suka jata tai gangancin kamuwa da sansa


Fajar ne zaune suna hira da abokinsa muktar sai tsokanar sa yake ango ansha ƙamshi fajar na dariya dan har ga Allah har cikin ransa yake jin daɗin maganar .


  Ya dubi muktar yace pls in tambayeka mana muktar yace inajinka wai kuwa mutum zai iya san mace biyu a lokaci guda muktar yai dariya sabida abune mai yiwuwa shi yasa Allah ya halatta mana mu aure mace huɗu inji muktar hakane fa fajar ya faɗa me yasa ka tambaya inji muktar.


  Murmushi yai yace bari kawai a twitter nagani nake ta kokwanto wasu sunce eh wasu a'a muktar ya ce ah abune me yuyuwa mana fajar yace aransa ai na yadda tunda nima misali ne zuciya ta tanasan mace biyu alokaci guda muktar yace what ashe a fili yake magana yai saurin cewa share kawai ganin muktar ya takura masa yasashi shigewa gida.


  Yau ta ƙara tabbatarwa kansa tabbas san fatiha yake soma me tsafta dan bayajin yanama Faiza rabin san da yakewa fatiha yanzu ya gano me yasa yake tsoron kar alaƙarsu ta ja baya ya saba da ita sosai uwa uba tausayinta da ya mamaye ilahirin zuciyar sa.


  Yau ya yanke shawarar faɗa mata ɗaurin aurensa duda kuwa duda kuwa ba iya hakan yake san faɗa mata ba sai dai yanajin kamar bazai iya faɗa mata sauran abinda ya kunsa a kasan ransa ba.


  Zaune take tana duba takardun soil science best course ɗinta dan in ta kai ƙarshen sauran courses shi take kuma ɗauka tahau bita duda kuwa komai na ciki ta jima da haddacewa sai dai yadda take san course ɗin yasa bata gajiya da karanta shi lokaci lokaci takan ɗaga ido ta kalli hanya ko zata hango malam.


  Ta baya ya biyo hakan yasa ko kaɗan bata ganshi ba sallamarsa yasata ɗagowa tana murmushi ta gaidashi cike da fara'a ya amsa shima yana murmushi gami da kallon hannunta a'a ana duba aminin ne tai murmushi dan shi da kansa ya gane handout ɗin sabida yadda ta sarƙeta to Allah yatemaka tace amin.


  Ajiyewa tai suka hau hira sun jima suna hira wanda duk na karatu ne kafin ya miƙe bari in wuce inada uziri yau inaga ma bazamu samu tafiya tare ba zan tafi gida da wuri ok tace ya miƙa mata IV ta karɓa badai bikin Fatima bane dan duk tasan yan gidansu abaki yanzu yai murmushi ki karanta dai.


  Ta jima tana kallon IV ɗin sai dai ta kasa ɗagowa dan tana jin kamar inta ɗagowa hawaye zasu iya wanke mata fuska su bata kunya daurewa tai ta ɗago alokacin da zuciyarta tace mata ta ɗago kawai itafa jaruma ce ta iya shanye abubuwa da dama ma bare ɗan wannan abin murmushi take tana faɗin gaskiya malam baka kyautamin ba shine sai yanzu zaka faɗan duk dan kar inbada gudunmawa.


  Yai murmushi yanzu ma ai bance bance karki bada ba abubuwa ne sukazo a gaggauce shi yasa da yawa ma ban sanar dasu ba tai murmushi Allah yasa albarka yace amin yai motar sa yana barin gurin hawayen da take boyewa ya zubo tai saurin gogesu dan bata buƙatar su a cikin makaranta.


  Ya jima a motarsa kafin ya fito ya dawo inda take ta tsurawa takardar hannunta ido kai kace tana fahintar me ke ciki sai dai a zahiri babu abinda take gane wa har ya zauna bata san ya zo ba saida ya ɗan taɓo ta tai saurin kallon sa.


  Ganin shine yasa tace lah malam ka dawo yai murmushi eh malam ɗin nan dai yaƙi barin bakin ki ko nace bana so anƙi denawa tai murmushi ayi haƙuri malam yai murmushi ai shikenan inda gabaki ɗaya sukai shiru.


  Fatiha ya faɗa a sanyaye ta ɗago ta dubeshi idansa na kanta karo na farko da ya taɓa cika mata ido har taji bazata iya jurar kallon da yake mata ba tai saurin ƙasa dakai pls in roƙeki alfarma tai saurin kallonsa inda ta kuma yin ƙasa dakai tana faɗin baka buƙatar alfarma agurina kawai ka ban umarni yaɗan murmusa sabida jin daɗin zancenta.


  Zaki iya aurena tai murmushi ba wannan zancen so kake antina Fa'iza taji wannan wasan naka tai zaton gaske ne inji sanmaci yai murmushi ba wasa nake ba Fatiha I mean my words I really love u wallahi banjin inasan Faiza yadda nake sanki duda bazan ɓoye miki ba itama inasanta tai sororo tana kallonsa.


  Ya ci gaba will you marry me pls say yes karki ce no kunnuwa na basa san jinsu dan Allah kice yes tsintar bakinta tai da cewa yes ya kamo hannunta cikin farin ciki do u really mean it tai murmushi I always mean my words nasan haka ya faɗa.


 Ta kwace hannunta gami da cewa zan iya cewa zan soka sai dai ko nace zan aureka kasan ba abune me yiwuwa ba gobe ne ɗaurin auren ka an u are proposing to someone else taya kake jin zuciyata zata yadda sona kake da gaske indai kana sona ke yasa baka nemi aurena ba kabar waccan.


  Yai shiru yana kallon ta ko kuwa kana nufin ita ka aure ta ni kuma kawai soyayya kake san muyi ko kuwa yaudarata kake sanyi yai saurin riƙo hannunta yana girgiza kai wallahi ba haka bane i really want be ur husband ita umarnin mahaifiyata ce duda kuwa yanzu inasanta sannan ada nai zaton kawai tsaɓar tausayinki ke ɗawainiya dani sai dai daga baya na fahinci ba haka bane lokacin kuma an gama batun auren mu da ita.


  Ki yadda dani pls wait for me ki ban lokaci wata daya wata biyu ta faɗa ya girgiza kai No just 2 years by then insha Allah kina level 4 ni kuma na gama gini na pls kice eh u will wait pls karki ce no tai shiru kawai tana kallon sa inda na rasa shirun mene na taso nai gaba😂


Kwace hannunta tai gami da cewa naji I will wait but pls karka kuma riƙen hannu inba haka ba zanyi tunanin wani abu daban bata jira cewarsa ba tabar gurin ya bita da kallo duda can cikin ransa yanajin zuciyar sa ta gaza yadda da zata jirashi ɗin 


  Tana barin gurin tai animal science department student toilet ta faɗa tana shiga tasa kuka ko kaɗan batasan ya akai ta amsa masa ba taya ma za'ai ta amsa masa ai koda ba sauran kwana uku ɗaurin aurensa ba tasan tai kuskuren amsa tasan duk sanda yake iƙirarin mata wanda batama da tabbacin sa tasan da yaji me ake cewa akanta bazai aureta ba.


  Ita kuwa Farida ɗan zuwan da take game da project ɗinta yasa suka saba da malam dan yanzu har hira suna ɗanyi har ta WhatsApp ma wani zubin sukan gaisa ɗan zaman tai dashi ta fahinci rabin yadda suka fahince shi ba haka yake ba mutunne me barkwanci da faran faran anan ta fahinci kallon da yake mata wato shi kallon mutum me jiji dakai da ji da gata yake mata dan har tsokanar ta yake yar gatan dadyn ta ko kaɗam batajin daɗin hakan sedai ba yadda ta ita dashi.


   Yau taje office ɗin sa ita kaɗai ce tai sa'a bai koreta ba dan duda sun saba in yaso rashin mutuncinsa sai yace sai taje ta zo dawani .


  Sun gaisa cike da mutunci da girmama juna harda ɗan tsokanar ta wai yar gidan dady yau shugowar ɗaya aka mana tai dariya kawai yace ki ajiye file ɗin inna duba zan kiraki ki amsa inada uzuri tace ok sir ta miƙe zata fice har takai bakin ƙofa yace yar gidan dady tai saurin dawowa aranta tana cewa bafa nasan yar gidan dadin nan sai dai ta kasa faɗe a zahiri.


  Iv ya miƙo mata gashi ina gayyatarku keda su Asma'u in ba'a samu zuwa ba asamana albarka ta amsa tana karantawa aranta jitai ƙafafunta sun gaza ɗaukarta tai saurin durƙushewa a gurin yai saurin tasowa yana kiran sunanta hawaye kebin fuskarta lafiya yake faɗe tai saurin miƙewa tabar office ɗin ya bita da kallon mamaki.


  Motar ta ta shige tahau kuka ashe duk yadda takejin kamar ta cireshi aranta ba haka bane wannan wace irin masifa ce ashe ɗan ganinsa da take shike ɗebe mata kewa har takejin kamar ta dene sansan.


  *********


Duk yadda faruk yakai ga san ya haƙura abun yaci tura dom ji yake kamar kullun ƙara sanya mata sansa ake aransa.


 Saidai duk yadda zaiyi yayi kan ita fatihan ta fahince shi yayi anman taƙi dan gani yake kamar inta yadda mahaifin nata zai iya yadda ya aura masa ita dan duk sanda ya samu mahaifin nata maganar guda ce shine in bazai auri Asiya ƙanwar Fatihan ba karya kuma samunsa.


****** 


A kace komai lokaci ne in yayi babu jira sai anyi yau take jajuberin ɗaurim auren Fajarudden da Faiza murna gurin ango da amarya ba'a magana tsayawa faɗi bata lokaci ne.


 Duk su biyun ji suke kamar su janyo gobe tazo dan zumuɗi musanman amarya dan shi ango wani ɓarin na zuciyar sa yana hango masa fatihansa gami da tsoron rasata.


  Yayin da aɗaya ɓangaren Fatiha ta fawwalawa Allah ta rungumi rayuwar ta dan ta kasa yadda da maganar malam tafi yadda da kawai cewa soki burutsunsa ne.


  Inda ita kuwa farida tama kasa kuka tunda ta baro makaranta kwana uku kacal tabi ta rame abinci ma ba ita ci take ba inda wani abu da aka kira da takaici yazo ya tsaya mata a wuya inda yaƙi gaba yaƙi baya komai taci ɗaci yake mata inda duniyar duk ta mata duhu.


********


Yau takw ɗaurin auren Fajar da Amaryarsa Faiza tun da wuri ango ya tashi kasantuwar baya gidansu agidan su muktar ya kwana dan gidansu ya cika da yan uwan ummansa sunata girke girke wanka ya shiga koda muktar ya tashi ya hau tsokanar sa wai ya cika zunuɗi ace tun bakwai har mutum yai wanka abinda sai goma yace anji ɗin ya hau sanya ɗan maɓallin rigar da zai sa dan jiya sai goman dare ma ya karɓo gurin tela bai kuma sa masa ba.


 Tara agurin da zasu taru ta masa shida abokansa sukai ta tsokanar sa daga nan sukai tsohuwar jami'ar bayaro dan anan ne zava ɗaura auren dan waliyyai ma tuni sunyi gaba abinsu.

  

 Kamar yadda aka tsara goma da yan mintuna aka ɗaura auren Fajarudden da Fa'iza kasantuwar ango da abokansa suna harabar masallacin ta waje inda waliyya ke ciki suna jiyo yadda abin ke gudana ta lasifiƙa aiko ana ɗaurawa abokan ango suka hau tsokanar sa kaga angon Faiza bada kanka asare yana faman washe baki.


  Tun bayan shigar kawun Fa'iza masallaci wayarsa ke ƙugi sai dai kasantuwar shine waliyyin amarya yasa bai ɗaga ba seda aka ɗaura auren ana ɗaurawa ya fito dan ganin me kiran mamaki ne ya kamashi ganin kiran mahaifin Fa'iza to kiran mene haka bacin yasan da cewa shi ya wakilta ai yasan iyanzu yana fama da jama'a.


 Kafin yai shawarar kira ko rashin kira wani kiran ya shigo ya ɗaga daga ɗaya ɓangaren cikin faɗa mahaifin Fa'iza ke faɗin haba yaya tun ɗazu ina kiranka kaƙi ɗagawa tsaki kawun yaja yace aikasan me nake eh yaya sanin hakan yasa na kira kasan haka kawai ai bazan kira a wannan lokacin ba.


 Naji menene dalilin kiran yaya dan Allah kar'a ɗaura auren nan yaya dan Allah kamar yaya kar'a ɗaura tun ɗazu fa aka ɗaura muna hanya mota ce ta samu matsala da tuni munzo nace maka fa an ɗaura tun ɗazu yaya a warware ai babu dama sai dai saki cikin sauri yace yah dan Allah kasa ya saketa sabida me yah nidai kasa awarware ina nan zuwa ya kashe wayar yabar wan nasa cike da tunani.


Towo wata sabuwa saki ko me yasa ko fajar zaiyi sakin.


Ya kuke gani?