HAYATUN NAUM

Episode 2

by @aishat1149

🍇HAYATUN NAUM🍇


EPISODE2️⃣


Daga alqalamin🖊️

Queen Eeshert


***


Bismillahirrahmanirrahim


Gaba daya a tsorace take zuciyarta nata dukan uku- uku abinda duk take fargaba shi ke shirin faruwa, "baiwar Allah ke muke saurare" cewar fulani.


Dagowa tayi ta dubi Fulani sannan kuma ta dubi jakadiya saita sake yin k'asa da kanta, Fulani ta dubi jakadiya tayi mata alamu da ido alamar cewar me hakan yake nufi? Jakadiya tayi saurin fad'in " ki gafarceni ranki shi d'ade na mance ban sanar dake ba nifa wannan baiwar Allah tunda ta bak'unci wannan masarautar ko sau d'aya banji ta furta wata kalma ba saidai duk abinda na fad'a mata zata tashi ta aikata shi ba tare da ta amsa ba wani sa'ilin kuwa saidai kawai tayi murmushi" Fulani ta sake duban jakadiya cikin rashin fahimta tace " kamar yaya?kina nufin kurma ce kenan?".


Jakadiya tace "a gaskiya ranki ya dad'e abinda nake zargi kenan" Fulani ta numfasa ta d'ora da cewa "lallai hakan zai iya zama gaskiya don nima na kula da hakan amma kuma alamu sun Nuna cewar kamar tanaji mayarwar ne bata iyawa" "wannan gaskiya ne" cewar jakadiya.


Fulani tace " baiwar Allah ko kin iya rubutu na sanya a kawo miki takarda da alkalami ki rubuta mana sunan naki? Da sauri ta dago ta girgiza kai alamar A'a "OK tashi kije" cewar gimbiya.


Da hanzari ta mike tayi waje tana sauke sansanyar ajiyar zuciya, azuciyarta taci gaba da yiwa Allah godiya da ya fitar da ita a wannan karon, domin kuwa ya zama dole ta nemi wata mafitar, don bazata dawwama da k'in yin magana ba matuk'ar tana cikin wannan masarautar, don haka wajibi ta nemi wani labarin k'anzon kuregen da zata bayar a matsayin tarihinta, don ta zauna lafiya domin kuwa bayarda ainihin sahihin tahirin rayuwarta reshe yana iya juyewa da mujiya domin kuwa hakan na iya haifar mata da tsana da tsangwama watak'il ma ayi waje da ita daga cikin masarautar ko kuma ma garin baki daya.


Haka Fadeelah taci gaba da kasancewa acikin wannan masarautar ta sarki abdurrashid tana zaune cikin farin ciki da kulawa daidai gwargwado sakamakon kyakkyawar kulawar da take samu daga jakadiya da wadansu daga cikin hadimanta kana uwa uba uwargida fulani tana nuna mata so matuka kasancewar Fulani mace ce mai son mutane ga kirki da halin mutuntaka, faran faran da jama'a kwata kwata babu inda tabaro halin mai gidanta wato mai martaba sarki Abdurrashid, sarki mai cikakken iko da mulki,da nagarta, ga nagartattun halaye nagari ababen koyi.


Inda Fulani ta bambanta da abokiyar zamanta kenan wato wato gimbiya zainaba (Amaryar mai martaba sarki abdurrashid) inda ita kuma gimbiya zainaba ta kasance mace mai mummunar izza da tink'aho, girman kai, wulakanci,raini da kallon talaka ba a bakin komai ba.


Sannan wani abinda zai baka mamaki da lamarinta shine itafa gimbiya zainaba ba jinin sarauta bace, uwar gida Fulani wacce asalin sunanta Aysha itace 'diyar sarkin wani birni da ake kira da birnin zarewa dake kudancin k'asar, sarki( lukmanu bini sa'ad) Wanda ya kasance amini ga mahaifin sarki abdurrashid wato (sarki usumanu bin mas'ud)Wanda ya kasance abisa karagar mulkin wannan birni na garga a wancan zamanin.


Akwai zumunci da shak'uwa mai k'arfi a tsakanin wad'annan sarakuna guda biyu wannan shine ya zamo musabbabin shakuwa a tsakanin iyalansu inda kusan duk lokaci bayan lokaci suna ziyartar junansu, inda aka sami fahimtar juna da soyayya tsakanin tilon 'yar sarkin zarewa (sarki lukumanu bini sa'ad) me suna gimbiya Aysha wato( Fulani kenan) da d'a ga sarki (usumanu bini mas'ud) wato mai martaba kenan sarki abdurrashid bini usmanu Wanda yake kan karagar mulkin birnin garga a wannan zamanin.


Inda ita kuma gimbiya zainaba ta kasance d'iyace a gurin wani amintaccen hadimin sarki lukmanu mahaifi ga fulani a wancan lokacin, hakan ne ya baiwa itama gimbiya zainaba damar kasancewa a matsayin babbbar hadimar Fulani kuma ta hannun damanta tun zamanin 'yammatancin su, kusan sa'o'in junane domin kuwa Fulani bata baiwa zainaba shekaru sama da daya a haihuwa ba.

Bayan anyi bikin gimbiya aysha wato (Fulani kenan) tareda sarki Abdurrashid Bini usmanu Fulani da kanta ta rok'i alfarma gun mahaifinta domin ya barta ta taho tareda amintacciyar hadimarta zainaba zuwa birnin garga inda tayi aure, sarki lukumanu ya amince ya bata zainaba suka taho tare taci gaba da hidimtawa uwar gijiyarta, ita kuma Fulani taci gaba da kyautatawa zainaba kamar yadda suka saba.


Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah gimbiya aysha wato (Fulani ) ta shekara biyar cif a masarautar garga daidai wannan lokacinne ta sami juna biyu, aikuwa murna a gurin wad'annan ahalin guda biyu abin fa har ba'a cewa komai, nan fa mutuncin Fulani da darajarta ta k'ara d'aukaka da hauhawa a idanun mijinta da iyayenshi, kulawar da suke bata ta nunku ninkin baninkin musamman a gurin mahaifiyar abdurrashid wato gimbiya sa'adiyya wacce suke kira da (inna wuro) mace mai dattako da mutunci.


Wanda wannan tagomashi da fulani ta samu shine abinda ya soma d'arsa wutar kishi da k'iyayyarta a zuciyar babbar hadimarta wato wato gimbiya zainaba. 


Hmmn!! Wato hausawa sunyi gaskiya da suke cewa( d'an Adam kayan Allah ana d'auke da kai kana d'auke da halinka)

Ku ci gaba da biyoni labari yanzu aka fara shi da yardar Allah.


Like:

Comment:

Share:


Written by🖊️

Queen Eeshert

***

Join the link👇👇

***